Skip to content
Part 11 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Aunty ta fito daga matattakalar bene inda dakin barcin ta yake zuwa daki na rike da ‘yan mukullan motar ta “Siyama na fita, zani Wuse Market kayan cefanen mu sun kare, da dai-dai kike da na nemi rakiyar ki, to duk kin bi kin susuta kan ki akan da namiji, kin susuta min Abban ki babu gaira babu sabar na kasa gane kan sa. Ga nan Nadia ki kula da ita kafin na dawo.”

Ta fada tana miko min ‘yar autar mu Nadia, babu kiwa ba komai yarinyar ta taho zuwa gare ni tana bangale baki, ta bani jakar jegonta mai dauke da abincin ta na frisco cream da kayan canjawa da su pampers din ta.

“Sai kin dawo Anti, in kin ga radio please ki sayo min, latestone”.

“Radio kuma? Yaushe kika koyi sauraron radio naga dai da bata dame ki ba?”

“Ina neman abinda zai ke debe min kewa ne ya hana ni tunanin auren dolen da ake son yi min.”

Aunty ta gyada kai kamar kadangaruwa ta sa kai ta fita tana mamaki. Ita bata ga aibun Omar ba, yaro saurayi matashi jazur da shi kamar sai ka wanke hannu kafin ka taba, ga tsafta ga addini, a irin shakuwa ta da shi bata taba zaton haka zata faru ba in aka fara maganar auren mu.  Duk da na dade ina cewa ai Yaya na ne.

Zata so kwarai ta ga wannan dream man din na Siyama, ta ga shin me ya taka har haka da ya narkar da zuciyar Boddo-Siyamah a murya da mafarki kadai? Ta san dai ba fin Omar kyau yayi ba yaro kamar Balaraben kasar Kuwait. Kuruciya ce kawai take damun Siyama ta ke neman kai ta ta baro, to wanda ya ki bin maganar mahaifin sa ai kuwa ya kai kan sa ya baro.

Anti da ta tashi dawowa ta sawomin Radio mai quality kirar LG wadda babu inda bata kamowa gida da waje. Na yi mata godiya mai yawa sosai. Na ji kamar ma na hadu da shi na gama. Tamkar ta cikin radiyon nan zai bullo ya cimmani, ya wanke tsatsar kaunar sa da soyayyar sa da ke zuciyata.

Tun daga ranar na yi mata saitin kamo tasoshin ko’ina, na dukufa sauraren tasoshin radio daban – daban na gida Najeriya, da ban kara jin  muryar dana ke nema ba sai na karkata ga sauraren International Media masu magana da Harshen Hausa, nice kullum BBC ke har ma da VOA dana fi karfafa zaton a can naji shi, kuma ita ce major din Abba, da wuya ka ji yana  sauraron wata tasha ba VOA ba, amma abun kamar delusion na samu a waccan ranar. Don kuwa ban kara jin waccan muryar ba ko mai kamar ta, ko sunan da ya ambaci kan sa da shi wanda na yi ta kokarin in tuna na kasa, sai a mafarki na kuma.

Ni dai na tabbata na ji ta real a Radiyon Abba, saidai ban samu naji ko daga wace tasha bane, in na yi kamar in tambayeshi “Abba kwanaki wace tashar rediyo ka kunna ranar dana fadi dinnan ake maganar hantsi? Sai kuma in kwabi kaina da cewa zasu manna min hauka, zasu maida ni Psychiatry da zama, Abba likitan ilmi ne wadanda duk wani kankanin mental abnormality ba wuya zasu dangana shi da asibiti.

Tunda an ce mai nema yana tare da samu, to zan ci gaba da nema da saurare har Allah yasa in kara jin sunan sa da muryar sa, ko da bazan gan shi a zahiri ba.

An jarrabce ni da babbar jarrabawa mai girma a kan sa, wani iftila’i ne ya same ni wanda ban taba jin mai irin sa ba, na san ba zan fadi wannan jarrabawar a banza ba, yana can yana jira na ko ba dade ko bajima shima.

To amma shin Siyama Abba (Dr. Mamman Gembu)”, ya cancanci ya saka kara ki tsallaka a kan wani mutumin da baki da tabbacin a duniya yake? Ya cancanci butulcin da kike shirin yi masa na bada masa kasa a ido akan tsohon burin sa?

Amsa ce mai nauyi da bana son baiwa kaina amsar ta. Shi kan sa Ya Faruq wani jigo ne a rayuwata da baya bukatar sai an tuna mini girman matsayin sa a gareni. Amma a fannin aure zuciyata bata zabi kasancewar sa abokin rayuwata ba. Sai kuma aka yi rashin sa’a ni mai sakarwa zuciya linzamin kanta ce.

Idan a baya ina tababar wanzuwar sa da kasancewar sa dan Adam, to daga ranar da na ji muryar nan tasa a Radiyon Abba, ya fadi sunan sa da nasabar sa na tabbata Dream Husband dina is a Human Being… he’s somewhere far away from me, but he’s in existence a tashi duniyar wadda nemo ta a yanzu shine babban kalubalen da ke a gabana.

Wato nemo wanda zuciya da ruhi na suka afu a kan sa…. nemo shi ya zame min wajibi don shine kadai cikon farin ciki na, zan nemo shi a duk inda yake against all odds, sai na shiga rayuwar sa nima kamar yadda ya shigo tawa ya hana ta sukuni tun ban san so ba, sai na nemo shi da yardar Ubangijin da ya daura min son sa da kaunar sa…

Na rantse ba zai yiwu in sha wannan wahalar ni kadai ba, we must share the FEELINGS and all these emotions together… ina fatan har sai nasa ya fi nawa, insha Allahu.

Ina da kyakkyawan hope (fata) da yaqinin (tabbacin) watarana Abba zai sauko har ya sa min albarka, idan ya dauki ‘ya’yan mu a hannun sa, idan ya gan shi a zahiri zai karbe shi matsayin surukin sa. Zai yaba da zabi na. My dear Abba is not that harsh anymore (Abba na bashi da wannan tsananin), na fara zargin wannan ba Abba na bane wani ne dai mai tsananin kama da shi.

Shi kam Ya Omar ina masa addu’a da fatan zai samu mata wadda ta fini son sa, wadda ta fi ni komai tun daga asali, nasaba, arziki da kyawun halitta. These are my wishes for him. Bai yi min komai ba sai alkhairi wanda yawun baki yayi kadan ya bayyana shi, zan saka masa alkhairin sa gare ni ta hanyoyi da dama musamman addu’a, amma ba ta hanyar aure ba, zai kasance cikin kowacce addu’ar sallahr farillah ta, har sai ranar da na daina numfashi.

Domin hakika Ya Umar ya kaunace ni da kauna ta musamman wadda karfin ta da tasirin ta ya zarta ta ‘yan uwantakar da ke tsakanin mu. Wanda hakan ne yasa bazan iya rayuwar aure da shi ba. Ba zan aure shi in zo in kware shi ba, in na yi hakan ni kaina ba zan taba yafewa kaina ba. Ya Omar dina, bai cancanci irin wannan auren na rashin so ba.

A cikin wannan yanayin na rashin nutsuwa na zana paper ta ta farko ta waec wadda ta kasance darasin Geography.

An ce Juma’ar da zata yi kyau tun daga Laraba a ke gane ta, wannan jarrabawa da na ke zanawa kam tun daga Talata na gane sai wani ikon Allah zai sa in samu abin kirki. Tamkar an yi wiping duk wani ilmi da experience din dana ke tunanin na samu a Regent tsayin shekaru hudu an maye gurbin su da tunanin sa, babu komai a cikin kaina sai zallar tunanin (how would he look like a zahiri? Yadda yake a mafarki haka yake a fili? Ta yaya zan gane shi ranar da ya bayyana? Ko chimpanzee ne shi sabida muni haka nake son kaya na. A kullum da tunanin hanyar da zan bi wajen kaiwa gare shinake kwana nake tashi. Amma kullum bana samun wata idea in ba ta in dauko Radio in kunna ba in soma lalube daga wannan tasha zuwa waccan, sai ko in duniya zan shiga neman sa ba.

Daga ranar dana bar gida kuma zuwa neman mutumin da ban taba gani a zahiri ba, kuma bani da tabbacin inda zan same shi (neman gaibu) nima kaina bana bukatar a kaini psychiatry zan mika kaina Dawanau ta jihar Kano dana ke jin labari, in basu damar kada su bar ni in fita ko’ina daga nan har illa masha Allahu. Zan tabbatar wa kaina hankali na ya gushe.

Bakon Calabar

Mota  kirar Luxurious irin masu tasowa daga Kudu dinnan ta sauke Ya Omar a daya daga cikin tasoshin motar da suke tsayawa cikin Abuja wato tashar Jabi. Daga nan yayi Bolt zuwa gida. Ya fito sanye cikin kayan NYSC yayi kyau matuka don kudun ta karbe shi sosai, dauke da jakar kayan sa wadda bata cika girma ba.

Mai Bolt din da ya sauke shi ko fita bai yi ba daga harabar gidan mu motar Abba ta shigo, suka yi ido hudu da dan sa Umar.

Abba ya fito da azama ya rungume Umar suka karasa cikin gida yana yi masa barka da zuwa. Daga baya Anti ta fito daga kicin tare da su Maryam-Jamila da Nadia a hannun ta, itama bakin ta ya ki rufo da ganin bakon Calabar, yau watan sa shida rabon sa da gida sai da ya kammala gabadaya tun bayan sunan Nadiya ya tafi.

Faruq Ya karbi Nadiya a hannun Anti yana fadin “yarinya kamar Boddo tana Baby”. Anti tace ai Siyama da kai take kama, Nadiya ko da Abban ku take kama, don dai Siyamar ce a ranka shiyasa ka ga sun yi maka kama”. Dariya yayi, wadda ta fiddo fararen jerarrun hakoransa kamar kankara dasu don haske, yace cikin jin nauyi. “Anti ni tana ina ne? Ban ji motsin ta ba” Anti ta ce ” ka san sun fara WAEC tana can tana zanawa. Yanzu zaka gan ta.”

Bata rufe bakin ta ba nayi sallama a falon, rungume da takardu, sanye cikin uniform din Regent. Na rame sosai na kuma yi duhu. Ya Omar ya bi ni da kallo affectionately yana tambayar Anti dalilin wannan ramar tawa da duhun da ya ga na yi, ina ganin Abba ya harare ni cikin takaici. Anti ta ce cikin son kawar da zancen,

“Ka san jarrabawa take kuma kwana biyu dai bata ji dadi ba.”

Da haka ya bar zancen ba don ya gamsu ba sai don Abba na wurin, bay a son ya zurfafa nuna damuwar sa a kaina a kan idon Abba. A sanyaye na dube shi nace “ban san yau zaka dawo ba Ya Omar ban share dakin ka ba, amma bari in ajiye takardun nan in canza uniform ina zuwa yanzu zan gyara maka” da kulawa yace “na yafe Boddo, jikin ki babu kwari sam, zan share da kaina, da gajiyar jarrabawa zaki ji ko da gyaran daki?”

A yadda yake min magana loving and romantic  tamkar ba Ya Omar din ba yau,kamar ya maida ni cikin sa don so da kulawa, idanun sa na ta karakaina a kaina da duk wani motsi na, sai da yasa Abba da Anti jin kunya sosai suka soma kokarin barin wurin. Na wuce ban ce komai ba, don nima yau na ga sauyuka masu yawa a tare da Omar da suka sanyaya jiki na, shikuma Abba yace da shi da safe yana son ganin sa kafin ya fita ko’ina.

Washegari ni da Anti muka shirya breakfast na musamman sabida dawowar Omar, yana gefen Abba ni ina gefen Anti da Maryam-Jamilah akan cinya ta ina bata dankali Anti kuma tana baiwa Nadiya abincin ta, Abba da Omar suka riga mu kammalawa sai Abba ya dauko mukullin mota ‘Ranault’ sabo dal ya ajiye ma Omar a tafin hannun sa.

“Na cika alkawari kamar yadda ka cika alkawari ka fiddomin ‘first class degree’ Omar, Allah ya sanya albarka.

Ka kammala hidimar kasa lafiya, gashi tuni na bada sunan ka a ECOWAS sabida na kusa yin retiring.”

Abba ya dakata yana duban mu dukkan mu, ganin duk mun nutsu muna sauraron sa sai ya samu karfin guiwar ci gaba. Kafin ya ce da Umar.

“Me ya saura maka yanzu? Ginin gidan ka na Katampe ya kammala, zaka bar gidan nan daga yau, don BQ ya maka kadan, ka koma gidan ka, ka riga ka zama babban mutum yanzu Umar, kafin ta karasa jarrabawar a daura muku aure ta tare.

Na baku daga nan zuwa ta kammala jarrabawa ku fahimci juna ba irin waccan fahimtar ba, fahimta ta zama miji da mata.         

“Siyama!”

Abba ya kira sunana da kakkausar murya kafin in dago in dube shi tuni na fara kakkarwa sabida ban zaci a gaban Ya Omar zai yi zancen nan ba, “har yanzu kina kan bakan ki na iskokai cewa wani kike so ba dan uwan ki ba, ko kuwa kin dawo cikin tunanin ki?”

Ya ilahal alameen ka kawo min agaji, ko daren jiya na sake mafarki da shi ya kara yagalgala zuciyata da nau’ikan soyayyar sa. Bana ji bana kallon kowanne namiji da idanun soyayya sai shi. Kan Omar yana kasa bai iya yayi ko kwakkwaran motsi ba, Abba yace “na kashe wancan maganar taki ko bayan raina kada ki kara tada ita.

Wannan shine mijin da addini yayi min umarni in zaba miki, shi na yarda ya zama uban ‘ya’yan ki. Ina so daga yau in ga irin matsayi na a idanun ki Siyama, in ga kuma shin na isa da ke ko kuwa hoto nake a gare ki ba Uba ba?”

Ya maida duban sa ga Omar yace “Faruqu I trust you beyond words, pls don’t let me down. Su mata ka sani daga karkataccen kashin hakarkari aka halicce su kullum a karkace suke. Kwakwalwar su a baibai take. Sai ana yi ana mikar dasu, sai an yi hakuri ake cin gajiyar su, balle Siyama da har gobe yarinya ce shiyasa ma nake mata uzuri a wasu lokutan irin wanda nake so kaima ka koyi yi mata har komai ya daidaita a tsakanin ku.

Allah yayi muku albarka zan fita, ina so yau ta zamo ranar da zaka fara zuwa zance gun kanwar ka officially.”

<< Sakacin Waye? 10Sakacin Waye? 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.