Skip to content
Part 40 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

The Broken Vow (Karyayyen Alkawari)

“A lokacin da dan Adam ya yi wani kyakkyawan alkawari, ya kuma karya shi cikin ganganci ya cancanci a yi masa uzuri???”. Ita ce tambayar da Mr. Hamzah ya yi wa kan sa, a lokacin da ya daga kwalbar barasa a hannun sa yana tantamar ya sha ko kada ya sha? Sai yake hango fuskar Siyamah tana kallon sa ta na cewa “cika alkawari shine cikar kamala kuma shine cikar dan adam”.

To amma sai wani irin kwadayi ya zo ya rinjaye shi, wani irin kwadayin barasa mai tsananin karfi irin wanda bai taba ji a kafatanin rayuwar sa ba.Ya tabbatarwa kan sa in bai sha ba hadiye kwadayin zai iya kashe shi Siyaman ta rasa bakidaya. Sai ya rufe ido kawai ya soma kwankwada da Wani irin infatuation.

Hamzah ya dade a ‘Bar’ yana zazzagawa cikin sa giyar da ba koyaushe yake zabar ta ba saboda karfin ta, sai lokutan da yake son moderating wani excessive yanayi da yake ciki, misali na farin cikin da ya yi masa yawa ko bakin cikin da ya kasa controlling, wai ita (Desire) maimakon giyar (Trophy) wato ‘brand’ din barasar da yafi son sha ko yaushe.

Har sai da ya ji shi a daidai, yadda ya zaci jin kan sa wato kamar yana a kan gajimare, ta yadda tunanin sa da perception din sa suka bashi cewa excitement din sa na first night din sa da matar sa a bar son sa wato Siyama, ya koma masa daidai, yadda yake jin ba zai cutar da zuciyar sa ba (a tunanin sa).

Amma kuma tana kai masa karo da cewa dadin dandanon ta ya karu, zakin ta da gardin ta duk sun karu, aikin da take masa cikin kwakwalwar sa ya kara kyau har ya fi na baya, kada ya daina shan giya wai don ya musulunta, hakan ba komai bane kuma ba zai zama komai ba, Siyam bazata taba sani ba don bazai bada kafar da zata gane ba. Kuma har kullum dama yana gayawa kan sa ai zunubin giya ba shi da girma kamar na Zina, shikuma Allah ya san baya zina, da sauran manyan zunubai da musulunci yayi hani da su. (A ruwayar Hamzah zunubi akwai babba akwai karami, tunda dai ya amshi musulunci ya kuma auri Siyam shikenan ba zai takurawa kan sa ba).

Haka giyar sa ta yi ta ingiza shi tana fada masa abubuwa na yaudarar kai da zallar kaico a cikin kan sa.  Da wuya Barasa ta bugar da shi duk karfin ta, don mai tsada yake sha kuma jinin sa yana da karfin daukan ta, don haka ne har ya iya driving back home. Amma karerayi da ingiza mai kantun da take ta yi masa a kan addinin da ya san ya karba ne da zuciya daya, har gara ta bugar da shi din, ya bi gefen hanya yana tambele a kan su. Domin gaya masa take addinin kamar akwai takura da wahala.

A daidai sanda Hamzah yake kokarin shigowa gidan sa a motar sa, a lokacin ni ina bisa sallaya na idar da sallahr walha (salatul Dhuha) ina addu’a a kai na da Hamzah, tare da addu’ar Allah ya kawo sanadin shiryawa ta da Abba na ko farin cikin rayuwa ta ya cika, sai na ji dawowar sa wajejen karfe goma na safe.

Haka kawai nake jin babu dadi tun bayan fitar sa. Wata zuciyar na cewa in je in tambaye shi ina yaje haka da sassafen nan ko wanka bai tsaya ya yi ba balle karya kumallo? A lokacin da ya kamata a ce muna cikin bargo guda, muna karasa huta gajiyar jikkunan mu da basu samu hutu ba a tsayin daren jiya bakidaya? Wata zuciyar tace ba hurumin ki bane Siyama sanin inda ya je, da can in zai fita kafin ya san ki gaya miki inda zai je yake yi?

Ban san meyasa ba amma haka nan naji gaba na yana faduwa a kai a kai, tun bayan fitar tasa. Wanda hakan yasa na alaqanta faduwar gaba na da fiyar sa. Ban san meyasa na damu da fitar da yayi din ba. Zuciya ta ta ki nutsuwa wuri daya, tana kuma yi min rade-radin cewa ba alkhairi bane ya fitar da shi a safiyar nan ba.

Yayin da zuciyar soyayya mai tsananin son Hamzah ke cewa in kyautata zato ga miji na abin kauna ta.

Hamzah kai tsaye dakin sa ya nufa wato dakin barcin sa (master bedroom) din gidan gaba daya, wanda ke daura dana Siyama. He’s half intoxicated wato dai rabi a buge yake, duk da karfin jinin sa kuwa, rabi kuma ya san me yake ciki, amma duk da haka wani ikon Allah Siyama na ran sa, duk shirmen da giya ta gama gaya masa bai hana shi son sanin halin da ta wayi gari ba. Bai hana shi tunanin ya boye kan sa kada ta gane a buge yake ba, har zuwa lokacin da zai samu kan sa.

Ya ji yana so ya je ya ga ya ta tashi, amma yana tsoron ta yi noticing tun ba’a je ko’ina ba ya karya dokar musulunci, ya karya alkawarin da ya daukar wa Young Abba da gangan, ya yi abinda zai karya zuciyar ta; ya ci amanar Islam, tunda ya sha giya a washegarin samun Siyama!

Sai ya ji tsoron hada ido da Siyam ya kama shi (ba tsoron mahaliccin sa ba). He felt a sense of guilt overwhelm him, ya ji kamar da ta kalli idon sa zata gane me ya aikata, a yanzu kam yana tantamar idan musuluntar sa kacokam! Dinta ba don Siyama bane.

Sai ya ji zuciyar sa ta karye rugu-rugu, kada dai ace ya lalata imanin da yayi da addinin musulunci tun ba’a je ko’ina ba?

Yayi saurin cewa a’ah, shan giya bai taba imanin sa ba, imanin da ya yi da Allah da Manzon sa da gaske ne har zuciyar sa, shan giya shima daban, dabi’a ne mummuna tunda mai shan ta ba abinda ba zai iya aikatawa ba, amma (for now) bazai iya barin giya ba bai san gaba, yau ya tabbatar da hakan, yayi gaggawar amsawa Young Abba cewa zai bar giya sabida idon sa ya rufe da son samun auren Siyam a lokacin, yanzu kuma ai ya same ta, a nasa dan kankanin sanin, ya san musulmi da yawa da suke shan ta, kuma suke sallah as well. Abinda bai sani ba shine sallahr tasu tana inganta ko a’ah?

Shi ya san dama da wuya ya iya barin wasu abubuwan da ya taso a cikin su da sauki wadanda ya saba dasu a can baya musamman (wine) giya, wadda a ganin sa ba koyaushe yake sha ba. Yana mamakin yadda son Siyam ya kama zuciyar sa har haka, cikin dan kankanin lokaci ya canza rayuwar sa, har yayi gangancin saurin daukarwa Young Abba alkawarin ya bar shan giya, amma dai ai yayi togaciya da kalmar (GRADUALLY). To zai bari, amma gradually din cikin yardar Ubangiji da taimakon sa.

Duk da haka damuwar abinda ya aikata din ta hana shi sukuni a dakin nasa, ya kai gwauro ya kai mari a tsakiyar dakin yana so giyar ta sake shi ya tafi gun Siyama, ya tabbatar ba zai iya wuni cikin dakin sa sur shi kadai yana boye kan sa da buguwar da ya san yayi, alhalin ya san Siyama na cikin gidan ba, cikin halin da ta fi bukatar sa a kusa da ita.

An dauki kusan awanni biyu kafin giyar ta dan soma sakin sa, ya soma dawowa cikin cikakken hayyacin sa. Sai ya soma tuna irin gurbataccen tunanin da giyar da ya sha ta sanya masa dazu, na cewa musuluntar sa ba zai hana shi shan giya ba. Ya yarda da hujjar musulunci na haramta giya saboda abubuwan da take haifarwa. Ya tunawa kan sa cewa yana son Siyama ne sahihin SO, ba don ita ya musulunta ba, sai don ya dade yana yi wa kan sa sha’awar addinin musuluncin, dama Allah ya rubuta zai musulunta, amma ta dalilin auren Siyama.

Allah ne ya yi nufin sai ta shigo cikin rayuwar sa sannan zai bashi ikon shiriya, ya aure ta ne domin su rayu tare, daga nan har karshen rayuwar su, su haifi ‘ya’ya nagari, su yi musu tarbiyyar kwarai ta addinin musulunci.

In haka ne kenan dole ya yi kokarin barin duk wani abu da addinin musulunci ya yi hani da shi komai girman sa ko kankantar sa.

A yanzun kuma da zai je gaban Siyam bayan ya san ya sha wine din,  he must be careful wajen ganin ya aro cikakken hankali ya sakawa kan sa dake reto in ya je gaban Siyama yau, har azahar yana buyar mata, don ba duka giyar ta gama sakin sa ba, tsoro yake kada Siyama ta gane ya ci amanar Muslunci nan da nan haka, eh, ya ci amanar musulunci mana! Tunda an gaya masa tun kafin ya shigo musulmi nagari baya shan ta. Hakanan ta wani fannin ya ci amanar yardar da Siyam ta yi masa, na cewa ya musulunta ne da dukkan zuciyar sa tun ba’aje ko’ina ba ya karyata hakan.

Action din sa na yau haka da wurwuri a kan giya, bayan samun Siyamah ko ya ki ko ya so yana kokarin nuna don ya samu Siyamah ya musulunta. Ya zama rashin godiya ga Ubangiji bias rahmar sa. Tunda a wurin ita Siyam, babu sauran dabi’ar kafurci ko wacce iri a tare da shi yanzu. In haka ne me yasa ya yarda da zigar zuciyar sa kan cewa giya ce kadai zata rage masa farin ciki?

Ya sani ko ba’a gaya masa ba wannan dabi’a ce tasu ta kafirci, cewa giya magani ce ga wani abu da ya addabe su ba dabi’ar cikakken musulmi bace.

Shin farin ciki da excitement din in suka yi wa mutum yawa suna kisa ne? Idan da ya yi hakuri ai zasu wuce ne baza su kashe shi ba.

Sai ya ji zuciyar sa bakidaya ta idasa karye wa. Ba don yana ji a jikin sa wannan ne karo na karshe da zai sha giya ba. Don ji yayi kamar yau ma ya fara son ta, kamar bai taba shan mai dadi da gardi da ta yi cooling mind din sa irin ta yau ba. A hakan ya mike ya nufi toilet din sa yana rangaji cikin mutuwar jiki. Ya sakarwa kansa shower ko ya samu sassauci.

Sai da yayi wanka na sosai, yayi brush ya sake yi yadda ya kamata, hoping kada Siyam ta ji warin giyar nan daga bakin sa, ya canza kayan jikin sa zuwa Pajamas farare sol, sannan ya fesa turaren sa ‘guerlain vetiver’ ya tako zuwa dakin Siyama a hankali (with so much guilt in him), don gani yake kamar ilahirin jikin sa hoton giyar ‘desire’ din da ya sha ne.

Ya yarda ta ci sunan ta ‘desire’, shan ta da yayi a yau ba ‘accidentally’ bane a’ah ‘desire’ ne na zuciya ba kuskure bane, ganganci ne.

Tsabar guilty conscience din da ya lullube shi har gani yake yana bude baki da zummar magana a gaban Siyama zai yi aman giya ne. Ya yarda yadda yake tsoron bacin ran Siyam, ko yin abinda zai sa ta yi fushi ko ta yi Allah wadai da shi ko ta ce zata fasa zama da shi baya tsoron Ubangijin da yayi Imani da shi haka.

Yana shiga dakin ya tadda Siyama cikin Sujjadah, sai ya ji zuciyar sa ta tsinke, gaban sa kuma ya yanke ya fadi sakamakon wani irin kwarjini na hasken Musulunci tasirin sa da izzar sa da Siyama tayi masa, ya rasa takamaimai wane aiki gare shi na kwarai a duniya da Allah ya bashi sa’ar mallakar wannan salihar yarinya ma’abociyar addini.

A can baya ya san yana shirka, duk da a kasan ran sa ya san addinin musulunci shine kadai addinin gaskiya, yana shan giya, yana caca, yana yin abubuwa da yawa da ko addinin sa na Littafin Injila ya yi hani da aikata su.

Abu daya ya san baya yi a rayuwar sa, kuma bai taba yi ba shine ZINA ko neman maza, hakika Allah ya kebance shi daga wannan dattin, sannan a rayuwar sa ba ya munafurci, baya nunkufurci baya giba, ba ya gaba da kowa. He’s a straight forward person a kan komai kuma a kan kowa da wata mu’amala ta hada su. Shi kan sa ya san kan sa a mutum mai fadin gaskiya komai dacin ta koda bazata yi maka dadi ko daidai da ra’a yin ka ba, wadannan sune dabi’un sa na zahiri da badini da ya dade da sani akan karan-kan sa. A yau ya yi wa Allah godiya sau ba adadi da ya bashi Siyama ya tabbata ba don ya cancanta ba, sai don Allah yana son shi da shiriya da rahma ta hanyar ta, da kuma karamci irin na al’ummar musulmi da darajja soyayya iri na wasun su (Young Abba), ya kuma gode wa Allah a karo na biyu da ya bashi addinin musulunci a yanzu, ya tsarkake shi daga shirka da kafurci. Yana rokon Allah giyar ma watarana ya barta bakidaya.

Karo na farko da Hamzah ya samu kan sa yana addu’ar Allah ya sa kada ya sake maimaitawa (shan giya bisa ganganci) idan hakan mai sauki ne a gare shi, idan kuma mai yuwuwa ne Allah ya raba shi da giyar baki daya cikin kankanin lokaci, tun kafin Siyama ta kai ga ganowa.

A cikin ran sa ya roki Allah ya bashi ikon kiyayewa dokokin sa a fili da boye. Duk sabida kwarjinin da Siyam ta yi masa da ya same ta cikin halin sujjadah.

Bai tsaya jiran Siyam ta sallame sallahr ta ba don baya son ta gan shi cikin guilt din da yake ciki, da nadamar da ke shimfide kan kyakkyawar fuskar sa. Sai kawai ya kashe wutar dakin da ta kunna, ya lallaba ya shige cikin duvet din ta, kamar barawon da aka kama dumu-dumu ya dauko kayan sata.

Yana addu’ar Allah yasa baya smell din giyar nan, duk da wanka da brush din musamman da kakkamsan turaren sa na Guerlain Vetiver da ya dauka, domin gusar da kowanne irin smell da ba kamshi ba a tare da shi.

An dauki mintuna kusan ashirin a haka kafin na kammala addu’a ta da salloli na na walha, wadanda duk ina yin su ne a kan Hamzah da nema mana albarkar rayuwa gurin Ubangiji.

Addu’a sosai na yi a kan mu, zaman lafiyar mu da karuwar soyayya a tsakanin mu, na rokawa ‘ya’yan da zamu haifa a gaba shiriya irin ta addinin musulunci. Na roki Allah yasa kada tushe da asalin mahaifin su da (past religion) din sa ya yi (haunting) din su, ko ya yi tasiri ga (upbringing) din su. Na kuma roki Allah ya bani ikon cika buri na na zuwa gaban Abban Abuja, kafin na samu rabon haihuwa a tare da Hamzah.

Dana gama duk abinda zanyi, sai na canza kayan sallah ta zuwa kayan barci, yanzu ne zan yi barci sosai in huta gajiyar jiya yadda ya kamata, dama na tashi ne don in sallaci Dhuha, making sure ban zabi wadanda zasu dauki hankalin sa a kai na ba, sabida a yanzun hutu kawai nake bukata. Na kuma ji sanda ya shigo dakin ya dade a tsaye kafin ya kasha wuta ya kwanta.

Riga da wando ne sakakku kuma masu kauri na saka, daga jiya zuwa yau na fahimci babban abinda ke kidima shi jiki na to gashin kai na ne, da kuma dukiyar nan dake kirji na. Don haka har hijab na kawo na saka a kai kamar mara gaskiya. Wai dai duk don kada Hamzah ya sake tayawa.

<< Sakacin Waye? 39Sakacin Waye? 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×