Yau Litinin, aka ce babbar rana da ko bature yana tsoron ki, na shiga kitchen ina tunanin me zan girka masa kafin ya dawo ofis? Bayan na yanke shawarar sanyaya zuciya ta in maida komai ba komai ba. Kusan duka abincin kabilar Birom na iya shi yanzu, wasu na koya a yanar gizo, wasu a wurin shi kan sa Hamzan, domin sau da dama Apron yake sakawa a lokutan mu na dadi a yawancin weekends din da yake gida mu shiga kitchen tare yayi ta koya min ire-iren girke-girken su.
Ya iya wasu a wajen Kakar sa tun yana karami amma kafin yayi aure baya yi sabida rashin lokaci da rashin zaman gida, sai dai ya je restaurant ya zauna ya ci ko ya taho da shi gida idan ya baro office. A haka ya rayu a can baya.
Na yanke shawarar yi masa faten Acca, tunda lallashin sa nake son yi, kafin ya dawo, na yi faten Acca wanda na wadata shi da ganyen alayyahu da yakuwa sosai, na zuba koda da hanta a ciki wadanda na yanka kanana-kanana. Sannan na yi masa lamurjen Zobo da Abarba da zuma na sanya kananun kankara a ciki.
Hamzah bai shigo gidan ba sai wajen karfe shidda na yamma, haka kawai yau bai biya ‘Bar’ ba yace bari ya bari zuwa dare yanzu yunwa yake ji sosai, wani abu mai kyau cikin tarbiyyar Siyamah ko tana fushi ba ta horon yunwa ga mijin ta, kullum sai ta dafa masa abinci ta aje a dining, bata damuwa da ya ci ko bai ci ba gobe ma sai ta sake yi ta aje. Ya jinjinawa matan Hausawa a kan girki ga mazajen su wadda a ganin sa al’ada ce mai matukar kyau. A nashi al’adar maza sun fi mata yin girki.
Lokacin da ya shigo gidan ina daki na ina wanka a toilet dina, kasancewar da nasa mukullin yake amfani sai ya bude gidan ya shigo, a matukar gajiye ya dawo, rataye da falmaran din Suit din sa a wuyan sa, hannun sa rike da jakar kwamfutar bisa cinya, anan falo ya zauna yana tunanin abubuwan da suka faru daren jiya, zai iya tuna wasu bazai iya tuna wasu ba, kamar dai ya zagi Siyamah cikin maye, Ya Allah! Hamzah ya kama kansa da hannuwa bibbiyu yana jiran ganin ta inda Siyam za ta bullo, don ya kasa shiga dakin ta sabida nadama.
Duk kamshin abincin ta ya cika falon ya cika hancin sa, ya kai duban sa ga dining table nan ya ga na shirya abinci da komai da zai bukata, amma bana wajen. Kuma bai ji motsi na daga daki ba.
A wannan dan tsakanin da suke ciki bakidaya ya rasa abinda ke damun Siyama, gabadaya ta canza masa rana daya, ta aro wasu munanan halaye farat daya ta canza kyawawan halayen ta da su, ya rasa walwalar ta da annurin ta, ya rasa farin cikin ta, ya rasa soyayyar ta kullum sai dacin rai da bakin rai, amma an ce masu shigar juna biyu na samun irin wannan mood swings din. Ko Siyam na bashi hakkin sa na aure ko ta daina bayarwa sabida ya bata mata rai bisa rashin sani ko bisa sanin sa she will forever remain a DARLING a gare shi kuma sanyin zuciyar sa (his Sweetheart).
Shi ya san Siyam na da shigar ciki, wanda watakila ita bata sani ba, ya kyale ta da maganar fara zuwa antenatal ne don ta sha ce masa baza ta yarda ta haihu yanzu ba sai ta kammala karatu. Sai kace ita ke baiwa kanta haihuwar a sanda taga dama ko a sanda take so.
A kullum yana mata uzurin da yake yi mata bias dole na cewa pregnancy mood swings shine dalilin canzawar ta da (harsh behaviours) a kan sa, shi yasa ya fita sabgarta ya kyaleta ya daina lallashin nata ma don ya lura in ya matsa da son jin laifin sa ma kara tunzurata yake yi. Ba don ba zai iya seducing din ta ya kwata a sanda yake so ba, sai don baya son duk abinda zai taba lafiyar wannan Babyn dake jikin Siyama wanda tun bai zo duniya ba ya saka masa suna ADAM (Junior). In mace ce kuma Little NASARA.
Domin wadannan mutanen guda biyu ko ko ya ce ma’auratan/surukan nasa, sun masa karamci, halacci da gatan da bashi da abinda zai saka musu, tunda suka bashi auren Aisha-Siyam, ba don ya cancanta ba, sai don darajja soyayya da sanin muhimmancin ta ga rayuwar dan adam, da kuma son su da addinin Musulunci su ya samu kari, sannan kuma shi da Siyam su samu kwanciyar hankali su cika burikan zukatan su, su girbi wahalar soyayyar dake zuciyar su.
Dining din ya hau ya zauna ya zuba gwaten accan a plate ya soma ci sosai, kunnen sa har wani irin motsi yake yi, a cikin ran sa ya ce akwai ‘karama’ wato ‘miracle’ a cikin hannun girkin matar sa Siyama, ko me ta tsaya ta sarrafa sai ka ji kamar kunnen ka zai fita don aroma da dadin dandadano. Ba karamar yunwa ya kwaso daga VOA ba, don yau ko ruwan tea bai tsaya ya sha ba ya fice tana barci akan sallayar data yi sallahr asubahi. Don haka yaa yi wa abincinnan kyakkyawan ci.
Sai da ya koshi ya kora da zobon Siyam mai tsananin gardi da sanyi. Ta dade bata yi masa irin wannan girkin na nutsuwa da gamsarwa ba. Daga ji ya san yau ta tsaya ta baiwa girkin attention din ta da lokacin ta yadda ta ke yi masa a baya, ba kamar a ‘yan kwanakin nan data canza musu tsarin rayuwa ba.
Ta canza masa fuska ta kuma canza masa launin abinci. Ji ya yi ba abinda yake so yau irin su shirya, ko ba zasu yi komai na auratayya ba ta daina yi masa wannan kwanciyar ta kai da kafa da filallika a tsakiya, wadanda sai yau ya ga ba karamin izgili da raini bane ga miji kamar sa, kuma yayi mamakin kan sa da ya kyaleta tana masa hakan kwana da kwanaki bai taba ce mata komai ba.
Shi ya san idan akwai abinda yafi mijin-tace to shi Hamzah ne. A kan Siyam ba shi da katabus. Yana da sanyin hali a kanta, shiyasa Siyama ta same shi yadda take so take murza zaren ta son ran ta, ba shi da saurin fushi ko kankani a kan kowa ma ba akan Siyam kadai ba, amma in yayi fushin, kafin a samu ya sauka za’a ci wuya, don an ce dama mai hakuri bai iya fushi ba. Kuma zai furzar da abinda ke zuciyar sa don ya huce ko zai maka dadi ko bazai yi maka ba kamar yadda ya tabbatar ya yi wa Siyama jiya.
Ba zai taba yin mummunan fushi da Siyamah ba, kome zata yi masa zai dube shi ne da fuskar kauna da soyayya, idan ya tuna sacrifices din ta a kan sa. Har gobe ya san ba zai samu mai son sa da kaunar sa a duniya kamar Siyama ba. ‘Her own love is different, is unique and is made in the heaven’. Har guba ta sha akan dai ta auri wani nata ba shi ‘dream husband’ dinta ba. Ta saba wa iyayen ta musamman mahaifin da ya haife ta duk a kan sa. In ya tuna wadannan, sai ya dauko uzurin da yafi kowanne girma duk duniya yayi mata.
Yana shirin mikewa don zuwa dakin Siyam din domin ya lallashi ‘yan kayan sa yau, akan abinda kwakwalwar sa ke son tuno masa ya yi mata jiya a sanda yake a buge ko ya samu ta yi hakuri ta daina yi masa kwanciyar kai da kafa, wannan abu na ci masa rai, ko bata bashi damarmakin data bashi a baya ba ya samu kalaman bakin ta masu nuna laifin da ya yi mata wanda bai san ko na menene ba, sai kawai wayar Kaka Veronica ta shigo masa a daidai lokacin.
Saida ya ji gaban sa ya tsinke ya fadi, domin yau sati biyu kenan suna artabu shi da ita a waya, ta ce gidan sa zata dawo da zama, bazata yarda (Muslim girl) ta raba ta da shi ba, ita bata taba sanin akwai kauna ko soyayya tsakanin Musulmi da dan kabilar Berom ba, kuma ta ga alama Moslem girl din ta dauko hanyar hakan (hanyar raba sun), tun da yaushe rabon da ya je gida Jos?
Yaushe ya taba daukan tsahon wannan lokacin ba tare da yaje inda take ba kafin ya yi aure? Yayi aure da diyar musulmi, alhalin ta ce masa bata yarda ba, bazata taba yardaba ko bayan ran ta, yayi kunnen uwar shegu da ita ya yi kan gaban kan sa, har kwanciya tayi a asibiti hawan jinin ta ya tashi sakamakon hakan amma bai je ba, sai kudi da ya rika turawa likitan da ke dubata yana kuma communicating da shi ta waya a kan lafiyar tata.
Da ya tabbatar ta warke an sallame ta ta koma gida sai ya fasa zuwan da yayi niyya don a lokacin yana kan ganiyar cin amarcin sa.
Again aka zo aka yi ‘Nzem Berom Festival’ na wannan shekarar, Kaka ta kira shi ta gaya masa ta kuma jaddada masa muhimmancin halartar ‘Nzem Berom’ a gare shi amma still bai je ba. Kai shi fa yanzu ba ya son duk abinda zai janyo masa cudanya da kiristocin nan, don wani wari-wari karni-karni suke masa, kallon su yake wasu dabbobi haka, marasa alkibla kuma masu najasa da rashin tsaftar jiki da ta zuciya. Hatta Kakar don jinin sa ce, kuma bashi da wanda ya fita a duniya.
Yau sati biyu kenan Kaka na masa rigimar yayi mata visa ta taho United States, a cewar ta, bata ce zata zo don ta raba shi da matar sa ba, amma ta gaji da zama ba tare da shi ba.
Ta azabtu da rashin sa a kusa da ita. Tunda ya san shikadai ta ke da a duniya. A ranta kuwa ta kudire idon ta idon matar Mawonmase…. sai dai iyayen ta su haifi wata ba ita ba.
Hamzah ya san rigimar Kakar sa sarai, bayan rikicin tsufa tanada rigima akan karan-kanta, in bata son abu bata son shi, ta tsani musulunci da musulmai gata da kabilanci mugun gaske, don haka bai ga me zata zo ta yi a gidan sa ba banda ta tada ma Iyalin sa hankali, suna tsaka datasu ‘yar tsamar shi da Siyama, shi yasa yayi ta yi mata hanya-hanya har zuwa yau. Dalilin da yasa kenan duk sanda ta kira shi yanzu sai gaban sa ya fadi.
To yanzun ma hakan ce ta faru, da ya ga sunan Grandma akan screen din wayar sa sai da gaban sa ya yanke ya fadi, gashi ba zai iya ignoring call din ta ba no matter what rigimar da ta zo da shi, tana da matsayin Uwa ne a gare shi ba na Kaka ba. Uwar ma ta musamman, wadda ta yi masa abinda ko mahaifiyar sa da ta kawo shi duniya bata yi masa ba.
Sai ya gyara zama a kan kujerar dining din da yake zaune, sannan cikin nutsuwar sa ta halitta da sanyin murya mai ‘yar sassarfar nan ya amsa mata.
Hamzah ya fara da gaishe ta, amma ko kafin ya rufe bakin sa sai yaji tsohuwar ta rushe da wani irin kuka mai gigitarwa da rikita kwanya iyakar iyawar ta.
“Mawonmase mace ta raba mu ko? Mawonmase yau ka zabi mace a kai na ko? Kusan shekara guda ban gan ka ba, ban sa ka a ido na ba, yau ni ce baka so in zo inda kake sabida ka auri mata Musulma?”
Kaka ta fada da yaren Berom, sannan ta fyace hanci cikin kakabi da hargagin kuka tace “Oh Jesus! Inama Ezekeil (Baban Hamzah) ya dawo duniya yau, ya ga yadda Mawonmase ya juya min baya yau a kan mace!”.
Hamzah ya sauke numfashi a hankali, kirjin sa ya hau bugawa da jin irin kukan da take yi, yace “GrandMa, you know I love you koh? And I care for you more than anybody, me yasa kike tunanin mace ta raba mu, ko bana so ki zo inda nake?
Ina da wadda ta fi ki ne duk duniya? Aiki ne kawai yayi min yawa, sannan mata ta mutuniyar kirki ce, mai kaunar ki, ki kwantar da hankalin ki da ita”.
“Ba zan yarda da hakan ba sai na ganta da ido na, sai na kaita wajen Pastor David ya duba min zuciyar ta, ban yarda haka ta barka ba, don na yi mafarki kana karanta littafin su, I’m afraid Mawonmase kada ta ja ka kaima cikin addinin ta…!”.
Hamzah ya runtse ido yana hango Malamar Musulunci (Islamic Scholar) kuma Hafizah Siyamah Mamman Gembu gaban Pastor David ana karanto mata ayoyin Bible a kan ta. Wani abu da ya san ko sama da kasa zata hade Siyam bazata taba yarda da shi ba, shi kan sa ta hakura da shi duk da son da ya samu labarin ta yi masa, lokacin data ji cewa shi ba musulmi bane ta hakura. Ko a cikin musulmai Siyama is Pious wato Aabidah ce (mai ibadah) wadda bata dauki addinin ta da sauki ba, bata kuma hada shi a muhimmanci da komai ba. Wannan kuma ya biyo bayan zuzzurfan ilmin addini data samu a (Daar Al Uloom Al Madaniyyah) kamar yadda ya samu labari a bakin Nasara.
Shi yanzu sallahr ma kanta wuya take bashi, ya rasa me yasa, ba kullum yake iya yi ba, ko don kusan kullum sai ya shagiya ne yanzu? Idan yayi kokarin yi, sai yaji kasala da nauyin jiki sai kuma ya manta ya shiga sabgogin sa, yana mai cewa sai a hankali, a hankali din da bai san ranar zuwan ta ba, ita kuwa Siyam sai ta kwana tana yi bata gaji ba, duk wani bude ido ko juyi da zai yi cikin dare zai gan ta akan sallaya ko cikin sujjadah. Tunda ta daina yarda ta hada jiki da shi. A kan laifin da bai sani ba.
Ajiyar zuciya Hamzah ya yi, sannan a kagauce cikin gajiyawa da tarin korafi irin na Kaka ya ce “Yanzu dai Kaka me kike so a yi?” Da sauri ta amsa “ka kawo ta Jos nace, nan Riyom, in kai ta wajen Pastor David yayi min bincike da addu’a a kan ta.
(A ran sa kuwa ya san tarko ne Kaka ke son haka masa, muddin ya kai Siyama cikin ‘yan kabilar su suka kuma samu labarin ya musulunta a kan ta ba abinda zai hana su kashe ta, don kasha musulmai ba komai bane a wurin su).
Data ga alamarwannan idea din bata samu karbuwa wajen Mawonmase ba sai ta canza. “Ko kuma ni ka bar ni in zo inda kuke ko sati biyu ne nayi na ga irin rayuwar da kuke yi, in tabbatar bata cuta maka, tana kula min da kai kuma bata ja ka cikin halaka ba!”.
Ta cigaba da fyace hanci tana sheshshekar kuka tana cewa “Da Ezekiel yana raye (Dan ta, mahaifin sa) da ba’a yimin wannnan tozarcin ba, Mawonmase dana gama ginawa na gama shan wahalar sa da dawainiyar sa har ya kafu, shine yayi aure yau ba da yawu na da sanya albarka ta ba, kuma ya dinga gudu na bayan auren sabida ya samu jikin mace!”.
Shi kunya ce ta kama shi a kan kalaman ta, ya ce “Kaka shikenan kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, ki yafe mini in na bata miki rai ban yi da niyya ba, ki so mata ta don ina son ta sosai, ina kaunar ta Kaka, kuma tana girmama ki tun bata gan ki ba.
Wani lokacin har cewa take in bata labarin zuwan mu gona, yadda muke yin shuka da girbin Cocoa, da yadda ake noman Irish, tana matukar so na Kaka, a dalili na ta bata da iyayen ta, tana min duk wani girki irin namu, tana son jin labarin rikice-rikicen kabilar mu na Riyom dana Berom Kingdom.
Sau tari tana son jin yadda ake yin ‘Nzem Berom festival’ da….”.
Kaka ta kara harzuka fiye da tunani. Jin ya tsinke da bata labarin matar sa cikin shauki na soyayyar da ga dukkan alamu bai san yana yi ba, kamar ya manta da wa yake magana. Kaka ta ce a ran ta,
“Oh! Jesus have Marcy on my grandson, he’s caught by an evil woman” (Almasihu ka yi afuwa ga Da na, shaidaniyar mace ta kama shi).
Amma da yake so take ya bar ta ta je U.S, kota halin kaka, a fili sai tace masa “to shikenan, yanzu yaushe zan taho?”
Yace “ki shirya zan turo a kai ki Visa Abuja, in an gama zan turo miki tikiti sai ki taho, it may take few weeks.”