Skip to content
Part 62 of 73 in the Series Sakacin Waye? by Sumayyah Abdulkadir Takori

Wato ji nake tamkar Hamzah ya dauke ni yau yana yawo da ni a kan ‘blue sky’ gajimare mai rainbow kala daban-daban, sabida duniyar shaukin farin cikin da ya jefa ni a ciki. Hawayen farin ciki ya ki tsayawa daga idanuna, shi kuma yasa tausasan tafukan sa yana ta share min ba tare da jin nauyin mutanen wajen ba, har aka kawo mini ‘hot pizza’ gaba na bai bar share min hawaye da tafukansa ba.

“Now, eat what my baby wants to eat”.

Na nade hannun riga na soma cin Pizza, wani irin ci nake mata hannu baka hannu kwarya kamar yau na taba cin abu mai dadinta.

Har tashin ma tura min ya yi duk na hada na cinye kamar Kura. Hamza sai dariya yake yana tsokanata wai baby ya mayar da ni kwadayayya, sai da na gama tsaf muka wuce gida. Wuri na musamman na samu na adana wayar da Ya Omar ya ba ni, don mu dinga magana cikin sirri har ya taimaka min mu gyara komai.

“Siyaman VOA lend me this night in dan ziyarci babyna mana”. Hamzah ya fada daga baya na, immediately ina gama boye wayar a kasan tufafi na da ke cikin wardrove.

Sai da gaba na ya tsinke ya fadi kafin na juyo. Amma jin abin da ya fada yana shigowa da kumb a hannunsa yana sharce ruwa daga lallausar sumar kansa, wadda ya wanke cikin kumfar Arganavita sai hankali na ya kwanta. Na tabbatar bai ga wayar ba

Na juyo ina murmushi na ce, “Wai da so nake ka ja mu sallar isha first”.

Ya kwaikwayi murya ta shi ma, ya ce, “wai da so nake in samu alfarmar ko da one round first?”

Dariya ya ba ni sosai sabida irin rungumar da ya kai min kamar wani zai kwace masa.

And it was a wonderful night, in the Chronicles of the Berom Man and his Damsel Siyama, cikin ire-iren dararen da ba za mu manta ba, sabida karfin al’amuran da suka wakana cikin sa, kasancewar zukatan yau a wanke suke tas, babu kuncin juna a cikin su. Hamzah ya nuna min har gobe shi Hamzah na ne, Mawonmase dina ne ta fannin soyayya da iya min a gado, ba zai taba canzawa ba. He is always unique a wannan bangaren, and will forever remains Siyama’s DREAM MAN, and also Siyama’s everlasting choice of a HUSBAND.

              ***  ******

Tun daga wannan rana abubuwa suka soma gyaruwa a gidan namu, ni da Hamzah soyayya ta dawo sabuwa. Kwarai yake kokarin yin sallah yanzu don kullum Ya Omar da hanyar da zai gaya min wadda zan biyar da shi, ya yi sallah cikin lallami da dadin rai. Sannan bayan kowanne intercourse dinmu ba na bari ya shiga toilet shi kadai sai na bi shi, na ce mu yi wankan sallah tare yana yi ina gyara masa. Ya Omar ya hana ni yin fushi da shi ko ‘sex denial’, kuma ya ce in ya yi kokarin zuwa ‘Bar’ in ce zan bi shi mu sha tare, kada in kara ce masa Allah wadai a kan shan giya. Rana tafarko da na ce zan bi shi musha tare cewa yayi na tabu, shi ko dan sa ba zai girma ya ga kwalba a gidan sa ba. Shima rokon Allah yake ya yaye masa gabadaya. In na sha giya ko kurba daya ba zai taba yafewa kan sa ba. Allah ba zai taba yafe masa masa ba, Young Abba ba zai yafe masa ba. Ya ce “Siyam ba dadi ne da ita ba masifa ce kawai da jarraba, ko coca cola ya fita dadin dandano”. Daga ranar wadda yake shigowa gida da ita a da babu shakkar ido na to yanzu boyewa yake, ko kuma in ya zo gidan kwata-kwata ya hakura da giyar sai idan ya fita cikin motar sa. Gashi ba ya iya zama a mashaya ya sha giya sai ya ce wai wajene na watsatstsu, marasa aji da kunyar Allah (lol). Shi kuma fuskar sa sananniya ce a duk wani International Media, in aka gan shi a mashaya ajin sa zai bare, ya zubar da kima da darajar sa a idon mutanen da Allah ya bashi da respect din da suke bashi. Ya ce ko a TRT World babu wanda ya taba sanin yana shan giya kallon musulmi mai tsantseni suke masa, a rayuwar sa baya son duk wani abu da ya zama ruwan dare a cikin al’umma, shi mutum ne mai kiyaye martabar sa, ya sha ce min shi a karan kan sa ya san ba abun kirki bane addiction ne matsalar sa, kuma yana rokon ceton Ubangiji da yafiyar sa musamman a wannan lokacin da zai ajiye kwan sa a duniya. Ya kuma san bai manta da shi ba tunda shi ya umarci bayin sa da suka kasa barin wani laifi da suke aikatawa da tuba akai-akai da yawan yakanah.

      ****          ****             ****

        KADDARA TA RIGA FATA

Na kira ranar yau da kaddara ta riga fata, hakika boye wani abu ko da da kyakkyawan nufi ne a mu’amala ta aure, musamman irin nawa da Hamzah is a scandal, and it will eventually backfired.

Hamzah ya yi min sallama zai wuce TRT WORLD din su, wato ma’aikatar da yake aikin broadcasting da su yanzu a kasar Turkiyya, fitar sa ba da jimawa ba na dauko waya ta daga maboyar ta, na danna wa Ya Omar kira.

“Ya Omar albishirin ka, yau Hamzah har Tahajjud ya yi, shi Liman ni Maamu, ya kuma yarda da asubah na kara masa suratul Dhuha ya haddace ta wallahi”.

Ya Omar ya yi tafi yana fadin, “You see! Komai na rayuwa dan a hankali ne (ya dan dakata yana magana da yaron sa Aryan, kafin ya sallame shi ya ce), “Keep up the good work, my good darling sister, endure, persevere! (Daure, jure).

Insha Allahu sakamakon jihadin ki da ladan aure tun a duniya za ki same su. Hamzah will insha Allah become a good moslem the way you wants him. Yau dai zan gaya wa Kausar muna tare, ina tsoron kishin ku na mata ne duk da tawa matar mai hankali da fahinta ce, amma a wannan fannin sau tari rasa hankalin ku kuke yi, musamman da yake ta dade da sanin ba wanda nake so a duniya sama da ke bayan Abba”.

Dariya na yi cikin jin dadin abinda yace “ba wanda yake so sama da ni a duniya bayan Abba”. Ya Omar bai taba faranta min irin yau ba, na ce, “Ya Omar ni ma haka. Ba wanda ya kama kafar ka a zuciya ta, kuma har abada ba za’a yi ba. I love you my brother like no other…!!!”.

Kafin Ya Omar ya ba ni amsa sai na ji huci kamar na mesa a baya na. Juyawar nan da zan yi na yi ido hudu da Hamzah fatar bakinsa har rawa ta ke yi, kamar yadda jiki da zuciyar sa ke raurawa. Ban san lokacin da na saki wayar kasa ba na hada hannayena biyu cikin saranda, sannan na soma kokarin yi masa bayanin da zai fahimce ni…

“Hamzah… please… ba ni lokaci I will explain, wallahi…”.

Belt din jikin sa na ga yana zarewa, idanu na suka kara raina fata, idanun sa bakidaya sun jirkice sun koma upside down, kokari yake ya buga kan sa da bango. Na yi maza na rike shi. Ya fizge, ya buga kan sa da bango.

“Gara in kashe ki kafin bakin cikin cin amanar da kika yi min ya kashe ni. In ya so nima in sha poison din in mutu. Allah wadaran soyayya tunda babu ta gaskiya…

Wane Omar din ne? A ina ku ka hadu? Har waya ya ba ki? For how long kuke tare? To ko sharing din ki muke yi ni da shi?”

Tambayoyin Hamzah sun fi kama da saukar aradu cikin kwanya ta. Na kasa amsa ko guda sabida tambayoyin sun yi min tsauri, kuma na kasa fahimtar ta inda zan billo musu.

“You, the lier, the hypocrate… the betrayer… mai fuska biyu yau sai kin gaya min wane Omar din ne?”

Ya saki belt din a kasa domin ya kasa dukan nawa, yana gayawa kan sa da babbar murya mazan kwarai basa dukan matan su, marin da ya yi wa Siyam a baya alhalin tana cikin halin bikin haifar masa da duk da cikin maye yake lokacin har gobe yana cin ran sa, ya soma buga kansa da bango yana rokon Allah ya kashe shi ya huta da kishin da ya samu ran sa a ciki, na ga cewa zai ji wa kansa ciwo ba dan kadan ba, na yi kansa da gudu na rike kafafun sa ina kuka, na ce, “Is not what you are expecting Hamzah, Ya Omar Yaya na ne, cikin mu guda…”.

Ban karasa ba na ji Hamzah ya fizge kafafun sa. Hamzah bai yi la’akari da cikin jiki na ba haka ya janyo hannu na keeeeey har zuwa falo, ya kuma dakin sa ya dauko passport dina ya wurgo min.

“Don’t do that Hamzah, ka yi komai don ka huce, ka doke ni iya duka in zaka iya amma ban da saki, ka doke ni in dai za ka huce daga baya zan yi maka bayani…”.

Hamzah ya ce, “Har abada ni da kara yarda da mace, har abada da ni da kara yarda da kalaman yaudarar bakin ki…da kunne na naji me kika ce masa ba wani ne ya gaya min ba”

Na ji na kuma yarda Shaheed, na ce ma Ya Omar I LOVE YOU! Amma don… Allah don soyayyar ka da Manzo sallallahu alaihi wasallam, kada ka furta saki”.

“Za ki bar min gidana in ban yi sakin ba?”

“Wallahi zan bari, yanzunnan kuwa, amma in ka furta kalmar saki har abada tare za mu zauna babu inda za ni ko za ka kashe ni”.

“Ba kya so in sake ki kika ci amana ta? Gaya min gaskiya cikin jikin ki nawa ne ko nashi? Tun yaushe kuke tare a kasar nan yaushe kuma ya baki waya?”

Hawaye masu zafi suka balle min, zuciya ta soma yunkuro min ina danne ta ta hanyar ambatar innalillahi wa’inna ilaihi raji’un… Allahumma ajirni fi musibati. Astagfirullah Ya Allah wa atubu ilaika…”.

Kayan falon Hamzah ya soma watsi da su a tsakar falon yana hada center table da talabijin, ji ka ke taratsatsa! Yana fadin, “Allah wadaran kalmar soyayya tunda babu ta gaskiya in existence, idan har Siyam zaki iya cin amanata har haka to babu soyayya in reality,  ki fita min a gida kafin na yi abin da zan zo in yi nadama…”.

Da rarrafe da jan gindi na gusa daga gaban sa don na tabbata a wannan halin ba zai taba sauraro na ba, na dauki passport dina da ya jefo min babu inda ba ya rawa a jiki na, kamar wadda miji ya kama da kwarto, kuma da rarrafen na rarrafa na fice daga gidan ba tare da na dauki komai ba ban da passport din nawa.

Ta gaba na Hamzah ya zo ya wuce zuwa motar sa, ya shiga ya fisge ta ya bar harabar wajen. Taimakon da Allah ya yi min shi ne a lokacin hantsi ya dubi ludayi, ba dare ba ne da dare ne ban san ina zan saka rayuwata ba.

Zama na yi dirshan a kofar gidan mu makalkale da passport dina a hannuna na dama, ni ba kuka ba, sai nishi da numfarfashi kamar nakuda zata zo min. So nake nutsuwa ta zo min, hayyaci na ya dawo kafin in yi tunanin abin yi. A nan kofar gidan mu akwai terrace sai na kwanta a wurin na yi lamo! Ina maimaita innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!

Daga haka na ji gani na yana tafiya, jina yana yin nesa-nesa kafin ya dauke gabadaya. Ban kara sanin abin da ke faruwa da ni ba.

Na farfado ne na gan ni a gadon asibiti ana yi min karin ruwa, wanda ya kawo ni asibitin ne ban sani ba. Daga baya na ga wata Baturkiya ta shigo tare da likita. Ido na kafa musu ba ko kiftawa ina kokarin tuno abin da ya faru da ni, amma na kasa tunowa. Har sai da likitar ta dafa ni tana tambaya ta,

“How are you feeling now?”

Na lumshe mata ido kawai, domin kan nawa da ya kamata in gyada mata ya yi min nauyi, ya yi min wani irin gingirigin. Baturkiyar, wadda akalla za ta yi shekaru arba’in ta kama hannuna ta ce, “Suna na Ahlaam Naadir, ni makociyar ki ce. Na fito zan fita na gan ki kina kwance a kasa, na kuma nemi wani a kusa ko maigidanki har tsayin lokaci ban ga kowa ba, so I decided in kawo ki asibiti in ki ka farfado sai ki bada lambar waya a kira mijin ki”.

Sai a lokacin ne na tuno Hamzah da irin janyowar wulakancin da yayi min kamar kayan wanki ya fito dani daga daki na, da korar da ya yi min daga gidan sa da ciki. Da sauri nasa hannu na shafa cikin nawa na tabbatar yana nan yadda yake, sai ma wani tudu da tsini da ya kara yayi min kabe-kabe tabbacin ya kara kara girma.  Na soma tunanin laifin da na san na yi wa Hamzah, amma ko kusa ko alama ba laifi ba ne, waya ya tarar ina yi da Ya Omar, zuciyar sa ta kishin bala’I ta gaya masa abin da ta ga dama. That’s the problem with Hamzah, as an alcoholic addictor, yana da saurin daukar hukunci and he’s not giving things a second thought. Kawai don yaga ina waya da Omar sai kishin haukan sa ya gaya masa amanar sa nake ci, bayan ko a lokacin abin alheri nake fada a kan sa.

Wata zuciyar nan da nan ta tuna min cewa Hamzah bai san ina tare da Omar ba, bai san Omar ya ba ni waya ba, it backfired, kuma ba laifin kowa ba ne, nawa ne da tun farko ban gaya masa gaskiya ba.

Amma a halin yanzu ba abin da zan gaya masa ya yarda da ni, yana bukatar in ba shi sarari kamar yadda ya bukata har zuwa lokacin da zai nemi cikakken bayani don kan sa.

Ya Omar, dan uwa na ne da banda kamar sa, jini na ne kuma barin rayuwa ta da bai isa ya raba mu ba wai don taqamar yana aure na kowanne irin kishi ne da shi. So gara ma tun yanzu ya saba, Boddo da Omar tare aka goya su, tarbiyyar su daya jinin uwa dana uba ya gauraye jikin su, amma tunda ya ba ni passport dina, ya kuma nemi in gusa daga inda yake daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, zan tafi gida har sai ya neme ni.

Na gode wa ita Ahlam din, godiya maras adadi, likita ta dudduba ni yadda ya kamata ta ce bani da matsala stress ne ya sumar dani. I need to rest for two days. Ahlam ta tambaye ni lambar maigida na sai kawai na ba ta lambar Ya Omar wadda na riga na haddace ta.

Wayar tana shiga ta miko min, “Assalamu alaikum, Hello”. Inji Ya Omar. Ai jin muryar sa kadai na yi raunin duniya da kukan duniya bakidaya suka rufto min. Yana jin kukan kuwa ya canka cewa ni ce, “Boddo am, Boddo sarkin shagwaba me kuma ya faru? Muna magana na ji kamar wayar ki ta fashe? Me aka yi miki? Me ke faruwa? Na kira ki ya fi sau shurin masaki ba ta shiga ba. Kina ina? Me ya same ki?”

Ya jero duka tambayoyin a urunce, hankalin sa a mugun tashe. Ganin na kasa magana sai gunjin kuka nake masa, Ahlam ta karba ta yi masa bayanin asibitin da muke, wato, “Hisar Intercontinental”. Ko mintuna talatin ba a rufa ba, Ya Omar ya bayyana a dakin da taimakon ma’aikatan asibitin. Gaba daya a rikice yake, ba nutsuwa ko kadan a tare da shi yake tambaya,

“Me ya same ta? Boddo what happened? Ina Hamzah na gan ki a nan ke kadai?” Likitar da Ahlam suka fita daga dakin don a tunanin su shi ne mijin nawa. Na ce, “Ya Omar…!” Sai kuka ya ci karfi na.

Lallashi na yake ta yi cikin sanyin murya har na har na gaya masa komai ya kwabe min. Hamzah ya kama ni ina waya da shi and he assumed it otherwise, “Laifi na ne Ya Omar don ban gaya masa ba, tun farko na boye sabida sanin halinsa na zafin kishi a kan ka. Yanzu dai ya ce in bar masa gida, ya jefo min passport dina”. A fusace Ya Omar ya ce, “Ya dake ki?” Na ce “a’ah, ya dai kore ni” “wallahi da ya dake ki da ya daki auren sa, marin da yayi miki a baya ma don bana nan ne ya sha shi basillah, ba namijin da ya isa ya dinga dukan ki da sunan aure ina raye. Na da din ma don ba ma tare ne, kora sai kace ya samu dabba? Smart ass kawai, daga yau zai san ya yi na farko ya yi na karshe korar matar sa daga gidan aure. Kishi hauka ne? Ina passport din naki?”

Na hau lalubawa, sama ko kasa na rasa passport din. Tabbas yana hannu na kafin in sume a terrace din kofar gidanmu.

“Tashi mu tafi Boddo, gida na zan kai ki, ai za ki iya takawa ko? Ko in goya ki zuwa mota?”

Rudewar sa ta sa watakila ya manta jiya ba yau ba ce. I’m no more his little kid Boddon Mambillah, da yake durkusawa in dane bayan sa mu tafi makarantar allo. Ban san sanda na yi murmushi ba, duk wata damuwa ta ta yaye domin har na hango kaina a tsaunin Mambillah a cikin dakin Ummati kan gadon bonon ta. To amma ina! Na yarda passport dina.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Sakacin Waye? 61Sakacin Waye? 63 >>

2 thoughts on “Sakacin Waye? 62”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×