Skip to content
Part 5 of 5 in the Series Sakamakon Zunubi by Fatima Rabiu

Fitowar da Amali zatai kawai taji an d’auketa da wani gigitaccan mari tassssss tassssss.

A gigice Amali ta dafe kumatunta, da masifar sauri ta d’ago tana duban wacce ta mare ta. Ba kowa ba ce face Asma, tun d’azo ta hangi Amalin dake fitowa daga part d’in Henry, wani irin kishi ya ciyota har bata san sadda ta k’araso inda Amalin take ba, dan ita a tunaninta sonshi take tana shishshige mai dan har idonta ke mata gizo da Amalin tana fitowa tare da wani murmushi a fuskarta.

Kamin zafin marin ya saki Amali ta k’ara jin saukar wani a tsakiyar idonta, runtse idonta tayi da mugun sauri lokaci d’aya jini ya kwanta ta jikin idon, tama kasa magana sai bin Asma take da wani kallon takaici.

Can ta tsinkayi muryarta cike da tsananin masifa tana cewa “wato kwartonci kesa kina shishshige ma Captain Henry ko? Saboda y’ar iska ce ke dama mai bin mazan mutane, to ki bud’e kunnanki da kyau kiji ni, wallahi tallahi na k’ara ganin kina shishshige ma Henry wallahi zan iya halakaki indai a kansa ne, ke kowa ma zan iya kawarwa mudun zai bani matsala akan na mallaki Henry, ke kuma k’aramar alhaki bazaki min wahalar b’atarwa ba, dan haka tun wuri kima kawar da maitarki akan Henry, domin Henry na Asma ne ni kad’ai, dan haka ki kiyaye ni ki fita ido na rufe tunkan nasa a b’atar dake a doron duniyar nan gaba d’aya, kinsan waye uba kin san abunda na fad’a mai sauk’i ne, baki da kowa, ke idan baccin k’arfin hali dake gare ki ina ke ina d’and’an president, ai kaurin idonki ma ya isa Amali, nidai gargad’i nayi miki idan kunne yaji gangar jiki ta tsira”. Tana idasa fad’ar haka tayi wucewarta tabar Amali tsaye tana tsiyayar da hawaye.

Part nasu na masu aiki ta nufa tana tafiya tana kukan zuci da hawaye dake anbaliya a fuskarta. Tana gaf da shiga d’akinsu taji kukan Julia da Hannah, suna shashshakar kuka. Da hanzari ta fad’a d’akin tana faman tabbayarsu mike faruwa?. Da sauri Hannah ta rungume Amali tana cewa “Amali tsoron gidan nan ya cika min zuciya kina gani fa daga kawo Julia baifi sati d’aya ba, amma yau wa’incan na mamajon Isaac da d’an uwansa suka farmata suka lalata mata rayuwa, Amali sun tarwatsa mata rayuwa, ina gudun wata rana nima abun nan yazo kaina anya bazan gudu daga estate d’in nan ba”. Wata irin fad’uwar gaba ce ta riski Amali da sauri ta runtse idonta wasu sabbin hawaye suka sake wanke mata fuska, kallon Julia take da duk tasha kuka ga fuskarta data kunbura da shatin mari a fuskar tata, kai hatta jikinta duk ciwo ne domin fara ce Julia. Amali tana kallonta bata san sadda ta k’ara fashewa da kuka ba, tana shanye duk wani abu na yau da akai mata, tana fuskantar Julia. Tama rasa da wata kalma zata fara rarrashinta, tabbas ko wacce kalma da zatayi anfani wajan bata hakuri tayi kad’an tabbas an cuceta an gama da ita. Da kyar ta samu bakinta ya furta sunan Julia tana cewa “Julia na rasa ma ta ina zan fara baki hakuri, Julia tabbas an cuceki amma ki sani idan ba nan akwai can, wadda Allah da kanshi zaiyi maku hisabi keda so, kiyi hakuri kawai ki mik’a kukanki wajan Ubangajin da baya bacci kiyi hakuri kiyi hakuri kawai, amma tabbas mutunan gidan nan gaba d’ayansu basu da imani ko musuk’ala zarratin”. Julia na kuka, da gurb’atacciyar hausarta ta ce “tabbas Allah zai saka min, Allah ya saukarma da mutunan nan bala’in da bazasu iya maganinsa ba, Allah ya nuna masu ba komai kud’i ke maganinsa ba”, ta k’are maganar tare da gunjin kuka. Hannah ce ta sauke lumfashi tana cewa “tabbas duk da ke ba masulma ba ce amma Allah na kowa ne tabbas Allah zaiji kukanki kuma zai kawo maki d’auki dama mu duka gaba d’aya domin ana shiga hak’k’inmu”.

Da kyar suka taimaka Julia ta gyara jikinta tanayi tana kuka tsabar yadda gabanta ke mata zugi abunka da ba’a sababa, ba k’aramar illa sukai mata ba, dandanan zazzab’i ya rufe ta. Su Amali suna tare da ita suna bata kulawa. Har sadda sauran ma’aikatan gidan suka dawo, sai tabbayarsu suke ko lafiya. Inda basu sanar ainahin abunda ya faru ba, saboda wasu koda ka fad’a k’aryata ake koda mutum ya sani, kai koda abun ya tab’a faruwa dashi shima, amma yadda kasan asiri ake masu haka suke ji basa iya d’aukar ko wane irin mataki bare har suyi magana akai, to idanma sunyi magana masu kasar ne fa gaba d’aya miye doka zatayi masu suda sune dokar gaba d’aya, dama ance wata shari’ar sai dai a lahira.

K’ASAR INDIA

Zaune Sir Benjamin yake a gaban wani k’aton mutum mai sanye da wasu layu da jajayen kaya a jikinsa, wata irin dariya yake b’ab’b’akawa wacce tsabar dariyar da yake tasa d’akin da suke zaune fara gigizawa kamar kasar wajan zata tsage gida biyu. Wata murya dake fitowa daga bakin bokan kamar saukar aradu mai cike da wani irin amo marar dad’in sauraro. Yana cewa “tabbas tunda kazo nan da buk’atarka ta gaba biyu zaka koma akan kujerar milkinka, amma sai kayi wani aiki mai hatsarin gaske idan kaga zaka iya to ba shakka gaka can kaci zab’e. Sir Benjamin dake zaune ba alamar tsoro ko damuwa ya ce “tabbas boka ko miye zan iya yi tunda kaga na d’akko k’afa yau tun daga Nigeria zuwa nan ai kasan babu abunda bazan iya yi ba, kawai a fad’a min miye zanyi boka”. Wata dariya bokan ya sake kecewa da ita yana cewa “zaka samu y’an mata guda biyu y’an shila wadda ba’a tab’a kusantarsu ba, zakayi anfani dasu amma harda ta duburarsu, wannan ruwan maniyar da zaka zubar wajan saduwa dasu zaka ajiye jan kyallen a wajan da kake saduwa dasu.

Ana so maniyin ya zuba a jan kyallen, sannan kana gamawa dasu kayi masu yankan rago jinin da zai zuba a jikinsu zamu aiko da aljani zai tsutse sa, daga nan zai d’au jan kyallen da ka tara maniyinka dana y’an matan, abu na gaba za’a samu jarirai sabowar haihuwa aljani zai sha jininsu”. Koda gama wannan bayanin sab’anin Sir Benjamin yaji tsoro ko ya ce bazai iya ba, sai ma wani mugun murmushi ke fita ta fuskarsa, ya ce “shine kad’ai abunda za’a aiwatar boka”.

Wata shegiyar dariya boka ya saki yana cewa “tabbas irinku muke so wadda basa da tsoro ko shakka wajan cikar burinsu, tabbas idan ka aiwatar da komai yadda na fad’a maka zaka yi mulki yadda kake so”.

Shima Sir Benjamin dariyar ya saki yana cewa “dana koma duk za’a aiwatar da abunda kasa”.

“Idan kuwa kayi haka kaima zaka ga sakamako ranar zab’e.

Koda Sir Benjamin ya fito kai tsaye mota ya shiga sauran jami’an dake tsoronsa suka rufa mai baya kai tsaye filin jirgi suka nufa, koda suka isa jirgi shi kad’ai yake jira domin shi kad’ai da jami’an tsaronsa zai d’auka. Basu wani b’ata lokaci ba suka tashi, sai da sukayi kwana d’aya da yini sana suka iso Nigeria. Wasu matsitan motaci ne suka zo tarbarsa kusan guda ashirin bak’ak’e ne masu mugun kyau tare da jami’an tsaro kota ina. Yana hawa mota suka fara tafiya akan titi duk inda suka gifta sai ansan wani ne a k’asar ya wuce.

Sir Benjamin suna cikin mota ya kalli P’A d’insa, wadda duk wani abu da suke shiryawa ta rashin gaskiya ya sani tare suke yinshi shi yake samo komai. Ya ce “ina so a samo min y’an mata guda biyu akai min su gidan hutawa ta, sannan abu na gaba ina so a samu min jarirai d’anyar haihuwa”. Gyara zama P’A yayi ya ce “ranka ya dad’e samo y’an mata bazai wahala ba domin yawancin y’an matan yanzu son kud’i gare su, dan ayi masu wayau a halaka su ta sanadiyar kud’i ba wani abu bane mai wahala. Kawai dai samo jariran ne kamar zaiyi wahala”. Wani murmushi Sir Benjamin yayi yana latsa wayarshi ya ce “idan komai ya tafi dai-dai da mutanan da kukayi aikin dasu kowa zai iya samun million goma-goma”. Zaro ido P’A yayi yana had’e wani miyau yana mai-maita million goma.

“Kwarai million goma”, cewar Sir Benjamin.

Har jikin P’A na kyarma wajan cewa “ai ranka ya dad’e kasama ranka anyi an gama, zuwa gobe duk za’a samo komai kake buk’ata”, wani d’an murmushi Sir Benjamin ya saki ya sake kallon P’A ya ce “kuna gama aiki ka turo account zan saka maka kud’in duka”.

Har suka isa wajan gari sosai zasu nufi estate d’insu, Sir Benjamin ya dakatar dasu yana ma P’A d’insa su juya su koma cikin gari gidansa na hutawa zasu je har zuwa sadda zai kammala aikinsa.

Kamar yadda P’A yayi al’k’awari hakance ta kasance an samo jarirai koma nan take aka masu yankan rago, dandanan aka tsutse masu jinin jikinsu. Y’an matan ma an samo su.

Sir Benjamin yana zaune daga shi sai wata y’ar rika da gajeran wando, P’A d’insa ya shigo tare da y’an matan da aka samo, su biyu ko wacce ta ci wanka na k’in k’ari suna shigowa wata mai suna Luba ta kalli y’ar uwarta tana zare ido ta ce “Zainab ki duba fa da gaske wannan mutunan wajan president ya kawo mu, wow gaskiya yau mun fito da sa’a zamu samu mugan kud’i”. Murmushi Zainba ta saki tana cewa “tabbas duk da ban tab’a ba wani d’a namiji kaina ba sai dai ayi d’an tab’e-tab’e, amma president da kansa dole na basa kaina, Luba kallesa fa da kyau ya had’u over”, wani lashe baki Luba tayi tana lumfashe ido yadda take k’arema Sir Benjamin kallo. Tabbas Sir Benjamin kyakkyawa ne na gidan gaba ma kuwa, domin kyansa ne Captain Henry ya gado, sai yazo yama fi Sir Benjamin d’in kyau shi yasa da yawa y’an mata ke hauka akan sa.

Cike da yanga da jan hankali suka nufi kan kujeru suka zauna, bayan P’A ya fita yana wani mugun murmushi yana cizo yatsa yana cewa a zuci “zaku ci ubanku ne koba y’an iska ba”.

Cike da jan hankali Luba ta matsa sosai kusa dashi ganin yadda yake jifarsu da wani irin murmushi mai zautar da zuciya, ai ko Zainab bata san sadda ta d’are akan cinyarsa ba. Ya fara basu wasu zafafan kiss a tare. K’arshe dai suna ji suna gani da mugunta ya rabasu da mutumcinsu, tun suna marmarin abun har suka dawo kuka da magiya ya kyale su, haka nan sun gaji, amma ina sai da suka kai basa ma iya d’aga hannunsu tukun abunda ya k’ara basu tsoro da haushi yadda yake saduwa dasu ta duburarsu, ya sauka daga kansu, tare da d’auke jan kyallen daya shinfid’a a kai a sadda yake masha’arsa dasu.

Sai da yayi wanka ya fito, suna zaune da kyar suke zama ma, sai faman share hawaye suke, sun d’auka yana fito zai sallamesu amma suka ga sab’anin haka. Zaro ido Luba tayi jin Sir Benjamin yana waya yana sanar da P’A d’insa ina wuk’ar da kwaryar da zai tari jinin dasu, ya gama aiki na farko ya shigo da kayan aiki na biyu. Su duka cikinsu ne ya fara wani irin kuka na tsabar tsoro.

Da mugun sauri Luba ta mik’e bakinta na kyarma wajan furta “mimm miiiimiiii kake nufi ne wai ka sallamemu mu tafi”

Wani kafurin murmushi ya saki yana dubansu ya ce “mi kuke ci na baka na zuba yanzu zaku tafi ai inda ba’a dawowa”, ya idasa maganar yana sakin wata dariyar ta zallar mugunta.

Zainab da Luba ko zaro ido suke kamar kwayar idonsu zata fad’u k’asa bakinsu na kyarma a tare suna kiran sun shiga uku.

A sadda P’A ya shigo rik’e da sharb’eb’iyar wuk’a tare da wata kwarya rik’e a hannusa, sai dai kamin P’A da Sir Benjamin su ankara tuni Luba ta tashi a zabure ta fisge wuk’ar dake rik’e a hannun P’A tana nufar Sir Benjamin gadan-gadan da ita a zuciye tana zuwa ta cak..

<< Sakamakon Zunubi 4

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×