Skip to content
Part 10 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Ba wanda zuciyata ke kawo min kullum, sai hoton MA’AROUF dan wajenka, shi ne na yo tattaki in nemi wannan iri mai albarka. Ba na bukatar komai sai sadaq (sadaki) da Allah Ubangiji ya yi umarni. Amma idan Ma’arouf bai amince ba, don Allah kada hakan ya yi sanadiyyar da gaisuwar makwabtakar da muke yi da juna za ta tawaya, kuma kada a takura masa. Abu ne dai da nake da yakini a kai ba zai samu matsalar komai da Aisha ba, saboda ko cikin ‘yan uwanta ta fita daban wajen hankali da kyakkyawar tarbiyya.”

Malam Habib ya ja numfashi ya sauke, ya dubi Alhaji Mansur cikin murmushi.

“Wato dauki ne Allah ya kawo mini ina zaune a kan tabarma ta. Wallahi Alhaji tashin nan da ka ga ya yi zancen da nake yi masa ke nan, a da in na yi ya ce karatu, hidimar kasa, project, masters. Amma a yanzu babu ko daya, bai dai kai ga ba ni amsa ba ka zo, amma na san ba zai ki abin da na yi masa umarni ba. Sai dai kamar yadda ka ce, ba zan tursasa shi ba, zan ba shi zabi ba umarni ba.

Duk da haka wani hanzari ba gudu ba, ‘yar wajenka Aishatu ka ce sunanta ko? Za ta iya zama a wannan muhalli da Allah ya hore mana? Domin dai yatsun ba daya ba ne, kuma babu karya ko yaudara a tsakaninmu.”

Alhaji Mansur ya yi murmushi, “Ko a bukka ne cikin jeji na yi wa Aisha aure za ta zauna. Ina tabbatar maka da wannan. Tana da gida nata na kanta da ta gada daga mahaifiyarta, amma a gidan mijinta za ta zauna ko ya ya yake. Don haka kada ka kara wannan tunanin.”

Suka yi musabaha suka yi sallama, cike da aminci ga juna, Alhaji Mansur ya tafi.

Saboda farin ciki Malam Habibu da kyar ya bari garin Allah ya waye suka tafi masallaci sallar asubahi, da suka fito tun a hanya yake gaya masa yadda suka yi daren jiya da Alhaji Mansur.

Shiru ya yi kamar mai tunani, jinsa yake kamar a kan gajimare, yana shawagi don farin ciki. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, bai tabbatar cewa ita ba ce. Su hudu ne kuma bai san sunan kowacce ba. Baba ma bai sani ba, balle ya tambaye shi, yadda Baba yake murnar nan ba zai iya tula masa kasa a ido ba, kawai sai ya yi kundumbala ya ce, “Idan ita yarinyar ta amince ni ma na amince.”

Baba ya kama hannayensa ya rike cikin nasa, yana ta sanya masa albarka.

Baba da kansa ba aike ba, ya je ya sanar da Alhaji Mansur amincewar Ma’arouf wa auren Aisha. Gadan-gadan suka shiga shirye-shiryen auren shi da Alhaji Mansur. Ta fannin Baba, ya sa an yi fenti na farar kasa a sassan da ya ware wa dan tilon dan nasa, aka yi shafe na sumunti, daki ne ciki da falo matsakaita sai wani falle daya a gefe. Falle dayan Ma’arouf ke zaune ciki matsayin nasa, ciki da falo aka bar wa amaryar, sai makewayi guda biyu, na wanka daban, na bayan gida daban, sai ‘yar rumfar kwano da aka bari matsayin madafi. Tsakar gidan ya sha sumunti fes gwanin sha’awa. Gidan sai kamshin sabon fenti yake yi mai dadi.

‘Yan uwanta uku Khalisa, Halima da Zainab sai rawar kai suke wajen hidimdimun biki, ita kam a sanyaye ta ke, ko can ba shiga sha’aninsu ta ke ba saboda ba ta da wannan kuzarin (power). Ban da iya shege ba abin da suke mata, wai Baba ya ba da sadakarta wa malamin makaranta. Ko lefe ba a yi mata ba. A zuciyarta cewa ta ke, ‘Ai gara zama da malamin makarantar da zama a gidan da ko dariya ban isa in yi ba, gara zama da malamin makaranta da zaman gidan da ban taba farin ciki a cikinsa ba, tunda aka haife ni. Gara zama da malamin makaranta da zaman gidan da ba ni da ‘yanci. Ya Allah ka sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare ni.”

Duk abinda Alhaji Mansur ya yi wa sauran ‘yan uwanta shi ya yi mata a dakunanta, amma dole aka koma da wasu kayan saboda babu wajen sanyawa.

Aka daura aure lafiya da mafi kankantar sadaki, kafin nan ya je sau biyu domin su fahimci juna a bisa umarnin iyayen, sam ta ki yarda ya ga fuskarta, cikin hijabin islamiyyarta ta ke daga sama har kasa. Ta dai gaishe shi da ‘yar siririyar muryarta, shi kuma ya rasa me zai ce mata. Sai suka zauna shiru. Da shirun ya ishe shi ya bude jarida wadda ke tule a kan wani tebir na falon kala-kala, hakan ya sa ya gane falon Babansu ne. Da ya ga dare ya yi, sai ya yi mata sallama ya tafi. A ransa ya kudurce ko kuturwa ce zai zauna da ita a haka, in har hakan zai sa Babansa farin ciki. Wanda ba abinda bai yi masa ba a rayuwa.

An yi biki lafiya aka kai amare dakunansu.

*****

Wani irin zama ake yi tsakanin Ma’arouf da mai dakinsa Aisha, kowa na dakinsa, ko da ta fito yin wata sabgar ta ji motsinsa zai shigo, ko zai fito daga dakinsa komawa daki ta ke sai ya fita, ko ya shigo ya shige nasa dakin. Ga shi an kawo ta da gara don haka ba ta bukatar komai daga gare shi, shi kuma kullum zai tafi aikin koyarwarsa sai ya ajiye mata kudin cefane a kasan kofar dakinta yadda tana budewa za ta gani.

Baba ne ya samar mata almajiri kullum yake zuwa ya yo mata cefane, da aike in ta yi girki ta zuba masa. Amma ko sharar tsakar gida ba ya yi mata, ita ta ke tsabtace abinta ciki da bai dinsa.

Aisha ta samu kanta cikin wani irin kwanciyar hankali wanda ba ta taba samu a gidansu ba, sai tsangwamar matan uba da ‘yan uba, kawai don Babanta ba ya iya boye kaunar da yake mata. Tuni ta murmure, kyanta ya soma fitowa. Ta yi kiba, ta yi (fresh) da ita cikin watanni uku. Da kuwa kamar sillen kara aka kawo ta, ga cima mai kyau da tafi ta gidansu. Sammata abinci ake a gidansu kamar an zuba wa karamin yaro, a nan kuwa ita ta ke dafa abin da ta ke so ya ji kifi ko nama, saboda kudin da Ma’arouf ke ajiye mata kullum ya fi karfin cefanen rana daya, haka ta ke ta tara ragowar a ranta ta ce, banki zan saya in yi ta tara masa abinsa.

Wani sabon salo, sai Inna Luba matar Baba ta soma zagayowa wajen Aisha in sun fita aiki. Ita Aisha ba ta san halin Inna Luba ba, da zuciyarta daya ta ke girmamata, in ta yi girki kullum sai ta zuba ta ba wa almajirinta ya kai mata, tunda mijinta bai ba ta iznin ta dinga fita ba.

Ta zauna ta sa Aisha a gaba ta yi ta surutun banza da wofi tana bata Ma’arouf a idonta, tana fadin ba abin da ba ta yi masa a rayuwa ba tun yana jariri, amma ko gaisuwa ba ta isa ya yi mata ba. Musamman da ta lura ba abin da ya taba shiga tsakaninsu. Tana tsoratar da ita akul ta shiga turakarsa ko ta bari ya shigo dakinta ba mutumin kirki ba ne. Da ya samu abin da yake so wulakantata zai yi, ita ma haka ta ke hakuri da ubansa.

In za ta fita kuma ta ce ta auna mata sukuri ko shinkafa nata ya kare bayan  tana aika mata abinci sau uku a rana. Wataran ta ce, “Kina gani ko garar nan da aka kawo ki da ita ba a ware min nawa ba, saboda ba a dauke ni a bakin komai ba. Kullum sai ta tuhume ta ko Ma’arouf ya zo inda ta ke ta ce, “A’ah.”

Aisha ta zauna tana tunani a karan kanta, me ye matsalar matar nan ne da irin zaman da nake yi da mijina? In ba mutumin kirki ba ne Baba ba zai aura min shi ba. Ba ta taba fadar alheri ba a kansu shi da mahaifinsa alhalin tana matsayin matarsa. Tana tunanin ba ni da nawa tunanin ne ko ba ni da hankali ne?

Ranar da Allah ya tashi kama Inna Luba wata litinin ce.

Ma’arouf ya yi sammakon tafiya wajen aiki. Har ya je makaranta ya tuna bai barwa Aisha kudin cefane ba. Haka ya juyo ya dawo duk da akwai ‘yar tazara daga makarantar da yake koyarwa zuwa gidansu.

Ya sako kai ke nan ita kuma tana kokarin fitowa daga sassan rungume da kwarya cike da shinkafa, ledar maggi, galan din mankuli da sukari leda guda, suka gabza karo kayan hannunta da wanda ta dora aka suka watse a kasa. Ta kasa tattarawa ta shiga ‘yan mutsu-mutsu na rashin gaskiya, gabadaya ta daburce don ya kalle ta ne da wannan fuskar tashi ta (seriousness) wadda ba alamun wasa ko sanayya a ciki.

Jiki na rawa ta ke so ya ba ta hanya ta yi ta kanta, shi kuma ya ki, sai da ya tabbatar ya gama ladabtar da ita da idanunsa masu sheki (oily eyes) sannan ya ba ta hanyar. A fusace ya danna kai dakin amaryar tasa.

Aisha ta sha wankan safenta, ta ci ado da atamfarta mai barewa, kan nan ya sha kitso yiri-yiri, ta yi daurinta (simple) da dankwalin atamfar, jelunan kitso sun zubo a dokin wuyanta da rediyo a hannunta tana ta murdo tashoshi ta ga mutum tsaye a kanta.

Da sauri ta dago, sai idonta cikin nasa. Nasa cikin nata. Wannan saurayin ne mai karatun jarida, wanda ya dade yana farautar zuciyarta kwana da kwanaki, wata da watanni…!

Da ma an ce kowa ya bi iyaye zai ga da kyau a rayuwa. Haka Babanta yake gaya mata kullum.

“Ki bi ni, da zabin da na yi miki, ba za ki yi da na sani ba”.

Ta tuna kalaman Babanta na karshe lokacin da za a taho da ita gidan miji.

A nasa bangaren kujera ya laluba ya zauna, don kafafunsa sun gaza daukarsa.

“Baba na fi-sauran babanni ne, what an amazing father Allah blessed me with!!! Tsarki ya tabbata ga Ubangijin da ya yi mana umarni da mu yi wa iyayenmu biyayya.

Ya ga idan bai yi magana ba, zai zama ba namiji ba, su taru su zama matan shi da ita. Hannun damansa ya mika mata yana gayyatarta musabaha.

“Sunana Ma’arouf… ina nufin Ma’arouf Habibu Ji-qas, cikakken sunan ke nan, ko ya sunan Malamar?”

Shi kansa ya yi mamakin sautin da ya yi amfani da shi wajen yin wadannan kalaman. Shi ne mafi kankanta da sirantar sauti da Allah ya halicce shi da shi.

Kanta ta sanya a tsakanin cinyoyinta tana wani irin murmushi, ta kasa ba shi hannun, har ya gaji ya maida abinsa aljihun farar shaddar da ke jikinsa.

“To da alama abotar tamu ba za ta yiwu ba, tunda malamar rowar muryarta ta ke min. Bari in koma makaranta, da ma kudin cefane ne na mance ban ajiye ba. Ga su”.

Ya ciro daga aljihunsa ya mika mata. Har yanzu ta kasa dagowa ta karba.

Ya karasa gabanta ya ajiye mata, “Tattara kayan da ta zubar a tsakar gida ki kai mata, sai dai ina rokonki ba umarni ba, wannan ya zamo mu’amala ta karshe da za ta kara shiga tsakaninku.”

Cikin nutsuwa ya juya ya fita, ya koma wajen aikinsa.

Hatta dalibansa sun lura yau Malam Ma’arouf yana cikin farin ciki. Wata koyarwa yake yi musu cike da nishadi wanda ba su taba gani a tare da shi ba.

Ana tashi ba inda ya tsaya sai gida, ya tarar ta gyara tsakar gidan tas ta shige uwardaka ta kure karatun alkur’ani mai tsarki a rediyo. Ta turare gidan da turaren wuta mai dadin kamshi. Wanka ya fara yo wa ya yi alwala ya nufi masallaci. Da ya dawo ya tarar ta shirya masa abinci, amma yau ba ta ajiye a kofar daki ba ta shigar masa da shi ciki. Ya yi murmushi, a ransa ya ce, “An samu ci gaba ke nan.”

Ya ci abincinsa ya yi kat! Ta iya girki sosai. Yau ba fita kofar gida karatun jarida. Kananan kaya ya sanya, ya fito a gogaggen dan bokonsa. Kansa ba hula, babu tarin suma, kuma bai dade da yin saisaye ba. A very smart guy.

Ga turare ya fesa mai dadin kamshi, ya nufi dakin matarsa.

Zaune kawai ta ke tana sauraron karatun da ta kunna, da alama bi ta ke a zuciyarta. Jin zuciyarta ta ke kamar an yi mata rahma ga dukkan zunubanta. In ba ta gode wa Allah ba me za ta yi? Ba ta ankara da shigowarsa ba, sai da ya kai hannu ya kashe rediyon. Wani irin shiruu! Ya ziyarci dakin, idonta yana lumshe ne don haka ta bude su don a tunaninta kaset din ya kare ne, suka sake yin arba da juna a karo na biyu.

Zama ya yi a kusa da ita har kafadunsu na gugar na juna. Aisha ta samu kanta cikin wani sabon yanayi, ga ba wurin gudu. Sauran abinda ya biyo baya ba zai taba gogewa a tarihin rayuwarsa ba. Kullum yana tunawa, tunanin na kara masa sonta da kaunarta. The first life-partner ever, yet the best! The very best!!!

<< Sanadin Kenan 9Sanadin Kenan 11 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×