Yau asabar 9/9 ita ce ranar zabe. An tafka zabe, kowa ya fidda gwaninsa daga manyan jam’iyyun guda uku, NPC, APP da PCP. Masu magudi sun yi duk iya abin da za su iya na magudi, sun yi sun more. In banda ‘Sai Ji-kas, wallahi sai Ji-kas, insha Allahu sai Ji-kas’ ba ka jin komai daga bakin matasa, sai fastocinsa da ake ta rabawa ana lillikawa a ko’ina. Hakan ce ke faruwa a kowanne yanki (ward) da kowacce karamar hukuma local government na Bauchi guda ashirin da biyu.
Can na gano Ilyan Goggo ya jefa wa Ji-kas kuri’a, Dr. Turaki da matarsa, Amina da Goggonta da Inna Zulai duk Ilya ya tattago su sun zo zabe sun jefa wa (NPC). Amina na ta mitar Ilya ya sa ta sha rana babu gaira babu dalili. Ya dauko naira dari biyar ya ba ta.
“Ungo ki sha lemo mai sanyi ki jika makogaronki, ni ai kun yi min komai tunda kun kada wa masoyina kuri’a.”
Ta wafce 500 din, ta ce, “Wallahi ta zo kenan ba zan ba ka ba, Mirinda biyu zan sha mai sanyi. Na gaji da kunun Aya. Mu yi maza Goggo, wallahi ina da aiki yau a gida, tunda yau da gobe kadai nake (free), zan yi bitar wasu littattafai.”
Goggo ta kyabe baki, “Haka dai, nan aka fi kauri.”
Ba ta tanka ba, don ta san me Goggo ta ke nufi. A ganinta (at 25) tana da sauran lokaci da Goggo za ta damu kanta. Sai ga likita Umar Bolori shi ma ya je ya jefa wa Ji-kas tare da matarsa, kannensa maza da mata Alhaji Mansur da iyalinsa kaf ba a barsu a baya ba. Matasa da talakawan gari kuwa maza da mata duk sun tafi suna ta jefa wa NPC.
A daren wannan rana aka tabbatar da Engnr. Ma’arouf Habibu Ji-kas a matsayin wanda ya lashe kujerar gwamnatin jihar Bauchi. Sai addu’a ake da fatan alherin Allah ya taya shi riqo, ya kama hannunsa Ya fidda shi kunyar al’ummar jihar Bauchi wadanda suka tsaya karkarshin ranar nan da kishirwa da yunwa suka zabo shi don ya shugabance su, sabida kyakkyawar shaidar da suka yi masa.
A lokacin da aka fadi sakamakon zaben kansa na kasa, ya yi sujjada a Maqama Ibrahima. Ji ya yi kansa ya yi wani irin nauyi, at the same time gabansa ya fadi. Irin yanayin da ya tsinci kansa a lokacin da aka tabbatar masa da ya haye kujerar dan majalisar tarayya mai wakiltar Bauchi North. Nauyin dubun-dubbatar al’umma ba abu ne mai sauki ba.
Sai da ya koma inda ya yi masauki (hilton), ya yi shirin kwanciya bacci, sannan ya kunna wayoyinsa guda uku.
Sakonni ba adadi, har ya rasa na wanda zai bude. Sai ya ce akwai na iyaye, bari in fara da su, throughout yau ban gaisa da su ba.
Na Baba ya fara budewa, “Wallahu galibun alaa amrihi… Ka ce alhamdu lillahi har sau uku. It is done. You are the elected governor.”
Yadda Baba ya fada haka ya yi, wani farin ciki ya lullube zuciyarsa. Mulki zuma!
Sai ya bude na Hajiya,
“Mun ji abin alkhairi, Amina kanta ta yi murna, na gaya mata babanta ya zama Gwamna. Allah ya taya ka riko, Ya kare ka a duk inda ka shiga, Ya kauda idon makiya da mahassada a kanka.”
“Amin Hajiya ta. Allah ya bar min ke”
Abin da ya tura mata kenan.
Ya kira Baba suka shiga hira, Baba na ba shi labarin yadda gumurzun zaben ya gudana da ruwan masoyan da Allah ya ba shi. Ya kare da cewa,
“Bana jin ka Ma’arouf, amma ka san mutanen da za ka dora a karkashinka”
Sai na wata wai ita Laila, kwata-kwata ya manta da ita, sai yanzu ya tuna ashe fa yana da mata. A wurinsa duk wanda ba zai ji kan Amina ba, ya tausaya mata ba masoyinsa ba ne. Amma ita wannan ya zai yi da ita? Ta zame masa dole.
Ya bude sakon nata a nitse.
“Duk da na san fushi ka ke da ni, ina yi mana congratulation. Ka dawo da Amina zan kula da ita wallahi”.
Ya amsa da gajeren sako.
“Thank you”
A zuciyarsa ya ce, “Ta baya ta rago. Da ban san badininki ba ne”.
Haka ya yi ta bin ‘yan uwa da abokan arziki yana amsa wayoyinsu da sakonninsu, babu nuna kosawa ko girman kai. Har ya zo kan na Dr. Usman.
“Monday din nan zan yi wa Dr. Amina magana insha Allah. Heartiest congratulation”.
Ya sauka a filin jirgin sama daga kasar Saudi lafiya. Jama’a jingim suka zo tarensa, suka isar da shi har gidansa na Bauchi. Laila ba ta san da zuwansa ba, ta cika gidan da kawayenta ana taya ta murna, kuma kowacce tana fadin abin da ta ke so Lailan ta yi mata da sun shiga ofis.
A haka ya tarar da su sun cika masa falo. Ji ya yi kamar ya fatattake su, sai ya tuna shi din fa dan siyasa ne, ba shi da wannan damar. Suka gaisa sama-sama ya wuce.
Laila ta tsallake su ta bi shi. Ita ba ta san dukkansu daga masu auren har marasa auren kishinta suke yi ba. Wannan ‘handsome governor’ ita ke da shi, ita kadai ranta, sannan gidan gwamnati za ta koma nan ma ita kadai. Hassada da bakin ciki duk ya lullube su.
Ga shi kuma tunda ta bi shi daki ta manta da su, ba su gama alkawarirrikan mukaman da za ta nema musu wajen maigirmaGwamnan ba. Da suka gaji da zama dole suka tattara suka tafi cike da bacin rai.
A can (master bedroom) din Ma’arouf hakuri Lailan ta zube tana ba shi a kan kasa kulawa da Amina da ta yi. Ajizanci ne irin na dan Adam, amma ba don ba ta son Amina ba. Abinka da mace da mijinta, dole ya sauko ya karbi tuban nata, ko ba komai yana bukatarta a lokacin tunda ba shi da wata matar sai ita, girman kai ba nasa ba ne. Amma ba don zuciyarsa ta yarda da ita 100% ba ko ya manta da girman abinda tayi masa.. Tana nan dai a matsayin matarsa amma ba aminiya ba, wadda zai dauki amanar gidansa ya baiwa, ko ya yi (sharing) wani abu muhimmi daga (personal life) dinsa da ita ba.
Laila ta kasa bari ko tsarkake jikinsu su yi, ta soma fada masa abin da ke cinta a zuci. Wato tana so ya ba ta shugabar ‘family support programme’ da za ta bude don ci gaban mata.
Dariya ta kama shi, ya yi abarsa sosai, “Da dai kin tsaya kin yi karatun yadda ya kamata ne, amma yanzu ba ki da maraba da dan sakandire tunda ko takardar tsire ba ki da ita.”
Laila ta kulu, ta sanshi da yaba magana a gare ta in ta yi masa ba daidai ba, amma ta yau ta fi kowacce yi mata zafi. Ta kuma rantse sai ya ba ta wannan mukamin in dai maganin mata na aiki kamar yadda su Nazi suka zuzzuga ta.
*****
Dr. Amina Mas’ud tana (ward round) ranar litinin da safe aka aiko wata nurse ta gaya mata Dr. Turaki na nemanta in ta gama abin da ta ke yi. Ta amsa da, “Toh”, ta ci gaba da duba marassa lafiyanta har ta gama, sannan ta nufi ofishin (consultant) din nasu. Zuciyar ta cike da tunanin ko menene dalilin kiran kasancewar bai cika yin hakan ba in ba da dalili mai muhimmanci ba.
Da sallama ta bude kofar, ya amsa, “Have a seat please”. Ya fada yana mai nuna mata kujerar dake fuskantarsa.
Amina ta zauna sannan ta gaishe shi. Ya amsa cikin sakin fuska ya dora da fadin.
“Dr. Amina, na san kin san Engnr. Ma’arouf Ji-kas ba sai na gabatar da shi a gare ki ba”
Amina ta gyada kai.
“Na sanshi a bakin Yayana Ilya, da kafafen sadarwa. Saboda son da Yayana Ilya ke masa sai da ya tattage mu muka je muka sanya masa kuri’a har da Goggo.
An shaide shi da cewa, mutumin kirki ne, that’s all i know about him, bayan wannan ban san komai da ya dangance shi ba Dr”
“Da kyau, kin taba sanin yana da (paralysed daughter) mai shekaru biyar?”
“Gaskiya ban sani ba, don ban san personal life dinsa ba. May be Ilya ya sani sabida shige-shigensa a kansa.”
Ya yi murmushi,
“To shi ne yake neman wani taimako daga gare ki, kodayake ta wani fannin ba za a kira shi taimako ba, tunda abu ne da ba kyauta za ki yi shi ba. You are on your profession, yana so ki koma gidansa da zama ki ci gaba da bawa yarinyarsa ‘treatment’ zuwa shekara daya mu ga abinda Allah zai yi. Kin san dai yadda Paralysis yake ba abu ne da za a ce yau ko gobe an tashi ba, tunda warkewarsa ba shi da kayyadadden lokaci.
Ya yi alkawarin ninka miki albashin da gwamnati ke biyanki sau hudu a kowanne wata. Duk ‘weekend’ za ki tafi gida ki dawo ‘monday’ ko Lahadi da yamma. Na yarda da kwarewarki a kan aikinki da sadaukarwa shi ya sa na zabo ki cikin dubu. A ganina wannan wata hanyar samun alkhairi ce mai dimbin yawa gare ki da iyayenki. Amma za mu ba ki lokaci ki yi tunani, ki kuma nemi amincewar iyayenki ko ya ki ka gani?”
Amina ta nisa, tunda ya fara magana ba ta katse shi ba. Lallai ilimi mai zurfi ya yi a rayuwa. Albashi sau hudun nawa ashe ba da jimawa ba burina zai cika a kan Goggona? Allah ya sa ta amince.
*****
An rantsar da shuwagabannin Najeriya a rana daya. Litinin 2/2 His Excellency Ma’arouf Habibu Ji-kas, ya shiga ofishinsa cikin nasara.
Cikin dan lokaci komai ya yi ‘settling’. Su Laila an yi hijira zuwa ‘Government House’ abin ba a cewa komai. Domin wani gammon girman kai ta dauka ta aza a wa kanta fiye da na matar shugaban kasa suka shiga ‘government house’ tare.
Danginta babu wanda ya isa ya rabe ta. Mahaifiyarta kadai ta ke wa ihsani, shi uban ta ma manta da shi. Duk sanda Ma’arouf ya ce ya kamata ta je gida ta gaida iyaye da dangi, sai ta ce masa gobe za a sauke kayan da ta yi (order) har ya gaji ya rabu da ita.