Skip to content
Part 23 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Babu inda ake bincikarsu har suka tadda ‘Mansion’ din masu gidan.

Dakinsu ta nufa kai tsaye da kejin tantabarunta a hannu. Ba ya dakin sai Ameena. Tana ganinta fuskarta ta yalwata, ta ce, “Mama?”

Amina ta aje kejin a kan tebir ta karasa ta tayar da ita zaune, ta dora ta a cinyoyinta ta rungume ta. Sai kuma ta sunkuce ta sai bandaki, ta wanke ta tas! Ta yi mata duk abin da ta saba yi mata ta fito da ita. Tana yi mata messaging’ ya murda kofar, sannan ya yi sallama ciki-ciki. Ta amsa ba tare da ta juyo ba, ko ya zauna ko bai zauna ba? Ita dai ba ta sani ba, ta ci gaba da abin da ta ke yi. Sai ta ji ya ce, “Ki yi hakuri, na sa an dauko ki da wuri, wasu abubuwan na kasa ne”

Ta yi murmushi, “Babu damuwa. An ba ta magungunanta na safe?”

“Na manta ban ba ta ba, rashinki a gidan ya dan maida ni upset, ga su ki ba ta”

Ya mika mata ledar magungunan. Ta karba ba tare da ta juyo ba.

“Amma ka ga lokacin shan ya wuce ko? Ba haka muka yi da kai ba kafin in bar maka amanar Amina ba.”

Ya yi murmushi, ganin yadda ta ke maganar kamar mai yi wa kaninta fada, ba karamin jin dadin maganganunta ya yi ba masu nuna kulawarta a kan Ameena, don haka da sauri ya ce, “Allah ya huci zuciyar Dr. Amina. Amma ina yin kokari fa, da wanne zan ji? Ni ne ‘messagin’, ni ne ba da abinci, ni ne amsa tambayoyin Amina a kan ina ki ka je, ni ne wanka da canza ‘pampers’, sannan gidan ya zama wani irin ‘incomplete’, Dr. Amina kin shaci fili cikin rayuwarmu da yawa. Ko mene ne sirrin?”

Da sauri ta juya ta dube shi, don ta tabbatarwa kanta da gaske da Ma’arouf Ji-Kas ta ke magana ko waninsa? Da gaske fuskar da ta karade fastoci da akwatunan talabijin ce, wani kyakkyawan magidanci dan hutu da jini a jika, kyau da kwalisarshi a fili, har sun so su yi masa yawa. Ba ta da amsar tambayarsa, abin da ta sani kawai shi ne ba zai taba iya yin abin da mace za ta iya ba, kuma ya ce ya ji ya gani ya daukar wa kansa, saboda matarsa shafaffiya da mai ce.

Anya musulma ce mai zuciyar imani? Tausayin Ameena ya kara kamata. Ta kara jin son Goggonta, tana rokon Allah cikin zuciyarta ya bar mata ita. Maraici babban abu ne balle ga karamin yaro. Shi kuwa me ya yi masa zafi da dole sai ya zauna da matarsa? Bai yi kama da ragwayen maza ba, dole akwai wani boyayyen al’amari cikin auren nasa.

Amina ta nisa, “Ga tantabarun Ameena na kawo as promised.”

Ta nuna kejin da ke gefe da dan alinta, ta guje wa waccan tambayar da ya yi mata kenan, don ba ta da amsarta. Ya karasa ya tsugunna yana dubawa, ya dauki aure daya farare kal ya dora a cinyarsa.

“Beautiful, Ameena ta gode saura na Babanta”

Dr. Amina ta dan ciji lebe, “gaskiya BABAN ya yi hakuri.”

“Na yi hakuri da account number, ban kara tambaya ba. Amma wannan ina so lalla, kuma rabin gabadayansu za ki ba ni daki zan yi musu. Ko saboda ni ba abin tausayi ba ne sai Ameena shi ya sa komai na roke ki ba za ki ba ni ba? Shin akwai abin tausayi a duniya ma irina?”

Amina ta juyo ta kalle shi, a kan ‘resting chair’ yake a zaune, kafarsa daya kan daya. Sosai ta ga ya zame mata abin tausayin a fannin da ba ta sani ba, Sai ta ji zuciyarta ta karye.

“Kana da mita.”

“Kina da tsiwa.”

Ta yi dariya har fararen hakoranta suka fito. Lokaci daya ta ji ba Tantabaru ba, za ta iya mallaka masa duk abin da ta mallaka in har zai sa shi farin ciki. Muryarta ta yi kasa sosai a sanda ta ke cewa.

“Wane bayani zan yi wa Goggo cewa zn kyautar maka da rabin abin da na gada daga mahaifina, na rene su shekaru goma sha biyar, ban taba bai wa kowa ba? A matsayinka na wa a gare ni?”

Murmushi ya yi, ya mike tsaye, “Matsayin da ki ka ba ni shi za ki gaya mata. Well, ban san matsayin da ki ka ba nin ba. Ni ban boye ba already na gaya miki, kin shaci fili mai fadi a rayuwarmu ni da Ameena cikin dan lokaci kalilan”. Da wannan ya karasa ficewa daga dakin.

Amina ta yi dan jim! Na sakanni, sai kuma ta watsar da tunanin ta ci gaba da abin da ta ke yi. Ba ta son tunanin maganganunsa da tasirinsu ya yi ‘distracting’ dinta. Kai ita ba barin komai ya shiga cikin aikinta. Amma Baban Ameena na son ya kara kansa cikin ayyukanta, wanda ita ba ta shirya wa hakan ba.

Misalin karfe takwas na daren ranar, suna zaune a falo shi da Laila, ta ci ado ta kashe dauri kamar mai shirin zuwa gasar sarauniyar kyau. Tana rike da tambulan na gilishi mai garai-garai cike da tataccen inibi mai sanyi, tana kurba a hankali. Kowannensu da abin da yake yi kamar ba ma’aurata ba, ita kallon talabijin ta ke yi, inda ake nuna ayyukan mijinnata a kananan hukumomi, wani alfahari na kara shigarta. Shi kuwa na’ura mai kwakwalwa ce da takardu fal a gabansa yaan duba tsare-tsaen ‘udget’ na shekarar da ma’aikatar kasafi da tsare-tsare (ministry of budget and planning) ta gwamnatinsa ta tsara, ta fitar ta damka masa don ya sa hannu. yana dubawaanutse yana gyare-gyare kafin ya sa hannun.

Yadago ya dubi Laila, wadda tunda ta dawo ba ta tambaye shi ina Ameena ba ko ya ya jikinta?

Haushi ya kama shi ganin yadda ta wani cokali dauri a gaban goshi, bakin nan ya sha jambaki jajawur ram! Jagira har kusa da kunne. Ya sha gaya mata ba ya son ganin ‘artificial beauty, bai saba ganinsa a Aisha Maman Ameena ba, in don shi ta ke yi ba ya so. Tsaki ya sak, har sai da ya shiga kunnenta, ta dauko kanta daga akwatun talabijin ta dube shi.

“Ya ya dai?”

Ya hadiye haushinsa.

“Me ya sa ba kya gaisawa da Physiotherapist mai kula da Ameena?”

Ba ta ce komai ba, ya ci gaba da cewa, “Sunanta Dr. Amina, suna zaune a dakunan ‘downstairs’ na ‘apartment’ din nan, amma kamar ba ki san da su ba a gidan nan.

Na hore ki da gaisuwar mutunci tsakaninku, ban yarda da ko kallon banza ba balle a kai ga magana mara dadi. Zaman Ameena ta ke kadai, ba na wani ba.”

Laila ta cuno baki.

“A kan me zan gaishe ta? Ta fiya girman kai, ba ta taba nemana a gidan nan ta gaishe ni ba sai ni zan zubar da girmana in dinga zuwa inda ta ke?”

Ya yi mata shiru ya kyale ta, ya ci gaba da abin da yake yi.

*****

Wannan satin da Amina ta zo gida, Goggo ta lura da ta faya shiru-shiru, ita kuma ba abin da ke damunta kamar ta inda za ta dauko wa Goggo zancen Tantabaru, ga shi ba za ta iya kin ba da su ga Baban Ameena ba a kan dalilai masu yawa wadanda ta sani da wadanda ba ta sani ba. Duk da ta san za ta kasance cikin kewa mai yawa idan ta bada rabin tantabarun nan. Amma abin mamaki zuciyarta ta ki zama lafiya idan ba ta bada su ga Gwamna Ji-kas ba. Kuma ba a kan ko sisi ba.

Da yamma tana dakin Goggo da manyan littattafanta a gabanta tana nazari, amma da aka dan jima sai ta rufe su ta ture su gefe, ta zuba uban tagumi.

Goggo ta shigo ta ganta a haka, ta karasa bakin gado ta zauna, yayin da Amina na zaune a kan kilishi ne har Goggo ta zauna ba ta ganta ba, sai da ta kai hannu ta taba ta. Ta juyo firgigit ta dubi Goggo.

“Me ke damunki ne Amina? Tunda ki ka zo wannan satin nake ganinki cikin damuwa. Wannan uban tagumi na magani da mene ne?”

Amina ta ga cewa, dole ne ta gaya wa Goggo tunda dai ba za ta dauki tantabarun nan ba tare da saninta ba. Sai dai ba ta san ya ya Goggo za ta karbi maganar ba, kada ta yi wani tunanin ‘otherwice’. Duk da haka dai ta daure ta ce.

“Goggo, wai Baban Ameena ne ya ce na ba shi rabin tantabaruna.”

Goggo ta dan yi shiru, “Me zai yi da su? Wace irin hira ku ke yi tare da har ki ka yi masa maganar tantabaru? Me ya hada ku ban da aikin ‘yarsa?”

Ta bi ta tsattare ta da ido, sai da Amina ta daburce.

“Ba abin da ya hada mu Goggo, amma kullum kafin ya fita office da bayan ya dawo sai ya shigo ya ga lafiyar ‘yarsa, in har yana gari. Farkon zuwana gidan ko kallona ba ya yi, ko inda nake ba ya kallo. Ko magana za mu yi a kan lafiyar yarinyar ba ya kallona, ni ma bana kallonsa muke yi. Sau uku Hajiyarsa ta zo ita ta sanya muka fara magana da juna, don cewa ta yi ya yi wa matarsa fada ta dinga zuwa inda nake muna gaisawa tana ganin lafiyar Ameena, to matar ta ki mu gaisa, ta kuma ki zuwa ganin Ameenar. Daga lokacin ne ya soma yi min ‘yan tambayoyi a kan rayuwa ta ina ba shi amsa. Rannan ya ce in dawo da wuri ranar lahadi, na ce masa ba zai yiwu ba don ina kiwo, ya tambaye ni na me ye na fada masa, sai ya ce zai saya wa Ameena aure biyu na dauka na ba shi. Wannan satin kuma gabadaya rabi ya ce in ba shi.”

Goggo da ta tsura mata ido ta nisa, ta ce, “Ni dai ina kara gargadinki da tsare mutunci a ko’ina. ba ni da mummunan tunani a kanshi, a kwashe a ba shi, ai hayayyafa suke.”

Amina ta ji kamar an sauke mata Dala da Goron Dutse daga kanta. Ta ce, “To Goggo, zan gaya masa kin amince ya turo a kwashe.”

Rana ta farko da Amina ta yi tunanin buga wa Ma’arouf waya a rayuwarta. Sai dai wani barin na zuciyarta na hana ta. Amma barin a yi kiran ya rinjayi na kada a yi kiran.

Yana tura Ameena cikin wheel-chair a wata farfajiya da ke cikin gidan ya ji kira daga wayarsa da ya kunna yanzu-yanzun nan. Ya yi magana da Turaki, ya manta bai sake kashewa ba ya sanya a aljihu. ‘Sunan da ya ba wa lambar Amina’s Doc’ ya bayyana a fuskar wayar. Ya amsa ba tare da ya ce komai ba.

Da dai ta fuskanci ya amsa, sai ta fadi sakonta kai tsaye, “Goggo ta amince a zo a kwashi Tantabarun.”

Murmushi ya yi mai sauti, “Babu gaisuwa sai sako kai tsaye?”

Amina ta yi shiru, jikinta har rawa yake yi don wani tsoro-tsoronsa ma ta ke ji byan ganin kima da girmansa. Maimakon ta yi gaisuwar sai bakinta ya subuce da fadin abin da ke zuciyarta.

“Ina Ameena? Ya ya ta ke? An yi ‘messaging’ din yamma? An fito da ita shan iska?”

Ya dan russanar da ‘gazing’ dinsa kan Ameenar da ke cikin wheel-chair, a zuciyarsa ya ce, ‘Ameena kina da wadda ta damu da lafiyarki, bayan ni da Hajiya. How I wish Laila ce haka! Da tsarukan da na yi wa rayuwa ta ba su soma kokarin rushewa ba…’

Ya lumshe ido ya bude, bai ce komai ba. Sai ya kara wa Ameenar wayar a kunnenta.

“Ameena ga Mama”

Ameena ta fada da iyakacin karfinta, “Mama, yaushe za ki dawo? I’m missing you… I prefer your messaging than Daddy’s…(Ina kewarki, na fi son tausarki a kan ta Daddy).”

Dr. Amina ta yi murmushi, “Kin manta na ce kullum na tafi ki kirga kwana sau uku zan dawo?”

“Na kirga, yau ne ko?”

Amina ta ce, “That’s my girl, I’m coming soon.”

Ya dage wayar ya mayar kunnensa, “Za a zo da wata motar daban a dauka, na gode Dr. Amina tunda an ce ba na sayarwa ba ne. Duk abubuwan da ki ka tambaya an yi su. Ki gaida ILYAS!” Ya kashe wayarsa.

Amina ta zaro ido, “ILYA? A ina ya sanshi?”

Ta ajiye wayarta a gefe cike da mamaki. ta fito da gudu tsakar gida, ilya ba ya nan sai Talatu tana hada zobo, “Talatu ina Ilya?”

Talatu ta ce, “Kaf yau bai shigo ba, ya je karbar balance.”

Ba ta rufe baki ba ta ji alamar shigowar sako a wayarta. Ta koma ta zauna ta bude. Abin da ta gani ya ba ta mamaki, (alert) ne daga banki na zunzurutun kudin da ba za ta iya fadar adadinsu a fatar bakinta ba. Ta dauko calculator ta hau lissafi. Ga dai albashinta kamar yadda aka yi alkawari sau hudunshi a kowanne wata, har watanni biyar. Ga kuma wasu makudan wadanda daban suka shigo daga account din wani mai suna Usman Turaki.

Amina ta tabbata Dr. Turaki ne, Ma’arouf ya turo kudin daga account dinsa. To shi Turakin wa ya ba shi? Da sauri ta danna masa kira.

Kwamishinan yana gida cikin iyalinsa, yau lahadi. Ya amsa kiran Amina.

“Ya ya dai Dr. Amina?” Ya fada cikin kulawa.

Amina ta hau in-ina, “Umh—um da ma na ga alert ne.”

Ya yi murmushi, “Ta inda aka hau ba ta nan ake sauka ba?”

Amina ta yi murmushi jin da muryar da ya yi maganar kamar mai yi da karamin yaro. Tana so ta ce, ‘to daya alert din fa? Ba ta san cewa a fili ta fada ba.

“Na Tantabaru ne”. Ya fada cikin murmushi.

Ta karyar da murya, “Wallahi ni ba siyar masa na yi ba, kuma na gaya masa.”

“Ya ce idan ba ki karba ba ki nar tantabarunki.”

Ta yi hanzarin cewa, “Na karba”. Sanin cewa dukkaninsu babu sa’an ja’in’jarta. Magana daya ta makale mata a makogaro, ta kasa yo waje da ita. Wato, ‘a ina suka samu account number dinta?’

“Kada ki tsaurara bincike…” Ya fada tare da karashew cikin dariya, “Insha Allahu SANADIN KENAN da dukkaninku za ku amfana da juna, har hakan ya haifar da alkhairi. Ke dai ki ci gaba da kokari, muna yaba kokarinki a kan Ameena. Allah ya saka da alkhairi.”

Kan Amina ya dau zafi, ta kasa warware komai a maganganun Turaki. SANADIN me? Ita fa ba ta sa wa kwakwalwarta abin da ta gagara fahimta balle har ya dame ta. Su suka sani iyayen daure wa mutum kai.

<< Sanadin Kenan 22Sanadin Kenan 24 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×