Skip to content
Part 32 of 50 in the Series Sanadin Kenan by Sumayyah Abdulkadir (Takori)

Sun mori honey moon na tsayin kwana bakwai yadda ya kamata a wannan hotel wanda babu na biyunshi a Nigeria. Sun kara fahimtar juna, so da kaunar junansu ya kara habaka da shaharar da a da bai yi ba. Sun dinke zukatan junansu cikin na juna sun zama daya. Kowanne ya shiga tababar yadda zai rayu, rayuwa mai inganci ba tare da dan uwansa ba.

A Transcorp suka ajiye tarihin. A can suka baro shi kamar kar su baro, Ma’arouf Ji-kas ya yarda Allah ya sako Amina cikin rayuwarsa sanadin tashi Ameenar don ta gyara ta, ta maye mashi gurbin Aisha, ta kara farin ciki a rayuwarsa. Ta wanke bakin cikin Laila Ji-kas da yake kwana yana tashi da shi. Ta kawo sauyi mai albarka daga rayuwar da ya tsinci kansa a ciki tun bayan gushewar Aisha. Ita din ALHERI ce, kuma AMANA a gare shi (sunan wasu littattafan Takori).

Isowarsu gida ke da wuya tun kafin su isa dakin barcinsu wani mai share-share ya sanar da Ogan nasa, Anty Laila ta dawo.

Fuskarsa ba ta sauya ba, haka komai nasa bai canza ba. Amma Dr. Amina ta ji faduwar gaba matuka. Sai jin tausasan yatsun Ma’arouf ta yi cikin nata, ya rike ta gam ya ja ta sun fara taka matattakalar upstairs tare.

Laila na zaune cikin daya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon, ta dora kafa daya kan daya ta harde, ta ci ado da kayan Larabawa har ta gaji. Remote din talabijin ne a hannunta tana sauya tasoshi. Ta dago kai a yangace kamar yadda yake a al’adarta ta dubi masu shigowa.

Sosai ta saki baki tana kallonsu, Ma’arouf ba za ta taba kama macen da ba tashi ba, Wannan na nufin likitar Ameena wannan ‘yar rainin hankalin ya aura? An tabbatar mata Ma’arouf ya yi aure tana Saudiyyah, amma ba ta taba kawo Amina ba ce. Ta dauka iyakarta kenan sun rabu tunda Ameena ta warke.

Har suka zauna a kujera guda hannunsu na cikin na juna, Amina dai a tsorace ta ke ganin kallon kura ta ga nama da Laila ke mata. ta kawo karfin zuciya ta sanya wa ranta tana murmushi, ta ce, “Anty Laila, ina wuni? An dawo lafiya?”

Shiru ta yi mata ba ta amsa ba, har yanzu ba ta dauke ido a kansu ba, irin kallon nan na kun ci AMANATA.

“Wuce dakinki Amina ki huta, zan yi magana da ita.”

Amina ta mike ta nufi dakin nata. Ba ta kai ga isa ba ta ji an shako ta ta baya, an yi mata wani wawan naushi a wuya, an maka mata wani irin abu a tsakar kanta da ya fi kama da kofin gilashi. Ta yi gaba luuu! Ta fadi a kofar dakin nata, tana jin sanda Ma’arouf ya yi magana da karfin gaske da iyakacin sautinsa, ya ce, “Lailaaa! Kina hauka ne? Wallahi in ta mutu a bakin aurenki.”

Ya yi kokarin buga waya don kiran likita, amma ya aksa. Hannunsa sai rawa yake yi, haka jikinsa. Ita kanta Laila ta tsorata da ganin yawan jinin Amina da ke malala a kasa daga tsakiyar kanta, sai mazari ta ke yi. Ya samu ya lalubo lambar Dr. Isma’el personal doctor dinsa shi ma nasa jikin mazarin yake yi don kuwa Laila ta shammace shi, “Ka zo maza-maza har upstairs Isma’el…”

Babu tambayar ba’asi Dr. Isma’el ya amsa da, “Ga ni nan”. Kafin ya iso ya ciccibi Amina ya kwantar a doguwar kujerar falon bai damu da jinin da ya bi ya ba ta masa jiki ba. Ya soma yi mata firfita da babbar rigarsa da ya cire babu alamun numfashi a tare da ita. Bai kara bi ta kan Laila ba wadda ke tsaye a kansa tana kuka.

“Allah ya sa ban yi kisa ba zuciya ce, na shiga uku Ma’arouf ka yafe ni…”

Ko kallonta bai yi ba, firfita kawai yake wa Amina idanunsa sun kada sun yi jazur. A haka likitan ya iske su, bayan Ma’arouf ya ba da umarnin a shigo da shi.

Da kayan aikinsa yake tafe don haka a take ya fara bai wa Amina taimakon gaggawa, har ta farfado. Ya yi dressing din wajen da ke fidda jinin ya tsayar da gudunsa ya rufe da plasta. Ya dubi Ma’arouf da Laila mai kuka kashirban, Ma’arouf din ya ki ko kallonta hankalinsa da kulawarsa duk suna kan Amina da ke kwance ido rufe. Nan ya gano bakin zaren, ya dubi Ma’arouf ya ce, “Garin ya ya? Ya ya haka your Excellency? Wane ne da wannan danyen aikin? Wannan kam dole sai an je asibiti an yi hotonsa don mai yiwuwa akwai (Internal injury) da nake addu’ar Allah ya sa bai taba kwakwalwarta ba.”

Laila ta kara gigicewa, daidai da karuwar fushin Ma’arouf a kanta, ya ce da Doctor din, “Je ka ka zo da (nurses) ku tafi da ita a ba ta duk kulawar da ta dace.”

Cikin dan lokaci Dr. Isma’el ya yi waya asibitinsa, nurses biyu suka zo suka tafi da Amina. Aka barshi daga shi sai Laila a falon. Ya zauna cikin kujera ya tallabi fuskarsa da hannu bibbiyu cikin damuwa. Laila ta tsugunna a gabansa, ta kama kafafunsa tana kuka.

“Tunda ba ta mutu ba, don Allah kar ka sake ni, wallahi zuciya ce na tuba, zan zauna lafiya da ita insha Allahu.”

Bai saki fuskarsa ba har yanzu, haka fushinsa bai sauka ba. Da kyar ya yi mata magaan cikin muryar bada umarni, “Hada kayanki Akilu ya kai ki gida Ji-kas sai na neme ki.”

Laila ta rushe da kuka, “Na roke ka da Allah da manzonSa ka bar ni a dakina, in dai Amina ce na yi maka alkawarin za mu zauna lafiya.”

Zuciyarsa ta fara sanyi, sabida irin kukan da ta ke yi mai nuna nadamarta a fili. Amma ya yi rantsuwa cikin zuciyarsa sai ta je gida ko da bai sake ta ba.

“Hakuri na daya ne Laila, ki je gida sai na neme ki, amma ban sake ki ba, in kuma ki ka kara yi min musun raina zai kara baci, shiga ki tattaro kayanki.”

Ba yadda ta iya ta juya ta yi dakin nata tana share hawaye. Shi kuma ya kira Akilu a waya, “Zo maza za ka kai matar gidan nan Ji-kas.”

Ta gabansa Laila ta wuce ta yi lullubi da wadataccen mayafi, wanda a da ba ta amfani da shi sai raka-ni-gantali. Ta dube shi cikin ido da idanun neman afuwa, ya kauda kai don ba ya son ya ba wa tausayin da ke son rinjayar fushinsa dama ya yi tasiri. Wannan karon ya yi aniyar daidaita mata sahu in har tana son ci gaba da zama da shi, to dole ta bar duk abin da ba ya so ta kuma zauna lafiya da zabin ransa. Ba ita zabin iyaye ba. zaman hakurin da yake yi da ita inda tana da hankali adalci ne ya yi mata. Yaushe ta fara sonshi so na gaskiya da har ta san ta yi kishi a kansa? Kishin ma na jahilai da rashin hankali.

Bayan tafiyarta ya kasa zaune ya aksa tsaye, yana son jin halin da Amina ke ciki wayar Dr. Isma’el na kashe alamar yana bakin aiki. Shi ba abun ya fita da kansa ya je asibitin ba.

Ya daure ya shiga (master bedroom) dinsa ya yi wanka da alwala, ya yi sallah nafila ya roki Allah matsalar Amina ta zo da sauki.

Yana kan sallayar bai sauka ba bayan awa daya, sai ga kiran Dr. Isma’el. Da mugun sauri ya amsa wayar.

“Ya ya Isma’eel, is she o.k?”

“Alhamdu lillah babu internal injury, kuma an dinke inda kwalbar ta shiga. Amma ranka ya dade ya kamata a dinga kula a kuma dinga yi wa iyali punishment idan sun aikata ba daidai ba irin wannan, don dai matsalar ta cikin gida ce, amma da ba za mu barta ta tsaya a haka ba.”

“Kada ka damu Isma’el, it’s o.k, za a kiyaye za a dau mataki. Yanzu ina Aminan? Ya ya yanayin jikin nata?”

“Alhamdu lillahi, ta warware, amma za mu rike ta zuwa gobe don ta kara jin dadin jikinta.”

“Idan har an yi dinkin kasa a dawo da ita yanzu Isma’el, zan iya kula da ita. Ba zan iya nutsuwa ba ba ta kusa da ni.”

Murmushi Isma’el ya yi, “Za a kawo ta yanzu.”

Sai ga Amina da kafarta cikin falon, daidai lokacin da ya fito daga dakinsa. Karasawa ya yi da sauri inda ta ke tsaye ya rungume ta yana sakin ajiyar zuciya. Amina ta yi kwance lambam a kafadun mijinta ta runtse ido cikin jin ciwo, amma don karfin hali shi ta ke lallashi, “Daina damuwa Baban Ameena, don Allah. Na warke kuma na yafe mata. Kai ma ka yi laifi da tuntuni ba ka fada mata ba.”

“Ina na ganta Ameena? Kullum cikin gantalinta ta ke, ba ta da lokacina tunda na aure ta, sai yanzu ta san ta yi kishinta na banza a kaina? Na gaji da zama da ita wallahi na gaji. Ji na nake free yanzu, ina sonki Amina don Allah kada ki bari wani abu komai girmansa a duniyar nan ya raba mu in ba mutuwa ba…”

Da hanzari ta toshe masa baki da hannunta, wannan lokacin kowanne kokari yake ya nuna wa dan uwansa ya fi shi so da kaunar dan uwansa. Wannan ranar sun raya ta fiye da dukkan ranakunsu a Transcorp Hilton. Domin abin da Laila ta yi sai ya kara kaunar Amina a zuciyar Ma’arouf ya kara dakushe hasken Laila daga idanunsa.

*****

Yana sane ya kashe wayoyinsa tsawon kwana uku don ya san dole za a neme shi kan batun Laila. Ba ya zuwa ko’ina a kwanaki ukun nan, wakilai yake turawa. Daga (office) sai gida manne da Aminarsa. Hajiya da ta gaji da nemansa sai ta kira layin Amina, ta ce ta hada ta da shi.

Ba yadda zai yi don yana zaune a wajen. Ya karbi wayar ya soma gaida Hajiya cikin ladabi, ba ta bari sun gama gaisawar ba ta jefo masa tambayar da ta kawo ta.

“Me ya hada ki da Laila? Ta zo wajena ban barta ta karasa wajen iyayenta ba. Nayi-nayi ta gaya min me ya faru ta ki. Sai kuka ta ke tana fadin in nema mata afuwa a wajenku.”

Da ba Hajiya ba ce kashe wayarsa zai yi, amma wannan ita ce mace mai daraja ta farko a gare shi. Ya gaya mata duk abin da ya faru da irin zaman da yake yi da ita tun aurensu. Ya ce, saboda rashin kaunarta da tausayinta ga Ameena ya dauko Dr. Amina ya kawo gidan. Don haka ita ce SANADIN aurensa da Amina ko ta ina aka je aka dawo. Da ta bi yadda yake so su rayu shi da ba mai ra’ayin kara aure ba ne. To ta kwashi wasu dabi’u da halaye na kawayen banza ta daura wa kanta. Shi kam ya gama aure zai aiko mata da takardarta don ko ta ce za ta canza ba zai iya adalci tsakaninta da Amina ba, kuma Annabi (S.A.W) ya ce a zauna da daya, in ba za a iya adalci ba. A karshe ya ce, “Hajiya ki barta ta tafi gidansu, yanzu ne ta san ke mutum ce da za ta amfane ta? Ta taba zuwa har inda ki ke ta gaishe ki tunda na aure ta? Ta taba jin kan abin da na haifa? Ta taba nuna min kauna ta hakika ban da ta in na ba ta kudi? Laila ba matar zama ba ce Hajiya, don Allah kada ki takura ni in maido ta ta fita daga raina gaba daya. Ki barta ta je gida don Allah na sake ta saki daya…”

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel… Ma’arouf ni za ka bai wa aiken saki? Ka yi min adalci kenan? In don ta ni ne duk abin da ta yi min na yafe mata, na yi mata uzuri tunda ta yi nadama kuma ta kara jaddada min ba za ta sake duk abin da ba ka so ba, za kuma ta zauna da Amina lafiya. To na yafe mata duniya da lahira, ko tsoron surutu ba ka yi a ce don ka yi aure ka saki uwargidanka? Ce ne ka maida ita maza-maza tun wani bai ji ba bayan ni.”

“Sai ta ji na sake ta Hajiya wallahi sai ta ji, ba ni ita a wayar.”

Tunda ya rantse jikin Hajiya ya kara yin la’asar, ita kanta ta san halin Laila ba matar zama ba ce, ita ma dattaku ne kawai a matsayinta na uwa gyara ne nata ba bin bayan daya ba. Tunda kuma ya rantse ba za ta so shi da kaffara ba. A sanyaye ta mika wa Laila wayar wadda ke zaune gabanta dirshan tana tikar kuka, tana kuma jin duk abin da suke tattaunawa tana yarda da kuskurenta.

“Ma’arouf don Allah ka yi hakuri na tuba, na bi allah na bi ku…”

“Na sake ki saki daya. Amma alfarmar Hajiya ki zauna kada ki koma gidanku ki koyi tarbiyya a wajenta, na maida ke dakinki, amma ban yarda ki dawo ba sai bayan watanni biyu”

Muryarta na karkarwa ta ce, “Na gode, wallahi zan zauna, na yi alkawari zan zauna. Amma zan dinga shiga wani lokaci ina gaida Baba da Innata.”

“Ban hana ki ba”. Ya kashe wayar ya bai wa Amina abarta.

Watarana Amina ta taba yi masa maganar tana so ta koma aiki don ba ta iya zama waje daya ba ta komai ba.

Ya ce, “Ina! Matar Ji-kas da zuwa aiki? Ko zan amince sai ranar da ‘tenure’ dina ta kare muka bar wannan gidan muka koma gidana na Fati Mu’azu.”

Dole Amina ta hakura, ta maida hankali ga bautar aurenta, domin neman dacewa wajen Ubangiji, don a duniya kam ta gama dacewa. Alfarmar auren miji na gari irin Ma’arouf Habibu Ji-kas ba karamin dace ba ne. Ta kowanne fanni da diya mace ke buri.

Duk da an ce kowanne dan Adam tara yake bai cika goma ba, a wurinta ita nata mijin ya cika har ya wuce ya isa goma sha tara!

Bayan watanni biyu Hajiya ta dawo da Laila. Ta zama saliha irin yadda mijin ke so, kai ka ce Amina ce uwargida yadda Laila ta kwantar da kai ta ke binta suke zaman lafiya. Sai dai ita kanta ta san da gaske Aminar ta yi mata fintinkau a zuciyar Ma’arouf ko ta canza hali ko kada ta canza ba zai amfana wa Aminar komai ba, gara ma ta karbi canjin rayuwar da hannu bibbiyu.

Ameena karama ta zo hutu ta tadda Mamanta tare da Babanta a gida daya, ta kuwa hau murna ba ‘yar kadan ba, kullum tana manne da Mamanta Amina.

Shekaru biyu da auren Ma’arouf da Amina ta haifo santalelen danta mai kama da ubansa a komai. Hajiya ta ce da shi a lokacin da yake rungume da yaron kamar zai tsaga kirjinsa ya sanya shi.

“Kai dai jininka karfi gare shi, duk ‘ya’yanka kai suke debowa.”

Amina ta nemi mijin nata alfarma a sanya mata sunan Babanta, bai ki yi mata alfarmar ba, don ba ya jin ko ransa Amina ke so zai kasa mallaka mata da yana da iko. Ranar suna yaro ya ci suna Mas’ud Ji-kas.’

Duk dangin Amina na uwa da uba babu wanda ba ya jin sanyi karkashin inuwar Amina. Wannan kuwa duk sanadin ilimi ne (iyaye mata mu inganta ilmin ‘ya’yanmu mata, musamman a kan ilmin kimiyya da kiwon lafiya). Kusan duk sati Amina sai ta je wajen Goggonta ko a dauko ta.

Shekaru biyu cif da haihuwar Mas’ud Ji-kas Amina ta sake haihuwa. Wannan karon diya mace, wannnan karon ma ta sake neman alfarmar Ma’arouf a sanya wa yarinyar suna Aisha. Ga mamakinta sai ya ce, “A’ah sunanta Saudatu (Hajiyan Ji-kas) Ki kara himma zuwa shekara ta gaba ki haifo wata, watakila in sanya Aisha din.”

Laila dai haihuwa shiru tun tana damuwa har ta hakura. Abin yana bai wa Amina tausayi in ta ga yanda ta ke nan-nan da yaranta Mas’ud da Saudatu. Don haka da ta sake haihuwa, wannan karon da namiji ne, sai ta tattara kayan Saudatu ta sa Saudatun a gaba sai dakin Laila.

“Na ba ki rikon Saudatu har abada Anty Laila, ko da nan gaba Allah ya ba ki naki ba zan kwace ba. Allah ya dube ki da idanun rahmarSa ke ma.”

Laila don murna sai da ta yi hawaye, ta dauki Saudatu ta rungume, da ma yarinyar ta saba da ita fiye da kowa a gidan. Amina ta sha mamaki da ranar suna aka ce d ita ILYAS Ma’arouf ya sanya wa jaririn (daga baya Amina ta sha ba shi labarin irin tarin kaunar da Ilya ke masa in suna hira).

Lokacin da (tenure) din Ma’arouf ta cika, ya sake tsayawa kamar yadda al’ummar jihar Bauchi suka bukata. Ya sake hawa kujerar Gwamna a karo na biyu. Shekarunsu takwas ke nan a Government House, sai a wannan shekarar suka sauka. Jama’arsa sun so ya kara tsayawa Sanata, ya ki. A cewarsa, siyasa tana hana shi kulawa da iyalinsa yadda ya kamata. Don haka ya gama ta da izinin Allah. Wanda aka zalunta ko aka bata wa karkashin mulkinsa yana rokonsa ya yafe masa!

Wannan kalamin ya yi su ne a wata hira da BBC ta yi da shi. Ya sanya jama’ar Bauchi da yawa kuka.

Ilya ya yi murna sosai da samun takwara, haka ya ciko akwatuna da kayan Baby. Sun tattara sun koma gidansu na Fati Mu’azu Links. Amina ta ci gaba da aikinta, shi kuma ya ci gaba da (construction contract) dinsa. Laila ta koma makaranta.

<< Sanadin Kenan 30Sanadin Kenan 32 >>

1 thought on “Sanadin Kenan 31”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×