TSOKACI
Rayuwa cike take da ƙalubale, sai dai ko wani bawa da kalar nasa ƙalubalen. A nawa labarin Mahaifina shi ne ƙalibalena, duk yanda zan kai ga yin abu domin naiman albarkarsa ba na taɓa samu, duk yanda zan yi domin ganin na faranta masa ya ci tura. Duk abin da zan yi domin ya sa ya yabeni ba ya gani... Na amshi hakan a matsayin kaddarata, kuma zan kasance ina addu'a har zuwa lokacin da zan samu SAUYIN YANAYI.
Unguwar Dubantu Hadejia, Jigawa State Nigeria
"Salma Kinga yadda kika koma kuwa. . .