Skip to content
Part 2 of 4 in the Series Sauyin Yanayi by Fatima Rabiu

Villa for sale in Dubai hills Estates

Tsaye yake manne da waya a kunnansa. Ya juya baya gashin kansa kad’an daya sakko har bayansa ya d’ansa hannunsa yana shafawa.

Ya d’an d’auki lokaci yana wayar kamin ya sauke wayar yana jan lumfashi kad’an.

Turo k’ofar parlon da akai ne yasa shi juyowa gaba d’ayansa.

Jasmin dake tsaye ta zuba masa mayun idonunta ji take kamar ta cinyesa wani irin bala’in kyau taga ya k’ara mata na fitar hankali.

Wani irin miyau ta had’e tana k’ara binsa da kallo kamar idonta zasu fad’o.

Saukar muryarsa taji yana cewa “what look?, that’s enough”

Sauke numfashi tayi tana k’ara takowa tsakiyar parlon tana binsa da mayan kallo har yanzu. Cike da yanga da iyayi ta ce “ai ka kai a kalle ka ne My Salman, babu macen da zata kalleka lokaci d’aya ta d’auke idonta daga kanka”.

Tab’e bakinsa yayi wadda yake jawur kamar na jariri.Of course, he also knows that he should be looked at, but he is not in front of him. Ko wa’inda ake aura masa bada san ransa ake yin hakan ba, kuma da k’afafunsu suke guduwa saboda lalurar da yake fama da ita wacce take tashi akai-akai.

Muryar Jasmin ta katse masa tunanin daya fad’a.

“Ya kamata Salman izuwa yanzu ka amince dani, ka aure ni wallahi ina bala’in sonka”

Furzar da iska yayi yana bin Jasmin da kallo, kamin lokaci d’aya ya d’auke idonsa daga kanta. Kamar bazai magana ba, dan harta fidda rai da hakan, sai kuma taji muryarsa mai taushi da kaifi yana cewa “Jasmin nasha gaya miki nasha yin aure ba sau d’aya ba ba sau biyu ba, duk wacce zan aure basa iya zama dani, because I can’t curse those who have everything, even I have relieved the responsibility that God has placed on me. Dan haka please Jasmin ki manta da wannan maganar ta aure a tsakaninmu”

“Wallahi ko kashe ni zakai naji zan iya zama da kai nidai kawai ka amince ka aure ni dan Allah”.

Kallon Jasmin kawai yake. Tausayi ma take basa wallahi, fad’a kawai take a fatar baki kyan nasa ne kawai yake rud’arta, bawai shi ainafin kansa ba. Shi yasa mata da yawa basa birgesa, da yawansu kud’insa da kyan da Allah yayi masa ne ke sawa su soshi ba wai wani abu ba.

Bai sake magana ba ya fiddo wayarsa ya kira PA d’insa Fahad.

Ba’a jima ba saiga Fahad ya shigo parlon.

Kallon Jasmin Fahad yayi yana watsa mata harara harga Allah shi haushi take basa. Yadda take iya zubar da darajarta ta mace take zuwa wajan Ogansa kullum cikin magiyar ya sota kuma duk a banza tunda yasan ba saurararta zaiyi ba.

Maganar Salman ce ta katse ma Fahad tunanin daya tafi.

“Fahad ka tabbatar komai ya gama kammaluwa na tafiyarmu?”.

“Eh ranka ya dad’e k’arfe shidda jirginmu zai tashi”

Yana idasa fad’ar haka Salman ya fice daga parlon bai k’ara kallon koda inda Jasmin take ba.

Jasmin ji tayi kamar zata had’iye zuciya ta mutu tsabar yadda ya y’arfata, duk da ya saba mata hakan amma na yanzu tafi shik’a.

Da kyar ta samu ta fisgo magana daga bakinta ta kalli Fahad cikin jin haushinsa ta ce “ina kuma zaije?”.

“Iska na wahalar da mai kayan kara. Kin san dai Mai gida ba mazauni bane, yana harkar kasuwancinsa k’asashe-k’asashe. Kuma koba wannan ba ai yana da dangi a Nigeria, ko baki san haka ba?, to zaije ganin gida ne”.

“Hmmm PA kenan ba kaine sa’an yina ba, wadda ya ajeka shine dai-dai ni”

“Duk wannan haukan da kike hakan bazai sa Mai gida ya aureki ba. Saboda kyansa kika gani da dukiyarsa kike rud’e haka, amma ba dan Allah kike duk wannan haukan ba. Kuma na baki shawara Jasmin?. Mai gida koda yana da niyar aure yanzu to bazai tab’a auranki ba, domin baki dace dashi ba. Dube ki, dubi jikinki dubi kayan dake sanye a jikinki kwata-kwata kamar ba d’iyar hausawa ba. Kawai danki girma a ture sai akace ki yada al’adarki?”.

Jikin Jasmin tsabar b’acin rai har wani rawa yake so take ta gaggaya ma Fahad magana itama amma wani abu ya tsaya mata a wuya.

Ganin bata da bakin magana yasa Fahad wucewa yana murmushi dan yasan ta shak’a iya shak’a. Ai wallahi baya fatan Mai gidansa ya auri irinsu Jasmin ai sai su lalata masa rayuwa gaba d’aya ma.

*Canada Studio Faruk Galadima*

Zaune yake a studios yana sauraran wak’ar da ya gama rerawa yanzu cikin harshan turanci. Dafasa akai ne yasa shi cire abunda ke manne a kunnansa yana duban Henry daya dafa k’afad’arsa.

Henry ya ce “Ohhh Faruk, you should rest like this and work hard today, I see that your phone is being called and you should check”

Sauk’e goran lumfashi Faruk yayi yana lumshe idonsa yana d’an murza dogon gashin kansa. Wadda daka kalla zaka san irin na Fulanin asali ne.

Muryarsa a gajiye ya mik’e yana cewa “by God, I’m also planning to leave the studio and go home. I know, Amma I’m waiting for me”.

“You should do it because today we are working on this song”

Computers guda biyu ya d’auka sai wasu y’an abubuwa yana shirin barin wajan yaji Henry na cewa “yawwa kaga nama manta babbar mawak’iyar nan tazo nemanka wai tana so tayi wak’a da kai”

“Wa kenan?”

“Enisa mana”

“Ohhh, but I’m just singing, I don’t release the video of the song, but some people sing my song if we sing normal, but honestly I won’t sing, I can’t sing”

“Faruk na fad’a mata wannan duk da taso ku hau wak’ar tare amma ta amince zaku rera wak’ar kawai”

“Okay yayi ba bamuwa ita ce ta rubuta wak’ar ne?”.

“Eh ita ce yanzu hakama taban wak’ar a rubuce zuwa gobe zata dawo domin ganinka.Then decide when you think you will sing the song”

“Ba damuwa zuwa goben ma idan aiki bai min waya ba, zamu iyayinta kawai”.

Ficewa yayi daga studion yana fata yasa face mask ya rufe fuskarsa, gudun mutane suyo kansa, duk da dare ya tsala amma garin kamar safiya ce. Dan duk inda ya shiga a k’asar Canada to ansan sa ansan waye Faruk Galadima shahararran mawakin dake tashe a duniya. Ya fara wak’a tun yana k’araminsa da sun cikar burinsa na son zamowa mawaki. Kuma Amma ta basa goyin baya, sai dai duk da haka baisa ya manta shi d’in waye ba. Mahaifiyarsa kad’ai ta rage masa a duniya. Sunsha wahalar rayuwa acan baya amma wak’ar daya ke tasashi d’aukaka, d’aukakar da zato bai zata ba. Shi kansa baiyi tunanin zai zama wadda duniya take alfahari dashi kamar haka ba, it’s a good thing for everyone to join him wherever he goes or where he goes.

Abunda ya maido sa zama Canada shida Amma bayan wak’a yana aiki a wani kanfani na k’era wayoyi da computers da dai sauran na’oruri daya danganci electric. Yasan takan waya da computers duk idan sun samu matsala zai iya gyara maka a d’an k’ank’anin lokaci. All companies are proud of Faruk Galadima.

Katse tunaninsa yayi dai-dai yazo gaban wata Mota mai d’aukar ido. Bud’e gidan baya yayi yasa abubuwan dake d’auke a hannunsa, bayan yasa ya rufe bayan ya dawo ya shiga ya tada motar yabar cikin studion, da shima mallakinsa ne yanzu, mawak’a wadda basu kaisa ba suna zuwa sosai domin su buga wak’arsu a studionsa ba tare da ka bada ko sisi ba. Da yawan mutane abunda ke k’ara sawa su soshi kenan sunansa yayi zarra a k’asar Canada, kai harma da makwaftan k’asashe.

Wani ma dai-daicin gida wadda ya gaji da had’uwa yayi parkin d’in motar tasa kamin ya bud’e ya fito yana danna wani madanni dake hannunsa nan take get d’in gidan ya bud’e, shi kuma ya koma cikin motar ya data ita, ya idasa shigewa harabar gidan. Wajan aje motoci yayi parking.

Fito yayi daga motar ya d’auki kayansa dake bayan motar ya nufi cikin gidan.

   Yana shiga babban parlon gidan ya iske Amma dake zaune zaman jiransa.

  Ganinsa ya dawo k’alau yasa Amma sauk’e ajiyar zuciya. Har saida Faruk yaji yadda ta sauk’e ajiyar zuciyar.

Murmushi ya saki yana ajiye kayan dake hannunsa yazo kusa da Amma ya rungumeta yana cewa “Ohhh Amma idan na fita sai kace wani k’aramin yaro, wadda idan ya fita akesa ran bazai iya gane gida ba?. Amma nafa girma yanzu”

Kumatunsa Amma taja tana cewa “kaci gidanku Faruk, yaushe aka haifeka ma da zaka wani ce ka girma yanzu?, ni a waje na kai yaro ne”.

Murmushi ya sakar mata ya ce “hakane fa Amma, ai kin san ina kan hanya gashi na dawo kuma lafiyata lau”.

“Kaji ja’iri baccin ka gama tada min hankali, ka kalli k’arfe nawa ne yanzu kuwa?”

  Da sauri Faruk ya kai dubansa akan tsintsiyar hannunsa dake d’aure da agogon hannu. Waro ido waje yayi yana cewa “Ohhhh sorry Amma sha biyu saura ashe na dare. Mi yasa baki kwanta ba?, aiki ne yau yayi min yawa wallahi”

Shafa kansa tayi tana cewa “nayi tunanin hakan, amma kasan idan ba dawowarka na gani ba bazan iya bacci ba. Kaida kota ina mutane nemanka suke ya za’ai kullum hankalina bazai tashi ba idan zaka fita?”.

“Amma nemana mutane suke amma ai soyayya ce tasa hakan ba wai cutar dani zasuyi ba”

Murmushi Amma ta saki irin na manya ta ce “har yanzu kai yaro ne Faruk, ai cikin hakan ake samun mak’iya, wad’anda basa son ci gabanka, kai dai kawaii Allah yayi mana tsari da su. Allah kuma ya k’ara k’are min kai a duk inda kasa gaba”

Kiss ya kai mata a goshi yana amsawa da amin.

Yana niyar tashi Amma ta ce “abinci fa?”

“Bana jin abincin nan zai shiga yanzu Amma”

“To miye kaci yau?”.

“Na d’anci wani abu a studio”

“A’a bazan yarda ba saifa kaci abinci, nasan ba wani abinci kaci ba, yanzu haka Chacolate d’in daka saba ci kayan zak’i sune kayita sha. Kazo ga abinci nan akan darning table kaci”

D’an tab’a cikinsa Faruk yayi sai yanzu nema yaji lallai yana jin yinwa, dan rabonsa da abinci tun safe da zai fita aiki. Sai Chacolate d’in da sha.

Shigewa yayi d’akinsa dake sama. Yana shiga toilet ya fad’a ya watsa ruwa, bayan ya fito yasa wasu k’ayan bacci. Yana d’aukar wayarsa dake ta aikin ringing tun d’azo.

Wayarsa ta gida wacce y’an uwansa na kusa da friend’s nasa ne kad’ai ke kira ta cikinta yaji ta fara k’ara.

D’aukan kiran yayi yana k’arawa a kunne.

Cike da kulawa yake yin wayar wani lokacin yayi dariya daka gani kasan da abokinsa yake waya.

Can ya ce “Okay kuna gaf shiga jirgi?. Ni banso ka koma Nigeria ba yanzu friend, miye zakai a Nigeria ne?, kasan kuma ciwonka yafi tashi idan kana can”.

Daga cikin wayar aka ce “to ya zanyi ina son k’asata kuma Daddy ya kirani yana son gani na nima nayi kewarsa sosai kasanfa rabona da Nigeria zanyi shekara biyu, tun sadda naje Momy ta matsa nayi aure, akayi a daran aka samu matsala dole na saki matar tun lokacin na bar k’asar”

Faruk cike da kulawa ya ce “Salman ya kamata fa asan miye asalin mike damunka gaskiya ba yadda za’ai ka zauna ba aure”

“Abunda bana so kana min maganarsa kenan Faruk ka sani. Nigeria is the only thing I don’t want to come to where I went and Daddy pressured me to get married, kuma bayan yasan bazan iya zama da kowacce mace ba a haka”

“Insha Allahu Salman komai zai wuce zamuyi waya idan ka sauka. Wai ina Jasmin ne taka?”

“Kai ko? Bana son wannan zancan, ko kasan Jasmin bata da kamun kai?, kai kwata-kwata ma bata cikin jerin matan da nake so. Kuma duk fad’a take duk sadda a gaban idonta ciwo na ya tashi wallahi a ranar guduwa zatai”

“Hakane aboki ai da yawansu badan Allah suke son mutane irinku ba”

“Harda kai ma ai Faruk kaifa sele ne”

Dariya Faruk ya saki yana cewa “kai Salman na kaika ne nifa wak’a ce ta d’aukaka ni kaifa tsaye kake da k’afafunka kaine ka kafa kanka da kanka, ai matsiyin da dabanne”

“Ka cika wasa Faruk wallahi”

Sun dad’e suna waya kamar kar su daina sai da jirgin su Salman zai tashi tukunna sukai sallama……….

<< Sauyin Yanayi 1Sauyin Yanayi 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×