Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja Nigeria
A hankali yake sakkowa daga matakalar jirgi. Gilas ne manne a idonsa, wata irin iska ya shik'a ta k'asarsa Nigeria, wata irin nutsuwa na saukar masa a zuciya.
PA dake janye da akwatunan su na kaya. Wasu jifga-jifga motoci ne suka zo d'aukar Salman sun kai su biyar a jere.
Gaba d'aya Airport d'in kallo ne ya dawo garesa. Mata y'an gayu wa'inda suke ji da kyau da kud'i ko wacce na binsa da kallo kamar idonsu zasu fad'u, ko wacce mace dake wajan. . .