Skip to content
Part 5 of 6 in the Series Sauyin Yanayi by Fatima Rabiu

Cottage Hospital: Kiri Kasama Road, Hadejia Jigawa State Nigeria

Ahmed a sukwane ya koma asibitin, yana zuwa ya iske su Hajiya wani doctor ya tara su sun kai su goma yana masu jawabin micece ma Sikilar kanta. Da yawan wa’inda ke wajan duk y’an K’auye ne.

Duk da su Hajiya sunsan wasu abubuwa da doctor d’in yake fad’a amma bayanin da yake ya d’au hankalin mutane da dama. Shima Ahmad samun waje yayi ya zauna yana sauraron abunda doctor d’in ke fad’a, kamar haka.

(CUTAR SIKILA(SICKLE CELL DISEASE )

*”Yakamata* ace kowa yana da ilimi akan wannan cutar…

Mutane sun rabu gida uku(A sauqaqe amma)

*AA* =sune wanda basu da cutar kuma baza su iya yaɗa cutar ba

*AS* =Su ake kira da *Carriers,* ba suda cutar amma idan suka auri masu irin jinin su zasu iya haifar mai cutar

*SS* =Sune masu cutar

Kafin ku shaqu da wani wajen soyayya adalcin da kowa zayyi ma kanshi da yaran da zai haifa shine yasan wanne kalar jini ne dashi ta ɓangaren Genotype yaga ko zasu iya Aure

*AA+AA=* ✓Za su iyah aure

*AA+AS* =✓Za su iya aure

*AA+SS=* ✓Za su iya aure

*AS+AS* =×Ba a son suyi

*AS+SS* =×Ba a son suyi

*SS+SS* =×Ba a son suyi

Ciwon Sikila(Sickle cell disease) Wata cuta ce da ta take shafar sinadarin da yake ɗaukar iskar da ɗan adam yake shaqa lokacin numfashi

*Illolin da masu cutar suke fama dashi*

1-Ciwon gaɓoɓi mai tsanani

2-kamuwa da cututtukan infection Saboda garkuwar jikin su yana da rauni

3-Shanyewar jiki

4-Qonewar jinin jiki

5-mutuwar gaban namiji

6-Rashin girma sosai

Da sauransu

*Shin za a iya magance cutar?* Eh,ta wani bangaren kuma nace A’a

Akwai abin da ake kira *Stem cell transplant* inda ake canjin ɓargon mai cutar yakan iya magance cutar… yana da tsada a qalla wasu asibitin ka kashe 10million kuma ba kowanne asibiti ake ba

Zan tsagaita anan saboda kar rubutun yayi yawa Amma kowa yama kanshi adalci kar soyayya ta saka ka cutar ko ki cutar da kanka”

Cewar Doctor d’in ya k’are maganar tare da duban mutanan dake wajan. Wata mata ce ta mik’e tana cewa “to idan masu cutar gaba d’aya sukai aure zasu iya haihuwar yaro wadda bai d’auke da cutar?”

“Tabbaya mai kyau”,

Cewar Doctor d’in yana duban matar kamin ya gyara tsayuwarsa ya sake cewa “Eh zasu iya haihuwar yaro wadda bai d’auke da cutar, sai dai abune mai wahalar yiwuwa. Amma komai daga Allah ne, amma ina so ku sani gara ka aure wadda baza’a zo asha wahala ba, ku a wahale yara ma a wahale. Ina fatan kun fahimta?”

Kowa ya amsa domin gaba d’ayansu sunji dad’i bayanin daya yayi masu.

Daga nan su Hajiya suka nufi Office nashi, ya duba Salma sosai ya rubuta mata magunguna ya k’ara bata shawarwari sosai da wasu abubuwan daya kamata mai Sikila ya rink’a ci. Sosai Hajiya taji dad’in hakan.

Bayan sun fito daga Asibitin Hajiya ta kalli Ahmad cike da mamaki ganin ya taro masu napep, ta kasa hakuri ta ce “wai Ahmad ina motar ne?”

Wani murmushin tak’aici yayi kamin ya ce “dana koma gida na iske su Abba da abokansa ne zasu fita wani waje, to dama jiran motar yake, shine ya ce a baki hakuri mun dawo a napep”

Wani kallo take bin Ahmad dashi na rashin yarda da abunda ya ce mata d’in. Can kuma sai ta ce “Abban naku ne zai fita unguwa? to ina zashi tare da abokai?”

“A’afa Hajiya ba wani waje ne mai nisa ba zasuje, k’ilama mu koma muga sun dawo”

Girgiza kai kawai Hajiya tayi tana kamo hannun Salma suka shiga napep d’in. Haka kawaii bata yarda da abunda Ahmad ya ce mata ba, akwai wani abu dai bayan wannan.

Koda suka koma gida, Hajiya taga motar Abba sai bata ce komai ba. Hatta su Hajara data iske a tsakar gidan nasu bata tankama kowa ba, suma ko kallon inda suke basuyi ba, ko sannu ya mai jiki?, basu ce ba, Hajiya abun ya mata ciwo sosai, ai sannu bata cire ciwo amma ai tana da dad’i, kwafa kawai tayi tana jaddada rashin mutumci irin na Hajara da Y’ay’anta.

Ta lura da taken-takensu kamar suna jiran ko zata ce masu wani abu ne, sai sukaga sab’anin hakan.

Duk da Hajiya ta lura akwai abunda ya faru bayan Ahmed ya dawo gidan da sunan ya zai d’akko masu katin asibiti. To amma miye ya faru haka?.

Ba mai bata amsa ganin kuma Ahmed d’in baya so ta sani, sai kawai itama ta kyale abun.

Washe gari Salma ce kwance akan kujera sai kanta data d’orasa akan cinyar Hajiya, ba laifi ta d’an samu sauk’i. Hajiya tasa hannunta tana zare k’aramar wayar dake manne a kunnan Salma, data ke sauraron wani book mai suna Bak’ar wasik’a da abokiyar fira ta karanta, tayi nisa a sauraron book d’in taji Hajiya ta zare wayar. Tashi tayi tana kallon Hajiya.

Hajiya ta kalleta ta ce “wai ke bakya gajiya ne da sauraron wa’innan labaran?”

Dariya kawai Salma ta saki tana cewa “Hajiya da dad’i fa littafin, nima wallahi Hajiya ina son fara rubutun book, kiyi min addu’a Hajiya na fara a sa’a”

Dariya itama Hajiya tayi tana cewa “da wace wayar zaki rink’a typing d’in to?”

Sai kuma Salma ta tab’e baki kamar mai shirin kuka, data tuna cewa fa bata da babbar waya.

Ahmed ne da Ismail suka shigo d’akin. Ismail yayi wajan Salma yana d’arewa akan cinyarta, murmushi ta saki tana k’ara gyara masa zama akan cinyat tata.

Ahmed daya ji abunda suke cewa. Sai shima ya ce “Hajiya indai zata iya rubutu wadda mutane da yawa zasu k’aru da ita, to insha Allahu zuwa gobe zan kawo miki sabowar waya ki fara kawai”

Ai da jin haka Salma ta saki k’arar murna ta fara zafgama Ahmed godiya bakinta tsabar murna yama ki rufuwa, kawai saita k’ara rungume Ismail dake jikinta tsabar jin dad’i.

Dariya Hajiya da Ahmed suke mata yadda duk ta rud’e da murna haka.

“Tohm Masha Allah ai ko ta gode, nima na bata goyan baya ba’a san inda baiwarta take ba ai”

Cewar Hajiya tana kallon Ahmed.

“Hakane Hajiya Allah ya bada sa’a Salma”

Da amin Salma ta amsa tana ta aikin sakin murmushi.

Washe gari kuwa kamar yadda Ahmed yayi mata al’k’awari ya cika sabuwar waya mai kyau ya kawo mata y’ar dai-dai wacce kud’inta bai wuce dubu arba’in ba.

Sosai Salma taji dad’i kamar ta taka rawa.

Bata b’ata lokaci ba wajan samun number Khadija candy domin cikin marubuta ita ce kad’ai Salma ke mahaukacin so da son kasancewa kamar ita.

Kuma tayi sa’a Khadija candy ta amsheta hannu biyu-biyu, duk da dama tasha jin Khadijar bata da girman kai ko kad’an ta iya ma’amala da mutane kowa nata ne.

Ita ta fara bata shawara ta fara typing kawai kamin tayi posting ta rink’a turo mata tana duba mata kamin ta samu kungiya ta shiga idan tana da ra’ayin hakan.

Salma dama ta dad’e tana ya y’an rubuce-rubucenta ta aje cikin littafin makaranta. Kawai saita tuna da wani labari can baya data tab’a fara rubutasa tun kamin suyi candy, tasha wahala kamin ta samo book d’in, duk yayi k’ura duk da bata dad’e da gama secondary ba, dan har yanzu basu gama hutun da zasu tafi wata school d’in ba, shi yasa ma take zaune a gida har yanzu, jira kawai Abba yake hutun ya k’are ta sani ya sata wata makarantar.

Cikin ikon Allah ta samu labarin hatta sunan labarin dama ta riga tasa mai, kuma bata canza ba, shine *YADDA K’ADDARA TA SO*

Abun fa kamar wasa Salma ta fara typing d’in yadda kaddara taso cikin ikon Allah tana turama Khadija candy ita kanta tayi mamakin yadda book na farko amma ba wasu kurare da yawa, ga daga jin labarin zai d’au hankalin jama’a da yawa. Ita ta bata shawarar bud’e Facebook ta rink’a posting har a can, ta turo mata groups na novels a yawa ta shiga, a d’an k’ank’anin lokaci ta fara posting nasa a duniya kamin ka ce mi mutane sun karb’i littafinta na farko.

Cikin nasarar Ubangiji daya bata da ikonsa, ta kammala book d’inta na farko, wadda tayi mamakin yadda mutane suka amshesa sosai ta yadda ma batai tsammani ko tunani ba.

Bata tab’a zaton abokiyar fira zata karanta mata book ba, sai gashi tana gama book d’inta na farko Khadija candy tayi mata hanya ta had’ata da abokiyar hira ta fara bata kyauta ta karanta mata na farko kamin tayi wani zata siya. Karku so ganin yadda Salma taji dad’i kamar ta taka rawa, kowa na gidan sai da ya gane farin cikin da take.

Hajiya dake kallonta yadda ta rik’e waya sai murmushi take yasa Hajiya cewa “nikam Salma wannan farin cikin duk na miye haka?”

Murmushi ta k’ara sakar ma Hajiya kamin ta ce “Hajiya dole nayi murna, ina abokiyar hira nan wacce nake sauraron book’s d’in data ke karantawa?”

“Kware na tuna ta”

“To yawwa Hajiya ita ce fa zata karanta min book d’ina wadda na ce miki na gamasa jiya”

“Kai Masha Allah Ubangiji ya k’ara d’aukaka d’iyar albarka. Ai insha Allahu sai kin zama wani abu, sai kin zama abun kwatance da yardar Ubangiji”.

Khadija ce tsaye a d’akinsu ansha wata uwar kwalliya kamar wacce zata fita gasar kyau ta duniya, a fesa wannan a fesa wancan.

Jafar ya kirata yana k’ofar gida yazo zasu fita yawo cikin gari. Sauri take dankar ma Abba ya ganta duk da ta gaya masa d’an ajinsu ne dama.

Bayanta gama ta kalli Maryam dake kwance akan gado ta mak’ale waya a kunnanta, hula ce akanta tasa ta mak’ale wayar, tana sauraron book na ji.

“Wai ni ko Maryam kin gama jin fitar tsoro kuwa?”

Sauk’e lumfashi Maryam tayi ta zaro wayar ta kashe littafin data ke ji tana cewa “shine nake ji yanzu haka ma”

“Ayya please karki gogesa dan Allah ina son nima na turasa. Domin naji k’awayena nata cewa yayi dad’i”

“Ai wallahi da gaske suke yayi mahaukacin dad’i, bare akace miki kuma abokiyar hira ce ta karantasa ai dad’in ba’a magana. Nifa sai inkai sha biyun dare ina sauraron littafi, indai abokiyar hira ce zata karantasa to wallahi ina sonsa, babu book d’in da zata karanta bazan jisa ba”

Khadija data fiddo wayarta cike da zumud’in a tura mata fitar tsoro ta ce “please y’ar albarka ki turo min kamin naje na dawo kanji. Akwai ma wani book a wayar tawa shima naji ne, amma D’an Hamza ne ya karantasa wai mai suna FANSA shima yayi dad’i amma fa horror story ne”

“Wow ke dan Allah?, ai ko ina son horror story sosai ma. Ai ko kawo na tura miki sai nima na tura FANSAR”

Mik’a mata kawai Khadija tayi, kamin ta fice daga d’akin.

Tana fitowa taci k’aro da Mama dake fitowa daga shashin Abba.

Tsayawa tayi Mama ta k’araso tana dubanta ta ce “wai dama tun d’azo baki fita ba?, tun yaushe naji yaro ya shigo gidan nan yana cewa ana sallama dake?”.

“Mama na d’an tsaya ne wajan Maryam zata turo min littafin abokiyar hira fa”

“ke dan Allah harta k’ara yin wani sabo?, kinsan fa nima littafinta data karanta kawai nake iya ji, sai kuma na gidan redio”

“Eh Mama ta sake karanta wani wai fitar tsoro, kije Maryam zata tura miki”

Kamar zata tafi sai kuma ta tsaya tana cewa “ni ko Mama a cikin book baki ganin akwai inda ake cewa bin Bokaye da Malamai babu kyau kuma masu yin hakan kina jin yadda k’arshen su yake kasancewa. Mi yasa baza……. D’aga mata hannu Mama tayi tana zare mata ido kamin ta ce “Kinga duk nasan wannan tunkan a haifeki nake jin wa’azi, dan haka babu abunda zan fasa, indai hakan wancar matar ce da y’ay’anta dan haka tunkan waje ya k’ure miki kama hanya ki tafi inda zaki”

Da sauri Khadija ta fice daga gidan gaba d’aya tana d’aga k’afad’arta irin ko a jikinta d’in nan.

A waje kuwa Jafar ne tsaye yana waya da wani abokinsa yana cewa “haba abokina kasanfa motar nan maido maka da abunka zanyi ba wani dad’ewa zanyi ba zan dawo”

Daga cikin wayar aka ce “kaga Jafar ya kamata wannan k’aryar ace yanzu ka daina ta. Tunda kana da mata da y’ay’a har uku, ace kuma hakan bai isa ba sai ka k’ara yin wata k’aryar ka auro wata kuma. Kana ganin rayuwa zata tafi a hakane?”

Jafar ya murtuke fuska kamar yana gaban wadda suke wayar dashi kamin ya ce “kaga Baffa please ka rik’e gaskiyarka bana so. Amma aure saifa na k’arasa, idan ba haka kake ma matan yanzu ba tofa ko kallonka basayi, yo akan mi? ai wallahi kamar yadda na auri Hafsat ta gama haukanta wai bazata zauna a gidan k’asa ba, bazata ci tuwo ba, ta gama haukanta ba gashi dole tayi hakuri ta rungume kaddara ba. To itama haka wannan dole ne zatayi hakuri kota k’i kota so”.

“Ka dai rink’a sassauta k’arya a rayuwarka wallahi Jafar”

“Kaga bawan Allah naji rik’e wa’azinka zaiyi anfani amma fa wata ran”

Yana fad’in hakan ya tsinke kiran ganin Khadija na tahowa inda yake tsaye.

Tana k’arasowa ya sakar mata murmushi yana cewa “Ohh My Khady wannan kyau haka?”

Dariya ta saki tana sa tafin hannunta ta rufe fuskarta kamin kuma ta sauke tana cewa “ai duk kaine akai mawa”

“Wow duk ni d’aya”

“Eh man”

“To yanzu dai da ina da ina kike so muje yau?”

D’an fari tayi da ido kamin ta ce “eh ina so muje shopping da wajan cin abinci haka”

Dariyar yak’i Jafar ya saki, danma yana da y’an kud’insa daya rantab’o ma kansa bashi, kullum cikin cin bashi yake da aron kayan jama’a, shine aro mota can, shine aro kayan sawa can shine kaza shine kaza.

Bud’e mata mota yayi yana k’ara washe baki ya ce “Bismillah ki shiga”

Shiga kawai motar Khadija tayi ta zauna, shima ya rufe motar ya shiga ya zauna.

Ya data ita suka fice daga unguwar taso.

*Gurbi K’aramar Hukumar Jibia Katsina State Nigeria*

“Nanah kizo ku wuce Islamiya fa ko, gashi har shidda tayi safiya ta farayi, naga alamar baki son zuwa Islamiyar asubar nan”

Nanah data fito daga d’aki tana faman murmuza idonta dake cike da bacci, ta kalli Inna dake bakin murhu tana dama Koko, ta ce “Inna wai Baba bai dawo bane?”

Gaban Inna ne ya d’an fad’i har sai da ta d’an dafe k’irjinta kamin kuma ta samu kanta da addu’a a ranta, sai kuma ta dawo da dubanta wajan Nanah data k’araso inda take yanzu.

Ta ce “bai dawo ba, nima nayi mamaki anayin sallar Asuba fa yake dawowa gida, indai sukai kwanan dajin nan”

Murmushin yak’i kawai Nanah ta saki, dan itama taji irin fad’uwar gaban da Inna taji kawai ta d’aure ne dan kar Inna ta fahimci hakan.

Auta ta jawo yasha Kokon kamin ta kama hannunsa zasu fice daga gidan taji Inna ta tsaida ita tana cewa “ke kuma fa bazaki sha kokon bane?”

Wani abu Nanah ta had’e a mak’oshinta kwata-kwata yau bata jin dad’i, bawai rashin jin dad’i na jiki ba, a’a kwata-kwata yanayin yau bata jin dad’insa.

Da kyar ta ce “a’a Inna na k’oshi, idan na dawo naci wani abu kawai”

Itama Innar bata sake magana ba, har su Nanah suka fice daga gidan. Kawai saita samu kanta da tagumi hannu biyu-biyu ta rasa mike mata dad’i itama.

Tafe suke kan hanya ita da Auta zasu dawo gida bayan an taso daga Islamiyar, Auta sai tsaida ita yake yana y’an wasanninsa.

Tsawa ta daga masa tana cewa “wai kai Auta mi yasa baka da natsuwa ne?, muna tafe kan hanya ka natsu mana muje gida”

Auta daya firgita da tsawar da Nanah tayi masa, yasa ba shiri ya natsu yana binta da kallo kamar ba itama ba, bata tab’a masa irin wannan tsawar ba. Kodai bata da lafiya ne?.

Sai kuma ta kamo hannunsa suka cigaba da tafiya.

Sun shawo kwanar gidansu kawai taji Auta na cewa “lahhh Nanah dubi k’ofar gidanmu cike da mutane”

Kan Nanah a k’asa yake ai da sauri ta waiga inda k’ofar gida nasu yake. Wata wawar bugar zuciya ce lokaci d’aya ta riski Nanah had’e da wata fad’uwar gaba. Tunkan ace mata mike faruwa ta fara hawaye kawai domin jikinta ya bata ba lafiya ba.

Da gudu Auta ya warce hannunsa da Nanah ta rink’e yayi cikin gida.

Nanah ma ta tsakiyar mutanan ta rab’a ta wuce yadda taga sai binta suke da kallon tausayi, an shinfid’a tabarma ga Liman yazo wasu na alwala duk jikin mutane a sanyaye.

Da sassarfa ta idasa shigewa cikin gidan. Tana shiga abunda idonta yayi mata tozali dashi shine Gawar Baba shinfid’e a har an gama shiryata duk jini ya b’ata jikin likafanin. Wata irin razananinyar k’ara Nanah ta saki a haukace ta nufi inda gawar Baba take wata irin wawar runguma tayi masa, kawai ta fashe da wani irin kuka mai zuma zuciyar mai saurare.

Auta dake jikin Inna shima sai kuka yake duk da bai san mutuwa ba amma yasan idan aka tafi ba’a dawowa shikenan kaida mutum har abada.

Da kyar aka b’anb’are Nanah da har sumewa tayi a jikin Gawar Baba sai da aka shafa mata ruwa bayan an fita dashi.

Matsuwa Nanah tayi jikin Inna tasa kanta akan k’afad’ar Inna tana hawaye tana magana cikin muryar kuka ta ce “Inna miya faru da Baba?”,

“Nanah y’an Ta’addar nan ashe dajin dasu Babanku suke b’uya sun gane cewa dama b’uya suke subar matansu. Wani d’an lek’en asiri suka turo ya kwana a garin shine yaje ya sanar dasu komai har inda su Babanku suke. A daran sukai ma wajan dirar mikiya sun kashe da yawan mazan dake wajan hatta Balah shima sun kashe sa Ibro ne kad’ai ya tsira shima sunji masa mugun ciwo”

Kuka kawai Nanah ta saki tana tsinema y’an Ta’addar nan a zuciyarta yafi a k’irga sai tsine masu take tana jawo masu bala’in duniya dana lahira.

Gaba d’aya garin Gurbi ya zama shuru da yawan mutane a ranar basu k’ara kwana a garin ba, a hankali garin ya fara zama kamar ba gari ba. Duk wadda ka kalla a cikin garin bashi da natsuwar zuciya kullum da tashin hankali suke kwana suke tashi. Dan yanzu har tsakiyar rana y’an Ta’addar shigowa suke.

Tsaye Inna take yau kusan wata d’aya da mutuwar Baba tana shirin saida gidan da suke ciki ta tattara y’ay’anta su koma cikin garin Jibia da zama, ko sun samu kwanciyar hankali, duk da taji Jibiar ma shiga suke idan sunyi niyya, amma ai gara can da yawan mutane a garin.

“Yanzu Inna waye zai siya wannan gidan da daraja a garin nan?”

Inna ta kalli Nanah dake mata magana. Inna ta nisa ta ce “na dai aika Auta gidan Saminu dallali, yaji idan zai iya siyan gidan nan, dan bana ma so mu k’ara wasu kwanaki a garin nan gaskiya”

“To Allah yasa ya siya d’in, kin san yanzu tsoron siyan gida ake a garin nan ma”

“Yo Nanah ba dole aji tsoron siyan gida a garin nan ba. Ai dan a zauna ake siyan gida, to k’iri-k’iri idan ka siya zai gagareka zama indai a cikin garin nan ne………

<< Sauyin Yanayi 4Sauyin Yanayi 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×