wp-content/uploads/2022/10/Tsaka-Mai-Wuya-by-Umar-bin-Ally.jpeg

Tsaka Mai Wuya

Umar Bin Ally ba shi da aikin yi a kullum face kula ‘yanmata a shafin sada zumunta na facebook. Kusan kullum sai ya yi sabuwar budurwa, bisa tsautsayi wata rana sai ya fara soyayya da matar ministan tsaro na Æ™asa ba tare da ya sani ba.

wp-content/uploads/2021/12/Muazzam-by-Fatima-Ibrahim-Dan-Borno.jpg

Mu'azzam

Irin biyayya da kuma soyayya da Mu’azzam ke yiwa mahaifiyarsa, Goggo, ya sa duniya ke kallon shi a matsayin da nagartacce. To amma a badini kuma yana da wata rayuwa da ko makiyinsa ne ba zai yi farin ciki da ganin sha a ciki ba. Wannan ya hada da rashin adalcin da yake tafkawa a tsanin matansa uku. A hakan kuma Goggo ta umurce shi da kara auren Husna, wacce ta ke kamar kanwa a gare shi, adalilin wani mummunar kaddara da ta fada ciki. Shin ko rikicikin da ke cikin gidan Mu’azzam zai barshi ya zauna lafiya?

wp-content/uploads/2022/01/Fadime-by-Asmau-Abdallah-Ibrahim-Bingel.jpg

Fadime

Bayan Uwale ta yi wa ‘yar mijinta FaÉ—ime asiri ta haukace,’ yarta Hainsai na ganin cewa ta fidda ita kawai daga Æ™auyen kowa ya huta. Sai dai Uwale ba za ta iya ba saboda sharuÉ—É—an da aka gindaya mata. Kuma a shirye take ta bi takan ko waye domin cikar burinta. Sai dai Æ™addarar da ke cikin rayuwarsu duka mai girma ce.

wp-content/uploads/2023/03/Abul-Khair-by-Salmeert-Sani-Salman.jpg

Abul-Khair

‘Yan biyu masu matuÆ™ar kama da junansu wato Abul da Khair kyawawa ne na gaban kwatance. Saboda tsabar kamanninsu ma ba kowa ke iya bambance su ba. Sai dai kuma akwai wani É“oyayyen lamari game da su. Shin ko wane irin lamari ne?

wp-content/uploads/2021/12/Tekun-Labarai-by-Danladi-Z.-Haruna.jpg

Tekun Labarai

Bayan Sarki Shamsuddini da matarsa sun gudu da tsakar dare domin su tsira daga harin da waziri Ashfanu da mabiyansa suka kawo musu. Dole tausa suka bar ɗansu jariri a tsakiyar dokar daji. Bayan komai ya lafa sai suka yi neman duniya amma basu ganshi ba. Sai dai ƙaddara ba ta gama jaraba su ba, domin kuwa ɗa ya dawo gidan ubansa ba tare da shi kanshi ya sani ba.

wp-content/uploads/2021/12/Tsanin-Nasara-by-Hamza-Dawaki.jpg

Tsanin Nasara

Duk da cewa amaryar ta jima a gidan mijinta har ma ta tara yara. Gwalagwalan shawarwarin da mahaifinta ya ba ta sun zamo mata tsanin hawa matakin nasara a gidan aurenta da ma rayuwarta baki É—aya.

wp-content/uploads/2021/12/Marubuci-by-Umar-bin-Ally.jpg

Marubuci

Yayinda wani matashin marubuci ya saurari wata tattaunawa da aka yi da wani fitaccen jarumin fina-finai, hakan ya ƙara mishi ƙwarin gwiwar ci gaba da rubutu tare da zama tsanin samun nasararsa a harkar rubutu.

wp-content/uploads/2021/12/Bincike-by-Umar-bin-Ally-1.jpg

Bincike

Sipeta Sani ƙawararren Ɗan Sanda ne da bai san faɗuwa ba a aikinsa, sai dai garkuwa da ɗan minista da wasu ɓata gari suka yi na nema ya kai masa ruwa rana a bincikensa.

wp-content/uploads/2021/12/Fatalwar-Sinu-by-Haiman-Raees.jpg

Fatalwar Sinu

Katoɓara da ɓarin baki suka sa Haiman bayyanawa duniya irin abubuwan da yake so a bashi a matsayin kyautar barka da sallah. Sai dai ya samu kyautar da ta fi ƙarfin shi, yayin da wata kyautar ta fito daga lahira kuma daga hannun wani gagarumin maƙiyin da bai san yana da shi ba.

wp-content/uploads/2021/12/Bakar-Kaddara-by-Haiman-Rarees.jpeg

Bakar Kaddara

Wasu lokutan ba sai ka aikata mummunan aiki ba kafin baÆ™ar Æ™addara ta afko maka. A wasu lokutan kuma, halayen mutane ne ke kaisu ga faÉ—awa cikin bala’i.

wp-content/uploads/2021/12/Yini-Sittin-Da-Daya-by-Hamza-Dawaki.jpg

Yini Sittin Da Daya

A fadar sarkin namun dawa, wato Zaki. Dabbobin dawa, manya da Æ™anana kan zo masa da labarai iri-iri domin tattaunawa da samo mafita a cikin al’amuran yau da kullum irin nasu na dabbobi wanda yake kamanceceniya da namu na mutane.

wp-content/uploads/2021/12/Baba-Dattijo-Dan-Bursin-by-Mukhtar-Spikin.jpg

Baba Dattijo Dan Bursin

Yayin da wani É—an jarida ya je gidan yarin Kurmawa da ke Kano ya gamu da wani dattijo mai ban mamaki da ke rayuwa a wannan gida na kaso. Shin ko ta yaya za a iya shari’ar kashe mutumin da ya riga da ya mutu tun shekaru 29 da suka gabata?

wp-content/uploads/2021/12/Ina-Matsalar-Take-by-Rahma-Sabo.jpg

Ina Matsalar Take?

Yayin da aka nemi Safwan sama ko Æ™asa ba a gan shi ba har na tsawon wasu kwaki, sai mahaifiyarsa Amina ta matsa wa mahaifinsa game da nemo inda yake. Domin har ta fara fatan ina ma ace masu garkuwa da mutane ne suka sace shi, a tunaninta ko ba komai za su ji yana raye kuma su san nawa za su biya. Babban abinda ya fi tayar wa da mahaifin Safwan hankali shi ne irin yadda ya ziyarci ofisoshin ‘Yansanda har biyar amma babu inda aka yi mishi tarbar kirki, sai ma tayin kuÉ—i da suke masa. To ina matsalar take?

wp-content/uploads/2021/12/Rayuwata-by-Aliyu-A.-A.-Engr.jpg

Rayuwata

Zuwan ‘Yan Bindiga rugar su Naja’atu ya yi sanadiyar mutuwar mafi yawa daga cikin ‘yan’uwanta. Yayin da ita kuma garin gudun neman ceton rai ta faÉ—a hannunsu har shugaban ‘Yan Bindigar ya mayar da ita tamkar matarsa.

wp-content/uploads/2021/12/Indo-A-Birni-by-Rashida-Usman.jpg

Indo A Birni

Indo ta gallabi mutanen Æ™auyensu baki É—aya. Kowa Æ™orafi yake yi da ita, abu ya yi tsamari dai har da kai ta Æ™ara gaban Mai Gari, kullum iyayenta mutanen kirki suna zarya wajen magance matsalolin da take jawo musu amma kamar ba sa yi. Sai dai duk da wannan hauka da rashin kan gado nata, Allah ya jarrabe ta da soyayyar Muhammad Mustapha wanda ke zuwa daga birni. Anya kuwa za ta samu shiga a wurinsa? Musamman da yake akwai wata ‘yar uwar tasa ma a birni da take son shi amma ba ya ko kula ta.

wp-content/uploads/2021/12/Laifin-Wa-by-Mustapha-Abbas-RLemo.jpeg

Laifin Wa?

Ladidi matashiya ce mai ji da Æ™uruciya, hakan ya sa ta faÉ—a harkar bin maza domin ta hucewa kanta haushin rashin É—auke mata É—awainiya da iyayenta suka kasa. Duk da cewa sun san irin abin da É—iyarsu ke aikatawa, amma ba su da ta cewa. Saboda wani lokaci ma wurinta suke zuwa su yi ‘yar murya.

wp-content/uploads/2021/12/Allah-Daya-Gari-Banban-by-Bukar-Mada.jpeg

Allah Daya Gari Banban

Yayin da matar Abdullahi masunci ta haihu a karo na goma a rayuwarta, sun yi farin ciki sosai. Hakan ne ma ya sa Abdullahi tafiya bakin kogi domin ya yi su ya samo abinda zai ciyar da iyalansa. Amma wani abin mamaki shi ne, sai da ya yi kwanaki arba’in yana zuwa su ba tare da ya kama ko da kwaÉ—o ba, ga shi yana matuÆ™ar jin kunyar mai gurasa wanda ke binsa bashin da yake ta bashi a kullum ba tare da gajiya ba.

wp-content/uploads/2021/12/Birnin-Sahara-by-Haiman-Raees.jpg

Birnin Sahara

Haidar ya farka daga suman da bai san ya yi ba, yayin da ya tsinci kanshi a wani babban birni da duniya kaf ba ta san da wanzuwarsa ba. Abin ya bashi mamaki Æ™warai da gaske da ya ga tsohuwar budurwar da yake so Nadiya ita ce ke mulkin wannan birnin. Sai dai mamakin shi ya Æ™ara nunkuwa ne bayan ya fahimci cewa yana da alaÆ™a ta asali da wannan birni, kuma ya zama wajibi a gare shi ya tsallake wasu matakai domin ya zamo sarkin wannan birni matuÆ™ar yana so ya ceci rayuwar ‘yan uwansa.

wp-content/uploads/2021/12/Kaddarar-Mutum-by-Mustapha-Abbas.jpg

Kaddarar Mutum

Tun bayan mutuwar mahaifinta, wato Malam Tanimu, Asma’u da mahaifiyarta Inna Hauwa suka shiga cikin tsangwama a wurin mutanen Æ™auyen Somayi. Hakan ko ya samo asali ne sabo da ta Æ™i amincewa da batun auren duk samarin garin, musamman Muntari da yake É—an Maigari. Ba zato ba tsammani kuma sai wani ya yi wa Asma’u fyaÉ—e har ta samu ciki. Wannan dalili ne ya tursasa mata barin Æ™auyen ba don tana so ba. Ko za ta samu mafita a inda ta nufa?

wp-content/uploads/2021/12/Daurin-Huhun-Goro-by-Rashida-Usman.jpg

Daurin Huhun Goro

Halin yunwa, talauci da kuma matsatsin rayuwa da ake ciki ne suka tunzura Tabawa har ta kai ga tana bin layi da lunguna tana zagin shugabanni, ‘yan siya da kuma ‘yan kasuwa. Domin ita a ganinta, duk su ne sanadin faruwar hakan a cikin al’umma. Ta kuma Æ™udiri aniyar kawo sauyi game da wannan lamari.

wp-content/uploads/2021/12/Wa-Ya-Kashe-Zahrau-by-Fatima-Galadima.jpg

Wa Ya Kashe Zahra'u?

Matakin tashin hankali da ruÉ—anin da ya É“arke a gidan Alhaji Aliyu Ibrahim MD ya kai maÆ™ura, yayin da aka wayi garin ranar É—aurin auren ‘yarsa guda É—aya tilo a duniya aka same ta a mace. Angon nata, wato Zayyan ya suma sakamakon jin wannan mummunan labari. APC da DCP Sardauna suna ta bincike domin gano wanda ya shigo har cikin gidan ya kashe Zahara’u duk kuwa da tarin matakan tsaron da ke gidan.

wp-content/uploads/2021/12/Yayanmu-by-Kabiru-Yusuf-Anka.jpg

Ya'yanmu

Rayuwar zaman marina ake yi a Unguwar Hayin Talaka. Unguwa ce ta talakawan da basu san ciwon kansu ba ballanta na ‘ya’yansu. Rayuwa ce ake yi cikin rashin tsafta, nutsuwa da sanin yakamata. Ko yaya rayuwar yara masu tasowa a wannan Unguwar za ta kasance a gaba? Shin ko za su samu mafita?

wp-content/uploads/2021/12/Dare-Daya-by-Yareema-Shaheed-1.jpg

Dare Daya

Salim ya shiga cikin jarrabawa babba. Shekaru uku kenan da kammala karatunsa amma har yanzu bai samu aikin yi ba. Kwatsam! Ana cikin haka kuma sai wani mai mota ya bige mahaifiyarsa, inda har ta samu karaya bakwai a jikinta. Likita ya bayyana za a yi mata aiki, amma ana buƙatar Naira miliyan uku domin yin aikin. Ga shi Salim ba shi da kosisi.

wp-content/uploads/2021/12/Ba-Kauyanci-Ba-Ne-by-Fatima-Abubakar-Saje.jpg

Ba Kauyanci Ba Ne

Alhaji AbdulÆ™adir mutum ne É—an zamani wanda kiyaye haƙƙoÆ™in addini bai dame shi ba, to amma ‘yarsa Salma da mahaifiyarta Hajiya Bilkisu suna da kyawawan halaye kuma suna matuÆ™ar kiyaye dokokin shari’ar Musulunci. Alhaji Sameer da Hajiya Samira suna da É—a guda É—aya da suka haifa mai suna Kamal. Duk iya Æ™oÆ™arin da Alhaji Sameer yake yi na ganin Kamal ya shiryu, ita mahaifiyarsa gani take takura ce. Kamal ya kama hannun Salma a wurin wani taro inda ta wanke shi da mari. Sai daga baya yake jin ashe mahaifiyar Salma mahaifinsa ya fara so ya aura kafin mahaifiyarsa.

wp-content/uploads/2021/12/I-am-Not-Your-Punching-Bag-by-Hauwa-Sale-Abubakar.jpg

I Am Not Your Punching Bag

I Am Not Your Punching Bag And Other Stories is a collection of short moral and interesting stories depicting the daily struggles of African woman.

wp-content/uploads/2021/12/Mutum-Da-Kaddararsa-by-Maryam-Ibrahim-Litee.jpg

Mutum Da Kaddararsa

Bilkisu matashiyar mace ce mai ƙarancin shekaru, sai dai ƙaddarar rayuwa ta sa zaman aure ya gagare ta. Da farko ta auri Aminu wanda suka samu ɗaa guda ɗaya da shi wato Amir. Bayan sun rabu ne sai ta auri Malam inda suke zaune tare da uwargidarsa Hajja. Kisisinar amaryar Malam ne tai ta jawo musu damuwa har aurenta ya mutu a karo na biyu. Bayan ta koma gidan gwaggo Maryam ne masoya biyu suka fito neman aurenta. Hassan mai shagon siyar da kayayyaki da kuma Ɗan Majalisa Hashim Bello. Kowa na mata kwaɗayin auren Ɗan Majalisa, sai dai ita kuma tunaninta daban.

wp-content/uploads/2021/12/Al-Mustapha-by-Asmau-Abubakar-Musa.jpg

Al-Mustapha

Malam Jibrin da matarsa Larai sun saka wa Al-mustapha (BaÉ—É—o) karan tsana tare da ba shi aikin wahala saboda mahaifiyarsa ba ta gidan. Wasu lokutan Malam Jibrin da kanshi kan yi mamakin irin yadda yake nuna wa É—ansa tsana tare da kasa tantance cewa Al-mustapha jininsa ne ko ba jininsa bane.

wp-content/uploads/2021/12/Kushewar-Badi-by-Kabiru-Yusuf-Anka.jpg

Kushewar Badi

Tsawon shekaru Almustapha da matarsa Lajja suna tare, suna matukar so da kaunar junansu, so irin na don Allah. Abubuwa biyu ne kadai ke damunsu a rayuwa; rashin haihuwa, da kuma wani al’amari mai firgitarwa da ke tare da Lajjar. Kwatsam! Wata rana tsaka a cikin ire-iren ranekun babi-babi na rayuwarsu, wani mutum mai suna Alhaji Hammad ya bayyana tare da shaidun cewar Lajja fa matarsa ce. Hujjojin da ya kawo sun tabbatar da abin da ya fada haka yake. Don haka alkali ta karbe Lajjar daga hannun Almustapha aka ba Alhaji Hammad. Shekara daya da faruwar wannan abu Allah ya yi wa Lajja haihuwa. To a wannan lokaci ne kuma wasu hujjojin suka kuma bayyana, kuma suka tabbatar wa duniya Lajja ba matar Alhaji Hammad ba ce! To matar wane ne?

wp-content/uploads/2021/12/Mutuwar-Tsaye-by-Hadiza-Isyaku.jpg

Mutuwar Tsaye

Dr. Deeni ƙwararren likita ne a ɓangaren jinyar cututtukan da suka shafi mata kawai. Rana ɗaya kawai ya tsinci kansa da cutar makanta wadda ta zo mishi a yanayi na bazata. Matarshi Deena, wadda ke ɗauke da tsohon ciki ta fi kowa shiga tashin hankali, domin kuwa mahaifiyarta ba son aurenta da shi take yi ba. A gefe kuma ga mahaifiyar su Deeni wacce ita ma ke fama da tata lalurar. Shin za su faɗa mata ne ko kuma za su ɓote? Yaya makomar aikin Deeni? Kuma yaya makomar aurensu da Deena?

wp-content/uploads/2021/12/Son-Zuciya-by-Maryam-Ibrahim-Litee.jpg

Son Zuciya

Hadiza da ‘yan’uwanta suna cikin halin jarabawa sakamakon irin son zuciyar da yake nuna musu. Ba ya basu ci balle sha, kuma bai damu da su ba, amma kullum yana tukubar mai nama ko mai shayi yana morewarsa.

wp-content/uploads/2024/01/Mai-Daki-by-Hafsat-C.-Sodangi.jpg

Mai Daki

Hauwa’u Idris É—aliba ce mai matuÆ™ar Æ™oÆ™ari a fannin karatu. Babban burinta shi ne ta zama malamar jinya yayin da ta kammala karatu. Sai dai kash! Mahaifinta ba shi da Æ™arfin É—aukar É—awainiyar karatun nata. Hakan ya sa ko da Ishak ya zo neman aurenta kuma ya tabbatar musu da zai barta ta ci gaba da karatu, sai nan da nan suka amince. Abin da ba su sani ba shi ne, Ishak bai da niyyar barin Hauwa’u ta ci gaba da karatu.

wp-content/uploads/2024/01/Uban-Da-Ba-Namu-Ba-by-Maryam-Shuaibu-Aliyu.jpg

Uban Da Ba Namu Ba

Tanimu Sambo wanda aka fi sani da Baban Nawwara malamin makaranta ne da ke koyarwa a wata makarantar mata. Jajircewa da ƙwazonsa a ɓangaren koyarwa tare da tsayuwa akan gaskiya suka sa ya ƙi yarda ɗalibansa su ba da kuɗi domin a basu amsar jarabawar fita daga Sakandare. Maimakon haka, sai ma dagewa da ya yi wajen horas da su yadda za su amsa tambayoyin yadda ya kamata.

wp-content/uploads/2024/02/Almajirai-Ma-Yaya-Ne-by-Habiba-Maina.jpg

Almajirai Ma 'Ya'ya Ne

Sa’idu da Halliru sun zamo tsayayyu kuma bayyanannun misalai na irin mummunan halin da al’majirai ke faÉ—awa a cikin rayuwarsu ta al’majiranci. Duk da cewa an nuna irin yadda mugun halin mutanen zamani yake game da al’majirai har suke cutar da su, Hajiya Maryam ta fita zakka tare da zamowa misalin da kowa zai so zama kamarta.

wp-content/uploads/2024/02/20240213_004529_0000.jpg

Auren Sadaka

Rayuwar wani naƙasasshen gyartai wanda hannunsa da ƙafarsa ɗaya suka shanye ta shiga cikin wani irin sabon salo na uƙuba sakamakon gashin da yake amsa a wurin matarsa. Sai dai ita ma ba daɗin take ji ba, domin kuwa kullum cikin ƙunci da zubar da hawaye take. Ko me ya jawo yin irin wannan auren wanda babu mai jin daɗinsa?