Skip to content
Part 3 of 11 in the Series Shameekh by Harira Salihu Isah

Shaameekh a harzuƙe ya ɗau ƙiran, wanda da alama har yanzu ɓacin ran maganan da Manseer ya masa bai wartsake ba, “Wai ke kam wace kalan mayya ce? Sau nawa ina gargaɗanki da ƙira na, na hana ki ƙira na amma sam bakya ji, sannan kina ƙira na da wani number daban, wai ke baki da aji ne? Ko baki iya kama mutuncinki irin na ƴa mace bane?”, ya ƙarishe faɗa yana mai jin, kaman ya shaƙeta ya huta.

A ɗaya ɓangaren kuwa mai ƙiran nasa fashewa tayi da kuka, cikin kuka ta tausasa muryanta ta ce, ” Haba Ya Shaameekh dan kawai ina sonka, ai kai ma kasan ba laifina bane, dan ba nice na ɗaurawa kai na ba, kuma mai son ka ai yafi mai ƙin ka, idan kana wulaƙanta ni kuma kai ma kada ka manta za ka haifa, idan aka yiwa taka ƴar ai ba daɗi za ka ji ba.”

A hasale Shaameekh ya ce, “Nace miki bana son ki, ki riƙe kan ki kada ki bari na ɗau mataki a kan ki, ni ba sa’anki bane da za ki dinga faɗa mini ko wani maganan da ya fito a bakinki.”

“Wallahi kana so na Ya Shaameekh, kuma sai ka aureni, wannan karon zan koma gida, kuma za a yi duk abinda za a yi, wallahi ina a shirye tsaf a kan ka ba wan da ba zan iya ja da shi ba, har Mom and Dad, kuma idan ma akan wancan figaggiyar kake mini wulaƙanci, to za ka sa na kasheta ne a banza, idan ya so daga baya nima a kashe ni  kowa ma ya rasa, dan a kanka ba wan da ba zan iya yiwa illa ba, ko waye kaji na faɗa”, ta faɗa a ɗaya ɓangaren a yanayin kaman wacce ke cacar baki da abokiyar faɗanta.

Wani killer smile Shaameekh yayi, domin shi baya son hayaniya, amma duk yacce ya kai da rashin son magana, wannan yarinyar sai ta ingiza sa yayi, ga shi ko yana faɗan ma ba za ka ce faɗa bane, kawai dai maganan nasa na zaratan maza ne amma a niste yake yi, cewa yayi, “Idan kika gwada aikata wannan kuskuren to lallai za ki yi danasani a rayuwanki na da baki zo duniyar ba ma, nothing concern me with our blood relationship, dan zan ɗau mummunan mataki a kan ki ne ko da kuwa zai raba kan family ne i don’t care, duk randa tayi ko da ciwon kai ne, kuma ke kika zama sanadi to za ki sha mamaki, stupid girl marar aji kawai, ba ta in da za ki haɗa kan ki da precious diamond mace mai aji da sanin ya kamata, kina ballagaza wawiya”, yana gama faɗa ya kashe wayansa yana huci, ga ɓacin ran Manseer ga wan da ta ƙara masa, a ce ayi mace a duniya bata san inda ke mata ciwo ba, dole ne sai ka so wanda baya son ka.

Tsaki ya kuma ja ya ce, “Mutane sai ka ce dabbobi mai zan yi da ke? useless girl kina zaune cikin ƴan iska kina abin da ranki yake so, bazan auri sauran wasu ba no matter how.”

Sai da ya ɗan saita zuciyarsa da yake ji a ɓace, sannan yayi dialing layinta, ringing ɗaya yana shiga ta ɗauka kaman wacce ke jira daman, cikin zazzaƙar sassanyar muryanta mai daɗin sauroro ga sanyi ta ce, “Assalamu’alaikum wa rahmatullahi wa barkatuhu abun ƙaunan Jidderh.”

Jin muryanta kaɗai ya saka shi samun wani ni’imtaccen nistuwa, idan ana neman mace tagari jin daɗin duniya to jidderh ta wuce in da ake nema ma, shiyasa maganan Manseer yayi mugun ɓata masa rai, dan nunawa yake kaman bai wani damu ba, amma a can ƙasan zuciyarsa yan da yake jin ta daban ne, duk cikin ƙannensa babu ya ita, dan ita ɗin kyauta ce daga Allah, ga duk wan da ke tare da ita.

Lumshe ido yayi yana busar da iska mai zafi a bakin sa, amma bai ce mata komai ba, sallaman ma a zuciya ya amsa, ita ma jidderh a nata ɓangaren  lumshe idon tayi, tana jin ta cikin wani irin yanayi, Allah ne kaɗai yasan irin ƙaunar da take wa wannan bawan nasa, ji take rashinsa zai iya kawo ƙarshen rayuwanta, tana masa son da bata yi wa kanta ko kwatansa, juyi tayi tare da ƙanƙame pillow a jikinta tana jin fitar ko wani sauti na numfashinsa a cikin wayan, kaman a fiskanta yake sauƙe numfashin, wani irin yanayin ƙaunarsa take ƙara stunduma, kuma shirunsa daɗi ya mata bai dameta ba, dan tasan daman ba lallai ya amsa mata ba muddin ta faɗi hakan.

A hankali ta raba laɓɓanta da junansu ta fitar da sautin, “Yayana abun ƙaunata fatan ka wuni lafiya cikin aminci? Ya gida? ya aiki?”

“Alhamdulillahi”, haka kawai Shaameekh ya faɗa a taƙaice.

“Masha Allah! Yayana abun ƙaunata ina matuƙar kewanka”, faɗin jidderh cikin shagwaɓa kaman ƴar jinjiran kule.

Shaameekh da shi kaɗai yasan abin da yake ji, da kuma yanayin da yake shiga musamman idan tayi wannan shagwaɓan nata, ajiyan zuciya kawai ya sauƙe yayi shiru bai ce komai ba, amma dai yasan yanayinsa a yanzu ya koma dai-dai, ya ma mance da ɓacin ran da yake ciki.

“Yayana yaushe za ka dawo? ka ga su Hajiya Mama sun fara surutu.”

“Soon Insha Allah”, yanzun ma a taƙaice ya faɗa hakan.

“To Allah ya sa, Allah ya dawo mini da kai lafiya, ya tsare mini kai, Allah ya hana ko wacce mace kallonka.”

“Ameen nagode da addu’a”, ya faɗa yana mai shafa sajensa.

“Bakomai Mijin Jidderh in Allah ya yarda.”

“Ki kwanta dare nayi, ki gaishe da kowa da kowa, gudnyt.”

Jidderh a ɓangarenta shagwaɓe fiska tayi kaman tana gabansa, amma ba yacce ta iya dole ta ce, “Allah ya tashe mu lafiya.” “Ameen take care byee.” “Byeee Yayana kuma mijin jidderh”, ta faɗa tana sakin murmushi.

Shaameekh ma murmushin gefen baki yayi wan da ya matuƙar fito da kyawunsa, sannan ya kashe wayan, ba ɓata lokaci kuma ya miƙe ya shige toilet,  sai da ya staya ya wanke toilet nasa tsaff da shi kaman ka zuba abinci ka ci a ciki, sannan ya fara wankansa.

Jidderh kuwa bayan ya kashe wayansa, rungume wayan tayi a ƙirjinta stam (kaman Shaameekh ɗin ta samu), tana sakin murmushi mai sanyaya zuciya, duk da ba hakan ta so ba  ƙanin miji ya fi mijin kyau, bata so ya kashe yanzu ba dan jin muryansa bai ishe ta ba, a hankali ta ce, “Yayana ina ƙaunarka, Allah barmun kai, Allah ya kulamun da kai a ko ina kake, Allah ɗaura ka a kan maƙiyanka.”

Taso wa jidderh tayi ta kashe wutan ɗakin, sannan ta koma ta kwanta da niyan bacci, sai dai dirin neman agaji wayanta ya shigo wayanta, tura baki tayi kaman mai ƙiran na kallonta, dan tasan babu mai ƙiranta yanzu idan ba maye Safwan uban ƴan naci ba, har kaman ba za ta ɗauka ba, sai ta fasa ta ɗauka tare da yin sallama, shi kuma ya amsa a nasa ɓangaren, tare da cewa, “Babe ya kike ya daren?”

“Alhamdulillahi!” Ta faɗa a taƙaice.

“Gud haka nake so, babe nasan yacce naji muryan kinnan bacci kike ji so, nima daman muryanki kawai nake buƙatan ji dan na samu yin bacci, so take care ko.”

“Nagode Allah ya tashe mu lafiya”, jidderh ta faɗa bakin nan a ture.

“U are welcome babe I love you soo much byee”, yana faɗa ya kashe wayansa.

Jidderh harara ta bankawa wayan sannan ta ce, “Ka taimaki kan ka da ka kashe”, tana faɗa ta ja blanket ta rufu sai bacci kuma, safiyar alkhairy jidderh.

A gidan big Dad kuwa, Hajiya Kubra matar big Dad wacce suke ƙira da Mom, zaune take a gefen Alhaji Sulaiman(Big Dad), da ke waya da su baba alhaji ta haɗa rai, duk abinda suke cewa tana ji, bayan Alhaji ya gama wayanne ya juyo tare da kallonta ya ce, “Hajiya ya aka yi?”

“Hmmn! wani irin yaya aka yi kake tambaya na, wai nikam du-du-du yarinyar nan a nawa take? kuma fa nasan tana dawowa ita ma soon.”

Big Dad murmushi yayi ya ce, “Kar ki damu kan ki da maganan su baba alhaji, soyayyan da yake yiwa jikokin nasa ne ya ja haka, kar ya dame ki dan Baba na son jikokinsa fiye da tunani, mu dai mu mata addu’an Allah ya dawo da ita lafiya shi ne kawai, duk wannan ba wani abun dogon magana bane.”

“Uhmn! Ameen to Daddyn Soffy.”

Shikkenan big Dad da Mom suka ci-gaba da hiransu kaman ba komai.

Shameekh bayan ya gama wankan ne ya fito ɗaure da farin towel nasa, ɗaure a ƙugunsa jikinsa duk ruwa, wannan lema-leman ruwan sai ya tafi da gashin jikinsa hakan ya ƙara masa kyau.

Ba tare da ya kunce towel ɗin ba balle saka kayan bacci, haka ya wuce direct kan gado ya faɗa ya kwanta haka, yayi addu’a ba jimawa bacci yayi gaba da shi mai daɗin gaske.

Ƙarfe huɗu 4am na dare na bugawa Shaameekh ya tashi, sai lokacin ya cire towel ɗin, ya sanya armless da 3quater  ya saka duka baƙaƙe, ficewa yayi a ɗakin da tafiyansa ta burgewa, wani hanya ya ɗauka daga palourn wan da ya sada shi da, haɗaɗɗen wajan mosta jikinsa.

Tun ƙarfe huɗu yana abu guda sai zufa yake haɗawa, kaman wan da ya yiwa sarki ƙarya, shi ne bai sarara ba sai da lokacin sallah yayi.

Yana fitowa a wajan ya ɗau goran ruwa a fridge ya kwankwaɗa tass, sannan ya wuce haɗaɗɗen ɗakinsa ya watsa ruwa sama sama bai staya ɓata lokaci ba, yayi alwala ya fito, jallabiyansa ya saka fari mai kyau ya ɗau keyn motansa ya fice a gidan.

Masallaci ya je yayi sallah, ko da aka idar bai baro masallacin da wuri ba, dan sai da yayi lazuminsa da azkar nasa, sannan ya juyo gida, nan ma bai yi komai ba ya zauna karatun Alqur’ani, shi ne bai rufe Qur’anin ba sai da ƙarfe bakwai tayi, yana rufewa ya jero addu’oensa ya shafa, sannan ya cire jallabiyan ya bi lafiyan gadonsa ya kwanta.

Ɓangaren jidderh ma da asussuba ta farka wajan ƙarfe biyar, da addu’an bacci da kuma salati ta fara buɗe bakinta, sannan ta miƙe ta wara idanuwanta a hankali, miƙa tayi ta sauƙo daga makwancin nata, ta wuce banɗaki, sai da ta wasta ruwa sannan tayi alwala ta fito, raka’atainil fijir tayi ta zauna yin istigfari har sai da aka shiga salla, sannan ta miƙe ta bi masallaci, ana idarwa ta taɓa karatun Alkur’ani, sannan ta miƙe ta mayar da komai mazauninsa, a cikin kayakinta da ke ɗakin Hajiya Mama ta sanya riga da wando ta yadi mara nauyi, sannan ta fice a ɗakin ta nufi kitchen, dan taya su baabaa Larai aiki, kasancewan ita ba mai son jiki bane, sannan tana son ta iya ko wanne irin girki ko dan ta burge masoyinta.

INDIA

Misalin ƙarfe shida na safe a agogon ƙasar India, yanayin garin yayi kyau da daɗi kaman hadari-hadari, wata rantsaststiyar haɗaɗɗiyar mota ce tayi parking, a harabar wani arnen hotel da ke babban birnin Delhi.

Wata matashiyar budurwa ce ta buɗe ƙofan motan ta sauƙo, fiska ba yabo ba fallasa tana tauna chewing-gum, sanye take da dogon wando wan da ya kama jikinta sosai, ya ɗameta har kana hango shatin inners nata, dan dai kawai ba mai jiki sosai ba ce, da sam-sam ba za ta ganu ba, sai dai dogo ne har ƙasa da rigansa, wan da bai  gama rufe ko cibiyanta ba, ga ƴar ficilan jakanta fashion na ratayawa, kan ta cike da attach (wig),  tana taunan chewing-gum nata ta ce, “Guy’s see you letter”, ta ƙarisa faɗa tana ɗaga musu hannu har suka ja motansu suka yi gaba.

Sannu a hankali take taku irin na cikakkun wayayyun matasan ƴan duniya, a haka ta yi cikin hotel ɗin, lifter ta shiga ya kai ta har floor da ɗakin da ta kama yake, tana shiga ta fara cire gashin dokin da ke kan ta(wig) (Ranƙwal kenan fan’s, an ce da wata wai acici ƙwalloji, kan ta ba gashi kaman an ci giginya da wuƙa).

tana cire wig ɗin ta koma kan kayan jikinta, sai da ta kwaɓe kayanta tass tayi stirara haihuwan uwarta, sannan ta nufi toilet a haka, ta shige ba addu’a balle salati, bata wani jima a toilet ɗin ba bayan mintuna ta fito ɗaure da guntun towel, ba sallah bare salati ta baje a kan gadonta sai bacci.

 Wannan matashiya kwance take tana sharar baccinta hankali kwance, ba batun tashuwa tayi sallah ko wani abu sai gwarti take yi, kukan neman agaji da wayanta ke yi, shi ya zama silar tashuwanta daga daddaɗan baccin da take kwasa.

Tana buɗe idanuwanta ta jawo wayan ba salati balle salallami, tana kallon numbern da aka ƙira ta da shi ta ja guntun staki, tare da ɗaukan ƙiran ta sanya a hands-free, ta na tura baki ta ce, “Hello!”

Muryan wata dattijuwan mata ce ta amsa a ɗaya ɓangaren ta ce, “daughter ya kike?”

“Ina lafiya Mom, please bacci nake yi kuma kunsan ba so nake ina bacci ana tashi na ba, ki bari zuwa anjima idan na tashi sai ki ƙira ni”, budurwan tayi magana cike da gadara, kaman wacce ki yi wa ƴar cikinta magana ba uwarta ba.

“Sorry lovely daughter, zan ƙira anjiman amma dai yanzu daman zan tambayeki ne yaushe za ki shigo ne?”

Tana tura baki ta ce, “Mom zan shigo zuwa gobe, i my self am very eager to be at home, akwai abin da nake son yi, a serious mission Mom.”

“No daughter, kiyi haƙuri ki taimaka ki dawo yau kin ji.”

Sai da yastine fiska sannan ta ce, “Anyway shikkenan dai Mom zan duba na gani, amma gaskiya sai na gama baccina, kuma zan dawo ne dan abin da nake so nayi.”

“Tun da za ki dawo ai shikkenan daughter, ba komai huta abinki Allah ya miki albarka ya dawo da ke lafiya, Allah kuma ya baki sa’a.”

Ba tare da ta amsawa Mom ɗin ta ba ko kuwa ta mata sallama, ba ko ɗaya ta kashe wayanta kitt, ta ajiye sa tare da jan tsaki ta ce, “Mutane sai takura, ni gaskiya ba don ina da mission na da zai kai ni gida ba, da ba zan koma ba dan nasan aikin masifaffen stohon nan ne, da ya ƙi mutuwa ya addabi rayuwan mutane kaman muna oldest day’s, mtswww to be in a family such like my family is a biggest problem, family ga girma ga girman maganganun”, ta ƙarishe mitanta tare da komar da kan ta kam pillow, ta ci-gaba daga in da ta dasa aya a baccin, domin bai ishe ta ba jiya kwanan club suka yi da freind’s nata (Allah ya kyauta Allah shirya mu.)

Washegari Ummiy bayan ta yi sallahn asuba ta yi azkar nata da komai, bacci ta koma sai zuwa ƙarfe tara ta tashi, da mamaki take kallon agogon da ke maƙale a bangon ɗakin nata, bacci tayi har haka ana neman ƙarfe goma, amma baby bata shigo ta tashe ta ba kam me kenan, hakan na nufin bata tafi makaranta ba tana can tana bacci, girgiza kai kawai Ummiy tayi, tare da ƙiran sunan Allah tana mai miƙewa staye, fitowa tayi ta nufi ɗakin da yake mallakin baby.

Tana isa ta buɗe ƙofan dakin tare da yin sallama, ai kuwa hangota tayi ta baje abin ta tayi ɗaɗɗaya akan madedecin gadonta, girgiza kai tayi ta ce, “Wai ke kam lafiyanki ƙalau kuwa da maganan bacci? Kina kwance har ƙarfe tara baki shirya kin tafi makaranta ba, baby zan haɗa ki da yayanki ya saɓa miki fa.”

Baby da tayi male-male a kan gado, tura baki tayi da yake tun da Ummiy ta buɗe ƙofan ɗakin ta farka ita kuma, cikin shagwaɓa ta ce, ” Ummiy kiyi haƙuri ni ba za ni school ba har sai mun dawo daga Yobe state.”

Kama haɓa Ummiy tayi ta ce, “To lallai kuwa sai kun dawo ki je school ba, in Allah ya yarda kuwa a kunnen yayanki, ko kuwa na fasa tafiya da ke, kiyi zamanki a gida kiyi gadin gidan da kyau, tun da makarantar ce bakyason zuwa.”

Baby kaman za ta yi kuka ta ce, “Ayya Ummiy dan Allah dai, kuma fa lecturenmu na yau ba amfani dan already na gama da course ɗin.”

“Koma dai menene ki fito ko haɗiye course ɗin kika yi, kuna da class by 10am amma har 9:30am kina gida, saboda samun waje ko? To kin fito ne ko sai na shigo?”

Baby shiru tayi ba ta ce komai ba sai shura ƙafa take kamar wata jinjira, Ummiy abun na baby ma dariya ya bata amma ta ƙyale ta ce, “To tabbas kin shirya yi wa yayanki bayanin abin da ya hana ki zuwa makaranta yau”, faɗin Ummiy  tana barin ƙofan ɗakin.

Baby jin haka kuma ta ga Ummiy ta juya alaman za ta je ta ƙira sa, ai da mugun sauri ta diro a kan gadonnata ta bi bayan Ummiy tana faɗin, “Na shige su ki rufamini asiri Ummiy kaman yacce Allah ya rufamini, Allah idan yaya ya dawo na san sai yayi sakwarata a gidan nan, wallahi zan shirya na je, har gobe ma zan je kiyi haƙuri kar ki ƙira sa Ummiyna.”

Ummiy ko kallonta bata yi ba, ta shige ɗakinta dan ita ma ta shirya wa zuwa asibiti.

Baby ɗakinta ta koma, kamun ka ce me, cikin mintuna kaɗan sai ga ja’ira ta fito a shirye staff sai ƙamshi take bazawa, ɗakin Ummiy ta nufa da sallama ta shiga, bayan Ummiy ta mata izinin  ta shigo,  cikin ladabi ta ce, “Ummiy na shirya zan tafi.”

“Rigimammiya da kar ki shirya mana yanzun nan na ƙira sa na sanar da shi, asaran kuɗinsa yake dan bakya son karatun.”

“Wayyooo! Ni baby wane ni, haka kawai ya dawo ya tarmaƙeni, ni fa da wani abun da yaya zai mini to na gwammace, ya saka ni a turmi ya kirɓa kaman bugun sakwaran Legos wallahi.”

Murmushi Ummiy tayi ta ce, “To iyayen surutu, wuuce kije ki karya dan ban yarda ki tafi ba ki ci komai ba.”

Baby ta ce, “To Ummiy”, tare da ficewa a ɗakin ta nufi dinning area.

Ummiy da ta sha kyau ta gaji da kyau, sai da ta gama yin duk abin da za ta yi, sannan ta fito ta samu baby ta ce, “kin gama ne?”

“Eh Ummiy na gama bari na zo mu tafi tare, sai ku sauƙeni a school namu”, baby ta faɗa tana mai bai wa Ummiy amsa.

Ummi ta ce, “Okay sai ki yi sauri dan na makara.”

Baby miƙewa tayi tare da goge bakinta, ta kuma ɗaukan gyalenta ɗan ƙarami da jakanta ta ce, “Ummiy we can go.”

Ummiy na gaba baby na bin ta a baya suka fice a palourn, bayan Ummiy ta yi wa aunty Talatu mai aikinsu sallaman sai sun dawo.

Driver na ganin fitowan Ummiy ya gaisheta cikin ladabi, ta amsa da fara’a, sannan suka gaisa da babu ma, suka shie mota dukkansu a gidan baya, sannan driver ya ja mota, ba su tsaya a ko ina ba sai a AMERICAN UNIVERSITY YOLA, a nan suka yi dropping na baby har wajan lecture hall nasu, dai-dai lokacin ƙarfe 10 saura mintunan da basu wuce uku ba, sannan driver ya ja mota su ma suka juya sai FMC Yola.

Suna isa Ummiy ta buɗe ƙofan motan da kan ta, ta fito kaman ko yaushe hannunta a riƙe da labcoat nata da kuma jakanta, sai da suka yi sallama da drivernta, sannan ta yi cikin asibitin, da yake kuma lokacin safiya ne to ko ina a asibitin a cike yake da mutane ko ina ta rasta ta wuce to sai an ɗaga mata gaisuwa.

Dai-dai gaban wani haɗaɗɗen office ta staya, daga saman ƙofan office ɗin an rubuta  Doctor Fatima.

Bayan ta buɗe ta shiga ta turo ƙofan ta kulle, direct wajan zamanta ta nufa, ta saƙala labcoat nata a gefe, ta kuma ajiye jakanta, sannan tayi bismillah ta zauna a lumstumemen kujeranta, tana mai sauƙe ajiyan zuciya.

Ba jimawa wata nurse ta shigo ɗauke da wasu tulin file’s a hannunta, cikin ladabi ta ce, “Good morning momy Fatima?”

“Morning Aisha”, Ummiy ta faɗa tare da mata nuni da ta ajiye file’s ɗin a kan table nata.

Nurse Aisha ajiyewa tayi tare da ficewa, Ummiy kuma ta jawo su ta fara dubawa ɗaya bayan ɗaya tana ayyukanta, tana kuma attending na patient’s nata, dan Ummiy likita ce da ke duba abin da ya shafi ciwon mata, waɗanda aka yiwa fyaɗe, ko haihuwa, ko wata cuta game da ciki ko private part etc, ita dai likitar mata ce.

<< Shameekh 2Shameekh 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×