Bismillaheer_rahmaneer_raheem
Tuki take a hankali saboda matukar gajiyar da tayi agurin aikinta, wayarta ce ta kawo haske alamar shigowar Kira, kallon wayar tayi tare dakai hannu ta dauka takara a kunnenta cikin sanyin murya ta furta"
Asslamu alaykum
Dan Jim tayi alamar saurare, wani kyakyawan murmushi ta saki cikin sanyi murya mai tattare da gajiya da shagwaba tace"
Ina kan hanya Ammi in sha Allah yanzun nan zaki ganni.
Murmushi tasakeyi tare dacewa
"Ameen ya rab.
Wayar ta ajiye tare da mai da hankalinta kan driving, duk da cewar dare ne kuma hanyar batada cinkoson ababen hawa kasancewarta hanyar fita. . .