Bismillaheer rahmaneer raheem
Bayan sallah Ishsha'i kwance take kan gado tana danna laptop, wayarta da takawo haske ta kalla ɗan sakin fuskarta tayi kamar zatayi murmushi.
Wayar ta ɗauka ta kara a kunne tayi sallama a hankali.
Sallamar aka daga daya bangaren tare da cewa
"Idan ba ni na neme ki ba ko shekara za'ayi bazaki nemani ba ko?.
Kwanciyar ta ta gyara cikin sanyin Muryar ta kamar ko yaushe tace"
Ba haka bane Yah Ansar na ɗan shiga sabgogi ne.
"A kullum ai maganar ki kenan NIDAL narasa gane inda kika dosa, wani lokacin har. . .