Da ranar tafiyar mu tazo ni kam sabanin ‘ya’yan gata da ake rakasu da nasiha da Addu’a ni da zagi da gori da habaici ‘ya’yan Hakimi da matan shi suka raka ni wai mu mayu ne, mun lashe kurwar Bashir da ta Hakimi to su kurwarsu ta fi karfin kankarar mu. Hajjo yarinyace ba hankali ga maida martani inda duk aka tsokalo ta sai ta yi masu gwalo da zata shiga motar Hassan ta ce,
“Alalalo! Zamu shiga jirgi dai ba ke Inna Kwaire”.
Daga Bashir har Hassan dariya su ka yi, ni ko har muka zo Abuja kuka na ke na tunanin iyayen mu da batacciyar jaririya ta.
A filin jirgin saman Abuja muka kwana tsimayen jirgi mai zuwa France ana ta cike-ciken takardu, da asuba muka bi jirgi ‘direct’ (kai tsaye) zuwa babban birnin Paris. Gidan da muka zauna yana nan a jerin gidajen ma’aikatan jakadanci na kasar.
Ba anguwa daya muke da Hassan ba don shi yana cikin gidajen ma’aikatarsu ne amma kullum ya taso aiki gidan mu zai yada zango su ci abincin rana tare da Bashir har dare.
Shakuwa mai tsanani ke shigar su shi da Hajjo. Da girman Hajjo da komi Bashir ya dauketa ya dankara a aji daya.
Hajjo ta sha tsiya wurin ‘ya’yan Faransawannan don tace mun har kungiya-kungiya suke yi zuwa kallon ta (katuwa a aji daya) ga wani sunan shakiyanci da suka lika mata (Mère) watau Mamar su kenan.
A rayuwata ban taba halartar makarantar boko ba, amma na yi karatun Addini mai yawa a wurin Baffan mu sanda ya ke da rai. Sai Bashir ya kashe muhimmin lokacin sa yana koyar da ni karatu da rubutu haka Hajjo komi ta koyo haka zata zo ta yi ta koya mun Bashir na aiki ya koma karo karatu (PhD) babbar Jami’ar Faransa yana kara zurfafa ilimin sa.
Shekara na zagayowa na haife ki Hidayah, asalin sunan ki Rahmah, sunan mahaifiyar Bashir ne kika ci, Hajjo ne ta sa maki Hidayah to sai muma din muka kama.
A shekarar Bashir ya halarci kwasa-kwasai da dama a kasashe daban-daban, da ta kai har a ka yi mai karin girma daga matsayin da ya ke da shi a wajen aikin su zuwa (Consultant) na kasar Nijeriya a Faransa.
Hassan bai taba furta mana son Hajjo yake ba har ta kare makaranta, kwazon ta da basirar ta yasa Bashir yayi cuku-cukun da ya nema mata aji biyu na karamar sakandire ta kuma lashe gwajin duk da suka yi mata tas. Sai da ta kai aji hudu a sakandire ne Hassan ya fito karara ya gaya mana shi fa kamun Hajjo ya ke.
Daga ni har Bashir mun yi matukar farin-ciki ko da yake dama tuni mun dago shi, bini-bini kaji shi yana “kanwata, me ya hada ki da wancan karmasashshen Bafaranshen? Ke fa yarinya ce har yanzu, baki isa yin abuta da maza ba. Babban farin-ciki na shine na kasancewar Hassan 100% ya cika kamilin mutum dan babban gida a jihar Borno, don mahaifin shi sanannen malamin Addini ne, duk da zaman shegiyar kasa irin France, ya canza wasu daga kyawawan dabi’un shi duk da hakan ni da Bashir ba mu ji ko dar na wanke Hajjo mu ba shi auren ta ba tun kamin kammala karatun ta na sakandire don mun san Hajjo na da wayo dole ta canza Hassan, barin ma yanzun da kanta ya bude da rayuwar turai.
Idan kin gan mu a lokacin zaki rantse bamu san wata aba miyar kuka da kalkashi ba don gabadaya sajewa muke da mutanen kasar, duka harshen mu ya juye da Faransanci zallah sai ma Bashir da ya ke baki shi ke tona mu, amma ko Hassan fari ne sol.
Ranar da nayi haihuwata ta uku a duniya wato ke Hunainah, ranar ne Bashir ya kammala Ph D din sa in da muka kara samun ‘promotion’. Mun dawo gida anyi gagarumin auren Hassan da Hajjo a garin Biu ta jihar Borno da Shanono ta jihar Kano, biki irin wanda ba’a taba yi a Shanono ba. Bashir Uban amarya kuma babban aminin ango an ba Naira kashi haka Hassan, sun nuna basu da abin so da kauna kamar kanwar su Hajjo.
To ni ma komawa na yi kamar sarauniya wurin matan Hakimi ko numfashi ji suke kaman su min. ‘Ya’ya na kuwa ko makota basa bari su dauke su wai kar su shafa masu datti, ni ko na balle bakin jaka na kara jike su da ‘yan yanzu, ai sai na kara zama kamar kwan da kaza ta nasa yanzu-yanzunnan, ko motsi nayi a ce “Hajiya Hadiza, me kike so?”
An sa Hajjo a lalle akayi sunan Baby, inda Bashir ya wanken dattin rai na ya mayar mun da sunan Innar mu (Hannatu), ke Hannatu Baban ki ke kiran ki Hunainah har yau din da ta bi ki. Bakar fatar Bashir da farar fata na ya mai da ku kalar coffee mai haske da har ake maku kallon ruwa-biyu, ya kuma sanya ‘nationality’ din ku ‘in doubt’ (cikin shakku) bayan a zahiri gaba da baya ku Fulfulde ne ziryan.
Da Hajjo ta kare sakandire suka zo Borno gaida Abban su Hassan da baya da lafiya, ai kuwa fir ya hana Hassan komawa aiki France kasancewar shi babba a gidan su kuma shi kadai ne da namiji. Duk kannin shi mata ne a gidan auren su ga tsufa mai wahala da ya kamashi.
To Hassan da Hajjo ke ma kin san takaici ba sai an fada ba wai an katse masu rayuwa. A nan Maiduguri Hassan ya sayi kankareren gida na garari suka tare, inda Hajjo aka rufe bakin mahaifa kif aka afka Unimaid inda ta ke karatun (linguistic) harshen Faransa da Barbarci ziryan. Daga baya ne aiki ya cilla su Lagos inda Hassan ke aiki da ma’aikatar ilmi ta kasa wato Federal Ministry of Education.
Shekarun ki Hidayah shidda, Hunainah biyar aka yi wa Baban ku Ambasada a kasar Russia, bamu dade ba aka canza shi zuwa Jordan inda a nan ne kuka kare firamare. Muna da shekaru uku a nan Allah ya yi wa Ambasadan kasar Nigeria a Saudiyyah rasuwa, aka sake yi mana (transfer) na wucin gadi zuwa Saudi-Arabia kafin a fidda sabon Ambassada, inda muka zauna a birnin Riyadh. Aka kai ku makarantar sakandire ta kwana.
Ba zan manta ba, ba kuma zan taba mancewa ba, a dan tsukin na yi ta mafarke-mafarken wai na ga jaririya ta da aka sace. Kuka zo hutun ku na farko a aji daya da kawar ku idan baku mantaba, yau shekaru biyar kenan da faruwar al’amarin da har yau yake damuna a rai domin na tabbata wallahi Fatimah diyata na gani”.
Hajiya Hadizah ta yi shiru hawaye na bulbular mata, jikin ta ya hau rawa. Hidayah da Hunainah, da suka yi jigum suna sauraron ta da dukkan hankalin su, suka juya suka dubi juna a gigice, cikin tsananin mamaki da ta’ajjibi mara misaltuwa suka hada baki, wanda su kan su basu san su yi ba suka ce
“Saratu Bello Makarfi???”
Dubawar nan da za su yi Mamarsu numfashi dai-dai ta ke fitar wa ba kuma ta ko iya shaida wanda ke kanta alamun hawan jinin ta ya tashi kenan. Hidayah ta fashe da kuka tace “Mamar mu don Allah kar ki mutu ki bar mu, Mamar in kin mutu ya za mu yi?”
Karamar wato Hunainah ita ta yi hankalin kiran mahaifin su, masu aikin gidan mata suka taimaka wurin sanya ta a mota aka nufi asibitin da suke zuwa da ita.
A daren nan Ambasada da yaran shi ba su rintsa ba, suka kwashe labarin data basu kaf suka gaya mishi, shi kansa ba karamin girgiza yayi ba yace idan yarinyar na makarantar ku ta Riyadh har yanzu, mai zai hana mu je mu neme ta? Idan har hakan zai dawon da farin-cikin Hadizah?
Kawanaki uku bayan nan jirgin safe ne ya sauke su a birnin Riyadh, garin da rabon su da shi shekaru biyar kenan cif. Motar musamman aka tura ma Ambasadan daga Saudi-Embassy ta kwashe su zuwa Kingston College.
Su Hidayah sun ga makarantar su ta da ta samu sauye-sauye ta fannoni da dama musamman ta fuskar cigaba, hatta ‘principal’ din da suka sani a da ba ita bace yanzun an canza a an kawo wata daga Asia maimakon Ayyush Siddiky da suka sani mutuniyar Madina.
Ita bata san ma yarinyar da su ke nema ba ta dai hada su da wani tsohon malami, malamin shine Sayyid-Ridhwan mai kula da shige da ficen dalibai ya kuma dade yana aiki a nan. Ga abinda yace da su,
“ayya! Yarinya mai hazaka irin Sarah, ban san maiyasa iyayaenta suka katse mata karatu ba a shekararta ta karshe. Inda duk kuka ganta ku baiwa iyayenta shawara su maido mana ita koda basu da ko sisin kobo ne, domin Saratou ‘yar baiwa ce”.
Daga Ambasadan har ‘ya’yan shi ji suka yi kamar su daura hannu a ka su rafsa ihu, Hunainah bata san sanda hawaye ya ziraro mata ba tasa hannu ta share. Su kanyi tunanin kaunar da sukewa Saratu Bello, a sanda suke makaranta, sun dauka kauna ce kurum ta haduwar jini daga Indallahi, da kuma ‘kualities’ na ita Saratun da ke sawa kowa ke sonta a (Kingston), to ashe Saratu jinin su ke gauraye dana juna shiyasa suke jinta har kasusuwa da bargon jikin su, barin yanzun kuma da suka ji wai ashe diyar Maman su ce?
Ba abinda ke damun su kamar lafiyar mahaifiyar su da ke ta walagigi, tayi-bata yi ba Allah masani. A gidan saukar bakin da aka yiwa ambasadan masauki cikin su ba wanda ya rintsa, kowanne abinda ya ke sakawa daban ne dana dan uwansa, zuciyar kowannen su cike take da alhini da taraddadi.
Hidayah dake kwance cikin kilishi tana kallon sama sai ta mike a gaggauce ta takarkare kamar gyare ta shiga jerawa ‘yar uwarta kira, duk ta rude sai rawa jikin ta yake kamar mazari.
A gigice uban da ‘yar suka sauko daga bene inda garin sauka Hunainah ta sulmiyo daga matakala ta biyar amma bata kula ba ta gyagije ta mike, don sun dauka wani mugun abu ne ya faru da ita, a tare suke tambayar ta “lafiya?” Tayi wata irin ajiyar zuciya kamar an ce ga Saratu a gaban su ta rungume ‘yar uwar ta tace “na tuna ne Daddy, Saratu ta taba gaya mana ita da iyayenta suna zaune ne a Lagos, kuma nan anguwar su Aunty Hajjo”
Hunainah ta ce, “kwarai anyi haka nima Daddy mantawa na yi.”
Ambasada Bashir sambo, bai yi barci ba a ranar sai da yayi masu ‘booking’ din tikiti na jirgi mai zuwa Lagos din Nigeria a washegari. A yau kam sun samu sunyi barci cikin natsuwa har da minshari, sun tabbata wahalar da Mamar su ke ciki ta yanke daga yau tunda kuwa za su kawo mata Saratun ta har asibiti. (Anya kuwa?)
Dawowar Hajjo kenan daga Ajaokuta inda take bautar kasa, ta tadda baki ba zato ba tsammani amma ba tare da Uwar su ba. Hajjo uwar ‘ya’ya ukku biyu maza da ‘yar auta mace, tuni ta hau tsallen murna kaman yarinya karama don har girman Hajjon bata bar wautarta ta kuruciya ba. Hassan ya je Maiduguri gabatar da wani aiki a ranar take tsammanin shi. To amma me?
Daga uban har ‘ya’yan fuska babu annuri, duk ta bi ta tsargu, abinda ta kawo ma ranta kawai Yayar ta ta rasu wajen haihuwa dan tuni ta san tana da ciki, tun bata nemi bayani ba ta soma kuka tace “yanzu shikenan ni daya na rage a duniyar Kawu Bashir?”
Duka sai ta basu dariya, daga kawun har ‘ya’yan sai da suka murmusa. Hakika Hajjo na kaunar Yayar ta fiye da kowa a duniya bata hada matsalar ta da ta kowa “a’ah Hajjo, Hadizah ta dage taga diyar ta Fatimah a Riyadh, shine muka zo mu bincika, don yarinyar wai ta taba gayawa su Hidayah a Lagos gidan su yake kuma a nan Bictoria Island” ta dafe kirji tace “anya? Yanzu haka ‘yar farar yarinya zata gani tace ‘yar ta ce, tunda tasa abun a ranta har ya dameta, ta jawo mana rikici da mutane ana zaune lafiya.
In banda neman tada zauna tsaye ma irin na Ya Hadizah, ta yaya ‘yar data bata a kauye za’a ce an ganta a babban birni irin Riyadh?”
Yace “Uwa ce, kada ki musa mata?”
Hidayah tace “kuma dai Anti Hajjo kin san babu inda Allah baya ikon sa. KUN-FA-YA-KUN ne fa, wanda in yace ‘kasance’ sai ya kasance. To in banda iko da kudurar tasa ta yaya kuma kuka tsinci kanku a France daga kauye ko ruga kamar yadda Mama ta bamu labari?
Wallahi ni kaina daga ganin da naiwa Saratu da farko na san jinin Mamar mu ce, ko ke kika ganta za ki yi mamaki, in banda haske da ta fi Mama, da digon tawadar Allah dake gefen hancinta ba abunda ba irin naku bane a jikin ta sai ko ‘beauty-point’ da bata da shi irin naku, ko yau kika ga Saratun wallahi sai kin dangantata da Mamar mu. A yadda na ji ta cikin raina a sanda na fara ganin ta, babu banbanci da yadda nake jin Hunainah”.
Maganar yarinyar ya ratsata kwarai, ta dage kai sama kamar mai irga ‘ya’yan taurari tace “shin ya sunan mahaifin ta?” Hunainah tace “Baba Makarfi ne ko Bello I’m confused?” Hidayah tace “Bello Makarfi, exactly sunan kenan”.
Hajjo ta dafe kirji, ta mike ta soma safa da marwa a kayataccen falon ta, bakinta na mai kakabin sunan da ya karade talbijin da rediyoyin gida Nijeriya tace
“Bello Makarfi, kuna nufin Brigadier Bello Makarfi? Dan takarar kujerar shugaban kasar nan da suka shirya juyin mulki a shekarar baya?
Ya zauna ne a wancan gidan dake kallon nawa, a sanina baya da wata diya mace, duk ‘ya’yan sa maza ne su goma cif, in ma ya haifa ban taba ganin ta ba, amma na san manyan ‘ya’yan sa su Faisal da Najib, don na kan gansu sun wuce a mota ko kuma tsaye a harabar gidan sai dai ko gaisawa bamu taba yi ba, a bakin Hassan ma na ji sunan su.
Mutane ne ‘unsocial’ watau wadanda basa shiga shirgin kowa. Ba zan karyata ku ba tunda ban san gaibu ba amma Makarfi yana kulle tun bara, don haka kuzo muje gidan Bello Makarfi. In Allah yasa Fatimar mu ce zan gane”
“ta yaya?”
Ta juyo ta dube shi tana murmushi
“jini baya boyuwa Baban su Hunainah. Yaya ta sha gaya mun a ranar da aka sace Fatimah, Baban ta ya tsaga mata biyu-biyu a tsakiyar kirjin ta na family din shi. Hakannan Fatimah nada tawwadar Allah a gefen hancinta da diga-digan ta tun tana jaririya” Bashir ko magana baya iya yi, ta sake yin murmushi.
“In kuma duka wannan bai yiwu ba, akwai shari’ah, akwai kuma likita mai auna jini, balle ma nasan ba yadda za’ai su ce ‘yar su ce in dai da gaske tsintar ta su kai iyayen ta kuma suka ganta”.
Hidayah da Hunainah duk sun yi tsit ne kamar ruwa ya cinye su. ‘Yar dan takarar shugaban kasa? Kada su je a harbe masu Aunty da Daddy in sun ce Saratu ‘yar su ce. Saratou ta sha gaya masu yadda iyayen ta da Yayyun ta maza ke son ta kasancewar ita kadai ce mace a cikin ‘yan uwan ta maza goma ris! Rana daya su kawo masu wannan magana mai rikitarwa?
Ita kuwa Hunainah sabanin tunanin ‘yar uwar ta ne. Ita tunanin da ta ke shin wace irin runguma zata yiwa Saratu a yau a matsayin ta na shakikiyarta ta jini?
Ta sha kimanta nedt haduwarta da Saratu Bello by destiny or phenomena…., (cikin wata kudura da irada na Ubangiji) tun bayan rabuwar su a Kingston.
Da da ne, a guje zata ruga ta rungumeta amma yau har bata san irin wadda ya dace ta yi mata ba.
Gidan da ta nuna masu kadai tace nan ne gidan Makarfi ya firgita su don ko a turai da U.A.E da suke zagawa samun mai irin wannan mahaukacin ginin kaman ba za’a mutu ba sai an tona. Baban su bai biyo su ba tukunna yana can masaukin sa don haka Hajjo tasa ‘ya’yan ta biyu a gaba suka doshi gidan Brigadier Bello Makarfi.
Rashin sa’a! Lallai ya tabbata gare su, ‘what was eben more unfortunate (babbar rashin sa’ar ma) get din gidan a garkame ya ke da wani irin azababben kwado, shi kansa kwadon yayi kura futuk tabbacin yayi shekaru biyu a hakan. Kafafuwan su sun sage, yawun bakin su ya kafe kat, tunanin su ya kare haka dabara ta kare masu. Shin me kuma za su yi su ceci rayuwar mahaifiyar su?
Wani kabila ne ya shawo giyar shi yayi tatul yana tafe yana tambele kamar ya kife, daya zo gabansu sai ya ja birki, ya dakata ya zaro ido yace
“wow…, gorgeous!” wato kyawawan yara.
Ya dubi Hajjo yana washe baki ya sake cewa “Madame, will u dash me dat rose Babe, plz?” Ya nuna Hunainah, wadda idon ta yai jage-jage da hawaye ta manna mai harara.
Masha Allah, muna godiya Takorinmu
Mun gode
Allah yasaka da alkhairi takorinmu
All the best
Allah ya kara basira takorinmu
Thanks
Muna godiya
Masha Allah, Allah ya bada ladan fadakarwa amin