Da gudu ta fada kitchen din ta kankame yar uwar ta, ta daga ta cancaras tana juyi da ita a kitchen din ta ce,
“Aunty Intisar sunan ki daga yau, kin yi mun abinda har abada bazan manta ba, me kike so in miki nima in faranta miki don Allah?” Ta ce,
“To aje ni in gaya miki, kada kirjin ki ya bude?” Ta dire ta tana dariya ta ce,
“Wallahi baki da nauyi, shafal kamar na dauki bokitin ruwa.” Ta bita da kallon mamaki ta ce,
“Hunainah, dama kina da karfi haka?” Ta juya mata baya cikin jin kunyar. . .
Muna godia Anty
Thanks alot
Muna godiya sosai.
A juri zuwa rafi dai Faisal
Allah ya kara basira