Tafe yake a mota zuciyarsa na faman tafasa da kuna, tunda yake ba a taba humiliating (Cin mutuncin) shi irin yau ba, ba a taba yi masa wulakanci irin na yau ba. Don haka maimakon sautin Khusairi kira’ar Mahmood Khaleel yake bi cikin Suratul Ma’idah. A ran shi kamar ya yi zagi, sai dai dadin kira’ar da yake sauraro na sanyaya masa zuciya, ya ce,
‘Ihsan din me har da za a daga wa mutum hankali kan auren ta? Ita nan har wata mace ce da za a tada hakarkari a dagawa mutum murya a kan ta. . .
Muna godiya Allah yakara basira da xakin hannu
Mun gode sosai
Mun gode
Masha Allah, pls aringa bamu 2 pages duk Rana, thank you.
Akwai kura