Skip to content
Part 18 of 22 in the Series Sirrin Boye by Halima Zakariyya

Kamin ɗaukewar jina gaba ɗaya ina jin a sanda na kusa dani ke waya yana cewa,”mun ɗauketa kamar aka bada umarni, yanzu haka muna kan hanyar barin garin gaba ɗaya.”

Yayi jim kamin ya sake cewa, “babu wani abu wai shi ɓacin rana a cikin aikinmu, mu nasara ko da yaushe tunkarmu take…idan muka ce zamuyi aiki to kawai an gama an wuce wurin, sai dai fa kuɗin fansarta dole zai tashi daga farashin da muka sa, dan naga yarinyar tafi ƙarfin farashin miliyan ashirin.”

Gabana ya yanke ya faɗi rasss saboda tsananin tashin hankali, da gaske yau ni Mairo akayi kidnapping? Abunda nake ji a labari, kuma har ake ambato waɗannan maƙudan kuɗin dan an amso ni, bayan Babana ba shi da su ba kuma shi da me bashi? kafatanin dangin uwata dana ubana su kansu aka haɗa basu kai iya adadin kuɗin ba, gatanmu a rayuwar nan shine Allah, shike rufa mana asiri ya kuma suturtamu, babu makawa Babana yaji batun wannan kuɗin to la shakka cigaban rayuwarsa abune mai wuya. wasu zafafan hawaye suka shiga sitiri a saman fuskata kamin daga bisani na ɗauke wuta gaba ɗaya.

Tafiya ce me nisan gaske mutanen sukai, tafiyar da kamar ba zata ƙare ba, aƙalla sun ɗauki kusan awanni takwas zuwa tara kamin su iso wani titi da babu gimlawar komai sai ƙarar iska dake kaɗawa. wajen ƙungurmin daji ne da tsirrai ke rayuwa wurin, motarsu bata jima da tsayawa ba a wurin saiga wasu mutane dukansu a tsamure sun fito daga cikin dajin hannayensu duka riƙe da wuƙaƙe da kuma bindiga.

A kallo ɗaya za kaiwa halittar fuskarsu ka san baƙaƙen azzaumai ne na ƙarshe, waɗanda babu ko ɗison imanin tausayi a zuƙatansu. ɗaya daga cikinsu ya dubi wanda ke riƙe da Mairo murya a shaƙe yace, “cika aiki ya ne? Ko firgici yasa ta mutu ne?”

Wanda aka kira da cika aiki ya bushe da dariya tare da yasar da Mairo a ƙasa yace, “haba bandalago zunubin ai sai yayi min yawa, kai kasan duk girman sheɗancina ina tsoron mutuwar rai a hannuna…bata mutu ba ta nan da ranta kawai dai an sata dogon bacci ne ehh yane ka gane kawai.”

Dukanninsu kuma kallonsu ya koma ga Mairo dake yashe a ƙasa kamar gawa, sanadin jefar da ita ta bugi dutse goshinta ya fashe jini sai tsiyaya yake. “kam bala’i jini naga yana zuba.” Cewar ɗayan cikinsu. “to Allah na tuba kai yau ka fara ganin zubar jini irin haka, kamar ba’a sha kashewa a gabanka…ku ɗauketa kawai kusa kai.”

Haka ɗaya ya saɓi Mairo a kafaɗarsa, kai baka ce mutum ya ɗauka ba, dan ɗaukar irin na dabbobi ne da mafarauta ke musu, suka nausa can tsakiyar dajin suna ta tafiya kamar ba za’a ƙare ba, kamin su sake ɓullawa wani dajin shima suyi tafiya me nisa kan su yada zango a wata bukka, suna isa suka jefar da Mairo kamar matacciyar dabbar da suka farauto, mutumin dake zaune kan kujerar ƙarfe yace,”wannan ce yarinyar?”

“Ehh oga itace.” “ok, to ku haɗata acikin waɗan can kajin, naga biyar ta kawo kai, idan mukayi sallar asuba sai mu wuce amma kuyi da sauri dan ina so mu shiga gari da wuri saboda aikin gobe me zafi ne.” suka amsa umarnin ogan nasu da, “yanda kace Oga”. sannan su kai gaba, sai kuma tsamurmurin cikinsu ya dawo da baya yace,”amma Oga nake ga kamar mu ɗau hanya tun yanzu ko, dan naji fa ance goben nan akwai tsaro me tsamari a hanya”. Ogan ya ɗaga masa hannu,”ba case, aikinmu baya da matsala da jami’an tsaro.”

Suna idar da sallar asuba suka shiga mota da yara sunfi biyar kuma har wannan lokacin Mairo ta farfaɗo ba, sannan suka ɗauki dogon titin da babu kwana balle kwane-kwane, tafiyar awa shida ta kaisu ga inda suke so, nan ma dai daji ne sai dai bai kai wancan dajin hatsari ba, kuma shi anan bukkoki sun kai shida saɓanin can da bukka ɗaya ce, haka aka taso ƙeyoyinsu har zuwa bakin Babbar bukkan, sannan duk mabiyan dake tare dasu suka tsaya, Wani wanda da alamar shine babba cikin ƴan bindigan dake tsaye bakin Bukkar da bindigarsa zungureriya ya kalli waɗanda suka kawo su Mairo yace,

“Ita wannan me yasa buku ɗaure mata ido ba.” “hoda ce ke aiki ajikinta”. ya girgiza kai sannan ya sunkuya ya shiga bukkar babu jimawa kuma ya fito yana takewa wani tsohon farin bafulatani baya, wanda alamu ya nuna shine babba a tsangayar tasu,

Tsohon ya zauna kan kujerarsa su kuma duk suka zube gwiwoyi ƙasa. ya dubesu kamin yace,”kun makara.” “bamu taso da wuri bane”.suka bashi amsa. ya jinjina kai sannan ya kai dubansa ga kajin da suke ikirarin an kawo, yay musu kallo ɗaya bayan ɗaya sannan yace,”amma ita wannan sumammiyar daka gani daga gidan yunwa ta fito…ko da yake koma dai yane dole za’ai aman kuɗin ƙwatarta, ku tasheta su kuma sauran ku kunce musu ido”. aka kuncewa sauran ido ita kuma Mairo anata zabgeta da mari amma bata farka ba, hakan yasa tsohon ya saki harbin bindiga nan kake ji duk waɗanda akayi kidnapping ɗin sun cure wuri ɗaya jiki na kyarma, take kuma ƙarar harbi na biyu daya kuma saki ya farkar da Mairo cikin ɗimauta da gigita, ta tafi ta rarumo ɗaya daga cikinsu ta cukwikwiye jikinsa tana fashewa da kuka tana faɗin,”Ya Kabiru kazo ka ƙwaceni daga wurinsu kar su cutar dani”. maganarta ta haɗiye saboda yanda wanda ta cure a jikinsa ya damƙo gashin kanta ya barƙalar da wuyanta, tsananin azaba yasa ta buɗe nauyayyun idanunta a wahalce ta dube shi da irin dishi-dishin da take gani. ya doka mata tsawa tare da cewa,”yi mana shiru”. sai kuma ya sake ce mata,”waye Kabiru?”. jiki na rawa ta shiga juya masa kai,”babu kowa a firgice nake ne”. tayi maganar a rarrabe. daga nan kuma duka aka tasa ƙeyarsu zuwa wani ɗan ƙaramin gini me ɗaki ɗaya da mitsitin windo sai banɗaki dake ciki, ana saka su aka janyo ƙofar aka rufe. anan Mairo taga ashe ba ita kaɗai aka sato ba ga sunan birjiki sun kusa kaiwa talatin daga manya har ƙanana kusan Manya ma sunfi yawa, dan idan tana iya gani sosai kusan ita kaɗai ce ma budurwa a wajen. ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka me ƙarfin sauti, nan wata dattijuwar mata dake daga can nesa da ita ta taso tazo kusa da ita ta zauna, ta ɗago kanta tasa hannu tana goge mata hawaye.

“Kiyi shiru ki daina kuka kinji ƴata, adu’a zaki yi Allah ya fitar damu daga wannan musiba amma kuka ba namu bane. idan kika ci gaba da kuka suka jiyo ki zasu zo su harbeki ne suyi miki irin ta wancan yaron”. matar ta faɗa tana nuna mata wani yaro ɗan kimanin shekara takwas yashe a ƙasa.” Kin gansa kuka yake suka zo suka harbe shi kuma har yanzu basu ƙara bi takansa ba alhalin sun san da cewar ya mutu.” Kukan daya ci ƙarfin matar yasa tayi shiru. Mairo ta dubeta tace, “Inna to me muka yi musu?”

Ta girgiza mata kai da cewar,”ba muyi musu komai ba, suna amfani damu ne kawai dan biyan buƙatar kansu, sun manta da cewar akwai wata rayuwar bayan wannan”. ita dai Mairo nata kukan sai ya tsaya ganin wannan matar tana kuka, jikinta duk yay sanyi, bata san da cewar yaron da aka kashe ɗan matar bane. matar ta yagi mayafinta ta ɗaurewa Mairo ciwonta dake tsiyayar da jini har yanzu, dan idan ba ita tayi hakan ba to ko jinin Mairo zai ƙare babu mai kulata.

Kano, Bichi

Yagana na gyara turken awakinta Saleh ya shigo, ta amsa sallamarsa tare da cewar ya shiga ɗaki ya ajiye mata saƙon, ba sai ta fito sun gaisa ba ita yau bata shirya karɓar ciwon kai daga wurin kowa ba.

Saleh ya wuce ɗakinta yana faɗin,”wannan tsohuwa ba zata taɓa sauyawa ba”. har ya aje mata kwanon abincin ya juya zai fita sai ya hangi ledar awara dan haka ya komo ya nemi wuri yay zaman dirshen, yasa awara a gaba ya fara ci, sai da ya kusa shanye ruwan shayin saiga Yagana ta shigo, tayi turus a bakin ƙofa tare da buga salati,”inda raina na sha kallo, me zan gani haka?”. Saleh ya rufe kofin shayin yana faɗin,”Kai Yagana guda huɗu fa kawai naci”. “to daka ci huɗu ce akai mu raba da kai, ƴan bani na iya…mtsww ƴaƴan Zulai ba dai shegen kwaɗayi ba sam bana son zuwanku gidana, ko da yake laifina ne da banje na sanar da iyayen naku ba su daina min aikenku ba daɗin sabga gareku ba…

Ni dai tashi ka fice min a gida tun ban gama harzuƙa ba”. ta faɗa tana raraka shi da muburgi, yay saurin ficewa kamin ta same shi a dukan data kawo masa. ta zauna tana ta jan tsaki da mita akan taɓa awar data ajiyewa Mairo, amma ɗan ƙwal uba yazo ya cinye mata bayan ita ba cin kaɗan take ba, kullum so take ta burge Mairo amma bata iya mata, ta hana cikinta ta ajiye mata ƙarshe Mairo ta karɓa ta kaiwa almajirai ko kuma kai tsaye tace mata hannunki ya taɓa ni kuma ina da tsantseni.

Ta kwashi ragowar awar ta juye cikin kwano tana faɗin, “Allah yasa idan tazo taci, amma wallah tana gani zata ce ci akai aka rage mata alhalin bani naci ba…ni dai Saleh ka cuce ni.”

Maganar tayita da damuwa. har Saleh ya bar gidan sai kuma ya dawo, ya ɗaga labulen ɗakin yace da Yagana,”Gwaggo tace idan Mairo ta tashi taje, idan bata tashi ba kuma ki tasheta tayi sauri taje zasu wuce kano yanzu ” Yagana na jinsa dai bata tanka shi ba, illa a ƙasan zuciyarta data furta,_”kai dama a Ƴaƴan Adamu ai kaine kafi kama da mara lafiya, ashe ma ba iyaka rashin lafiyar jiki bane harda ta ƙwaƙwalwa”._ ita bata yarda da zancen nasa ba a tunaninta shirmensa ne, saboda hakane taƙi ce masa kanzil, sai can dai data ga ya dage ya kafe kan cewar Baba yace idan bai sako Mairo a gaba ba ransa zai ɓaci sannan ta fara sauraronsa, to suna haka saiga Sunusi yay sallama, baima jira Yagana ta amsa ba ya jefa mata tambayar,”ina Mairo?”

Yagana ta miƙe tana gyara ɗaurin zane. “bana son shirmen banza karku cakar min da kai ni ba ƴar sholisho ba, wai wacce Mairo kuke nema ne Mairo da bata kwan anan ba kuma bata doka sammakon zuwa ba.”

Sunusi yace,”Yagana lokacin wasa ayi shi kawai…amma yanzu ana miki maganar Kawu na kano yazo zai wuce da ita asibiti dan haka dan Allah ki bar wannan wasan kije ki tasota, nasan dai tashin nata ne ba kya so shi yasa kike neman fakewa da bata nan.”

Yagana ta kauce daga hanya tana cewa,”ni naga idi zigidir, Sunusi leƙa ciki ka caje har kwanuka ka gani ko zaka ga Mairo…ƙila dai jiya ina mayen bacci nayi tunanin ko ta tafi ne”. Sunusi ya wuce ɗakin ya gama dubansa ya fito bai ganta ba, sannan ya dawo ya ƙara tambayar Yagana tsakani da Allah Mairo bata kwan nan ba, tace da shi”kasan girman Allah bata kwan anan ba, jiya fa muna idar da isha’i ta kama hanyar tafiya…ni abun naku ma ya daina bani mamaki ya koma bani tsoro, yanzu kana so kace min da gaske bata gida”. “wallah tun zuwanta nan jiya bata koma ba har yanzu, anyi tunaninma kota nan ne.”

Yagana ta zabari Hijabi tana jan salati sukai waje tana faɗin,”ni Rakiya na shiga uku, Yarinya kuma ta rasa ata silar wa zata ɓata sai ni marainiyar Allah salan ta jazamin bala’i”. Sunusi yace, “ke waya ce ta ɓata ta sanadinki?”

“Yo gidana fa tazo, daga nan kuma shikenan sai ɓacin rana ta sauka, kaga kuwa ko kame aka tashi Uwarta aini za tasa a kame tunda tasan wurina ta aikota…ohh ni Rakiya wannan musiba da mai tayi kama, ina zaman zamana ɗiyar Adamu zata jazamin jaraba, ita Mairo ba ƙaramar yarinya balle kace ko maƙota ta shiga, ba wayayya ba balle kayi tunanin ko ta bi saurayi, ko kuma ta taho bacci ya ɗauketa a hanya oho.

To Allah dai masani”. haka dai suka ƙaraso gida Yagana nata zuba zantuka da aikin gyara ɗaurin zanen daya ƙi ɗauruwa. tunda ta shigo cikin gidan kuwa ta tabbatar dai da babu Mairo saita kuma yowa waje a rikice. ta rasa me zatayi me ya kamata tayi sai ta rushe da kuka kuma.


Daga cikin gida kuwa Gwaggo tuni ta zama mutum mutumi, ta koma bin kowa da ido, cutar hawan jinin da bata da ita na neman kamata, da dai kunnuwanta suka gama gasgata da gasken Maironta ta ɓata sai ƙafafun dake riƙe da ita a da suma suka gaza, nan ta tafi luuu ta zube Inna Zulai data lura da ita tayi saurin taryota tana ambaton innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.

Gaba ɗaya hankali kuma sai ya dawo kanta, Baba ya ɗebo ruwa aka yayyafa mata nan ta farfaɗo, ta damƙi hannun Inna Amarya wacce hawaye ke sintiri saman fuskarta tana ce mata, “Amarya da gaske ne abunda kunnuwana keji wai Mairo ta ɓata bata nan kusa damu?”

“Insha’Allahu bata ɓata ba tana nan kusa”. cewar Amarya tana ƙoƙarin tsaida hawayenta. Gwaggo ta shiga girgiza mata kai,”ko kusa Amarya, inaji ajikina ɗauke Mairo akai…tarbiyar dana bata ba zaisa tayi nesa da gida ba akaran kanta dole akwai wani abu a ƙasa”. ta juya kan Baba da shima yayi jugum,”

Malam ba zama ne ya kamace ka ba ku tashi a nemo min ƴata da wuri tun rayuwarta bata gama tagayyara ba.”

Yagana dai na bakin ƙofar ɗakin Baba a zaune tayi tagumi idanuwanta duk a kumbure saboda kukan da tasha, ta ƙara sakin wani matsanancin kukan tana faɗin,”Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, ubangiji ka dubeni ka rufa min asiri ka dawo da Mairo gida cikin amincinka…

Idan ya Tabbata ta ɓace ban san ya zanyi ba, Allah ka dubi halin da muke ciki ka jiƙanmu. su kuma azzaluman bayinka da suka ɗauketa kai kasan yanda zaka yi dasu ya Allah kayi maganinsu.”

Ƙanin Malam me suna Mujibu wato autan Yagana ya shigo shida su Sunusi, gida dai ya koma kamar na makoki, ya ƙarasa gaban mahaifiyarsa ya riƙo hannunta yace, “kiyi haƙuri Yagana za’a ga Mairo insha’Allahu.”

Sannan suka maida bayaninsu ga Baba, “Daga wurin Mai Anguwa muke, yace a hanzarta aje a shigar da report a ofishin ƴan sanda.”

Baba ya miƙe yana sakin hannun Gwaggo, ko kaɗan tashin hankali bai bar fuskarsa ba, yayi ta maza ne kawai wajen haɗiye rauninsa, jiki babu ƙwari yabi bayan su Mujibu suka yi ofishin ƴan sanda. suna fita Yagana ma ta miƙe tana faɗin,”ai banga ta zama ba Mujibu ku tsayani ƙafata ƙafarku.”

Tana tafe tana haɗa hanya sai jin goshinta tayi ƙumm ajikin garu nan kuwa ta sake rushewa da kuka tamkar ta shiɗe faɗi take. “ni dai to duk wanda ya sace Mairo Allah ka tattara duka tsinuwarka ka ɗora masa, dan wallahi ba zan yafe ba”. ta dubi maƙociyarsu Gwaggo tana nuna mata goshin tace,”ƴar nan duba min naji kaman ya ɓurma ciki ko?”. matar tasa hannu zata lailaya mata gudun karya kumbura Yagana ta danƙara mata zagi.

“Ya daga cewa ki duba min kuma sai ki nemi hanyar da zanbi na mutu banje neman Mairo ba ayi ba wan ba ƙanin, ke kuwa wannan ƴa da ƙeta kike.” Matar tace,”yi haƙuri Yagana.”

“Allah dai ya yafe miki kawai amma cuta ce ai kin cuceni”. ta kunce bakin zane ta ɗauko ɗari biyar ta bawa Lukman tace,”maza ka karɓo ƙosai ayi sadaƙa Allah ya bayyana mana ita nan kusa kuma cikin amincinsa, dan Allah Lukman karka ci kaga na sadaƙa ne”. shi dai kuɗin ya karɓa ya fice da sauri shima hankalinsa duk bai jikinsa, dan Mairo ta wajensa ce.

Har kusan azahar su Baba basu dawo ba, daga nan kowa ya ƙara sarewa da ɓatan nata, Gwaggo dai na sheme sai firfita ake mata tana fitar da numfashi sama-sama.

Kulu na daga cikin ɗaki ta jingina kai da bango, idanuwanta sun kaɗa sunyi jazur, tsabagen tashin hankalin da take ciki ma hawayen sunƙi zuba, sai jakar kayan Mairo data zubawa ido, cikin ranta tana cewa,_”yanzu shikenan Hussaina kema na rasaki, ya zakuyi min haka, a lokacin da nake tsananin buƙatarku dukanku na rasa Hassan na tsira dake, kin kasance tare dani kema yanzu kin zama babu…banji da sauƙi ba wajen haihuwarku, ki taimaka ko dan wannan ki tausaya min ki dawo gareni, ba zan yanke tsammani da rasaki ba kamar yanda na yanke tsammani Hassan, ke kaɗai kika rage min bani da kowa, ke ɗaya ce jinina da nake ganin naji daɗi, na rasa kowa nawa da komai na…ya Allah kaine shahida ka duba rayuwar da nake ciki ka dawo min da Hussaina.”

Duk yanda tayi trying hard tayi controlling tears nata abun ya gagareta, sai ta fashe da kuka tana roƙon Allah ya kula mata da ƴarta a duk inda take ya kuma dawo da ita garesu cikin amincinsa, sai dai ta gama resolve kan matsawar rana ta faɗi Mairo bata dawo ba to zata bi bayanta ne.

To Fah!!! Masu karatu the Saga begins…

Wa kuma ya san me zai faru next, Mairo zata dawo kuwa? Haka kawai aka ɗauketa ko kuma sanyawa akai a saceta? ko Kulu zata bayyanar da kanta a matsayin da take da shi ga Mairo? Kai to waima tsakanin Gwaggo da Kulu wace Uwar ta haƙiƙa ne?

<< Sirrin Boye 17Sirrin Boye 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×