Skip to content
Part 6 of 25 in the Series Sirrina by Khadija Muhammad Shitu (K_Shitu)

Wani mugun zufi na gaske ramin yake dashi, tun da suka faɗa basu jisu ƙasa ba, sai da suka ja kusan mintuna ukku.

Da ƙarasowa macizzan basu yi wata-wata ba suma suka faɗo ramin, Wani wuri mai manya manyan bishiyu, gurin babu komai sai korayen shuke masu tsayi, faɗowa sukai a wani uba mai kama da rijiya, suna faɗawa murfin abun ya rufe kansa.

Gudu sahash ke yi na fitar hankali, har ta ƙaraso kogon da ta saba zuwa.
Cikin ƙasƙas da kai ta sunkuyawa ƙaton halitar dake zaune alamar girmamawa, ɗaga gabjejen ɗan yatsansa ya yi, alamar amsawa.

“A Halin yanzu na aikata duk kan abun da ka umarce ni, na zuba jinina a kabarin Nazaan, amma izuwa yanzu ban ga wani chanji ba…”

Wata dariya ya fara yi mai ban tsoro da firgitarwa, “Hahhaha! Dole zaki je JAZAL Ki ɗauko makullin sirrin daga kin yi haka dukkansu zasi dawo ƙarƙashinki, ayi yaƙi kiyi nasara masarautu ukkun su zama naki…”
“Amma a ina tekun yake?.” “Babu wanda ya san duniyar da tekun yake, amma akwai wata sarƙar sirri da zarar an same ta, zata yi jagora da farin tsun-tsun har zuwa wannan tekun, zaki haɗu da hatsarori masu ban tsoro da waɗan da baki taɓa cin karo dasu ba ko’a tarihi.”

Cikin nuna jarumta ta ce “Zan jure zan yi ƙoƙari zan jure duk wuya da tsanani na…” dariya fashe da ita “Yaro man kaza! zaki fara bincike ta inda jiniknki zai miko amfani.” Dogayen yatsu ya chaka mata a tsakiyar tafin hannunta, jini ya fara zuba wani ƙoƙo yasa ya tarbe, ya miƙo mata. Amsa tayi ta fiddo wani ƙaramin ganye ta saka jinin, “Tashi ki tafi ki aikata komai cikin zafin maita…”

NAHAAR
Mahaifiyar Karan ta dubeshi tana faɗin “Karan! ka aikata abun da ya dace kuwa? har yanzu shiru nake ji babu wani matsi ko bayani.”

Numfashi ya ja ya ce “Kiyi haƙuri ranki ya daɗe ina ƙoƙarin na dai-daita kom…”, “dakata! kar layi kuskuren faɗa man Aliya ce a zuciyarka. na faɗa maka a karo na ba adadi ka rabu da ita amma da yake ban isa na faɗa maka zance ka aminta ba ka kasa haka ko?.”

“Haba saauniyar nahaar ba hakan nake nufi ba in son na dai-daita yanda komai zai kasance dan gane da yanda masarautun ukku zasu cure gu ɗaya su zama mallakinmu.”

“Za ka iya ni na sani karan.”

“Ko mai zai faru ba zan taɓa baro Arman ka auri Zulmah ba, suna burin kanai-naiye mu don samun damar ɗanɗanar mulki ne kawai.”

Duban ta ya yi cikin damuwa ya ce “Mai martaba ya riga da ya furta dole na aureta, ni na tsaneta tsana mai muni ina jin tamkar na shayar da dabbobi jininta, Kimin alfarma dan girman abin bauta, ki dakatar da hakan”.

“Kar ka damu Arman hakan ba zata taɓa faruwa ba”. tana gama faɗar hakan ta fice zuwa gun mai martaba fuuu.

Bar bayyana ko’ina ba sai gaba mai martaba, cikin huci take duabnshi tana faɗin “Naji kana wani furuci akan Arman! to a gaskiya ba zan taɓa iya bari ɗana ya Zulmah ba koda hakan na nufin zan bar nahaar ke nan na har abada.”

Zama ya yi ya ce “Tabbas! dole ne ya aure ta koda zai rasa rayuwarsa nayi wannan alƙawarin. ke kuma zaki iya barin nahaar a duk sanda kika so.”
“haka kace?.” “haka na ce, ko akwai abun da zaki iya yimin.”

Wani shu’umin kallo ta bishi dashi, kawai a ɓace ba tare da ta tanka ɓasa ba.

HIZAAR
Sarki ahal ne ke ta kai kawo zuciyarshi babu daɗi komai ya chunkushe masa, ita kuma sarauniya halsha ta hakimce bisa kujera ta zubo masa idanuwa tana sauraron tambayar da ya ce zai mata.
“Halsha wai yaushe ne komai zai wuce? ina son naga na ɗauko muhimmiyar fansa, Amma cikin gogaggun hatsabiban sheɗanun nan babu wanda ya tashi cikinsu. hakan na nifin gwagwarmayar da muka sha shekaru bila’adadin ta tafi a banza.”

Murmushin ta saki ta wani kanne idanuwa cikin izza ta ce “Haba sarkin hizaar ya zaka kasya cikin sanyi haka? Tsohuwa ta tafi duniya sihiri tana mana muhimmin bincike inda zamu samu wani tsun-tsun da zai kai mu tekun jazal.”

“Amma kina tunanin za’a yi nasara….”
Dariya kawai ta fara bata bashi amsa ba.

“Sanaam ki dakata! kar ki yi wannan kuskuren A rayuwarki, hatsarin sarauniya Rahash ya fi ƙarfin tunanin ki, chutar mata da ɗanta karan da kike ƙoƙarin yi zai iya yin silar ki…”

Duk yadda Sarauniya kunjam ta so dakatar da sanam da yinƙurin chutar da karan amma ta kasa, hakan ta nufe ta da niyya taɓa ta, tun kafin ta idasa kai hannunta da niyyar janyeta daga bakin ruwan, wani abu ya jata zirr mai azabar zafi tamkar shocking.

Sanam tsaye take har lokacin bakin ruwa tana wani irin sihiri, Wata baƙar hoda mai haddasa tari da sarƙewar numfashi ta fesa a ruwan sannan tabi ta sake karyayyun akaifu, sannan ta fiddo dogon halshenta wanda ya tsage gida biyu ta sanya shi cikin ruwan.
Wani kalar tsanwan abu ne ya fito daga idanuwanta ya daɗe yana ɗigewa cikin ruwan sai wani turiri ruwan yake yi.

Girgiza ta yi tana duma hannunta ta yi tsakiyar ruwan, wani tafarfasa ruwan ya yi ta tsame hannuwanta, ta busa iska ruwan ya ɓace.

Sai sannan a juyo ta kalli sarauniya kunjam ɗin, da ta daskare sna mata wani kallo mai cike da mugun mamaki.

Wani shu’umin murmushi a sakar mata, ta ratsa ta gefenta ta ɓace.
Tashin hankali sarauniya kunjam ta shiga va na wasa ba, ta san Rahash farin sani bata da kirki ko kaɗan tana da wani irin ƙarfin iko, wanda ya yi matuƙar zarra.

Zaune karan yake suna fira da sarauniya Rahash Kawai kamar daga sam wasu ruwa kamar yayyafi masu azabar zafi rau suka, zubo masa, suna shiga cikin idaniwanshi yaji wani irin raɗaɗi, duhi ya bayyanan masa, komai ya ɗauke masa.

Bai yi wata-wata ba ya fara murza idanuwanshi yana kiran sunan mahaifiyar tashi.

Cikin ruɗewa ta ce “Karan lafiya! mi ya samu idanuwan naka ne?.”

Cikin jin azaba ya ce “Duhu!! Nake gani kina ina.” kallon idanuwanshin ta yi, a gigice dan a rufe suke gam. “Kana nufin baka gani yanzu?.”

Numfashinsu ne suka ji yana ‘ko’karin ɗaukewa, ga duhun dake gun ko tafukan hannayensu basa iya gani, Tari ya fara sarƙe ta bumdshina ya fama ƙoƙarin barin gangar jikinta.
A galabaice ta tuno da ƙarfin sihiri bata tsaya ba, ta shafo bakinta da tafukan hannayenta ta furzo da iskar waje suka ji wata irin iska mai daɗi, wani abu mai kauri kamar allura ta zaro daga cikin gashinta, ta laluba taji wani guri wanda bata da abun da zas fasalta shi, cakawa tayi iya ƙarfinta duk da bata iya ganin komai.

Ruwa ne ya fara feso musu inda ta fasa mai yawan gaske har bata iya zan numfashi, ɗaga hannun rigarta tayi ta jayo igiyar tsafi ƴar siririya mai kaurin sosai.

Chaka abun tayi ta yi ruwa na shigo musu mai yawan gaske, jin da ƙyar yake sauke nuɓfashi ya sata Lalubenshi ta sakar masa igiyar alamar ya riƙe, tare suka riƙe igiyar da ƙyar suke fizgar numfashi.

Ruwan ne ya kawo musu har wuya, da azama tayi sama sannan ta koma fanjam cikin ruwan tare da nutsewa ciki.

Ruwa suke yi kawai amma har lokacin basu yi nasarar ficeea daga cikin abun ba, sun nutsa sosai chan ƙasa suna yin ruwa.

Da ƙyar da suɗin goshi suka fara bugewa da duwatsu, har suka ji manayan luluyayyun duwatsu a ƙasan, da ƙyar su kansu basu san abun da ya faru ba sai farkawa suka yi suka tsinci kawunansu a ƙasan wani ƙatob dutsi kusa dasu kuma tazara ce marar yawa tsakaninsu da wani ruwa mai gudana.

Ruwan wani irin fari me tas ɗin nan gaahi daga jiki wani dutse yake zubowa, daga sama mai ɓatuƙar ɗaukar hankali dan ƙasan da ruwan yake ya kai manyan filaye biyu dan bas ma hango ƙarshen ruwan.

Daga bayanasu wata ƙasa ce mai kwachaɓi ta haɗe gu ɗaya, Duk gurin ya jamule ba kyan gani kwata kwata.
Wata ƙatuwar kada suka hango mai wani irin girma, jibgegiya guda ga baƙaƙrn idanuwa sai ƙarshenta kamar bindi abun da wata kanannaɗar mai yankan reza. Ja da baya suka soma, ganin irin yanda ta dunfaro su.

Da tari ya farka rana ta dalle sa yana jin ɗan gumi-gumi, hakan ya sa yai saurin tashi wata rana ce mai kyawun gaske ga tsananin haske, duban sa ya maida kan Aliya wacce gashi ya rufe mata fuskarta, ɗan mayafin kuma ya rufe mata santala-santalan cinyoyin ta masu tsananin kyau da sheƙi. A hankali ya yaye gashin fuskarta ta bayyana, ma sha Allah ya furta cikin zuciyarsa saboda tsananin kyawunta mai tafiya da zuciya, kallonta ya shiga yi tun da yake a rayuwa bai taɓa ganin wacce ta fita kyau ba, tunani ya fara tabbas a cikin film ɗin india actress ɗin da irinta ke nan basu da wani banbanci, gwana ce a fannin rawa da waƙa, sannan mutane na mamakin farintan nan da ya yi ɓau yai mugun ƙara mata tsantsar kyau.

Cikin barci ta ji, kamar ana kallonta hakan yasa ta fara motsi, ganin hakan ya ɗan fara mata taɓi a hankali wajen fuskarta yana mai kawar da kanshi gefe.

Zumbur ta tashi tana mai jan rigarta, sannan tayi rolling ɗin mayafin ya ɗan rufe har rabin fuskarta, ta tashi da yunwa abu na farko da ta fara tambayar kanta ina ne nan, ina kuma jakarta take.

Chan ta hango jakar iska na kaɗa ta saura kaɗan ta faɗa ruwan dake tafiya da mugun gudu, cikin azama ta fara sassarfa har ta isa ta ɗauko jakar wata ƴar ƙaramar ƙwarya ta fitar daga jakar, mai tsananin kyau.

Buɗewa ta yi wani farfesun yan ciki ne ciki mai ɗaukar ido yaji albasa iya albasa da niƙaƙƙen yaji, ɗauka ta yi takai bakinta, wani lumshe ido tayi jin sihirin bai kare ba akwai ɗan ɗumi-ɗumi, tana cin abincin ta hankali kwance shi kuma ya tsaya yana kallonta, waigowa ta yi ba tare da tayi magana ba ta miƙa masa, alamar ya ci karɓa ya yi bai tsaya jan aji ba dan ya san yana matuƙar jin yunwa ta gasken-gaske.

Yana kaiwa bakinshi ya ɗan lumshe ido a hankali, yana tambayar kanshi wane irin girki ne haka, da alama ba maggi gishiri ne kaɗai kuma kaɗan suka saka, amma duk da haka akwai daɗi, da sauri ya ci abinci yana gamawa ya miƙa mata ƙwaryar, ta karɓa.

Kusan A tare suka tashi suka nufi, bakin ruwan amma daga baki-baki inda babu yalawarshi da yawa. Sun ɗebi ruwan mai daɗi sosai ga sanyi-sanyi mai ratsa zuciya, sun sha sun wawwanke fuska da ƙafafuwansu, haka suka ɗiba a cikin ƙwaryar da suka wanke, sannan suka miƙe zuwa inda suke.

Ɗaukar jikkarta ta yi ta fara kalle-kalle, Rasa ma inda zasu nufa suka yi, sai ƙarewa gurin kallo suke, tabbas sun shigo wata duniya ta daban. A halin yanzu kowa cikinsu na jin kuzare hakan yasa suka bada himma suka miƙe suka ci gaba da tafiya ba ji ba gani.

Tafiya suke ba ta wasa ba jin ɗan sauri wanda bai yi yawa ba, sun nutsa sosai a tafiyar tasu, wani yashi-yashi mai mugun taushi ya jiƙe suka fara takawa.
Suna takawa da sauri jin sun fara nutsewa ciki ya sanya su saurin kallon ƙasan, ƙafafuwansu sun fara shigewa, da sauri aliya ta fara ƙoƙarin yin gefe tana jan ƙafafunta da ƙarafin gaske, wata ƙatuwar kunama ce ta fara doso ta mai girman gaske.

Ta kasa miƙewa tsaye sai ja take yi da baya-baya, ta kai gargara ke nan ta riƙe wani dutsi rabin jikinta ya faɗa ƙafafunta sun faɗa cikin ruwan sun nitse kanta kaɗai ne da hannuwanta ta a waje ta riƙe dutsin gam.

Ta baya Yarima haydar ya kore kunamar sannan ya miƙa mata hannuwansa alamar ta riƙe, a hankali cikin dabara ta miƙa hannu ɗaga, ya fara janyo ta.

Ji tayi kamar wani abu ya riƙe kafar ta ɗaya gam ya sata waiwayawa bayanta, ta razana matuƙa ganin mugun girman ruwan da tayi ga inuwar wani ƙaton abu da ya riƙe mata ƙafar.

Wani irin uhu ta kurma ganin, gun sahun jini-jini kamar an cinye ƙafar ta, a kiɗime ta jawoshi suka faɗa fanjam ba tare da tasan tayi hakan ba.

<< Sirrina 5Sirrina 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×