Skip to content
Part 11 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Yana fita y’an ajin suka fara tofa albarkacin bakin su, har da masu cewa ‘ai tayi sneaking ta shigo da waya dan da gani free call suka kwana suna yi jiya shiyasa daga ita har shi idanuwansu suka nuna alamun rashin barci. Wata Ramlat wadda hostel d’insu d’aya kuma k’awar Zainab ce k’ut da k’ut ta ce

“Tab! Yanzu girman kai zai k’aru, su o’o ba’a da had’add’en saurayi ma ana kallon mutane a kan hanci, ballantana yanzu anyi..”

D’agowa Zainab tayi ta kalleta a take tayi shiru bata k’ara cewa uffanba. Abinda ya bawa Maryam mamaki shine har suka koma hostel, aka yi lesson na evening, suka sake fitowa night prep kwata-kwata Zainab bata ce mata uffan akan maganar ba. Sai dai kawai ta ga tanata yawan kallonta.

Straight jss2 ta nufa tana shiga ta gansa a zaune a gefen sit d’inta kamar koyaushe.

Yana jin shigowa ya d’ago kai ya kafeta da ido har ta k’araso ta zauna ta gaidashi. A hankali ya amsa sannan yace “Ya hannun??

Itama a hankali tace “ da sauk’i.” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e jakarta domin da d’auko littafi ta samu ta fara karatu.

Littattafan d’azu ya mik’o mata yace “gashi, gobe sai ki bata nata ko?!”

D’agowa ta yi ta kalleshi sannan ta d’auka littafin ta bud’a da niyyar ta d’an k’ok’arta ta kwafa, saboda Yarinyar har ta fara mata maganar littafinta wai ‘tanaso za tai karatu’, amma kawai sai ta ga wani had’add’en rubutu ya baiyyana daga dai dai inda suka tsaya, dubawa tayi tai comparing da na k’awar tata taga Note d’in nata ya zama complete, kallonshi tayi taga shima Itan yake kallo da murmushi a kan fuskarshi kafin yace “Ko ban iya rubutu ba?”.

Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba saboda yadda yayi maganar yana wani langab’ar da kansa, kuma harga Allah tayi mugun jin dad’in taya ta d’in da yayi dan bata san ya za tayi ba, bata da wanda zata rok’a ya tayata dan kusan kaff y’an class da room d’insu daga safe zuwa yanzu kamar haushin ta duk suke ji wanda ita bata san dalilin su na Jin haushin nata ba.

Ganin tana murmushi kawai ya tsaya yana ta kallon ta dan ji yake kamar kar ta daina.

A hankali ganin ya kafe ta da ido tace “Ni ka daina kallo na.”

D’auke idanunsa yayi daga fuskanta yana murmushi….idanunsa suka kai
kan hannun rigarta, da yake da d’an jini jini a jiki tun na jiya, har zai tambayeta dalilin da ya sanya bata wankeba sai ya tuna da hannunta, kuma a yadda take da shiru-shiru d’innan ya san ba zata iya saka Junior wanki ba. Dan haka kawai sai yace mata.

“Ki dinga kawo kayan wankin ki zan na kai miki wajen wanki har zuwa lokacin da zaki warke .”

Murmushi kawai tayi tace mishi “to”

Sannna yace duk note d’in da bata yi ba ta kawo, da kyar ta bashi na physics, ragowar kuma tace “za ta k’ok’arta da hannun hagu.

Har aka tashi suna hira yau kam ta sake dashi, hakan kuwa yayi mishi dad’i sosai.

Washegari kam da bata zo da wankin nata ba taga b’acin ransa matuk’a, dan kicin-kicin yayi, kuma ko da aka tashi da kyar ya yarda ta tafi bayan ya sanya ta ta rantse akan washegari za ta kawo.”

Hakan kuwa aka yi, washegari ta saka a leda ta sako a skul bag d’inta ta kawo mishi.

Ko da yaje gida akwai washing machine, ga dry cleaning a arean da wajen wanki dai kala-kala, amman haka Abba ya zage ya tik’i wankin nan nata da hannunshi, abinda bai tab’a yiba kenan tun tasowarshi, cook d’insa kam da mai yi masa gyaran gida tsayawa suka yi suna kallon ikon Allah, dan babu yadda basu yi da shi ba akan ya kawo su wanke ba amma sam ya k’i.

A wajen ya zauna ya jira ya bushe, ya kwashe ya tafi d’aki ya goge mata, yana yi yana murmushi.

Haka nan ya mayar da abun aikin sa, note da wanki shi zai yi mata ko jinkiri ta d’an yi wajen kawowa ya dinga mita kenan yana fushi, hannun nata ya warke amman kwata kwata ya hanata wanki k’arfi da yaji.

Zuwa yanzu shak’uwa sosai ta shiga tsakaninsu, bak’in jini kuwa a wajen y’an class da hostel d’inta ta kwasheshi ba ‘a magana, dan zuwa yanzu kowa ya sani saboda indai ya shigo aji har ya fita hankalinshi gaba d’aya yana a kanta suna had’a ido kuwa zai sakar mata murmushi ba ruwanshi da inda suke.

Ganin da yayi shak’uwa da sabo ya shiga tsakaninsu ya yanke shawarar fad’a mata shifa sonta yake yi, duk da ya san zuwa yanzu ta fahimci hakan, amman dai gara ya fad’a mata baki da baki.

Dan haka ya yanke shawarar sai ranar da za a tafi hutu tukun nan zai gaya mata daganan ya karb’i land line d’insu (idan suna da shi) ta yadda za su dinga communicating.

Ranar hutun kuwa! Sunyi ita da shi a kan za su had’u 11, amma sai aka yi rashin sa’a ana bud’e gate motar gidansu ce ta fara shigowa, abunda bai tab’a faruwa ba. Suna hostel ma lokacin suna shirya wasu kayyayakin su metron ta zo ta kira su, a gurguje suka k’arasa shiryawa suka yiwa ragowan mates d’insu sallama.

Kamar kullum Madu da ya Usman ne suka zo d’aukar su kasancewar shi Ya Jamilu ba mazauni bane ba, daman tun kafin yayi wayo yake nacin zama soja shiyasa tun yana k’arami su Madu suka mik’a sa NDA.

Tana isowa bakin Admin ta hango Ya Usman wanda tun fitowarta shi already ya riga ya ganta ya kafeta da ido yana tsaye da Madu a gefensa, tana k’arasawa ta fad’a jikin Madu ta rungume sa, sannan ta juyo ta gaida Ya Usman, itama Zainab hugging Madun nasu tayi sannan ta yi huggin Ya Usman shima wanda yake ce
musu “suyi sauri su shiga su kama hanya.”

Sai da suka shiga motar tukunna suke ji, ashe ‘Madu da Shuwa da Ya Usman ne za su tafi Hajji, jirginsu 7 na dare zai tashi yau shiyasa aka zo d’aukar su da wuri dan a samu a kintsa komai a kan lokaci’ Ai kuwa nan suka hau murna.

Usman shi yake driving amman har kusan zubar da su yayi a hanya tsabar yadda gabad’aya hanakalinsa ya tafi kan Maryam wadda ta fara gajiya da kallo da murmushin da yake da zuba mata ta glass d’in saman motar tun tasowarsu.

A haka suka iso gida, ita Maryam gabad’aya zuciyarta a cunkushe take saboda rashin yin sallama da Abba, shi kuma Usman mamakin girma da kyan da Maryam d’in ta k’ara yake yI, .dan haka yana shiga gida bayan an d’an yi oyoyo ya samu Baaba Talatu da maganar “shifa gaskiya ya kamata a fara maganar auren su shi da Maryam.”

Har sai da Baaba Talatu ta fara yi masa tsiya tana cewa “shi, ko irin y’ar kunyar nan baya ji??”, Tukunnan ta samu ya kyaleta ya tashi ya fita yana murmushi.

K’arfe 5:30 kuwa, da Baba Bashir da Ya Jamilu da Maryam da Zainab da Bilkisu wadda take kuka sai ta bi Shuwa, suka rankaya suka yi musu ranki ya zuwa Airport. Sai da suka zo rabuwa tukunna itama Maryam taji kwalla na shirin zubo mata, dan haka ta yi saurin barin wajen.

Suna komawa gida, Baaba Talatu ta saka Maryam ta k’arasa had’a kayanta da na Bilkisu, daman Shuwa ta kusa gama had’awa, kafin su tafi. Suna gamawa kuwa aka rufe gidan suka dawo gidan Baba Bashir.

Sai yanzu Maryam ta gano tabbas son Abba take yI, ta yi mugun dana sanin rashin yi mishi kwatancen gidansu da tayi, babu yadda bai yi da itaba amman ta k’i.

Duk da cewa bai tab’a gaya mata ba ta san shima yana sonta. A haka da kyar a daddafe take gurgura hutun Allah Allah kawai take yi a koma.

A b’angaren Abba kuwa kusan d’an k’aramin hauka ya yi, ya je gandun albasa sau babu adadi, yana tambayar gidansu Maryam Muhammad amman bai samu ba (kasancewar Maryam d’in a file dinta ne kawai take amfani da Muhammad).

A haka aka kusan gama hutun yanata faman zirga zirga, daga k’arshe kawai rashin lafiya ta rufesa, sai da yayi doguwar jinya tukunna ya samu kanshi, yana ta Allah Allah a koma makaranta, dan duk tsawon rayuwarshi bai tab’a ganin hutun da aka yi yayi masa masifar tsaho kamar wannan ba.

Haka aka yi Sallah lafiya, a tsakanin Zainab da Maryam in dai sun yi magana tou a gaban mutane ne, sanin yadda Maryam take son Bilkisu ne ya sanya haka kurum idan Zainab ta lura ba kowa a wajen sai ita da Maryam kawai sai ta hau dukan Bilkisu, haka kurum ba abinda ta yi mata duk dan kawai ta bak’antawa Maryam rai, ita kam Maryam sai dai taje ta janye Bilkisu uffan ba zata ce da itaba, domin itakam yanzu sha’anin Zainba ba ya d’ad’ata da k’asa.

Yau tun safe a gidan Baba Bashir aketa shirye shirye, dan sun yi waya da su Shuwa yau za su taso tun asuba amman har wajen d’ayan dare shiru. Washegari ma shiru, wata washegarin ma haka!

A haka har aka shafe sati d’aya da kwana biyar.

Zuwa wannan lokacin y’an unguwa kowa hankalinshi ya tashi Baba Bashir kam shi da Jamilu shiryawa suka yi suka nufi Abuja.

Baaba Talatu kuwa sau uku ana mata k’arin ruwa, idan ka ga Maryam, Zainab, da Bilkisu sai baka tausayi, basu da aiki sai kuka, yau kam har da Baaba Talatu aka zauna ana shan kuka. Baaba Laraba wadda ta shigo ita da Sadiya ba da jimawa ba ne suke ta basu baki, duka kuwa itama Sadiyar kukan take yi.

Abun ya yi musu yawa gashi Babba Bashir da Ya Jamilu ma da suka je Abuja yau kwanan su hud’u suma basu dawo ba, ko ta landline ba su kira ba.

Suna cikin kuka kawai suka ji ana bud’e gate, da sauri da sauri suka hau rige rigen fitowa tsakar gidan, suna isowa suka ga motar Baba Bashir.
K’arasawa suka yi bakin motar da sauri, ta cikin glass d’in suka hango su Shuwa, ai kuwa da kyar suka iya barin su suka samu suka fito dan duk sun rufe motar ana ta kukan murna.


Sai da suka nutsu suka huta, sannan Madu ya hau basu labari…
“A cikin room mate d’in Usman na hotel d’in da suka sauka ne aka kama cocaine a jakar wani, shine aka kama Usman dan mai jakar yace shi ba tasa bace ba ta Usman d’in ce.
Har an tafi da Usman d’in sai wani bawan Allah d’an Nigeria (ambassador) ya tsaya musu tsayin daka dan yaga alama larabawan suna k’ok’arin yin son kai ne saboda wanda aka kama da jakar balarabe ne shima, amman d’an morocco.
Bawan Allahn nan da ya tsaya musu shine ya bada kud’in beli, mak’udan kud’i ba kad’an ba, sannan ya d’auko y’an rahoto aka tafi airport aka nemo vid wanda cctv camera ta yi capturing ranar da suka isa k’asar.
Allah ya taimaka ba a ga Usman da jakar ba, iyaka jakankunan su shi yake tare da. Bawan Allah bai bar wajen ba sai da ya tabbata an binciko video na ranar da wannan Yaro d’an Morocco ya zo, ai kuwa sai ga jakar ta fito a hannun wata Yarinya wadda ta zo tararsa, suna gaisawa ya amsa jakar suka ci gaba da tafiya suna hira.”

Baaba Talatu ce cikin tarar numfashin Madu, ta ce “Shi kuwa wannan bawan Allah wanne irin godiya kuka yi masa? a gaskiya ya kamata mu d’unguma gaba d’ayan mu muje gidansa domin yi mishi godiya”.

Usman ne ya tari numfashinta ta hanyar cewa i wallahi Baaba, abinda zai baki takaici, mutumin ya na gama had’a takardun komi da komi ya dank’a a hannun Abba Madu, yace su je su taho da ni. Tun a hanya da ake ba ni labari nake ta son in zo in ganshi dan ban ma san wacce kalar godiya zan yi masa ba, amma muna zuwa airport d’in bamu same sa ba sai note kawai ya rubuta yace a bamu wai ‘emergency ya taso mishi, ya tafi, an kwantar da k’aninsa a emergency.’
Su kuma suka k’i su bamu information a kansa ballantana mu ga garin da ya tafi, saboda kin san babban mutum ne. Amman na san garin a yake ba zai wuce Abuja ba.”

Shuwa ce tace “ai ba lalle Abujan ba, kawai dai yanzu muyi ta saka shi a addu’o’in mu muna yi mishi fatan alkhairi, inda rabo wata rana za a had’u ai.”

“Haka ne kam!” Cewar, wadda ta k’i tafiya ita da Sadiya sai da suka ji kwakwaf.

Haka dai kowa yayi ta tofa albarkacin bakinsa, sannan aka ci gaba da murnar dawowar su, daga baya Madu da Shuwa suka tafi gida, aka bar Bilkisu da Maryam a gidan Baaba Bashir saboda gidan ya yi k’ura sosai, aka bari akan washegari idan an gyara sa dawo.

A ranar Ya Jamilu ya koma saboda daman saboda case d’in ya dawo kuma akwai abubuwa da dama a kanshi.

Da daddare wajajen 8 Ya Usman ya aiki Bilkisu yace ‘ta kira mishi Maryam’.

Tana zaune tana tunanin Abba Bilkisu ta shigo ta fad’a mata sak’on Yayan nasu ta juya ta fita wajen Baaba Talatu.

Da farko kamar ba zata je ba, sai kuma kawai ta mik’e ta fita.

A can waje babban tsakar gida ta iske shi zaune a kan tabarma, gefen sa ta nema ta zauna ta gaida shi sama-sama
tunda ga nan daga ‘um’ sai ‘um um’.

Ko ba a gayawa Usman ba ya san cewa Maryam ta chanza mishi, dan gaba d’aya hankalinta baya gareshi, shi gani yayi ma kamar haushinsa take ji, dan tunda ta fito bata yi mishi dariya ba.

Da kyar! Ya samu ya kawar da tunanin da zuciyar shi take k’ok’arin dasa wa kwakwalshi, dan shi dai ya san makarantar mata take yi, babu maza ballanta tayi saurayi! Da wannan tunanin ya sallameta ya sanyawa ranshi maybe ko bacci take ji yau d’in.
Amman ga mamakinshi washegari ma haka ta yi mishi, wata washegarin ma haka, sai da aka shafe kwana biyar suna a haka.

Da yaga abun yayi yawa yau sai ya chanja lokaci, around 4 na yamma ya aika aka kirata a zatonsa ko yana hanata bacci ne amman yau sai yaga ma b’acin ran da take ciki ya fi na kullum, dan tun daga nesa ta had’e rai!

Ita kuma Maryam a nata b’angaren takaici ne ya rufeta, shi wannan Ya Usman d’in baya tashi kiranta sai ya daidai ci daidai lokacin da take tsakiyan tunanin Abba..

Kasa jurewa Usman yayi, hakan yasa ya ce mata, “Maryam anya har yanzu kina sona kuwa?”

D’agowa tayi ta kalle shi, kafin ta yi k’asa da kanta ta fara tunanin.

‘Gara fa ta fad’a mishi gaskiya, ita daman chan ba son shi take yi ba! Kar taje su yi aure tana tunanin wani ta yi ta kwasowa kanta zunubi!’

Wata zuciyar ce tace mata ‘to ke Abban aka ce miki sonki yake yi? ko ya tab’a gaya miki ne?’

Da sauri ta rumtse idanunta dan she can’t begin to think of the fact that wai Abba baya sonta! Sai yanzu ta kuma tabbatar wa kanta ta kamu da sonshi ba kad’an ba, dan da basa had’uwar nan ta yi kewarshi ba k’adan ba!’

“Maryam kin yi shiru. Muryar Ya Usman ta katse mata tunani.

Bud’e idanuwanta ta yi wadanda har sun chanja kala.


Zuwa yanzu kam tabbas Ya Usman ya fara kaita bango, domin kuwa ita
gaskiya bata son naci babu abunda ta tsana kamar takurawa, bata son yawan magana! Kuma ya sani.
Shiyasa a makaranta ake mata kallon mai girman kai, mutane ma dayawa tsoron mata magana suke yi karta yarfa su, a cewarsu masu kyau daman ance girman kai ne dasu.
Itakam basu san kawai yawan maganar ce bata so

“Hmmm, tou inaga dai kin d’auko kuramen aljanu a boarding d’in taku.”

Ya Usman ya sake fad’in haka.

A yanzu kam ta gama yanke shawarar.
‘Ko Abba baya sonta, za ta fad’awa Ya Usman gaskiya dan in dai ta aure shi a haka tabbas ba zata iya yi mishi biyayya ba, hakan yasa a hankali ta sago ta kalleshi!

Ya kuwa kafe ta da ido ko kyaftawa baya yi, nauyin shi taji shiyasa ta maida kanta k’asa ta fara magana a hankali.

“Ya Usman ka daina cewa ba na sonka, Ina sonka a matsayinka na d’an uwana mana, ai kai Yayana ne.”

Shiruuuu!! Ne ya wanzu a wajen, dan ya kai kusan mintuna biyar bai ce mata uffan ba, ita tama yi tunanin ya bar wajen ne dan haka a hankali ta d’ago tana juyowa kuwa suka had’a ido! Gabanta ne yayi mugun fad’uwa sakamokon idanuwansa da taga sun koma tamkar garwashi, bata gama fassara yana yin da fuskarshi take ciki ba taji yace “A matsayin saurayin ki fa? Mijin da zaki aura uban Ya’yanki??”
Ya yi mata tambayar yana mai kallon cikin kwayar idanuwanta.

K’arya ba halin Maryam bace ba, zuwa yanzu ta so ta d’an b’oye masa ko dan halin da taga yana shirin shiga a cikin y’an mintunan da basu gaza goma ba, amma sai ta tsinci kanta da girgiza mishi kai.

Wannan karon ta tsorata dan hawaye ta gani ya sauk’o ta idonsa d’aya, bata ankara ba taga d’ayan ma ya sake sauk’owa. Da sauri ya mik’e ya bar wajen yayi cikin gida ba tare da yace mata uffan ba.

A hankali itama ta tashi ta bi bayanshi tana mai jin wani nauyi yana sauk’a daga kan m k’irjinta.

Sai da tayi kwana biyar bata sake saka Ya Usman a idonta ba, a lokacin kuma sauransu kwana d’aya su koma makaranta, mutumin da tun tasowarta in dai yana gari to sai yazo gidansu sau hud’u a rana.

Tana zaune tana had’a kayanta a jaka Shuwa tace “ta je ta kira mata Zainab, Abba Madu yace a tambayeta idan akwai abinda take buk’ata bayan provision d’insu.”

Tana shiga gate d’in gidan gabanta ya fara fad’uwa, ba kowa sai motar Baba Bashir a parke a chan gefe, a hankali ta k’araso ta tura k’ofar k’aramin tsakar gidan ta shiga, nan d’in ma ba kowa. Har ta wuce zata isa k’ofar d’akin Zainab, ta ganshi yana fitowa daga corridor d’in kitchen da plate a hannunshi, bata san dalili ba kawai taji jikinta ya fara rawa kamar wadda ta yi laifi, sosai take mamakin ramar da yayi, tana tafe tana waigen shi dan a tunanin ta zai yi mata magana, bata yi auni ba kawai taji ta yi tuntub’e ta kusa fad’uwa, da sauri ta saita kanta ta tura k’ofar d’akin Zainab ta shige.


Wani abu da ya bata mamaki shine tabbas ta san Ya Usman ya ganta to amman kuma mai yasa bai ce mata komai ba?! Har fa kusan fad’uwa tayi amman bai kulata ba! Mutumin da ada idan ana hirar tsakar gida ko sauro baya so ya hau jikinta, ya dinga yi mata fifita kenan har a tashi.
Yo ai ko babu soyayya shi Yayanta ne so ya kamata ace ya kulata, lallai indai hakane kuwa to hakan yana nufin Ya Usman yayi zuciya kuma da alama ya hak’ura da ita kenan, a cikin zuciyarta tace “barka na”.

“Malama lafiya? Za ki shigo babu sallama?”

Muryar Zainab ta katse mata tunaninta.

Sak’on Shuwa ta fad’a mata, bata jira amsar da zata bata ba ta juya kawai ta fito gudun rikici dan yanzu kam itama bata ragawa Zainab.

Har ta kai k’ofa, sai kuma ta kalli y’ar barandar da zata kaita d’akin Baaba Talatu, tunani ta yi akan bari ta shiga su d’an gaisa dan haka ta nufi k’ofar d’akin nata! Tana isa bakin k’ofar ta saka hannu kenan zata tura taji muryar Ya Usman yana cewa “Baabaa to ai ni a tunanina share tan da zan dinga yi kamar zai janyo mini in sake fita a ranta ne, yanzu fa har kusan fad’uwa tayi ban kula ta ba, ku…”
Cikin fad’a fad’a taji Baabaa Talatu tana cewa “Yanzu Usman ina uwar ka amman ba zaka bi abinda nake gaya maka ba? Yo ai maganar fita a rai kuma ta faru ta k’are! Sai dai bayan auran ku ka nuna mata so ta yadda zata dawo kamar da, ka ji ai da kunnenka Zainab ta ce ‘Yaron balarabe ne!’ Shi ne ya rud’eta, kawai abunda nake so da kai shine ka nuna mata kamar ka hak’ura ta yadda za ta sakankance, ni iya in sha Allah da kaina zan je in samu Madu, ba zata k’are makarantar nan ba sai da auranka a kanta bi izinillahi. Ka kwantar da hankalinka, dan k’ank’aninka da kai ka bi ka d’aga hankalinka! Ai kana ji dai abinda Likita ya ce ranar ‘jininka ya yi mugun hawa, Allah kad’ai ya taimaka baka samu stroke ba, lokacin da ka fad’i ka suma wallahi na d’auka mutuwa ka yi, nayi mugun tsorata. Zancen banza ma kenan!!! Ita daa chan ta san ba ta sonka amma shine ta bari aka kawo har i yanzu?? Kodayake na san ba yin kanta ba ne ba, wannan Yaron ne yake neman juya mata tunani. Amma ba komai na san abunda zan yi kai dai kawai ka kwantar da hankalinka kaji ko??”

A hankali ya ce “to Baaba.”

Jin kamar zai fito yasa Maryam ta yi saurin barin wajen ta fice tana tafiya tana share hawayenta, da kyar ta kai gida dan har wani duhu-duhu take gani ga jirin da yake k’ok’arin zubar da ita, tana shiga ta wuce d’akin su ta kwanta a kan gado ko bi ta kan kayanta da take had’awa bata yi ba.

Banda tashin hankalin da take a ciki sosai mamakin Baaba Talatu ya turnik’e ta yake juya mata Kai! Tabbas tsakanin ‘da da uwa sai Allah, Baaba Talatu da take nuna mata tsananin so
har fa dukan Zainab take yi saboda ita amma wai yau itace take shirin k’ulla mata auren dole kawai dan taga d’anta ya suma, wata zuciyar ce tace mata ai itama tana da tata uwar, taje ta fad’awa Shuwa tun kan ayi mata auren dole.

Da sauri ta shiga girgiza kai ita kad’ai dan ta san yadda gidansu da nasu Baba Bashir yake, irin tsananin shak’uwa da zumuncin da yake tsakani ba na wasa bane ba, ita kanta ba ma ta san ba brothers bane iyayen nasu sai kwanaki da suka je Maiduguri karkarsu take fad’a mata.

Tabbas kuwa ta san Shuwa ba zata d’auki wannan shirmen nata ba.
Sai a lokacin ta fahimci kuskurenta, ta kuma gane ta d’aukowa kanta hanyar da ba zata b’ulle ba dan ta san iyayenta ko giyar wake suka sha ba zasu tab’a hana Usman itaba. Kamar ma Shuwa da Madu sun fi son Usman a kaf cikin y’ay’an Baba Bashir, don gashi Madu ya biya mishi hajji sun tafi tare ko Baba Bashir d’in bai biya ma ba.

A take ta yanke shawarar rabuwa da Abba duk da ta san za ta sha wahala, dan da wuya in wannan ba shine ajalinta ba, amman ya ta iya?
a haka bacci ya kwasheta sai la’asar ta farka.

Toilet ta fad’a ta yi alwala ta fito ta yi sallah, sannan ta mik’e ta yi waje, a hanyar kitchen suka had’u da Shuwa tana tsugunne kan kujera a bakin kitchen d’in tana gyaran alaiyyahu.
Gaidata Maryam tayi sannan ta zauna a kan takalmanta tasa hannu ta fara tayata.

Lokaci zuwa lokaci Shuwa tana lura da ita, sai da suka gama har za ta mik’e ta kai kitchen ta ji Shuwa tace
“Zauna Ina so za mu yi magana”

Da sauri ta kalleta sai kuma ta koma ta zauna a kan takalmanta da tayi kujera da su.

Cikin nutsuwa Shuwa ta ce,

“Mai yake damunki?

D’azu naga kin shigo kina kuka!
Ga idon ki duk sun kumbura.
Da alamun kukan kika yi ta yi ko?
A zuwa yanzu na san kin daina yiwa Zainab kuka dan haka ba matsalarta bace ba, ko?”

A hankali ta d’aga mata kai alamar ‘eh’.

“Fad’a min to? menene?”

Inji Shuwa.

Shirun da Maryam ta yi ne yasa ta sake tambayar ta tare da cewa “Ko kinada wadda ta fini da za ki gayawa?
Kin manta tun lokacin da Zainab ta daina k’awance da ke na yi miki alk’awarin na zama babbar k’awar ki?”

Cikin murmushi Maryam ta share kwallar da ta zubo mata tace “a’a”
A hankali Shuwa ta kamo hannayenta duka biyu sannan tace “fad’a min to, menene?”

Tun daga ranar da ta had’u da Abba ta hau gayawa Shuwa har yau d’in nan bata b’oye komai ba.

A hankali Shuwa ta sauk’e ajiyar zuciya, bayan Maryam d’in ta gama, sannan cikin nutsuwa tace “Maryam na san menene so, kuma zan so ki auri wanda kika ce kina so a yanzu, amman idan muka yi haka da ni dake da babanku za a yi mana kallon butulu.

Abu na biyu kuma ki yarda dani idan nace miki, har yanzu kina son Usman, tunda ai da kina son shi, kyale-kyale na wanchan Yaron shi ya rufe miki ido har kike nema ki guji Usman wanda na san in sha Allah bayan auranku komai zai daidai ta.

Sannan abu na uku, wanchan
Yaron daga yanayin labarinki na fahimci d’an masu kud’i ne, na gaske! Maryam ke Yarinya ce har yanzu, Yaran masu kud’in nan b’atawa mutum lokaci kawai suka iya.
Tabbas idan kika bincika already akwai yarinyar da zasu aura wadda aka riga aka had’a su dan basa tab’a yarda su auri y’ay’an talakawa.

Shawara ta anan shine ki auri Usman, ki zauna a cikin y’an uwan ki, ki manta da batun Abba kar ki bi zuciya ki zama butulu, daa chan baki ji rashin son auranshi ba sai yanzu? Usman zai kula da ke, tun kina k’ank’anuwar ki yake d’awainiya da ke dan zan iya ce miki laulayi da nak’udarki ne kawai Usman bai yi ba amma har Goya ki yake yi, kashi da fitsari babu kalar wanda baki yi masa ba.

Kiyi ta Addu’a za ki ji zuciyarki tana yin sanyi, kinji ko? Allah ya yi miki albarka.”

A hankali tace “Ameen.”

Ta yadda kuma ta gamsu dukkanin abunda Shuwa ta fad’a gaskiya ne, sai dai kuma tana ta so tace mata itafa tun farko daman murnar da taga suna yi ita da Baabaa Talatu ne ya sanya ta yarda da soyayyar ya Usman, amma sanin ko ta fad’a hakan ba lalle a fahimce ta ba tunda da chan bata fada ba sai yanzu da take son rabuwa da shi saboda Abba, hakan ya san kawai ta yi shiru ta mik’e ta koma d’aki.


‘Tana shiga ta nemi bakin gado ta zauna a hankali ta sauk’e ajiyar zuciya, sannan ta ce “Abban ma da nake ta abu a kanshi maybe ma shi bai san m ina yi ba.”

A haka dai sukuku ta k’arashe wannan ranar washegari da sassafe Ya Usman da Ya Jamilu wanda ya dawo jiya da daddare suka maida su makaranta, har suka juyo Kano Usman ko kallon inda take bai yi ba, Ya Jamilu ne dai duk da ya kasance Soja baya yawan dariya amman hakan yayi ta janta da hira ganin kamar tanata tunani.

Ana gama checking d’in kayanta ta fara k’ok’arin kaiwa hostel.

Isowarta bakin Unity gate kenan kamar ance ta d’aga kanta gabanta ya yi mugun fad’uwa sakamokon had’a ido da suka yi da Abba, ya kafeta da ido da alamun ya dad’e da ganin tahowarta, yana zaune gefen house mistress d’insu wadda ta mayar da second checking d’abiarta dan duk dawowa hutu bayan an gama duba maka kaya a main gate to itama sai ta sake nata a bakin Unity gate.

Da alamun checking d’in yake tayata, amman sai magana take yi mishi hankalinshi baya wajenta har sai da ta d’an zungureshi tukunna ya mik’a mata abun hannunshi ya taso ya taho inda Maryam d’in take, tana k’ok’arin k’arasowa wajen tana k’ok’arin kaucewa ya sha gabanta, had’a ido suka yi tana mamakin ramar da taga yayi, taji yace “Maryam I could hug u right now! Kin san yadda na dinga nemanki kuwa? You said za mu had’u 11 tun 10 nake Admin Ina jiran ki har kowa ya tafe, and now kin ganni k’ok’ari ma kike yi ki wuce kawai ki tafi, bakiyi missing d’ina ba??”
Ya yi mata tambayar yana kallon ta da yanayin sa kamar na mai shirin yin kuka.

Ahankali tace “sir, i want to pass, u are blocking my way.”

Shek’ek’e!! haka ya tsaya yana kallonta, anya kuwa Maryam ce? to ko dai wani abun yayi mata ana I gobe hutun, maybe ma shiyasa ta tafi ba ta jirashi ba.

Yana cikin wannan tunanin yaga tana k’ok’arin zagaye shi ta wuce.

Shan gabanta ya kuma yi, sannan yace “Wai me yake damunki ne? Kin san halin da na shiga kuwa? Ina ta Allah Allah a dawo makaranta don in sake ganinki, wallahi kinji na rantse har a asibiti na kwanta, all because of u and yanzu shine za ki zo mini da wannan sabon attitude d’in?

“To wallahi baki isa ba! Idan ma wani misunderstanding ne u better talk mu yi clearing d’inshi right away cos u can’t turn your back on me like this, ba zan iya jurewa ba, not now, not ever!!!”

Ya fad’a da d’an k’arfi da alamun ranshi ya soma b’aci.

A hankali Maryam cikin sanyin ta, tace “Y? Meye had’ina da kai?”

Ga mamakinta sai taga ya fara murmushi, kafin yace “do I really have to say it?”

Yayi mata tambayar yana kafeta da idanuwanshi data kasa jurewa kalla ta yi k’asa da kanta.

Y’an tsirarrun students ne a wajen, most of them ma y’an ajin su ne, kasancewar sai yamma sosai ake cikowar dawowa, sai house mistress d’in da take checking.

Tafa hannunwanshi Abba ya fara yi yana cewa “attention everyone.”

Cikin k’ank’anin lokaci ya had’a kan y’an mutanen wajen da basu da wani yawa, sai da ya tabbatar attention ya dawo kansu sannan ya durk’usa a gaban Maryam, ya sago yana kallonta ya fara magana.

“Maryam i Found the reason for my smile, the day i found you! In you, my life becomes whole, with you my days become bright. In your hands i would love to lay, for the rest of my life, you’ve got everything i’ve been searching for in life, i would love for you to grow old with me! The best is yet to be and it begins from the moment you say yes! I love you, so much Maryam, will you please be my soulmate?, will u marry me?, will u stay with me till death do us apart??”.

Ai kuwa nan students suka hau tafi, suna “Say yes, Maryam say yes!!”
Ihun su ne yasa house mistress d’in ta k’araso wajen.

“Stand up!” Ta ce mishi.

A hankali ya mik’e, tukunna tace “you know all this is not allowed right?”

Cikin sanyi jiki yace “yes”

Murmushi yaga tayi sannan tace “but I’m willing to sopport you a hundred percent, because I’ve never seen a perfect match like yours! But don’t do too much of zance at school because it’s not allowed, don’t cause problems for her, you can visit her as much as u want whenever she gets back to her fathers house.”

“Ok.”

Ya cewa house mistress d’in yana d’an murmushi sannan ya ce “tnx”.

Kamo hannun Maryam tayi tace “ta wuce hostel tayi freshening up, kafin wannan oyinbo boyfriend d’in nata ya hanata.”

A hankali ta wuce…Abba k’ok’ari yake su had’a ido amman tak’i ta bashi damar hakan.

Sai da suka yi kwana biyu tukunna aka fara night prep, ta so ta yi dodging kawai tayi class d’insu amman sai ta kasa.

A hankali ta k’arasa js2, tun ta window ta hango shi zaune wajen zamanshi, yana hango ta ya kafeta da ido har ta k’araso.

Cikin nutsuwarta ta gaidashi ya amsa mata yana kallonta.

Bayan sun d’an gaggaisa sun d’an yi hira tana ta jin nauyin sa ita dai, yace mata ”ya baki fito da wankin ki ba?”.

Da mamaki ta kalleshi tace “ai yanzu na warke!”

Kicin kicin yayi da kyar da nacin da yayi ta zuba mata washegari ta kawo mishi wanki.
*****
Duk wani gatan da ya dace Abba yana tabbatarwa ta samu, sai dai kamar yadda house mistresses d’insu ta fad’a mishi, baya takurata sosai gudun kar ya ja mata matsala, kuma itama house mistress d’in ta rufa musu asiri kar ya bata kunya, hatta prep d’inma yanzu sai ranar karb’ar wanki da dawowa da shi ne kawai yake zuwa, yana bada tazarar kwana bibbiyu dukda yana takura da hakan amma ya san hakan shine dai dai.

Soyayyarsu suke yi gwanin burgewa, Maryam ta ma manta ta wani Ya Usman sannan tunda yanzu Abba yace yana son ta,za ta fad’ama Shuwa itafa daman chan ba son Ya Usman take yi ba, don haka a d’aga mata k’afa. Addu’ar ta d’aya Allah yasa su fahimceta su kuma yadda da Abba.
Kamar kullum yau ma suna zaune a night prep suna y’ar hirar su, yake bata labarin yayanshi da irin son da yake yi masa, har yake ce mata yace masa first born d’inshi in Namiji ne takwara zai yi masa.

Murmushi tayi ta ce, “D’an gatan Yaya.” Tana dubanshi ta k’asa k’asa, dan a yanzu kam kunyarshi takeji kwana biyun nan, kuma take ji bata bari ta kalleshi dan suna had’a ido zai ce mata I luv u.

Garin kallon ne ta kalli fingers d’inshi, sai taga sun d’an kumbura ba kamar koyaushe ba, hakan yasa tace masa
“Mai ya samu hannunka?”

One thing about him bai iya k’arya ba, dan haka ya hau bata labarin tun ranar da ta fara bashi wanki, yadda yake wankewa da gogewa ya ce “maybe yawan tab’a ruwa ne ya sa hannun nasa ya yi haka” shi kam ya ma manta bai kamata ya gaya mata hakan ba.

Maryam haushin kanta ta fara ji, dan a yanzu kam yadda Abba ya damu da ita itama ta san sarai ta damu da shi.
Dan haka tayi fushi yayi yayi ta k’i kulashi, har aka zo tashi.

Ganin tana shirin mik’ewa yasa shi ya rik’e mata jaka, ya fara bata hak’uri, ganin ya k’i sakin jakar kuma Yara har sun fara kallonsu yasa ta koma ta zauna.

Sai da aka gama fita tace “zan hak’ura amman ba zan k’ara kawo maka wanki ba, ai hannun ya warke.”

Shi kuma yace “ba zai barta ta tafi ba har sai ta rantse zata kawo wankin, dan ba zai barta ta dinga shan wahala ba.”

Wasa wasa basu ankaraba, kawai alarm d’inshi na 11 wanda yasa dan lokacin exercise d’inshi kenan b4 going to bed kawai sukaji yana k’ara.

Maryam da taga time a firgice ta mik’e, ko sauraronsa ma bata yi ba ta suri jakarta tayi hostel tana adduar Allah yasa ba a rufe ba.

Shima Abba ganin yadda duk ta rud’e kuma yaga dare yayi yasa bai tsaida ta ba, ya tattare kayan shi ya tafi.

Adduar ta kuwa ta karb’u, dan ba a rufe unity gate d’inba sannan hostel d’insu ma ba a rufeba. Room d’inta nema aka rufe dan sai da tayi knocking tukunna Zainab ta bud’e mata.

Tana ganinta ta juya taje suka ci gaba da hira da ragowan mates d’insu ba tare da ta kalleta ba.

Fitsarin daya isheta tun a chan ga kuma tsoron daya sake ingizo shi yasa itama bata kalli Zainab d’inba kawai kan gadonta ta nufa ta ajjiye jakarta ta zari torch ta fice ta nufi toilet.

Bayan ta gama fitsarin ne taga ashema period d’inta ya d’auke, daman yau take expecting hakan ko gobe da safe, kasancewar ana tsula sanyi ga duwatsun garin na kusa da makarantar, ta san ba zata iya yin wanka da Asubah ba ga kuma isha hakan yasa kawai ta koma d’akin nasu
taje k’asan gadonta ta jawo bokiti mai ruwa. Towels d’inta guda biyu data sak’ale a jikin bunk ta kai hannu ta zari d’aya, ta wuce toilet ta je ta yi wankaan ta, ta dawo.

Hular kanta da ta yi sharkaf da ruwa ta cire, gashin ya zubo.
Ita dai ta san ta bar towel d’aya a jikin bunk amman da tazo da nufin d’auka domin tsane gashin kanta, sai ta neme shi ta rasa…dube dube ta fara yi har su k’asan gado, tana d’agowa suka kusan yin karo da Zainab tana mik’o mata towel d’in, sannan tace

“Sorry na wanke face d’ina ne kuma duk towels d’ina sun yi datti shine na ara na goge fuskana, ungo.”

Murmushi Maryam d’in tayi tasa hannu ta karb’a. Zainab d’in ce tace mata, “Me za kiyi ba ga wani a jikin ki ba?”

“Gashina zan tsane”

Ta bata amsar tana k’ok’arin fara goge kanta. Bata kawo komai a ranta ba, ta hau goge gashin da towel d’in, har ruwan ya d’an fallatsar wa Zainab.

Juyawa Zainab d’in tayi ta nufi Majalisar su.

Ita kuma Maryam sai da ta gama gogewa ta nad’e shi a kanta ta shiga corner d’inta ta shafa mai ta saka kaya, tayi addua abinta ta kwanta.

Har lokacin tana jin k’us k’us d’in maganar su Zainab dan ba suyi bacciba amman a hankali
suke maganar sunata k’us k’us, daga bayama tashi Zainab d’in tayi ta fita ita da wata k’awarta,ita dai Maryam bata san lokacin da suka dawo ba bacci ya kwasheta.

Kiran sallar farkon da aka maka a mosque d’in dake tsakiyar hostels d’in ne ya farkar da ita daga baccinta mai cike da mafarkin Abba, ‘yana ta zuba mata murmushi ya rik’e hannunta yana janta ita kuma ta kasa zuwa garesa, kamar akwai wani abu da yake janta baya’, haka ta ji a mafarkin.

                   

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 10So Da Buri 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×