Skip to content
Part 12 of 70 in the Series So Da Buri by Bulama

Da ‘bell’ ta yi amfani wajen tashi y’an hostel d’in nata tukunna ta wuce ta yi alwala ta fice mosque.

Sai da gari ya d’an yi haske tukunna y’an mosque d’in suka fara dawowa. A hanya ne wata roommate d’insu da suka fito daga mosque d’in tare take ce mata “gaskiya Maryam kin b’ata wayonki, ban yi expecting haka daga gareki ba, gashi yanzu kin janyowa kanki! Allah kad’ai ya san hukuncin da za’a yanke miki.”

Da mamaki Maryam take kallonta kafin tace “Ban gane ba Hafsa, mai nayi?!”.

Tsaki Hafsat d’in tayi kafin tace “Ai ga irinta nan, daman Zainab ta fad’a.. k’aryata mutane zaki yi! Ni dai shawara ta idan an je wajen principal ki rungumi laifinki, dan wallahi kin san halin principal idan kika yi mata k’arya laifin ki k’aruwa zai yi.”

Zuwa yanzu kam gaban Maryam ya fara dukan uku uku gashi sun iso bakin gate d’in shiga hostel, hakan yasa tayi saurin rik’o hannun Hafsat tace “Hafsa dan Allah d’an tsaya, kin saka ni a duhu, kiyi mini bayani, sai magana kike ta yi a baibai.”

Har Hafsat ta bud’e bakinta zata yi magana, wasu y’an mata biyu suka fito da bokiti a hannunsu, suma duk y’an d’akinsu ne, kallonsu sukayi kafin d’ayar tace, “Ah lalle Hafsa, me ake koya miki? lalube ko shafa mai??.”

Hararar su Hafsat tayi sannan ta cire hannunta a na Maryam ta yi cikin hostel ba tare data waiwayi kowa ba.

Su kuwa dariya suka saka sannan suka nufi unity tap d’in dake tsakiyar hostels d’in domin d’ibar ruwa.

Ita dai Maryam har ta shirya taje dining aka nufi assembly ground, duk tayi sukuku, k’ok’ari take yi ta fassara kalmar ‘lalube ko shafa mai’ amman ta kasa, saboda amsar da kalmar take bata ba abu ne mai ma’ana a tsarin rayuwar da take yi a makarantar ba.

Ana shirin roundin up assembly d’in Principal ta rambad’a kiran sunan ta a mic tace kar taje class ta sameta a office d’inta.

To fah!! Dan yanzu kam Maryam ta gama rud’ewa.

Da kyar a daddafe ta k’arasa office din principal d’in, gaba d’aya jikinta in banda karkarwa ba abunda yake yi, gashi gabanta sai fad’uwa yake.

Knocking tayi, ta ciki aka bata izinin shiga.

Tana shiga mamaki ya kamata sakamokon ganin Abba, metron da house mistress d’insu duk a zazzaune a cikin office d’in.

Da kyar ta iya k’arasawa ta zauna ta gaishesu, principal d’in ce kawai ta iya amsa ta Abba kuwa kanshi a k’asa yake tunda ta shigo, bai d’ago ba.

Gyaran murya principal d’in tayi sannan ta mik’o mata wata takarda, tace mata “ta karb’a tayi signing.”

A hankali ta mik’e taje ta amsa, tun kafin ta dawo wajen zaman ta ta fara dubawa, ai kuwa bata iya k’arasawa wajen zaman nata ba sakamokon rikicewar da ta sake yi tashi d’aya ta shiga matsanancin tashin hankali.

Karantawa take yi tana sake duba takardar ‘expell’ d’in da aka bata ga sunanta b’aro b’aro a jiki, hankalinta bai gama tashi ba sai da taga dalilin korar! “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un” shine abinda ta fara maimaitawa idanunta na zubar da kwalla, a hankali ta k’araso ta durk’usa a gaban teburin principal d’in ta fara magana muryar ta na rawa “Ma, wallahi this is not the truth, pls don’t expel me, i promise I won’t talk to Abba ever again!. I don’t want my parents to find out about this. I have been framed here I swear…”

Cikin rashin walwala principal d’in ta ce mata, “Don’t worry your parents already know about this since yesterday, they are on their way now as we speak.”

Rushewa Maryam tayi da kuka, ta fara magiya, tana cewa “sharri aka yi musu” tana alk’awarin rabuwa da Abba har abada, amman principal d’in bata saurareta ba kawai dai tace mata “Ita fa ta riga ta gama magana, so ta jira zuwan iyayenta kawai.”

Metron kuwa munafuka in banda zuga principal babu abunda take yi, hadda cewa “ai ranar tun a clinic ya fara rungumeta. Waye-waye” Sai faman zuba dai take yi, ba ita tayi shiru ba sai da principal ta aiketa ta je ta kira Zainab da wasu class mates d’insu.

Su Zainab sun shigo bai fi da minti goma ba Madu da Shuwa da Ya Usman suka shigo.

Da gudu Maryam taje ta fad’a jikin Shuwa tana kuka tana cewa “wallahi k’arya ake mata.” Kama kafad’unta Shuwa ta yi sannan ta ajjiyeta a kujerar gefe, ba tare da tace da ita komai ba! Ta k’arasa suka je suka zazzauna a kan kujerun suka gaisa da mutanen wajen.

Bayan an gama gaisawa ne principal d’in tayi gyaran murya ta nuna Zainab ta ce”, Yarinyar nan ta zo ta sameni last week akan maganar sister d’inta da wannan Yaron” ta yi maganar tana nuna Abba kafin ta d’aura da cewa “I was surprised because irin haka bai tab’a faruwa ba, dan it’s a very strict rule ‘ba a soyayya tsakanin malami da d’alibi’! I don’t know why they choose to break the rule. I called their house mistress first, Ina so ince mata ta sakama yarinyar ido but to my surprise sai take ce mini ‘ai ta riga ta sani already, amman kawai dai gaisawa suke yi, kuma basa zance. Ya dai ya fad’a mata yana sonta ne amma basa soyayya a makaranta because she warn them and sun yi biyayya da abunda ta fad’a’ She gave me good reasons, wanda reasons d’in da ta bani ne ya sa na yi deciding to just let it go, duk da na san it’s not allowed but kamr yadda tace if basa soyayya a makaranta I see no reason da zanyi interfering.

After two days ina zagaye da daddare, wanda ba kowa ne ma ya san ina yin hakan ba, saboda ina yi ne to make sure all is fine. A time d’in na bi ta jss2 block and I saw them together, I know Maryam very well tunda shadow prefect d’inmu ce and Abbas shima ba b’oyayye bane shiyasa nayi saurin gane su. Ban ji d’ad’in yadda na gansu ba! He was holding a book tana so ta karb’a ya hanata, and they are sitting too close to each other! Na so inyi musu magana but a yadda raina ya b’aci a time d’in sam bana zan ma iya kallon Yaran. So na yanke shawarar fara yiwa house mistress d’insu magana first, i was very disappointed a ita da su.

So, na sameta nayi mata magana and ta gaya mini cewa ‘wallahi bata san suna zama guri d’aya ba, that was when I called their metron, and she told me ‘ai tun time d’in da Abba ya fara zama night prep tare suke zama kullum, and sometimes they even hug, kuma basa tafiya sai kowa ya watse, in sun gama abinda zasu yi’.”

Kukan Maryam ne ya k’aru kafin tace “wallahi k’arya ne, Hajiya Shuwa dan Allah ki tsaya kiji nawa kar ki yarda da maganar su. ”

Cikin tsananin b’acin rai Ya Usman ya ce “Wallahi Maryam idan bakiyi mana shiru ba sai na b’abb’allaki a nan!!”

Ganin yadda ya taso yayo kanta kuma taga alamar ranshi a mugun b’ace yake dan bata tab’a ganinshi a irin wannan yanayi ba, ya sanya ta yi shiru, ta hau k’ok’arin tsaida kwallarta ta.

Numfashi principal d’in taja sannan ta ci gaba “Na kira 2 to 3 children a js2 and sunce gaskiya su basu tab’a ganin komai ba, kawai dai basa tafiya tare da su kamar yadda metron tace.

So hankali na ya d’an kwanta but dukda haka sai na kira Zainab saboda Ina son sake jin bayaninta dan Insan ta Ina zan fara “A nan ne ma take sake tabbatar mini da cewa ‘ai Maryam d’in already tana da mijin da zata aura a gida!.’

Na kira Yayan Abba dan in fad’a mishi halin da ake ciki ince ya yiwa Abban magana ko In d’auki mataki, amma wani abun mamaki kamar had’in baki sai shima yake gaya mini cewa ai shima Abba tun bai kai haka ba already Mahaifinsu ya zab’a mishi wadda zai aura cousin sister d’insu, kuma kowa ya san da maganar.
Shi Ya’yan nasa ma he was very surprise da yaji wai Abba yana soyayya da wata.

So definitely kunga ba soyayyar gaskiya Maryam da Abba suke yiwa juna ba kenan, ko?.

A time d’in bana son yanke hukunci cikin sauri, shiyasa na saka Zainab da those two” ta yi su maganar tana nuna k’awayen Zainab da suka shigo tare, tukunna tace “nace su saka musu ido sosai.!

Yesterday around 11 metron taje gidana, saboda nace musu ko k’arfe nawa ne idan abu ya faru su sameni a gidana na quaters in dai inanan…

Banji dad’in abinda metron ta gaya mini ba at all, although shine abunda nake suspecting but Maryam is one of our best students sannan d’a na kowa ne. Kasa bacci nayi da jin maganan metron that’s why nima kawai immediately na nemi land line d’inku…”

Shiruuuu!! kowa yayi kafin principal d’in tace “Zainab, ku maimata musu abinda kuka fad’a mana.”

Zainab ce tafara magana “daman kullum idan ya shigo aji sai yayi ta kulata, tun yana b’oyewa har ya daina, tou akwai k’anwar k’awar mu a jss 2 itace ta fad’a mana abunda suke yi, itace ta zo ta samemu jiyama tun kafin a tashi tace wai gashi chan ya d’auketa sun fita ba a san ina suka je ba!.

Mun yi ta jiranta a hostel bata dawo ba, daga k’arshe dai sai after 11 tukunna suka dawo kuma data shigo har wanka tayi dan sai da na tab’a gashinta na tabbatar!. Shiyasa naje na samu metron ita kuma tace yanzu zata je wajen ki ba sai gobe b..”

Sai a lokacin Abba ya d’ago kai ya kalli Zainab da idanuwanshi da suka chanja kala..wanda hakan ne ya sa ta kasa k’arasa maganar ta.

House mistress d’insu ce tace “amman ku, kun tabbatar fita suka yi kuwa? Because d’azu da sassafe naje wajen gateman yace min jiya Abba shi kad’ai ya fita kuma sai wajajen 11.”

Da sauri Zainab tace “Ai gidansu na coppers na staff quaters suka je…”

Ita kam Maryam zuwa yanzu muryarta har ta dishe tsabar kuka!! Madu ne ya kirata yace “ta zo!” Tana zuwa yace “Da gaske ne???”

Da sauri ta fara girgiza kai tana kuka, abin tausayi… Metron sarkin zuga tace “ki ji tsoron Allah har wanka fa suka ce kin yi!”.

Cikin k’ok’arin son fahimtar da su Maryam ta ce “Eh nayi wankan amman wallahi ba wank…”

Bataga k’arasowar Ya Usman ba sai sauk’ar marin da taji wanda yasa ta fad’uwa a wajen gefen bakinta ya fara zubda jini, tana k’ok’arin tashi taga ya sake yunk’urawa da nufin rufeta da duka.

Ta gama sadak’arwa tana jira taji sauk’ar dukan! Jin shiru yasa ta d’ago, Abba ta gani ya kare mata a hankali ya sunkuyo kanta ya kamo hannunta ya mik’ar da ita cikin tafin hannun nata ta ji yana cusa mata takarda karb’a tayi tana kallonshi shima Itan yake kallo da idanuwanshi da suka yi jazir!! A hankali yace “I luv u Maryam.”

Bai tsaya jin fad’an da su metron suke mishi ba na ‘ya kama hannunta a gaban iyayenta!’ Kawai ya juya ya fita.

Madu ne ya cewa Shuwa su tashi su tafi, hakan yasa ta mik’e ta yiwa principal sallama wadda take ta bawa Shuwa hak’uri tana cewa “She is just looking out for Maryam, ba dan hakan ba da ta barta a makarantar, gara ta tafi gidan iyayenta su saka mata ido.”

Jinjina kai Shuwa tayi sannan tace “ba damuwa.” Ta juya ta fice.

Ko kayanta su Shuwa basu bari ta koma hostel ta d’auko ba, cewa suka yi ‘Zainab ta taho mata da shi’. Haka nan tana kuka tana komai suka shiga mota aka ja aka yi gida da ita.

Zainab kuwa yau farin ciki a wajenta ba a cewa komai, murna take yi ai tunda Maryam ta tafi to fa duk wata hanya da zata bi sai ta bi ta cusa soyayyar ta a zuciyar Abba, kasancewar yau suna da period d’inshi daman yasa tun kafin su k’arasa class ta tsaya ta wanke fuskarta a tap, aka yi y’an shafe-shafe, k’awayen ta suka duba suka tabbatar mata tayi kyau tukunna aka nufi class ana tunanin hanyoyin da za a bi a karkato da zuciyar Abba gareta!

Sai dai kuma har period d’inshi ya shiga ya fita bai shigo ajin ba, washegari ma haka, a haka suka shafe kusan sati babu Abba babu alamar shi.

Zainab har office d’inshi taje ta tarar a rufe. Haka ta dawo jiki duk ba kwari zuciyarta ta a cunkushe, haka take rayuwa a makarantar gaba d’aya komai baya mata dad’i, sauk’inta d’aya ma ba Maryam.

A b’angaren Maryam kuwa tun da suka shiga mota take kuka har suka isa gida, a tunanin ta za a yi mata fad’a ko duka amman ba wanda yace mata komai, amma fa ko gaishe da Shuwa ko Madu tayi a cikinsu babu mai amsa mata, ko suna zaune idan ta zo ta zauna to zasu tashine su bar mata wajen, hatta Bilkisu da suka shak’u sosai a duk lokacin da Shuwa ta gansu tare sai tazo ta d’auketa ta kuma hau yi mata fad’a, tun Bilkisu tana kulata a b’oye har ta daina saboda a d’aki Shuwa take sakata ta kunna mata kallo, ko girki an daina girkawa da Maryam a gidan!

A wajen mutum d’aya kawai take samun sauk’i itace Baabaa Talatu dan a gidan ta ma take cin abinci sai kuma Ya Usman wanda yake wani sabon shige mata kwana biyun nan ta kasa gane mishi kwata kwata, itafa ko ba Abba ba zata auri Ya Usman ba! She is not suppose to be feeling this towards Ya Usman amman she can’t help it, kawai ita all she knows bata sonshi kwata-kwata bata sonshi ba zata iya zaman aure da shi ba.

Yau satinta d’aya da kwana d’aya da dawowa daga boarding, gabad’aya duniyar ta yi mata zafi, zuwa yanzu rashin kulata da iyayenta suke yi ya fara bata tsoro dan har ta rame ba kad’an ba.

In ba wajen Baaba Talatu taje ba tou kullum tana d’aki ita d’aya.

Yau ma ganin shiru zai haddasa mata wata damuwar bayan wadda take ciki ya sanya ta yanke shawarar fita dan shan iska ko ta samu ta d’an ji sauk’i.

Hijabinta ta d’auka ta nufi wajen Baaba Talatu, tana shiga a babban tsakar gidan ta had’u da Ya Usman tare da wani Abokin sa suna hira yana ta dariya, ta dad’e bata ga dariyar sa irin haka ba, tun kafin ta k’araso taji yana cewa “To kai ba ka tsaya wasa ba?! Kawai ka jira zan baka y’ata ta farko”

Magana Abokin yake mishi amman bata ji sosai sai dai taji kamar yace “Ranar juma’ar nan ne wai da gaske?”.

Ita dai bata gane me suke nufi ba ta zo ta gaishesu.

Sai a lokacin ma Ya Usman ya lura da ita, Abokin ne ya amsa yana cewa “uwar gida ya gida?” Da kyar tace “Lafiya” Dan in Abokanan Ya Usman suka ce mata uwar gida duk sai taji wani iri, shiyasa bata tsaya biyewa tsokanarta d’in daya shiga yi ba tayi wucewarta cikin gida.

Ta isa k’ofar Baaba Talatu kenan har zata tura taji suna magana, sai da ta kara kunnenta tukunna ta gano ita da Ya Jamilu ne, mamaki da murna take yi a ranta tace “yaushe ya dawo?”.

Har ta fara k’ok’arin shiga sai kuma taji maganar da yake yi daga ji ran shi a b’ace yake dan yana maganane cikin d’aga murya.

“Habaa Baaba! Yanzu abunda za a yi an kyauta kenan??? Shi fa Usman d’in da kansa yake ce mini ta ce ‘bata sonshi’! Garin son sake k’ulla zumunci sai kunje kun yi abinda zai tarwatsa komai!! Ku kanku fa kun san halin Maryam tun tana Yarinya tanada mugun taurin kai!! Ya kamata ku fahimci tunda har tace muku a yanzu wanchan Yaron take so to shi d’in take so a yanzun! Amma baku tsaya kun yi nazari ba, tashi d’aya kun rabota da shi sannan kuma kawai rana tsaka kun zo kun ce zaku d’aura mata aure wannan juma’ar ita da Usman?? Idan wanchan Yaron ne bakwa so kwata kwata ai at least dai kwa bari idan ma auren ne ita da Usman d’in ya kamata a bari su sake fahimtar juna, dan wallahi idan aka yi auren nan bata sonshi a haka a wannan yanayin da take ciki to ba zata tab’a son shi ba.”

Baba Talatun ce itama ta rufe shi da fad’a tana cewa “To ubana!!! wanda ya san salon so! Yaushe aka haife ka ne Jamilu?? Bari kaji, rud’u ne yake damun Maryam amman ba wani Abba da take so ni na san Usman take so, kuma bari kaji, ko da ace bata auri Usman ranar Juma’ar nan ba to tabbas Abban ta zai aurar da ita a sadaka ranar dan yayi wannan alk’awarin, furucin nasa ne ma ya sa Babanku yace ‘ga Usman’ to kaga ai taimakon tama zai yi! Wai dan ma ban ce d’a na ba zai auri ragowar wani ba!?”

“Haba! haba!! Baaba, bai kamata ku yarda da zancen su Zainab akan Yarinyar nan ba fa, idan y’an layi suna yamid’id’i kema sai ki biye su? Maryam fa kamar y’a take a wajen ki, kuma kin san basa shiri da Zainab dama.”

Da sauri Baaba ta karb’e tana cewa “Ai Maryam bata d’aukeni uwa ba tunda gashi k’iri k’iri tana so ta guji Usman. Kuma kana nufin dan basa shiri da Zainab d’in za ta k’ulla mata sharrine??”

Ji tayi Ya Jamilu yaci gaba da magana “Ni dai in za ‘a j….”

Maryam kasa tsayawa ta cigaba da jin maganar tasu tayi. Zuwa yanzu ta fahimci komai, tuni fuskarta ta jik’e sharkaf da hawaye da uban gumi, nan da nan ta fara ganin dishi dishi! Da gudu ta fita a gidan ko bi ta kan Ya Usman da yake kiran ta batai ba!

Ta ya mahaifinta wanda yake masifar sonta zai yi sadaka da ita??? lalle kuwa zata kashe kanta, wato sun yarda da maganar mutane akan ta kenan?

Da wannan tunanin ta isa gida tana shiga falon sukai kicib’us da Madu wanda yake shirin fita.

Goge hawayenta tayi sannan ta durk’usa a gaban shi ta hau magiya “Abba dan Allah ka yi hak’uri, na rantse da Allah sharri aka yi mini, wallahi Abba bana son Ya Usman, kar ka aura mini shi dan Allah…”

Zagayeta Madu yayi ya wuce ya fita ba tare da ya ce mata komai ba. Mik’ewa ta yi ta nufi Shuwa wadda ta fito daga kitchen yanzu itama ta fara yi magiya tana “Hajiya dan Allah ki kulani yau, ki yarda da ni wallahi sharri aka yi mini, baba son Ya Usman kar ku yi mini auren dole, wallahi k’arya su Zainab aka yi mini! Yanzu kin yarda da abinda suka ce??”

Da sauri Shuwa ta ce “Na yarda!!! Duk wani abu da aka fad’a na yarda, ko da ace zuciya ta tana son k’aryatawa, to zan tirsasa mata in tilastawa kaina in gasgata hakan ne.

Tunda har zaki iya k’etare umarnina! Maryam a nan” Ta yi maganar tana nuna k’ofar kitchen, sannan ta ci gaba “A nan na zaunar dake nace miki ki rabu da wannan Yaron, kika nuna mini kin amince, amman saboda kin raina ni, ban isa in baki shawara ki d’aukaba, kuma ki nuna ban isa dake ba shine kika ci gaba da kulashi!!

Jiya principal d’inku duk sai da ta fad’a mana komai har yadda yace “yana son ki a gaban kowa da yake shi bashi da kunya ke kuma kika biye masa bayan kin san da zancen Usman!

Daman na riga na gama yanke shawarar ko ba a kore ki ba to baza ki ci gaba da zama a makarantar ba!
Maryam kin bani mamaki matuk’a wallahi, ban yi tunanin haka daga gareki ba sam, kuma nima zan baki mamaki, dan wallahi idan baki tsaya kin auri Usman ba to ki saka a ranki babu ni babu ke! Idan taurin kai kike tak’ama dashi ina so ki san cewa a wajena kika gada! Da ni dake aga wanda zai janye.”

Kuka Maryam ta sake fashewa dashi, ita kuwa Shuwa ta wuce tayi hanyar d’akinta ta barta a wajen. Bilkisu ce ta zo tayi ta lallashinta har aka samu ta d’an yi shiru ta tashi suka tafi dakinta.

Haka ta wuni har dare sukuku, tana d’akin taji Baaba Talatu ta shigo tana tambayarta, wai “Usman yace mata d’azu taje ta lab’e mata ita da Jamilu”

Shuwa ce ta ce “Ai yanzu Maryam komai ma aka ce tayi ba zan musa ba, kiji fa har da lab’e ta koya, tabbas ta yi kam dan nan ta shigo tana ta faman yi mana haukan k’arya..”

Nan dai Shuwa ta hau labarta mata yadda suka yi d’azu…“Allah ya kyauta”
Baaba Talatu tace. Daga nan suka hau shirye shirye.

Bayan sun gama ne taji Baaba Talatu tana cewa “bari ta lek’ata kafin ta tafi, da mugun sauri ta shige bargo ta hau barcin k’arya, tana jinta ta lek’a har fuskarta tana cewa “Ashe ma tayi barci”.

Ita dai bata kula taba har ta juya ta fita, dan ita yanzu Baaba Talatu ta fara bata mamaki, k’iri k’iiri take nuna son y’ay’anta, sab’anin su Shuwa.

Da daddare tana daki ta idar da sallah abun duniya ya mata yawa, ita ta rasa ta gudu ne ko ta tsaya bama ta san ta Ina za ta fara ba amma idan akawai abunda yake da yak’ini akai shine ‘ko sama da k’asa zasu had’e ba zata tab’a yarda da auren Ya Usman ba!!’ Idan ta yarda kenan tama karb’i laifin sharrin da aka k’ala mata ta yarda ta yi d’in kenan!!!Shigowar Shuwa ne ya katse mata tunani.

Da sauri ta mik’e ta hau gaisheta, bata amsa mata ba kawai ta juya tace “ki je parlourn Abban ku yana son ganinki.” Daga nan ta sa kai ta fita.

Ninke sallayar Maryam tayi ta bi bayanta ta nufi parlourn Abban nasu.

Tana shiga ta sameshi yana shan shayi, da Al’Qurani a hannunshi, sai da ta jira ya kai aya ya rufe sannan ta gaida shi, cikin kulawa ya amsa mata kafin ya ce “Maryama.” A hankali ta amsa kanta a k’asa.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya fara magana cikin nutsuwa.

“Ki sani ko da ace duk duniya zasu yarda da abinda aka ce a kanki ni ba zan tab’a yarda ba.”

Da sauri ta d’ago kanta ta kalleshi wasu hawayen farinciki suna gangaro mata, bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba. Gyad’a mata kai yayi sannan ya ci gaba “na san halinki na san tarbiyyar ki, fiye da kowa. Amman Maryam ya zama dole a d’aura miki aure ranar juma’ar nan!!”.

“Innalillahi wainna ilaihir rajiun.” Shine abunda Maryam ta fara maimaitawa, tana hawaye sannan tace
“Abba yanzun fa ka ce ka yarda da ni.”

Jinjina kai yayi alamar ‘eh’, kafin yace “Tabbas Maryam na yarda dake amman kuma auren shine mafi alkhairi a tattare dake, makarantar nan da kika yi sananniyar makaranta ce, yanzu sun baki expel!! Ko kin san cewa babu makarantar da zata d’auke ki da saninsu? Sannan mahaifiyarki tace ‘ba zaki k’ara komawa makaranta ba!’ Zaman me to za ki zauna yi??

Sannan abu na biyu, ban san ya akayi zancen nan ya zagaye gari ba, amman jiya har meeting aka had’a da dattijawan unguwa, saboda ke!! Abun takaicin anan shine ba zan iya kare ki ba saboda all evidences are against u, abunda nake tsayawa tsayin daka dan ganin al’umma basu fad’a ciki ba, yau nine ake zargin y’ata da shi.

Maryam da a ce kin yi abunda ya kai ki makarantar kawai baki tsaya kula Yaron nan ba da duk haka bata taso ba, yanzu idan shekaru suka yi gaba, ba lalle ki auru ba domin kusan kaf layin nan maganarki ake yi, kuma kin san idan miji ya fitowa mace a wajen y’an unguwar su da makarantar da tayi ake bincika halayenta wanda inada tabbacin ba zasu bada shaida mai kyau a kanki ba! Maryam hakan zai fi yi mini ciwo fiye da aurar dake da zanyi a yanzu, ko ba komai hankalina a kwance yake da Usman, na san zai kula dake matuk’a.”

“Ki yi hak’uri, wanda ya riga ka zama dole zai riga ka tashi, ki rungumi k’addararki, ba ki da wayo shiyasa aka yi saurin k’ulla miki sharrin da ba zaki iya fitar da kanki ba…”

Kukan da Maryam take yi ne ya sanya shi sak’k’owa daga kan kujerar da yake, ya shiga lallashinta da fad’a mata kalamai masu kwantar da hankali har sai da yaga tayi shiru tukunna ya sallameta, jikinta a mace haka ta tashi ta fita.

A hankali ya saka yatsar shi ya d’auke kwallar data taru a idonshi, sannan ya koma ya zauna ya jingina da jikin kujerar had’e da lumshe idanuwanshi.

               

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 11So Da Buri 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×