Skip to content
Part 35 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Washegari Kamar yadda Mom ta yi niyya. Haka nan ta d’auki video d’in da ta shiryawa! Ta saman balcony d’in d’akin Mammy ta d’auki video d’in Aslam da Arshaad lokacin suna shirin fita. Ko ta kan Mammy wadda take ta faman tambayarta “me za tayi?” Bata bi ba, ta fice abunta tana cewa “In na dawo zan yi miki bayani.

Sai dai kuma tana zuwa gidansu Aslam d’in ta tarar su Gwaggo Asabe sun yowa Mommyn rakiya Flight d’inta nan da awa d’aya (9:00pm) zai tashi!!
Lokacin appointment d’inta da Neurologist d’in da Granpa yayi mata booking yayi.

Kamar Mom ta had’iye zuciya haka taji, ba yadda ta iya haka nan ta hau yi musu fatan alkhairi suka wuce ita da Aaima. Flight d’in Abuja za su bi, idan sun sauk’a a Abujan Aaima zata wuce makaranta ita kuma Mommy su wuce tare da Dad.

BAYAN WATA D’AYA!

(After a month!!).

Da gudu Jalila ta fito daga d’akin Umma. Bata kai ga k’arasawa band’akin da ta fito na niyyar zuwa ba! Ta hau kwarara aman da ya taho mata babu shiri a nan bakin rijiyarsu wajen wanke wanke!.Da sauri Mama ta fito daga d’aki jin mutum yana amai
Dai dai nan itama Umma ta fito da waya kare a kunnenta tana cewa
“Haba Zainab! tafiyar taku ba sai gobe ba? Ki yi sauri kizo muje mu kaita asibitin mu dawo a san abun yi. Kinga yanzun ma fa tana sa ruwa a bakinta kinganta ta fito ta hau amai! Gara a yi ta a gama dan ni wallahi jikina ya na bani c…” Ganin Mama ne ya sanya ta had’iye ragowar maganar tata.

Ita kam Mama ta Jalila ma takeyi, dan haka tayi saurin k’arasawa inda take ta hau shafa mata baya tana yi mata sannu. Dama fa ita kwana biyu ta d’an ga wasu changes a tattare da Jalilan
Kuma tana lura da yadda Umman ta hanata zaman tsakar gida kwata kwata! Maybe ko dan ta lura da kallon kurillar da take yiwa Jalilan ne? Oho!

Da kyar Jalila ta samu ta amayar da d’an ragowar ruwan da yake a cikin ta sannnan ta d’ago tana mayar da numfashi Dai dai nan Umma ta k’araso wajen nasu tana hararar Mama.
Da mamaki Maman take k’arewa Jalilan kallo!. Tayi wani haske na ban mamaki Bakinta sun yi pink sosai!
Sannan k’irjinta yayi mugun cika!
A hankali Mama da taji k’irjinta ya buga da k’arfi ta lumshe idanuwanta tace “Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Kafin ta bud’e su ta zuba su a kan Jalilan wadda itama ta kafeta da nata idanun. A hankali Maman tace mata
“Sannu, me yake damunki?” Jalila an cikin wata d’ayan nan ba k’aramin sanyi tayi ba, yanayinta ma gabad’aya ya sauya kamar ba Jalila ba. Ta bud’e baki za tayi magana kenan Umma tace
“Ina ruwan ki!? Sannan da kike wani salati shin aljana kika gani ko me?
Kinga! Maryam!! wallahi ki fita a harkaata ni da y’ay’ana. Ina jin ku jiya ke da Bilkisu kuna munafurcin Ja’afar
Bayan ke Huda ta fi sati bata a gidan nan Allah kad’ai ya san inda ta tafi wannan karon!! Ki fita a idona tun muna sheda juna wallahi.” Tana ga fad’in haka ta jaa hannun Jalilan fuuuu suka shige d’aki.

Mama kam kasa motsi tayi a wajen…duk kalar tarin rashin d’aa’ar da Jalila ke zuba mata hakan bai hanata jin tsananin tausayinta ba! Tabbas idan idanuwanta sun gane mata daidai to d’anyen ciki ta hango a jikin Jalila!
Bayan yadda ilahirin jikinta ya nuna
Aman da ta gama yi yanzu mai mugun k’arni ya sake tabbatar mata. Salati kawai take yi tana sake nanatawa a cikin zuciyarta. Ta ma kasa d’aga k’afafuwanta ta bar wajen! Da kyar ta samu ta d’an motsa ta jawo ruwa a rijiya ta d’auraye wajen daga nan ta sake luluwa duniyar tunani.

A haka su Ummu suka shigo suka sameta. Sai da su Sakina suka yi hugging d’inta tukunna tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunanin data lulu.
Ummun ce ta d’an k’ura mata ido sanann tace “Tunanin me kike yi haka?”

Wata nannauyar Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “Ba komai”. Daga nan suka d’unguma suka yi d’aki. Ba kalar tambayar da Ummu ba ta yi mata ba amman tace mata “ba komai” kawai!
Saboda hasashen alkhairi ake so a yayata, na sharri kuwa ba a fad’i!
Harshe na da kaifi!.

Ganin tak’i fad’a ya sanya Ummu kawai ta kyaleta dan ta san da tana so ta sani to da tuni ta fad’a matan. Shiyasa bata sake yi mata maganar ba ta sako wani zancen ta hanyar cewa
“Mama anata shiri. Gobe da sassafe duk zamu wuce. Dan Allah ki zo kema mu tafi mana Kin san In babu ke ba zan ji dad’in bikin ba.”

Murmushi Maman tayi kafin tace
“Bilkisu ke kad’ai fa kike ta gayyatata!
Jiya ina ji Zainab da Sadiya suna yada min magana bayan kin wuce. A haka kikeso In kwashi k’afa in tafi bikin y’arta har Kaduna? Besides kin san ba ishashshiyar lafiya gare ni ba those days kar inje su yi mini wani abun itama Hajiya ta d’aura da nata inje jinina ya hau!.

Dan Allah na rok’eki da girman Allah ku barmu a nan Ai naji Baaba Talatu ma tace ‘In an d’aukota daga Kaduna a nan gidan Kaka za a fara sauk’a saboda y’an tsofaffin da basu je su Kadunan ba!Bayan an d’auke su sai a wuce gidanta’. Nayi miki alk’awarin k’arfe takwas zan shirya ga anko na nan ma na wunin kai amarya an d’inko…duk inda takwas da rabi tayi ina gidan Kaka kuna zuwa sai mu wuce tare gaba d’aya. Banda abinki ma, In dai ke da Sakina kunje ai kamar munje ne ko?” Ta k’arashe maganar da d’an murmushi a kan fuskarta.
Murmushi Ummun itama tayi.
Ba dan ransu ya so ba haka suka hak’ura akabi tsarin yadda Maman tace. Sakina itama daa cewa tayi ba zata je ba Sai da Mama ta lallab’a ta tukunna ta yarda zata je d’in.

Kamar minti talatin da yin wayar Umma da Anty Zainab sai gata nan!
Tana shiga d’akin Umma tace
“Yauwa Zainab! Na gode da kika bani lokacinki, mu je ko?” Tayi maganar tana k’ok’arin tashin Jalila wadda tayi bacci. Dakatar da ita Anty Zainab d’in tayi ta hanyar cewa “Tsaya tukunna
Yanzun nan Baban Khadija ya kira yanata faman masifa wai danginshi suna chan sun fara mitar ya uwar amarya har yanzu bata k’araso ba!
Yanzu haka da nake yi miki maganar nan drivern da akayi shata zai kaini Kaduna yana bakin k’ofar gidan Kaka yana jira!. Yace ba zai you ince sai gobe zan je ba! Dole in tafi a yau…
So kiyi hak’uri ba zan iya rakaki asibiti ba gaskiya Amman ga wannan”
Tayi maganar tana zaro pt a jakaar ta, sannan ta ci gaba “Yanzun nan na tsaya na siya na taho dashi. Scanning ne kawai ba zai nuna ba! Amman ciki in dai akwai shi ko na kwana biyar ne to zamu gani. Tashe ta yanzun nan ta gwada mu gani.”

A hankali Umma ta sauk’e ajiyar zuciya sanann ta k’araso ta tada Jalila.

Dalla dalla Anty Zainab ta yiwa Jalila bayanin yadda zata yi amfani da abun
sannan ta d’aura da cewa “In babu za muga layi d’aya In kuma akwai za muga layi biyu”

Karb’a tayi ta fita zuwa band’aki!
Kamar minti biyar haka sai gata ta dawo.

Anty Zainab ta mik’awa, cikin rawar jiki Umma ma ta taso tazo ta hau lek’awa.

A tare suka saka salati kafin Umma ta zauna dab’ass!!! A k’asa ta d’aura hannu a ka ta fashe da kuka!.

Da sauri Anty Zainab ta tsugunna ta shiga lallashinta. Ita kam Jalila tunda ta shigo ta mik’a musu suka karb’a ta wuce kan gado ta zauna ta rafka uban tagumi! So take tayi kuka amman ta kasa…Wani irin tuk’uk’i ne yake taso mata daga k’asan zuciyarta! Inda ace zata ga Auwal yanzu wallahi da sai ta kasheshi! Ba abunda yake b’ata mata rai irin yadda ya dinga muamala da ita a wulakance! Kamar ma irin kyamarta d’innan yake yi sai kace an yi mishi dole!. Da kuma yadda ya fito k’iri k’iri ya zazzage ta ya gurza mata rashin mutunci! Taya zata haifi cikin nan??
Ta san ko sama da k’asa zasu hadu Auwal ba zai tab’a accepting cikin ba!
Ace ma ya karb’a yayi accepting.

Shikenan ta zama bazawarar k’arfi da yaji kenan?? Dan ita dai ba zata zubar da ciki ba! ‘Tana tuna wani lokaci. Akwai wata a ajinsu Ta tab’a yin ciki!
Malamin da yayi mata ya kwasheta zuwa wani asibiti dan basa so makarantar ta sani da kuma iyayen ita Yarinyar. Haka nan aka zo garin cire ciki Yarinyar ta mutu!. Sannan Akwai wata ma a bayan layin su Itama b’arin ciki kawai tayi ta mutu.’

Wata zuciyarce tace mata “ba gara to kema ki mutun ba! A haka ma tun baki haihu ba kina tunanin ta yaya Arshaad zai soki ballantana yanzu idan kika haihu ko kallon ki ba zai yi ba.”

Tunda Jalila take a rayuwarta bata tab’a jin tashin hankali irin na wanann rana ba! Ji take inama ace ba a halicceta ba. Banda wani irin huci da ajiyar zuciya ba abunda take yi

Chan!!! Kamar an tsikareta, da mugun gudu suka ga ta mik’e tayi waje
dan haka suma suka tashi suka rufa mata baya.

Da kyar bayan sun fita suka jiyo motsinta a kitchen dan kafin su fito har ta b’ace musu kamar wata aljana.

Da gudu kamar mahaukata haka suka nufi kitchen d’in! Tun kafin su k’arasa warin d’an kalanzir d’in da suke kunna icce da shi ya bakwanci hancinansu.vSuna shiga suka ganta tana k’ok’arin kunna ashana tana wani irin kuka zata had’iye zuciyarta! Ga jikinta sharkaf!! Ta kwarara kalanzir ta koina.

Umma kasa k’arasawa wajen tayi…
Ba abunda take jin tsoro sai ‘Kar taje tana matsawa Jalilan kuma ta kunna ashanar taje wutar ta tashi da ita!’.

Anty Zainab ce tayi k’ok’arin k’arasawa ta gudu ta kwace ashanar ta jefar sanann ta d’auketa da mari!!!
A take ta durk’ushe a wajen tana wani irin kuka abun tausayi.

Sai a lokacin Umma ta samu ta iya matsawa kusa dasu. Tana zuwa tasa hannu ta d’ago ta ta rungumeta a jikinta tana shafa bayanta tana lallashinta.

Da kyar suka samu tayi shiru.

A hankali Umma ta d’ago fuskarta tana shafawa, tace “Ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki daina kuka ki bani hankalinki mu nemo mafita!
Sannan dan Allah kar ki sake yunk’urin kashe kanki Jalila Ni Sadiya na yi miki alk’awarin ba zaki wulak’antata sanann zan bi miki hakkinki za kiyi dariya za kiyi farin ciki in shaa Allah Amman fa sai kin nutsu, sannan sai kina raye tukunna za kici ribar bak’in cikin nan da kike ciki a yanzu! Kin ji ko?”.

A hankali ta d’aga mata kai tana sauk’e wasu tagwayen ajiyar zuciya.

Nisawa Umma tayi kafin tace mata “Jalila ko da wasa bai tab’a gaya miki sunan unguwarsu ba?”

Shiruuu, ta d’anyi kamar tana tunani, fuskarta tayi mugun kumbura idanunwanta sun k’ank’ance sun yi jazir! A hankali ta ce “A jikin duk motocin da yake amfani da su Ina ganin ‘MT’ a sak’ale a jikin glass d’in gaban motar tashi amman turare ne irin wanda ake sawa a d’aki ko band’aki ko office dan k’amshi yake fitarwa na tab’a tab’ata ma hannunna ya kwana yana k’amshi.

Sannan na tab’a ganin wasu takardu a motar tashi shima an yi rubutun ‘MT’
Babba sosai! Sai kuma wasu bayanai a k’asa a cikin envelope mai kyau irin mai shara sharan nan. Ina ga ko yana da alak’a da company d’in ne. Watak’ilan in muka je ‘MT’ d’in mu same shi a chan.”

Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin ta juya wajen Anty Zainab tace “Kiyi tafiyarki kawai Zainab Kar yayi ta jiran ki! Zan dinga gaya miki halin da ake ciki ta waya. Bara mu tafi MT ni da Jalilan.”

Ajiyar zuciya Anty Zainab ta sauk’e kafin tace “Kar ki bari ya raina muku hankali! Ku bud’e mishi wuta sosai!!
Jalila kar ki bari ya ga lagonki ki daina wannan kukan. Sannan kar ki k’ara attempting abunda kika so kiyi yanzu
Komai yayi safi maganinshi Allah kin ji ko?”

A hankali Jalilan ta d’aga mata kai.
Shafa kanta tayi tana d’an murmushi tukunna ta yi ma Umma sallama ta wuce.

Tana fita Umma ta kamo hannun Jalila suka fito a kitchen d’in. Sai da ta dallawa k’ofar d’akin Mama harara a ranta tace “Munafukai na san sarai kuna jin mu.” Tukunna suka shige d’aki.

Babu abunda yafi bawa Jalila mamaki irin yadda taga Umma ta had’e mata kayanta kakaff!! Hatta inner wears!
Gashi Umman tace mata “Kar ta kuskura tace komai kawo yanzu har zuwa suje wajen Auwal a gama magana kar tace komai! Ta bar mata komai a hannunta.”

Sai da ta had’a Ghana most go uku manya!! Tukunna ta fice taje tayi wanka ta dawo d’akin. Tana gama shiryawa ana kiran azahar, dan haka ta cewa Jalila “ta taso su tafi! Kar su makara ya tashi a office d’in.”

Umman ce tayi jigilar kayan ta fitar ta tsare musu adaidaita sahu suka kama hanyar Mai Turare & Co.

A bakin tangamemen had’add’en company d’in mai adaidaitan ya sauk’e su.

“Hmm yana aiki a nan ai dole yayi ta wasa da kud’i yana yiwa mutane rashin mutunci.” Umma ta fad’i hakan a ranta bayan ta gama k’arewa k’ererren ginin kallo.

Kayan su suka kwasa sannan suka sallami mai adaidaita sahun suka nufi bakin gate d’in shiga. Suna zuwa wani soja a cikin masu gadin ya fito ya tsare su yana yi musu kallon tara saura kwata kafin yace “Where to? Maam!”.

Sai da ya sake maimaita tambayar tukunna tace “Muna son ganin Auwal.” Da mamaki yake sake k’are musu kallo dasu da kayansu kafin yace
“Sir Auwal? Mai Turare?”.

Da mamaki Umma ta d’an juya ya kalli Jalila da sauri sai kuma ta juyo gareshi tace “Yes yes shi.”

Dariya sojan yayi kafin cikin gurb’atacciyar Hausar shi yace
“Bar nan wajen! Ba na son raina.”
Yana gama fad’in haka ya juya
Sai a lokacin Jalila tace “sir”
Yana juyowa ta mik’a mishi wayarta.

Kallonta yayi kafin yasa hannu ya karb’i waya da mamaki yake kallonta yake kallon hoton da suka d’auka ita da Auwal a cikin mota! Yafi minti d’aya a tsaye yana kallonta da hoton
Daga k’arshe ya sauk’e ajiyar zuciya yace “ok” ya mik’a mata wayarta ya juya yayi ciiki.

Kallon hoton take yi a hankali tana shafa fuskar wayar tana tuna lokacin da ta d’auki hoton. Lokacin zuwan sa na biyu ne.

Tana y’an hotunanta Ita d’aya shi kuma yana driving

Ba tare da ya sani ba ta d’an karkato ta d’auke su.

Gashi nan ya fito tarr! Amman iya gefen fuskarshi sai dai duk wanda ya sanshi yana gani zai san shin d’in ne
.

“Jalila kar fa ki fara son Yaron nan!
Dan in dai kina sonshi to ba zaki iya abunda na shirya ba. Ki daina kallonshi ki goge hotonnan tunda yanzu na san ya gama aiki.” Muryar Umma ta katse mata tunani.

Murmushi kawai tayi ta maida wayar lock ta rik’e a hannunta. A chan office kuwa! Ana gayawa Auwal wata na nemanshi a waje yace “Ace musu aiki yake yi!” Shi bai ma kawo Jalila bace ba yayi tunanin a cikin tarin y’an matanshine wata ta boyisa har office, dan sun saba, sai dai kuma yayi mamakin yadda bata shigo har office d’in nashi ba Instead ta tsaya a gate!

Kamar bayan minti goma sai ga mai gadin ya sake dawowa. Yana zuwa yace matar da take tare da Yarinyar tace ace mishi “Dangin Mamansa ne suka zo daga k’auye!”

“Dangin Adama?” Suka ji muryar Granpa wanda ya shigo zagaye yanzu a bayansu!!! Sai da Auwal yaga wani duhu na y’an sakanni. Tukunna ya mik’e tsaye ya gaida Granpa cikin girmamawa. Bai amsa ba sai tambayar d’azu da ya sake jeho mishi!!.
A hankali Auwal ya goge wata zufa da ta karyo mishi a goshi sannan yace
“Eh, I think so, amman bb ba bamu yi maganar wasu za suzo da ita ba!”.
Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace “I’m leaving, ka zo muje gida sai ka kaisu wajenta! Su yi abunda ya kawo su su wuce. Make sure basu dad’e ba ka san ba na son kwashe kwashe!.”

Wani yawu mai mugun d’aci da tauri Auwal ya had’iye kafin yace “Ok Granpa.” Sannan ya bi bayanshi suka fice tare a office d’in hankalinshi a masifar tashe!! Tabbas ya san ba y’an uwan Mom bane suka zo!Ummi ita kad’ai ce cousin d’inta tunda mata biyu kacal kakarsu ta haifa! Da maaman Ummi da Maman Mom
Su kuma suka haifi mata d’aya d’aya
Ummi da Mom. Sai dai In ko relatives d’in kakar tasu, amman ya san Mom ba huld’a take yi da su ba dan tun tana y’ar k’ank’anuwarta ta kwaso kayanta ta dawo wajen Ummi Gramma ta had’a su ta rene su tare. Sannan har gobe sai anyi da gaske tukunna take zuwa k’auye wajen Mahaifiyarta ta d’anyi kwana biyu ta dubo ta ta dawo sam bata son k’auye. Sannan Maman nata irin matan nan ne masu fad’in gaskiya da tsananin imani acewarta kenan (mom d’in) D’an mistake kad’an Idan tayi nan zata had’u da fushinta!
Hakan ya sanya da taga tafiyar su ba zata zo d’aya ba sannan ita kuma (Mahaifiyar tata) ta k’i zaman birni, ta ajjiye ta a k’auyen ta siya mata gida take tura mata kud’i duk wata,
waya ma suna yi amman ba sosai ba.
Zuwa kuwa sai tafi shekara bata lek’a ta ba.

Yana wannan tunanin suka k’arasa wajen da suka yi parking motocinsu!
Granpa ne ya juyo ya cewa mai gadin da yake tare dasu yana yi musu rakiya
“Ina bak’in??”

Sai da sojan ya d’an rissina tukunna yace “Suna waje bara inje In shigo da su.”

“Okay hurry” Shine abunda Granpa yace yana mai gyara tsayuwar shi a jikin motar.

Wasu zufa ne suke tsatsafowa Auwal ta kowacce b’ular gashin dake jikinshi. Da ace Granpa zai lura dashi da kyau to da tabbas a tashi d’aya zai karanto tsananin tashin hankali tsoro da rashin gaskiyar da suke tattare da shi!.

Tabbas ya san kashin shi ya bushe yau!! Saboda bashi da tantama
wata a cikin y’an matan shi ce ta zo!
Duba kuma da irin yanayin halayyarshi tabbas!! Ya san ba alkhairi ne ya kawota ba.

Wata idea ce ta fad’o mishi dan haka da sauri yasa hannu a aljihu ya zaro wayarshi ya shiga message.

Yana gama sending message d’in dai dai su Umma suna k’arasowa wajen tare da wasu masu gadi da suka tayasu d’ibar kayansu.

Da mamaki yake kallonsu especially Jalila wadda yaga ta chanza! Itan ma shi take kallo ido cikin ido Tana mamakin yadda ya nutsu a gaban wannan tsohon, kamar ba shin ba.

Umma ce ta gaida Granpa wanda taga yana yi musu kallon k’urilla! Ba tare da ya amsa ba ya cewa Auwal
“Did you recognize them?”

Sai da ya d’an russunar da kai tukunna yace “No Granpa.”

“Call Adama” Granpa ya bashi umarni.

Wani sanyi Auwal yaji ya na ratsashi
a hankali yace “Ok” kafin ya danna kiran Mom.

Ya san ta d’auka amman bai saka wayar a handsfree ba Sai kawai yayi shiru chaan kuma ya kashe! Ya bada kamar minti d’aya dan ta samu ta karanta sak’on nashi sannan ya sake kiranta.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya kalli Granpa yana d’an murmushi yace
“Sai yanzu wayar ta shiga ina ga ba network ne.”

“Umm”, kawai Granpa wanda ya fara gajiya da tsauwar yace mishi.

Tana d’auka yasa a handsfree
a hankali ya gaisheta kafin yace “Ga wasu bak’i nan sunzo wai daga wajen Innaa ta san da zuwan su?”.

Tun kafin yayi shiru tace “Eh!
Sun yi chattn da Innar ta gaya mata zuwan su yarinyar distant relative d’in Innar ce, so za a yi mata aure suna buk’atar kayan d’aki shine zata d’anyi aikace aikace a gidan kafin lokacin aurenta ya isa! Su biya ta ta tafi.”

“Ok tam shikenan.” Auwal d’in yace
daga haka ya katse kiran ya juya yana kallon Granpa.

Lumshe ido kawai Granpa yayi ya bud’e daga nan ya jinjina kai.

“Thankyou Granpa “ shine kawai abunda Auwal yace daga nan ya ya fito wasu cleaners ya umarce su dasu kwashi kayan Jalila su kai motarshi
sannan ya zaro kud’i a aljihu ya mik’awa Umma ya ce “gashi tayi kud’in mota ta koma”. Kafin ya kalli Jalila yace mata “muje ko”. A hankali ta d’an kalli Umma, da ido Umman tayi mata sign d’in ‘ta bishi’ Kamar ta kurma ihu haka taji amman ba yadda ta iya haka nan ta wuce suka nufi motar tashi.

Sai a lokacin Granpa ya juya shima driver d’inshi ya bud’e mishi mota ya shiga yaja suka nufi MT estate. Motar Granpa na gaba tashi na a baya haka suke tafiya har suka isa makeken gate d’in estate d’in daga shi har Jalila ba wanda ya kalli wani babu kuma wanda yacl cewa wani uffan!

Jikin Jalila har rawa yake yi da aka bud’e musu gate d’in suka danna hancin motar cikin aljannar duniyar da idanuwanta suke gani. Kasa hak’ura tayi kawai ta hau jujjuya kai tanata faman kalle kalle! Tana ganin motar gaban su ta nufi gidan da yafi ko wanne girma aka bud’e ta shige.
Su kuma suka nufi d’aya daga cikin jerin gidajen estate d’in suma aka bud’e musu gate suka shige. Bata san lokacin da tace “woow” tana kallo tana murmushi ba!

Tsakin da Auwal ya jaa ne ya d’an dawo da ita hankalinta! A hankali ta d’an muskuta ta gyara zaman ta.
Har suka gama ya bud’e motar ya fita bata sake yin motsi ko tace komai ba.
Ganin ya fita ne ya sanya itama ta bud’e motar ta fito ta bi bayanshi a ranta tana cewa “Aljannar duniya!
Ma shaa Allah. Wai tab!! Dukiya tana inda take.”

K’ofar da taga ya shiga nan itama ta bi ta shige..

A tsaye ta ganshi da wata mata fara y’ar kyakkyawa mai matsakaicin jiki da tsayi suna magana. Tana shigowa duk suka jiyo suna kallonta! A hankali ta tako ta zo inda suke itama ta tsaya:

Runtse ido Auwal yayi da mugun k’arfi! Kafin ya juyo inda take tsaye ya d’auke ta da wani mahaukacin marin da saida ya kaita ga kaiwa k’asa!!
Bai damu da yadda yaga numfashin ta yana shirin d’aukewa ba! Ya fara k’ok’arin kwance belt d’in wandon jikinshi. Ko takan Mom wadda take ta k’ok’arin tsaidashi bai bi ba haka ya ture ta gefe ya hau zulawa Jalila belt d’in da ya samu nasarar zarowa daga k’ugunsa!

Sai da yayi mata uku tukunna Mom ta samu ta ture shi gefe da kyar!!!
Cikin fad’a tace “Baka da hankali? baka jin yadda take kurma uban ihu sai wani yaji ya shigo?”

In banda huci ba abunda yake yi, tare da da aikawa Jalila wani k’ask’antccen kallo wanda yake cike da tsana!

Dai dai nan Ummi ta shigo.
Kallonsu take tana mamakin yadda Auwal yake tsaye da belt a hannu yana ta faman huci, ga kuma Yarinya a kwance a k’asa tana ta faman kuka!!
Wanda ta tabbatar ihun ta take jiyowa tun a compound.

A hankali Jalila ta fara k’ok’arin tashi.
Hannu Ummi wadda ta k’araso yanzu ta saka ta d’ago ta ba tare da ta kalleta ba tace musu “Lafiya? Mai ya faru?” Tayi maganar tana kallon Mom. Mom ta bud’e baki za tayi magana kenan Jalila wadda ta k’arasa inda take ta d’auketa da mari!!! Basu gama fita daga wannan shock d’in ba kawai suka ga ta wage baki ta fara kwala kiran “Granpa” da mugun k’arfi!!!!.

“Innalillahi wa innailaihirrajiun”shine abunda Ummi ta hau maimaitawa kafin a gigice tace “Adama wacce mahaukaciyar Yarinya ce wanna??
Meye haka take yi? Ku yi mini magana mana!! Ke yanzu tsabar rashin d’a’a wannan bata haifeki ba?!” Ummi duk tana maganar ne cikin tsananin tsoro da firgice dan yadda Jalila take kiran Granpa tabbas in dai wani ya zo wucewa ta gefen gidan sai ya jiyota ta!! Gashi estate d’in tsit!! So definitely muryar ta zai iya fita koina ma.

Cikin tsananin tashin hankali mamaki da firgici da tsoro Auwal ya k’arasa inda take ya mata wata wawuyar shak’a!! Ba yadda su Ummi basu yi ba amman suka kasa kwatar ta a hannunshi. Ita kanta Jalila hannunta na a kan nashi da niyyar kwatar kanta amman ta kasa b’amb’are hannun nashi saboda ba k’aramin ruk’o ya yiwa wuyan nata ba!. Ganin yana shirin kaita lahira ne ya sanya ta tak’ark’are ta sa dukkannin ragowar k’arfinta ta d’aga k’afarta guda d’aya ta daki tsakiyan k’afafunsa da mugun k’arfi!!

A rikice ya cikata ya durk’usa a wajen yana jin azabar da bai tab’a jin kwatakwacinta ba!.

Ita kuma ta durk’ushe a wajen ta hau tarin wahala. A tsorace Ummi tace
“Adama ku yi mini bayani dan Allah
Ina kuka samo wannan y’ar dabar??”

Mik’ewa Jalila tayi tana d’an tari kad’an kad’an tace “Y’ar daba ko?
Ai gwara ni y’ar daba ce kuma a kan gaskiya ta sannan a wajen kwatar hakkina nake dabancin! D’anku fa?
Shi baku ga abunda yayi mini ba?
Baya ga dabancin daya gama nunawa a nan kunsan me yayi min? kun san ya alak’a ta take da shi???”

A hankali Mom ta lumshe idanunta kafin ta bud’e su ta d’aura akan Auwal wanda ya mik’e yanzun nan tace
“Auwal plss tell me you did not!!!”
Ta fad’i hakan wani hawayen takaici yana zubo mata daga ido daya. A hankali ta d’an matsa gabanshi ta tsaya ta sake cewa “Dan Allah
Of all people Auwal kar ka ce mini akwai wata mummunar alak’a tsakaninka da wannan Yarinyar!.”

Murmushi Jalila tayi kafin tace
“Tab!! Hajiya Adama ai kuwa ki tanadi drip mota mota dan na san hawayenki sai sun k’are tass kin buk’aci ruwa a wannan jikin naki! Bari kiji in gaya miki bayan mummunar alak’ar dake a tsakaninmu har da jika ko jikar ki nake k’unshe da a wannan cikin nawa da kike gani!” Tayi maganar tana shafa cikin.

A zabure gabad’ayansu suka juyo suna kallonta har Auwal! Kamar zaki haka ya sake fincikota ta matso daff dashi
kafin yace “K’arya kike yi wallahi!!
K’arya kike yi ki samu ciki da ni bayan magungunan da na baki kike sha kullum da safe for good 3 days!”

Tunkud’e shi tayi cikin had’e fuska tace “Auwal in banda kai dak’iki ne! Taya kake tunanin zan ci ko in sha abun da ya fito daga hannunka bayan abunda ka yi mini a wadannan kwanaki, ba tare da na san ingancin su ba?? Lura ne baka yi ba amman ko abinci ko ruwa idan ka kawo sai na tabbatar da ka ci na gani a gaban idona tukunna nake ci nima. Saboda haka duk wasu magungunan da kake tunanin ka bani fakar idonka nake yi in b’oye a k’asan pillow sannan inyi kamar nasa a bakina kana fita nake yin flushing d’insu a Masai! Dan haka In akwai wadda zaka ce ba zata yi ciki ba to Masai ce! Amman ba dai ni Jalila bint Usman ba!!!”

Dafe kai kawai Auwal yayi ya lumshe idanuwanshi! Wani kalar sarawa yake ji kanshi yanayi bana wasa ba!
Shi? Jininshi? Da na Jalila? Inaaaa, ba zai yiwu ba wallahi!!! Yana cikin wannan tunanin yaji tace “Idan kuma baku yarda ba Kuna iya zuwa muje
akwai wani test da ake yi wani abu ‘NA’ haka dai. Na san ku kun sanshi
Sai muje ayi a tabbatar muku amman kafin nan ina so ku nuna min d’akina in d’an shiga In huta in yi wanka!
Dan gabad’aya ilahirin jikina ciwo suke yi, sam! Ban saba da duka ba.
Sannan a had’o min abinci mai rai da lafiya dan…” A fusace taga Auwal ya k’araso inda take, cikin tsananin b’acin rai yace “Kin san Allah? In kika kaini bango zan kasheki In kashe banza wallahi!! Banza dak’ik’iyar Yarinya!!
Bari kiji in gaya miki ko taku d’aya ba zaki sake yi forward ciki gidan nan ba sai dai backward!! Sannan cikin nan yanzun nan za aje a zubar da shi!
Ko kina so ko ba kya so wallahi!!

Daga nan ko suna na kika sake kira by mistake ma, sai na datse miki harshe.”

Wata dariyar rainin wayo ta saka wanda hakan ba k’aramin sake k’ular da Auwal yayi ba.

Sai da ta d’an tsagaita sannan tace “To shikenan! Naji ba zan shigar muku gida ba amma inaso ka sani Billahilazim Wallahi Tallahi! Na fita daga nan direct gidan da naga wannann tsohon wanda naga kana mugun jin tsoro ya shiga
nan!! Nima zan nufa Kuma idan naje sai na fad’a mishi komai!! Sannan ince ayi test da jininka dana d’an da yake cikina aga idan k’arya nake yi”
Tana gama fadin haka ta juya zata fita.
Da sauri Ummi ta ruk’o hannunta.

Fincike hannun nata tayi kafin tace “Ai ke kad’ai ce naga alamar kina buk’atar sulhu amman da shi da uwarsa sam basa buk’ata! Dan haka daga nan gidan Granpa na nufa..”

A hankali taji Mom tace “Tsaya” Da sauri Auwal ya juyo yace “Mom!
Wannan Yarinyar shed’an ce
Ki barni da ita i can handle her
wallahi ba zata.” Cikin katseshi Mom tace “I think you have done enough Auwal!! Za ka barni in gyara kuskurenka? Ko kuma in barka ka ci gaba da lalata rayuwarka??”

A hankali Ummi tace “Wuce kaje kawai Auwal za mu san abun yi kaji ko?”

Ji yake kamar ya rufe Jalila da duka har sai yaga bata numfashi tukunna ya barta. A hankali yaji Ummi ta sake cewa “Kaje kawai, kaji?”

Sai da ya sauk’e wata k’akk’arfar ajiyar zuciya tukunna ya dallawa Jalila wadda ta tsare shi da manyan idanuwanta harara! Ya saka kai fuu!!
Ya fice daga gidan ko belt d’inshi bai tsaya d’auka ba.

Tab’e baki kawai tayi ta d’auke kai

“Muje in kai ki d’akinki”

Shine abunda Mom tace mata ta juya tayi gaba.

A k’asa ta nuna mata guess room amman Jalila furr tace “wallahi ba zata zauna a k’asa ba! Ya za ai tana ganin gida mai bene har biyu amman a ajjiye ta a k’asa?”

Ba yadda Mom ta iya haka tasa masu aiki suka kai mata kayanta d’akin sama na bak’i! A chan gefen side d’in Auwal. Sannan suka gyara suka goge aka wanke band’akin.

K’iri k’iri tana zaune Mom ta sanya cook tayi mata Girki Bata ce musu ba zata ci ba sai da cook d’in ta kawo ta ajjiye sannan tace “Allankatafir ba zata ci girkin kafira ba! Sai dai Mom ta dafa mata da kanta.

Cikin tsananin b’acin rai Ummi wadda take tolerating d’inta tun d’azu da kyar tace “Wannan ne kuma baki Isa ba
wallahi sai dai ki kwana da yunwa!”

Jalila ta mik’e kenan zata fara zuba tujara suka ji sallamar Daddy

Ganin da tayi su Mom sun maida hankalinsu gabad’aya a bakin k’ofar ne ya sanya itama ta juya tana kallon wajen.

A hankali Mom ta runtse idanuwanta da suka yi jaaa ta bud’e tace “zan yi miki” sannan ta nufi wajenshi.

Da mamaki yake kallonsu yana kallon Jalilan dan bai gane ta ba! Kuma kamar y’ar hayaniya ya jiyo suna yi, hakan ya sanya ko gaisuwar Mom bai amsa da kyau ba yace mata “wacece wannan?” Yayi maganar yana kallon Jalila da itama ta nufi wajen su.

Da sauri Mom tace “Yarinyar wata distant relative d’in inna ce! Akwai y’an aikace aikacen da zata tayani, zuwa k’arshen watannan sai in biyata in sallameta saboda suma suna buk’atar kud’in, aure zata yi
so suna buk’atar na siyan kayan d’aki!.”

Murmushi Daddy yayi kafin yace
“Shine kuma har sai tayi aiki?
Ko ba relative d’in Innaa naji kin ce ba?. Kamar nawa ne ta fad’a miki suke buk’ata d’in sai a bayar ai ko? Besides muna da masu aiki enough ai wanne kuma zata yi?”.

A hankali tace “Muje ka huta kaci abinci ko? Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya amsa gaisuwar Jalilan sanann ya wuce sama.

Babu yadda Daddy bai yi da Mom akan ta maida Jalila ba amman k’iri k’iri ta dinga kaucewa tana kawo mishi wasu silky excuses d’inta. A gajiye yake shiyasa kawai ya rabu da ita.

Ba abunda yafi d’aga mishi hankali sai yadda yaga d’akin Jalilan a sama gefen side d’in Auwal!

Da daddare bayan Jalila ta ci ta sha tayi wanka ta zo kwanciya. Ta kira Umma. Tun daga lokacin da suka rabu ta kwashe komai ta gaya mata
sannan tace “Umma in gaya mikii jikan Mai Turare ne Unguwa ce dasu guda! Ina ga shida y’ay’an shi ne da jikokinshi. Anan gidansu Auwal d’in yake.

A bakin gate d’in shiga unguwar tasu an rubuta Mai Turare.” Cike da tsantasr farin ciki Umman tace
“To ai hakan yayi dede, kai amman naji dad’i sosai! Yanzu abunda neke so dake shine ‘karki kuskura ki raga musu! Da shi da uwarsa da wannan wadda kika ce Aunty d’in nan nasa’
Ina fatan kin fahimci rashin tsoronsu d’in da kika nuna shi ya kwace ki har ya kaiki ga ci gaba da zama a gidan?”

Da sauri tace “Tabbas kam hakanne”

Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace “To inaso ki tashi ki tsayawa kanki nima kuma Ina nan Ina tayaki! Sannan duk bayan sati biyu ki saka mishi saiya dinga biyan ki kud’in kayan kwalliya da buk’atun yau da kullum. Sannan ki tashi ki tsaya ko yaya za suyi dake ki nuna musu ba zaki tab’a yarda ki zubar da cikin ba!
Ni na san yadda zan yi daga k’arshe.”

A hankali Jalila tace “Umma to ya za muyi da Baba?” “Kar ki damu!
Zan ce masa kin bi Hansai daman ya san da zancen za tayi tafiya
Inta kama ma Kaka zan saka yayi mishi magana Yadda ba zai iya cewa a’a ba Kar ki damu na san me zan yi.

Sannan abu na gaba Kar ki damu in shaa Allah zan tsaya miki ki auri Arshaad bi’izinillahi Ta’ala. Tunda yanzu dai babu maganar aurenshi da kowa in ba Hudan ba Huda kuwa k’aramin alhaki ce dan karki damu ki bar mini komai a hannuna kinji?”

Cike da farin ciki Jalila tace “na gode sosai Ummana”

Murmushi Umman tayi suka d’an yi hirara su Jalilan tana ta bata labarin bahon da tayi wanka aciki da gadon da take kai da d’akin da komai. Daga baya suka yi sallama bayan Umman ta gaya mata itama gobe da safe zata wuce Kaduna biki.


*****
Washegari da safe sai wajajen goma ta samu ta farka. Sai da tayi wanka tukunna ta fito parlourn k’asa. Kamar masu meeting haka ta tarar da Mammy Ummi da Mom sun had’a kai ko sauk’owarta ba su ji ba! A ranta ta ce “guda d’aya ta k’aru kenan!”

Bata ko kalli inda suke ba ta tako ta zo ta wuce su zuwa dining. Kamar daga sama taji Mammy tace “Ba ki iya gaisuwa ba?” Da sauri Mom tace
“Ki rabu da ita kawai mana! Ba na son rikici da safen nan wallahi.”

Cikin b’acin rai Ummi tace “Ai dama na gaya miki!! It’s like kamar fa tsoronta ma take ji! Ni kam ba zan iya zaman ganin abun takaici ba! Sai anjimanku.”
Tana gama fad’in haka ta mik’e tayi hanyar fita. Jalila tana ganinta amman tak’i matsawa Ita kuwa Ummi tana zuwa tabi ta kan k’afarta ta wuce
“Da sauri ta ruk’o mayafinta Sai kuma ta durk’usa a wajen ta kurma wani uban ihu!!!

A razane Mom ta taso. Mammy kuwa tsaki kawai taja tanajin tsanar Jalila na sake shiga ranta! Mom tana k’arasowa wajen Jalila ta mik’e a fusace tayi hanyar fita. Da sauri tace “tsaya Jalila tsaya dan Allah!” Dan ta san abunda take shirin yi.

Juyowa Jalila tayi tana musu wani kallon wulak’anci Da kyar Mom ta samu ta danne abunda take ji yana taso mata ta k’arasa gabanta ta tsaya tace “Kiyi hak’uri Itama kuma zan yi mata magana!! In sha Allah ba zata sake ba.” Ummi ji tayi kamar ta d’aura hannu a kai ta kurma ihu!! Yayin da Mammy take ji kamar tayi super ta shak’o wuyan Jalila.

Murmushin renin wayo Jalilan tayi kafin tace “Kinga Adama! Ta sake ko kar ta sake wannan duk ba damuwa ta bace ba! Kawai abunda nake buk’ata shine tazo ta durk’usa ta bani hak’uri!
In ba haka ba to babu abunda zai hana ni yin abunda nayi niyya!!” Tana fad’an haka ta fara k’ok’arin juyawa.

Ruk’o Jalilan tayi da sauri jikinta na d’an rawa tace “Tsaya zata baki hak’uri!” Sannan ta juya da sauri ta koma wajen Ummi ta kamo hannunta. Tun kafin tace wani abun Ummi tace
“Adama ba ki da hankali ne? Hak’urin kike so inje In durk’usa In bata ko me?
To bari kiji ‘Ba zan bayar ba!!’ Sai dai duk abunda zai faru ya faru!!”

Cikin b’acin rai ta kalli Jalilan tace
“Idan baki san hanyar gidan nashi ba kizo muje ni zan rakaki!! K’aramar mara kunya kawai!!”

Murmushi kawai Jalila tayi kafin ta d’aga kanta ta kalli agogo tace “Na baku minti uku!!”.

Kamar Mom za tayi kuka haka ta fara lallab’a ummi tana rok’on ta Allah Annabi amman furr!!! Ummi tace “ba zata bawa k’ask’antacciyar Yarinya kamar Jalila hak’uri ba!” Mammy ma bayan Ummi ta bi d’ari bisa d’ari!.

Ganin ba zasu bata had’in kai cikin sauk’i ba! Ga lokacin da Jalila ta bayar ya cika ya sanya kawai ta koma gefe ta tsaya tace “Duk ku biyun nan ba don ni ba da ban san halin da kuke ciki a yanzu ba! A tunanina ko mahaukaciya na d’auko a bola nace ku bata hak’uri saboda rufin asiri na ni da d’ana to za kuyi. Amman ba komai na gode
gwara da Allah ya nunamin wannan ranar! Sai dai inaso ku sani Wallahi sai dai ta fashe da kowa! Dan k’afata k’afar Yarinyar nan! Tana gama zayyane bayaninta nima zan zauna In zayyane komai!! Dan ba zai yiwu in share shekarun Ina taimakon ku ba
yanzu kuma tashi d’aya ni in shiga problem ni kad’ai saboda taurin kanku!” Tana gama fad’in haka ta taka inda Ummi take tace “Ga ki ga Jalila nan! In kinga dama ki bata hak’uri
In kuma kin shiryawa fashewar boma bomai a cikin estate d’innan dan Allah kar ki bata hak’uri.” Tana gama fad’in haka ta koma kan kujera ta zauna ta d’aura k’afa d’aya akan d’aya tana girgizawa.

Ummi ta jima tana tunani chan! kawai ta k’arasa inda Jalilan take tsaye ta d’an durk’usa kad’an tace “Jalila kiyi hak’uri nayi laifi ba zan k’ara ba”
Bata bi ta kan kowa ba tasa kai ta fice da sauri. Mammy ma tabi bayanta.
Mom kuma ta mik’e tayi sama.
Jalila kuma ta nufi dining tana tunani a ranta “menene haka sirrin da su Ummi basa so ya tonu?”.

BAYAN KWANA HUD’U!!

(After four days!)

Kamar yadda Mama tayi alk’awari haka nan yau ta shirya tsaf! Tun k’arfe takwas ta sanya atamfar ankon Khadijah da niyyar zuwa gidan Baaba Talatu. Tun bakwai suka yi waya da Ummu tace mata “sun fito tun tuni”
So ta san duk inda tara tayi sun k’araso in shaa Allah.

A kitchen ta fito ta samu Hudan tana d’an had’a musu abun kari da su da Ya Ja’afar dan shi ba a tafi da shi ba.
Ganin da tayi Huda bata k’arasa nata shirin bane ba ya sanya tace mata “ta wuce taje ta shirya ita zata k’arasa aikin” Already ma Huda ta ida, zuzzubawa ne ya rage da had’a shayi. “To” kawai Hudan tace daganan ta wuce d’aki.

Mama na shirin zama taji kamar kira ya shigo ya yanke dan haka ta zaro wayar daga purse d’inta. Tana dubawa taga Ummu ce! Ajjiye purse d’in tayi a gefe sannan ta gyara tsayuwarta ta hau kiran Ummun. Tayi mata misscalls sama da bakwai amman bata d’auka ba! Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba dan haka kawai ta yanke shawarar ta kira Shuwa tunda d’azu Ummun tace mata ‘a mota d’aya suke ita da Shuwa da Sumayya da Abba Madu da Ya Jamilu da suka je d’aurin aure a jiyan.

Su Baba kuma suna tare da su Baaba Talatu.’ Bugu uku a na hud’un ta d’auka! Bata ce komai ba ta dai d’auka ta kuma kara a kunnenta!! A hankali Mama tace “Ina kwana Hajiya, Bilkisu tana kusa? Inata kiranta bata d’auka.”

“Inaga wayar tana a silent ne” Shine abunda Hajiya Shuwa tace, daga nan tayi shiru. A hankali Mama tace
“Tam shikenan” Har zata kashe sai ta sake cewa “sai kun k’araso. Muma gamu mun shirya yanzu zamu tafi gidan Baaba Talatu mu jira ku a chan.”

Cikin yaren shuwa Hajiya Shuwa tace
“Ku yi zaman ku kawai ba sai kun zo ba! Maryam Ina cikin farin ciki kar ki ja a b’ata mini rai kokuma a gaya min magana a yau d’innan!! Na gaya miki kar kuzo mana cikin taro da ke da y’arki amman kin k’i yarda ko?? Taurin kan naki da kika saba shi zaki gwada mini ko?” Cikin fad’a sosai taci gaba da cewa “Wallahi idan naga k’afar ki a inda nake ranki in yayi dubu sai ya baci!” Tana gama fad’in haka ta yanke kiran…

Wayar Mama tana da volume sosai, duk da Huda ba wani yaren Shuwa take ji sosai ba amma tabbas ta fahimci abunda Hajiya take nufi.

A hankali Mama wadda take jin kanta na masifar juyawa da sarawa ta sa hannu ta share hawayen da ya zubo mata!

Juyowa tayi da niyyar d’auko kwano a kwando suka had’a ido da Huda wadda take kallon ta tana zubar da hawaye.

Wani tausayinta ne ya lullub’e Mama lokaci guda! A b’angaren Hudan ma hakan take.

Da sauri Mama ta zo ta giftata ta wuce ta fice daga kitchen d’in Dan kallon fuskar Yarinyar sake narkar mata da zuciya yake yi. Tana fita itama Hudan ta juya ta bi bayanta.

Duhun! Da ta fara gani ne ya sanya ta d’an tsaya ta dafe kanta. A hankali ta fara jin wani irin jiri yana kwasarta kafin daga haka taji jinta da ganinta da k’arfin jikinta sun d’auke lokaci guda ta tafi ta sulale a tsakar gidan ta fadi!! Kamar matacciya!.

Da k’arfi Huda tace “Maamaa!!!”
Sai kuma ta yi kanta da gudu tana kuka. Kuka take yi tun k’arfinta tana kiran sunanta amman ko motsi bata yi ba. Ganin hakan yasa ta sake gigicewa ta rikice ta rasa ma ta Ina zata fara!
Tana shirin mik’ewa sai ga Ya Ja’afar ya shigo. Da gudu ta k’arasa inda yake tace “Ya Ja’afar napep dan Allah ka nemo napep mu d’auki Mama a kaita asibiti dan Allah Ya Ja’afar..” ta hau rirrik’esa tana mishi magana duk ta gigice..

Kallonta yayi ya kalli inda Maman take. Kamar wanda zai yi abun arzik’i haka ya k’arasa inda Maman take kwance. Dai dai setin fuskarta ya d’an yayyarfa hannunshi (kamar wanda zai kore mata sauro) A hankali ya d’ago ya kalli Huda wadda take kuka kamar ranta zai fita yace “Wannan ai napep ba zata yi aikin komai ba! Sai dai a d’auko makara!! ayi mak’abarta da ita.
Kallifa ko uffan bata ce mini ba!
Bafa ta motsi.”

Cikin kuka Hudan tace Ya Jaafar asibitin dai! Ka nemo mai napep ka taya ni d’aukar ta Zata farfad’o in shaa Allah suma tayi.”

Banza yayi da ita ya juya ya nufi kan baranda sannan yace “bara in d’an rintsa In farka sai munje in yi mata sallah a mik’ata!.”

Sai a lokacin Huda ta lura da yadda yake tafe yana tangad’i!!! “Na shiga uku yau!” Tace tana wani irin kuka…

Ko mayafinta bata tsaya d’auka ba ta fita da gudu gidan da yake a jikin nasu dake suna da mota su wai ko zata samu a tayata a taimaka mata su mik’a Maman asibiti. Sai dai kuma tun kafin ta k’arasa ta hango k’atoton padlock mak’ale a k’ofar gate d’in gidan wanda hakan yake nuni da ba kowa ma a gidan kenan!.

A rikice ta juya ta koma cikin gidan tana shiga ta tarar Ya Ja’afar har yayi bacci. K’arar wayarta ta jiyo a d’aki sai a lokacin tunaninta ya bata kawai ta kira Arshaad. Tana shiga ko bi ta kan misscall d’in bata yi ba ta hau kiranshi babu k’akk’autawa.

MT & co. A lokacin Aslam ya je office d’inshi kenan Granpa kuma ya saka shi wani aiki na gaggawa. Duk ya rikice hakan yasa ko wayarshi bai tsaya d’auta ba ya wuce wajen da ake sarrafa turarurrukan wanda yake nan a gefen building d’in da yake d’auke da offices bayan ya cewa Aslam d’in ya jira shi a office d’in nasa nan da kamar 20 minutes zai dawo.

Yana fita ko 1 minutes bai yi da fitar ba wayarshi ta fara k’ara! Aslam, kamar zai bishi da wayar sai kuma yayi tunanin ‘bara kawai ya jira har ya dawo sai ya bi kiran kawai’

Ganin yadda aka jera mishi kusan 20 misscalls a jere ba hutu ne ya sanya ya yanke shawarar kai mishi wayar kawai, dan ya san dole its important!!
Yana d’aukar wayar wani kiran yana sake shigowa tare da wani message da alamun yanzu aka turo!“Life support” Haka yaga sunan b’aro b’ari ya fito a akan screen d’in. Ko ba a gaya mishi ba
Ya san Huda ce! A hankali ya lumshe kyawawan idanuwanshi ya bud’e su kafin ya maida wayar kawai ya ajjiye ya koma ya zauna yayi shiruuu.
Ganin tanata kira still babu k’akk’autawa ne ya sanya ya mik’a hannu ya d’auki wayar a karo na biyu
Yana d’auka kiran yana tsinkewa dan haka ya samu damar ganin sak’on data turo ta notification bar! “Ya Arshaad Mama ta suma ba kowa a gidan sai mu biyu ka taimakamin Dan Allah kazo mu kaita asibiti!”

Da mugun k’arfi yaji k’irjin shi ya buga! Tsintar kanshi kawai yayi da mik’ewa tsaya ya fice daga office d’in gaba d’aya bayan ya ajjiye wayar a kan tebur.

Ko takan wayar Arshaad d’in bai sake bi ba! Ya isa inda motar shi take ya shiga ya bata wuta ya fice daga companyn da gudun.

Babu nisa tsakanin company d’in da gandun albasa hakan ya sanya ya samu damar k’arasawa acikin mintuna k’alilan!

Yanayin parking ya fito da d’an gudu ya shiga gidan kanshi tsaye. A tsakar gidan ya hango su Hudan tana ta k’ok’arin d’aura Mama a bayanta tana kuka amman ta gagara!

Tana jin shigowar mutum ta d’ago idanuwanta tana kallonshi. Shima itan yake kallo! Wani sabon kuka ne ta ji ya kufce mata mai k’arfi ba tare da ta shirya ba!

Da sauri ya k’arasa inda suke yana kallon ta yana jin yadda k’irjin shi yake bugawa.

Da kyar ya iya ce mata “Muje”
Sannan ya durk’usa da niyyar d’aukar Mama.

Zabura!! Yayi bai san lokacin da yace
“Anty Maryam!!!” Da d’an k’arfi, ba.
Sai kuma ya sago yana kallon Huda wadda take yi mishi kallon mamaki.
Mayar da dubanshi yayi a fuskar Mama yana yi mata kallon kurilla
Kana ganinshi ka san a firgice yake!! Cike kuma da mamaki sannan kanshi a d’aure yake. D’agowa ya sake yi ya kalli Huda! Sai kuma ya sake maida idanunsa akan fuskar Mama.

Cikin kuka Hudan tace “Ya Aslam dan Allah mu je kar wani abun ya sake samunta.

Wani yawu mai d’aci ya had’iye kafin a hankali still idanuwanshi suna a kan fuskar Maman ya sanya hannu ya d’auketa yayi waje da ita.

Ita ma Hudan kanta a d’an d’aure yake, sakamokon jin yadda ya kira sunan Mama lokaci d’aya kuma har da
‘Anty’ wanda ko lokacin da su Jalila suna Yara ta san ba anty suke ce mata ba! Sannan bata tunanin ko Ya Arshaad ta tab’a gayawa sunan Mama balle tayi tunanin ko shine ya fad’awa Aslam d’in! Bata wannan take ba yanzu ta Lafiyar Mama take dan itace abun dubawa! Dan haka ta kawar da tunanin gefe. Tana ganin sun fita itama da gudu ta koma ta d’au mayafinta ta d’auko y’an kud’ad’en da suke dashi ta zuba a jakar Maman ta d’auko mata purse d’inta data bari a kitchen tasa a cikin jakar ta fito daga gidan lokacin Aslam har ya saka Maaman a Bayan mota yana gyara mata ruffin mayafinta daya d’an zame kad’an.

Ganin ya juya ya shiga mazaunin driver ne ya sanya itama ta bud’e motar ta shiga baya ta zauna ta d’aura kan Mama akan laps d’inta tana shafawa tana kuka.

Basu kai ga k’arasawa asibitin ba taji ya ce “Assalam Alaikum, Abba Ina wuni! Dan Allah duk abunda kake yi ka bari kazo emergency yanzu AKTH
Ba zan iya bayani a waya ba an Allah Abba ka zo dan Allah.”

Shiru taji ya d’an yi kafin ya sake cewa
“Ok tam Na gode.”

Ita dai Huda mamakin Aslam take yi yadda duk ya rikice da kuma yadda ya kira sunan Mama! Sannan yanzu taji ya kira wani ‘ABBA’ ya ce ya same su a AKTH! A hankali a chan k’asan zuciyarta ta ce “Waye ABBA???”.

                  END OF BOOK ONE

                       

<< So Da Buri 34So Da Buri 36 >>

1 thought on “So Da Buri 35”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×