Skip to content
Part 38 of 71 in the Series So Da Buri by Bulama

Sai da Arshaad ya dawo daga masallaci ‘sallar isha’ tukunna ya lura babu Mammy a gidan. A bakin cook d’insu ya ji komai bayan ya tambayeta.

Da kyar ya iya controlling kanshi dan ya san idan yace zai samu Abba ko Daddy a wannan lokacin a yanayin da yake ciki to tabbas za a samu matsala.

Dafe kanshi kawai yayi ya sallami cook d’in. Ya dad’e a tsaye! Bai ma san ta ina zai fara ba! Dan haka kawai ya sake komawa d’aki ya kwanta. Da kyar kuwa ya samu ya iya rintsawa a daren ranar.

WASHEGARI.

Sai bayan sallar isha, tukunna Granpa ya nemi ganin Huda Abba Gramma Daddy da Dad, wanda dawowarshi kenan ya tarar ana sallah dan haka ya kira Gwaggo suka k’arasa cika ita da Mommy shi kuma ya shiga masallacin, ana idarwa Granpa yace “su wuce side d’inshi”, ko gidan shi be bari ya lek’a ba.

A tare su duka hud’un suka iso parlourn Granpa. Ba tare da b’ata lokaci ba ya d’au waya yayi kiran Gramma ya ce “su zo ita da Huda!” Hijabin Gramma na salla mai hannu Hudan ta zumbula a kan abayar jikinta. Bayan sun fito. Hudan ta bisu duk ta gaidasu, cike da kulawa duk suka amsa mata apart from Granpa wanda ya kauda kai gefe! Tana k’ok’arin zama a k’asa Abba yayi saurin jawota ya zaunar da ita a kan kujera kusa da shi sannan ya hau tamabayarta “how is she?”

Tana shirin yin magana Granpa yayi gyaran murya! Sai da ya lura hankalin kowa ya dawo kanshi, sannan cikin serious voice d’inshi na tsoffi ya fara magana “Na san kowa a nan ya san abunda ya faru! Da kuma wannan Yarinya da Abba ya kawo yace ‘y’arsa ce’! Although ga kamanni nan na gani kuma su Ummi suma sun tabbatar da hakan, but duk da haka i need proof! Saboda ko dan abinda aka ce su Ummi sun yi jiya ya sa na saka jin ba zan iya trusting family members d’ina ba ma akan komai talkless of Maryam! Na lura ba zata iya hak’ura da Abba ba so she can do anything, zata iya tricking su kansu su Ummi d’in ta jira for years tukunna ta aiwatar da plan d’inta.

Wannan dalili yasa jiya aka d’au sample d’inta da kuma na Abban wanda ya nemi yayi mini rashin kunya bayan na kira shi za a d’auki jinin nashi! He looked at me yana cemin ‘ko da ace The girl is not his, shi already ya riga ya yi accepting nata, so tests d’ina babu abunda zasu saka ko su chanja!’.”

Shiru Granpa yayi ya d’an sauk’e ajiyan zuciya sannan yaci gaba “idan nace muku na tsani Maryam!!! Sai ku dinga ganin laifina, jiya kawai ya ganta suka had’u amman har ya zama mara kunya mara mutunci! I’m pretty sure inda a ce bai ganta ba to da ba zai iya gaya mini maganar da ya gaya mini ba!! He even hit his wife! Saboda kawai giyar ganin wannan matar yana yawo a jikinshi. Anyways duk ba wannan ne ya zaunar da mu anan ba!
Abba, ina so ka sani ko da a ce zan yi disowing d’inka kamar farko, i’ll make sure Maryam bata lik’a maka y’ar da ba taka ba! Shi yasa na saka aka yi DNA and results d’in sun fito positive, so she’s your daughter, although na san you don’t need it!

Magana ta anan ita ce, 29 years ago!!! Na fad’a maka na fad’awa Maryam cewa ‘I’ll never accept her and her children!!’ Dan haka wannan Yarinyar” yayi maganan yana nuna Huda, sannan ya ce “kasancewarta y’a ga Maryam hakan ya sa she cannot live with us in this estate! Kana da two options, either ka mayar da ita wajen Maryam Or You are free to leave this estate and family, with her Forever!!!.”
Yana gama fad’in haka ya koma yayi lamooo, a kan luntsumemiyar sofar da yake kai.

Shiru, parlourn ya d’auka, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan Huda. A hankali Abba ya mik’e rik’e da hannunta har yanzun. Gaban Granpa suka je suka durk’usa sannan ya fara magana “Granpa ba ni da bakin da zan yi maka godiya akan irin abubuwan da kayi mini tun haihuwata har kawo yanzu, bazan tab’a iya biyanka ba sai dai in kamanta! Ko da a ce kai ka cire Ni a cikin y’ay’anka Ni ba zan tab’a iya chanja uba ba! You’ll forever remain my Dad that same Dad that loves me so much! Wanda son zuciyata ya sanya a yanzu ba na jin akwai 10% out of 100 na son da yake yi mini. Na san ba lalle ka iya finding place a heart naka kayi forgiven d’ina ba, but i’ll keep on apologizing till the end of time, I’m sorry, so sorry, very sorry! Dan Allah kayi hak’uri ka yafe min.” Yana gama fad’in haka ya mik’e ya mik’ar da Huda itama sannan yace “Hudan and I are leaving!! Good bye.”

Da sauri Huda ta ce “dan Allah ka yi hak’uri, ka zauna da su, ni zan koma wajen Mamana, na ma fi son wajen ta a kan nan, kar kuyi fad’a saboda ni dan Allah!”.

Abba bai saurareta ba sai ma k’ok’arin janta da yake yi, dan so yake yayi sauri ya bar parlourn ba ya so su had’a ido da Gramma. Ya juya ke nan yaga Daddy a tsaye! Bai gama tunanin me ya mik’ar da shi ba yaga ya k’araso inda yake ya rik’e free hand d’inshi!
D’agowa yayi yana kallonshi da jajayen idanuwanshi, ganin Daddyn shima shi yake kallo ya sanya shi cewa
“Don Allah kar ka ce komai, kasan ba zai tab’a chanja decision d’inshi ba, ni kuma ba zan iya barin y’ata taci gaba da zama a gidan wani ba! Please don’t stop me.”

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, kafin ya ce, “i’m not trying to stop you Abba. I’m coming wit you!!.”

Da sauri ya kalleshi sannan ya juya ya kalli Granpa wanda ya lumshe idanunsa yana nan kishingid’e kamar mai bacci.

Shima Daddy juyawa yayi still rik’e da hannun Abba yana kallon setin Granpa sannan ya fara magana “Granpa! Laifin Maryam da Abba bai kamata ace ya shafi Yarinyar nan ba!
Ba fa mu ma santa ba, ba mu san ma tana existing ba, ta taso ba tare da kulawar d’aya daga ciki mu ba. I think yanzu lokaci ne da ya kamata ace mun yi welcoming d’inta warmly mu nuna mata gatan da bamu nuna mata ba a baya! Ba wai a hukuntata a kan laifin da iyayenta suka aikata ba wanda ya ci a ce yanzu ka yafe tunda Abban da Maryam d’in sun dad’e da rabuwa!!

To be honest Granpa What you have been doing is not right!! Kawai muna yi maka biyayya ne because we respect and love you as a father! But it’s like abun yana neman yin yawa! Tunda gashi kana k’ok’arin kai Abba wuta! Ko ba ka tunanin Allah zai tambaye shi hakkin y’arsa akan shi ranar gobe k’iyama??”

What you are about to do is wrong! Very wrong!! Dan haka i think it’s about time da ya kamata mu fara fad’a maka gaskiya! But na san ba lalle ka yarda ba, kamar yadda Abba ya fad’a nima na san ba lalle ka chanja decision d’inka ba so idan ka kori Abba, nima zan bishi, that’s it!!!”.

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya bud’e idanuwanshi, bai kalli ko inda suke ba, ya sauk’e idanunsa a kan Dad, a hankali yace masa “what about you Yahaya?? Wat’s your decision?”

A hankali cikin mutuwar jiki Dad ya mik’e, muryar shi na d’an rawa dan shi kwata-kwata abun nan da ake bai yi mishi dad’i ba! Ba ya son tension kwata-kwata a halin yanzu shi
ko da matsalar matar shi aka bar shi ta ishe shi, but he has to do whats right, dan haka ya ce “na zab’i side d’in brothers d’ina Granpa. I’m sorry, but whatever Yusuf just said is the truth.”

“Ok “, kawai Granpa ya ce, kafin ya juya wajen Gramma ya kalle ta itama ya ce “Ke fa??” Hawayenta ta sa hannu ta share, sannan ta ce “sun fika gaskiya!! Na rok’eka da girman Allah for once a rayuwan ka ka yi hak’uri ka yi abunda suke so dan Allah”

D’an murmushi Granpa ya yi kafin yace “If not kema ba ki da choice d’in da ya wuce ki bisu ko???”

Shiru, ta yi bata ce komai ba, har sai da ya sake cewa “ke muke jira, your decision is important.”

Tukunna,a hankali cikin kuka Gramma ta hau d’aga kai alamar ‘eh’.

Da sauri Abba ya durk’usa ya fara yi mishi magiya “dan Allah ka yi hak’uri ka barni In zauna da ku! Ka yi accepting Huda plss karka…”

Hannu Granpa ya d’aga mishi kafin ya mik’e tsaye! Yaje inda yake shima ya mik’ar dashi tsaye sannan ya fara magana “Already na riga na gama magana Abba, kai ka sani. And please stop pretending dan na san this is wat you want! Kana so inyi regretting akan abunda na yiwa Maryam tunda inda ina shiri da ita tun farko ai da duk haka bata faru ba, right? But inaso kan san 1 thing, ko d’aya, hakan bai sa naji ba dad’i ba, infact I’m happy because i’ve and i’m punishing the devil!!!

Ka duba fa kaga yadda Ummi ta koma, abunda suka yi ita da su Adama, duk saboda matar nan( Maryam), which I’m pretty sure ba halinsu bane ba! Laifinta ne she push and made them act that way!! And now look! Abunda dukkan ku ku kayi mini, all because of her!! Abba How? Ta ya ya kake tunanin zan yi accepting y’ar matar nan? Matar da ta mayar mini da family haka? Tunda nake da mahaifiyarku gata nan ku tambayeta bata tab’a yi min koda yaji ba nima ban tab’a tunanin tura ta gidansu saboda wata matsala ba amma yanzu kalli, she’s ready to leave. Because of Maryam! Maryam bad luck ce! Amman ka kasa fahimta kwata kwata. Ka duba kaga fa, tun lokacin da ka had’u da ita ba ka samu peace of mind ba har yau d’in nan! Iya jiya( just yesterday) da kayi spending time da ita kalli abunda ya janyo, bu.”

Mahaukacin kukan da Hudan ta fashe da shine yasa su kallonta gabad’aya, dukkanin k’arfin da Allah ya bata tayi amfani da shi wajen fincike hannunta a cikin na Abba, sannan ta d’iba a guje tayi waje a ranta tana ayyanawa “wallahi ba sojoji ba ko barrack ne a bakin gate d’in estate d’in yau sai ta fita, yadda ta kwasa a gujen nan ba zata tsaya ba sai ta ganta a titi sai dai ayi mata kallon mahaukaciya.

Shiyasa ashe Baabaa Talatu take rok’on ta akan karta kuskura ta yiwa Mama maganar Mahaifinta (Abba) ashe wannan ne dalilin kenan. Tunda take bata tab’a ganin hatred irin wannan ba, dan ko k’iyayyar Shuwa gare su bata kai ta wannan tsohon da ake kira da Granpa ba, gashi har yana k’ok’arin danna musu tambarin ‘bad luck’, kuma duk wanda yaji labarinsu tabbas zai yi musu kallon hakan, tunda gashi ita kanta iya kwana d’aya kawai tayi a estate d’in but familyn yana neman hargitsewa! What type of daughter will she be idan ta yiwa Mahaifin da yake k’ok’arin making up to her sanadin tarwatsewar family d’inshi? Besides tana so taje taga halin da Mama take ciki, so she has to leave, ta ko wanne hali a yau sai ta gudu daga estate d’in nan!” Da wannan tunanin ta dinga zabga gudu. Cikin ikon Allah ta hango k’ofar gefen gate d’in gidan a d’an bud’e kad’an dan haka ta k’ara gudu ta bi ta k’ofar ta fice. Tun tana jin muryar Abba wanda ya biyota yana kwala mata kira har ta daina.

Fitulu ta ko ina tarr!! Kamar rana, shiyasa ta samu damar ganin gabanta cikin sauk’i!.

Gudu kawai take tun iyakar k’arfinta. Tana gudu tana kallon baya taga fitowar Abba daga gidan Granpa inda ta fito. Mai gadin ya tsaya yana tambaya taga yana nuno masa direction d’inta, hakan yasa tayi saurin b’uya a bayan motar data gani a gefenta jikin wani gida, tana d’an lek’owa kad’an ta jikin glasses d’in, gadan gadan taga yayo inda take dai dai aka bud’e k’aramar k’ofar shiga gidan dake jikin gate d’in da alamun fitowa za ayi, Allah ya taimaketa Daddy ya biyo Abba yana mishi magana dan haka ya juya gareshi.
Wani wawan tsalle tayi da mugun sauri ta afka gidan.

Da sauri yasa hannunshi ya dafe bango d’ayan kuma ya dafe bayanta, wanda hakan da yayi ne ya taimaka musu basu zube a k’asa ba! K’amshin turaren shi da tun ranar da suka fara had’uwa ta sanshi da shi ne ya tabbatar mata da waye!! K’ok’arin barin jikinsa take yi amman bata san dalilinshi na rik’e mata baya ba!..
Dukkanin k’arfinta tayi amfani da shi wajen ganin ta raba kusancin nasu amman hakan sai ya gagara! Don ruk’on da yayi mata bana wasa bane, as if his life depends on it.

Gaba d’aya sai ta sake firgicewa, kukanta ya k’aru bare ma yadda taji zuciyar shi na wani kalar mahaukacin bugawa.

So yake ya cire ta a jikinshi amman ya kasa, idan ana maganar over racing to shine abinda zuciyar Aslam ke ciki a halin yanzu, tun daga lokacin da yaga tayo tsalle ta shigo da gudu tana kallon baya, har kawo yanzu da take a jikinshi.

Tun lokacin da Arshaad ya fara kiran sunanta taji, dan haka har d’an dukan Aslam take tana kuka akan ya barta! Amman kwata-kwata babu chanji a yanayinshi sam, it’s like yama k’ame a hakan ne ko yaya ne ita dai ta kasa ganewa.

Sai da Arshaad ya k’araso ya kama hannunshi wanda ya rik’eta gagam, da kyar ya iya b’amb’areta daga jikinshi tukunna hankalinshi ya fara dawowa jikinshi a hankali a hankali. Sannan da kyar ya cika bangon ya d’an seseta tsayuwar shi kafin ya kalli Arshaad wanda kafes hi da manyan dogayen idanuwansa.

He looks calm amma nfa idanunsa sun mugun chanja kala.

Gabad’aya kuma sai abunda ya faru ya dawo mishi, take yaji wata kalar kunya ta lullub’e shi, da kyar ya Iya tattaro y’ar ragowar jarumtarshi, yana shirin yin magana suka jiyo muryar Abba da Daddy suna dumfaro su, Daddy yana cewa “ga k’ofar a bud’e maybe nan ta shiga, dan na san ba lalle an barta ta fita ba lets check.”

Da sauri Hudan wadda har yanzun gabad’aya ilahirin jikinta ke rawa ta juya tana kallon Arshaad kafin a hankali tace “Ya Arshaad dan Allah ka b’oye ni dan Allah.” Tayi maganar tana had’e hannuwanta waje d’aya alamun rok’o, tana kuka.

Ganin sun kusan isowa ne yasa Arshaad d’in da sauri ya jata yasa a d’akin mai gadi sannan yace mata “ta shige toilet d’inshi(mai gadin) tayi shiru.”

Tana rufe k’ofar toilet d’in su kuma su Abba suna shigowa gidan, daidai Arshaad yana shirin fita shi kuma, suka yi kicib’is!.

Kallon kallo aka tsaya yi, kafin Daddy yace “kunga Hudan?”

Aslam yana shirin yin magana Arshaad yace “No” da sauri sannan ya d’ora da “Neman ta ake? ina tayi? Mai ya faru?”

Aslam kawai Abba ya k’urawa ido ganin yak’i had’a ido da shi yasa ya cewa Daddy wanda yake shirin yiwa Arshaad bayani “Mu koma kawai, ina ga wajen Gwaggo Asabe tayi. Ma duba ta anjima, lets take care of Granpa, na tabbatar biyo tan da muka yi yanzu ma case ne.”

100% Daddy ya yarda da hakan dan haka ya cewa Aslam “ya ci gaba da duba musu Hudan za suyi musu bayani anjima, shi kuma Arshaad yaje Gate yayi confirming in bata fita ba daga nan ya sa curfew a estate d’in har su samu su gama meeting da Granpa su fito.” Da “to” suka amsa musu daga nan su Abba suka wuce.

Suna fita shima Arshaad ya fara k’ok’arin fita a gidan, “ka ce mata zata iya fitowa.” Shine kawai abinda ya iya cewa Aslam ba tare da ya yarda sun had’a ido ba. Har ya juya yaji Aslam d’in ya ruk’o hannunshi. Da sauri ya runtse idanunsa da k’arfi, sai da ya d’an dedeta fushinsa kafin ya juyo yana kallonshi.

Aslam tunda yake bai tab’a jin nervousness irin na yau ba, dan haka ya fara kame kame “Um, I’m sooo sorry a b bout”

Da sauri Arshaad ya katse shi ta hanyar cewa “It wasn’t your fault, tayi laifi, so ko baka yi abunda kayi ba dole na san wata rana gaskiya zata fito, kuma za ayi punishing nata. Kawai dai i was disappointed in you ne that’s all”
Sai da ya d’anyi shiru yaji hucin da yake yi ya d’an ragu tukunna ya ci gaba da magana “ko sabon mai aiki aka chanja a gidan nan baka nan Aslam kana Uk but sai na kiraka na fad’a maka!

Ya kamata ace lissafinka ya baka ‘if Abba yana da y’a and bai san da ita ba, to dole akwai wani abu a k’asa’!

Da ka yi finding out about Huda you should have talk to me first mu samu mu fara bincike first! Because that is wat i’ll definitely have done if i were in your shoes. But you just went ahead and ruin everything.

Yanzu because of you Mahaifiyata is there a cell da anty Adama su da basu da laifin komai, they just help a friend.” A hankali ya ce “i tot we were brothers, best friends.”

Cikin katse shi Aslam yace “and yes we still are, yana matsowa kusa dashi da rik’e shi”.

Murmushi kawai Arshaad yayi ya zare hannunshi sannan ya zagaye shi ya fara k’ok’arin shiga d’akin mai gadi.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin ya ce “Ok, I’m sorry”,vyana mai sake ruk’o hannunshi. Sai da Aslam d’in ya maimaita sannan Arshaad ya juyo ya kalleshi na y’an seconds kafin ya ce “Apology accepted.”

“Thankyou”.

Shine abinda Aslam d’in ya ce kafin ya d’aura da “And about what you just saw, i’m..” Cikin katse shi Arshaad yace
“Aslam we’re good fa, komai ya wuce, let me check on her, ta shiga toilet d’in mutumin nan barefoot kuma i don’t even know ko yana ciki dan ban ganshi a d’akin ba.” Yana gama fad’in haka ya zare hannunshi sannan yayi cikin d’akin ya isa bak’in k’ofar toilet d’in yana cewa “Hudan open the door, it’s me, su Abba sun tafi.”

A hankali take bud’e k’ofar tana d’an lek’owa. Sai da ta tabbatar da shi d’inne tukunna ta k’arasa bud’ewa.

Murmushi ya d’anyi mata. Gabad’aya ta had’a gumi tayi zuru zuru! A hankali yace “matsoraciya kawai”
A hankali tayi k’asa da kanta sannan ta fito, Allah ya taimaketa ba kowa a toilet d’in kuma mutumin yana da tsafta dan band’akin tass yake gashi tiles ko ina kuma a bushe. Amman duk da haka sai da Arshaad yayi amfani da ruwan butan da ya gani bayan sun fito ya zuba mata akan k’afafunta.
Suna fitowa ya cire takalmin shi ya bata ta saka sannan yace “ta zo ta raka shi ya saka takalmi.”

A hankali ta fara kuka kafin tace masa “Ita wajen Mama zata je”.

Gabad’aya sai yaji wani matsanancin tausayinta ya kama shi. Shiru, yai yana tunanin ta yadda zai fita da ita bayan shi aka d’orawa alhakin curfew.

Dole ya lallab’ata ta d’an hak’ura ko zuwa gobe ne sai su je.

Matsowa yayi yana shirin lallashinta wayarshi ta hau k’ara, ganin sunan Sakina ya sanaya shi ce mata su k’arasa ciki akwai maganar da yake ai suyi da ita, dama. Tukunna sai ya kaita gurin Maman.

Ba tare da musu ba ta bishi suka yi hanyar shiga parlourn gidan, Aslam har zai bisu dan still ya lura Arshaad d’in is still mad, saboda da suka fito ko inda yake bai yarda ya kalla ba.

Sai kuma kawai ya chanja shawara ya juya kawai, duba da yayi ba shi kad’ai ba ne kuma ya lura soyayyar Mahaifiya ta rufe mishi ido, if not taya ya zai ce “ita da Mom basu da laifil!” ko kuma may be bai san story d’in gabad’aya ba, dai. Da wannan tunanin ya fita a gidan bayan ya yanke shawarar sai nan da 4 to 5 days haka zai neme shi ya sake bashi hak’uri, by then ya san ya sak’k’o.

Suna shiga parlour ya umarceta da “ta zauna akan kujera”. Bayan ta zauna shi kuma ya nufi fridge ya d’auko mata ruwa da glass cup a kan dining ya kawo. Dama kuwa tana buk’ata hakan yasa yana zuba mata ta k’arb’a ta hau sha. Sai da ta shanye tass sannan ta ajjiye tana sauk’e ajjiyar zuciya a jejjere.

Kallonta yayi da idanuwanshi da har yanzun basu gama dawowa dede ba sannan a hankali yace “in kara?”
Girgiza mishi kai tayi tana y’ar mitsitsiyar gyatsa kafin tace “Alhamdulillah”,vSai kuma anhankali ta mik’e tace “Bara inje wajen Aaima”
Mik’ewa shima yayi yace “ba ta nan, ba ta dawo daga school ba tukun! Mammy kuma tana cell! It’s just me.”
Ya fad’i hakan yana tsare ta da ido.

Saurin yin k’asa tayi da kanta, kafin a hankali tace “Kayi hak’uri dan Allah.”
Murmushi ya d’an yi yana kallonta kawai ba tare da yace komai ba.
A hankali tace “bara in tafi, nayi tunanin Aaima tana nan ma.”

Ba ta jira jin me zai ce ba ta fara k’ok’arin fita tana cewa “ka d’auko takalmin naka muje mu duba Mama da wuri, ko?”. Daidai nan wayar shi ta sake ringing, ganin me kiran ne yasa shi kai mata wayar har bakin k’ofa sannan yace “Na so muyi magana but it’s like kamar tsorona ma kike ji! Gashi ungo, Sakina ta gaya miki, bara in d’auko takalmin nawa”. Yana gama fad’an haka ya kara mata a kunne bayan ya amsa kiran daga nan yayi hanyar part d’in nashi.

Da sallama ta amsa wayar. Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e jin muryar Huda sannan ta ce “Alhamdulillah”.
Jin yanayin muryar Sakina yasa ta fahimci akwai matsala. Cikin sanyin muryar da bata santa da shi ba taji tace,v“Huda kuna Ina? bakya hawa watsapp, ba kwa amsa waya tun jiya, gamu kuma mun dawo gida ba kwa nan. Ina kuka je gabad’aya hankalin mu ya sake tashi.” Da sauri Huda tace “Sakina Mama bata gida? Ya naji muryar ki wani iri duk ya dishe?”
Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e, har zata fad’a mata kuma sai tayi shiru (saboda su Madu sun ce a bari a fara yin test na gawarwakin da ake expecting akwai Junaidun a ciki da jinin Baba, before ayi confirming nashi as dead ) Hakan yasa tace mata “Ban gane ‘Mama bata gida ba’ ba kwa tare? Ke kina ina?”.

Gefe guda Hudan ta koma kan kujerar dining ta zauna sannan ta fara bawa Sakina labarin tun daga sumewar da Mama tayi jiya da safe, har kawo yanzu da take son gudowa.

To fa!! Ana wata ga wata. Numfashi Sakina ta fesar kafin tace “With all that is goin on Hudan, congratulations!
Kin had’u da Mahaifinki finally, and ba ya gudunki, kamar yadda mutane suke fad’a. But first Maama, so yanzu ki bani kamar 20 minutes haka za sake kira in shaa Allah.”

Su Abba kafin su koma ciki suka tsaya shi da Daddy suka yanke shawara , suna zuwa suka sanar musu cewa
“Shi da Daddy za su bar gidan, Dad da Gramma kuma za su zauna. Addua suka dinga yi akan Allah yasa kowa ya yarda.

Ba dan su Gramma sun so ba haka nan suna ji suna gani suka amince da tafiyar su su kad’ai, Dad yaso a ce shi ne yabi Abba tunda shi ne Babba. Amman bayan sun keb’e sai suka yi mishi bayani akan kasancewar shi babban ne yasa suka ce ya zauna a estate d’in, sannan ya taimaka ya daidaita Gramma da Granpa, kafin ya koma Abuja, dan tun a wajen meeting d’in suka fahimci iyayen nasu suna fushi da juna wanda hakan it’s not usual. A haka ba dan rai yaso ba aka tsara akan gobe zasu bar estate d’in kafin a samu komai ya daidaita. In Granpa ya sauk’o su dawo, Dad ne ya basu mukullin makeken mansion d’inshi wanda ke anan bayan su kad’an ya ce “su zauna su biyu a tare ba sai sun raba gidaje ba.” Dan ana hoping d’in daidaituwar komai soon in shaa Allah.

Daddy yayi ta jiran Granpa ya kira shi ya ce “yayi resigning, ya kawo takardun companies d’in da yake rik’e dasu sannan ya sauk’a a md d’in MT UK branch amman ga mamakin shi sai yaji shiru, bai ce masa komai ba.

Sakina tana katse kiran ta mik’e ta isa inda Ummu take ta jaa hannunta suka koma gefe, ganin haka yasa Shuwa itama ta iso inda suke, nan Sakina ta zayyane musu komai.

Kafin awa d’aya gabad’aya su Kaka kowa ya hargitse a neman Mama har da Madu wanda ba kad’an ba kowa yaji dad’in yadda ya shiga cikin lamarin. Babu inda ba a duba ba har wajen 10 amman shiru. Ummu ce ta bada shawarar “aje asibitin malam d’in a sake bincika ta!.”

Nan d’inma ba Inda basu duba ba dan rarrabuwa ma suka yi amman shiru.

Tunda suka fito Baba yake ta maimaita magana d’aya. “Aje gidansu Abba! Shi ya tabbatar idan aka yi kwakkwaran bincike a gidan za a ganta. Ya san tabbas Abba ne ya d’auke Maryam ya b’oyeta bashi da tantama! A kira y’an sanda a kama Abba…waye waye.”

Su Ummu tun suna k’ok’arin fahimtar da shi har suka hak’ura suka kyale shi kawai dan sun lura abun nashi ba na k’are bane. Ganin dare ya lula yasa Ummu tace bara kafin su koma gida ta shiga masallacin can tayi sallar isha dan gabad’aya ta sha’afa bata yi ba gashi lokaci ya tafi sosai, sai a lokacin Sakina itama ta tuna bata yi ba hakan yasa suka nufi famfo suka yi alwalla tare daga nan suka shiga masallacin domin gabatar da sallah. Babu kowa a ciki sai wasu mata guda biyu a chaan k’uryar masallacin, d’ayar a zaune da Yaro a hannunta d’ayar kuma ta juya baya tana kallon bango alamun bacci ma take yi.

Cikin nutsuwa suka gabataar da sallar su suka d’ora da doguwar Adduar Allah ya baiyyana musu Mama.
Daga nan suka mik’e suka fara k’ok’arin fita. Ummi ji tayi kawai gabanta ya yanke ya fad’i, kamar kuma ance ta juya, bata san daliliba amman taji tana buk’atar juyawan…
Matan nan na d’azu ta sake kallo still suna a yadda suke, har tana shirin juyawa idanunta suka kai kan atamfar jikin matar kwance da mayafinta, sai a yanzu ma ta lura da kayan dan sanda suka shigo kwata-kwata hankalinsu baya tare dasu, gasu a gajiye.

Kusan a tare zuciyoyinsu suka buga ita da Sakina wadda itama taga atamfa da mayafin jikin Mama Tabbas mayafin Mama ne wannan Atamfar kuma ankon wunin kai amarya Khadijah ne.
Da sauri Sakina tace “Maamaa!” Sai kuma ta k’arasa wajen da sauri ta hau tab’ata ganin bata motsi yasa ta sa hannu ta juyo da ita.

“Innalillahi wa innailaihirrajiun”

Shine abinda Sakina Ummu da matar dake gefen Mama suka fad’a a tare.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 37So Da Buri 39 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×