Skip to content
Part 4 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

A nan ya tafi ya barta a tsaye kamar wata gunki, kana ganin fuskarta ka san ranta a b’ace yake, ita sam! Ta kasa gane kan Auwal kwata-kwata, bata son halayyar nan tashi, kalli yanzu k’iri k’iri ya had’a uwa da d’anta fad’a, shi kuma Arshaad ta tabbata kunyar ta ce ta sanya ya k’i cewa komai, gashi
Daddy ya rok’eta akan dan Allah su taru ita da shi su dinga rufa ma d’ansu asiri, shi kad’ai Allah ya basu su daina yayata wasu halayyar shi da kansu a cikin family, domin kuwa duk ranar da aka yi rashin sa’a granpa ya ji to tabbas kashin Auwal ya bushe.

Tana cikin wannan tunanin ta ji an dafa ta, tana juyowa suka had’a ido da Mijinta Alhaji Yusuf MT murmushi ta yi kafin ta ce, “Daddy yaushe ka dawo?”

Sai da ya d’an k’ura mata ido kafin yace “Auwal ne ko?” Murmushin ta sake yi sannan ta ce, “amsa tambaya da tambaya, are we??”

Sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya yi kafin ya fara magana. Ta windown kitchen na hango ku Ina waya da doctorn Abba, shi ne na fita ta karamar ƙofa na rufe na tsaya a ƙaramin compound saboda bana son Auwal ya ji ni.

Kin san yadda suke shi da granpa, ba ƙaramin aikin sa bane ya kwashe komai ya fad’a mishi.

Tunda ya san in dai da Granpa a case babu abinda zan iya yi masa.”

Shiru ya yi da alamun damuwa a kan fuskarsa kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “Adama akwai matsala fa, don sun sake yin wani fad’an da Granpa har ya ma fi na last time, sannan shi kuma ya sakawa kanshi damuwa over gashi yanzu har ya kusan shiga next stage.”

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”.

Shi ne abinda Mom ta ce idanunta suna kawo kwalla kafin ta kalle sa sosai ta ce, “to ai ni da ka bari Auwal d’in ya ji ya fad’a ma granpa d’in watak’ila hakan ya sanya shi ya d’an sauk’o daga fushin.

Na ga kwana biyun nan ma ai kamar yad’an yi sanyi ai ba kamar da ba, ko?”

Dan murmushi Daddy ya yi tukunna ya ce “babu fa abinda ya chanja daga halin Granpa, kawai dai kwana biyun ba a samu wanda ya taɓo sa ba ne ba shiyasa kika ji shiru, dazun fa Malam Iliya ya kira ni ya ke ce mini Auwal ya fatattake sa, da na tambayi drivern Granpa d’in ya ce mini shi Granpa d’in ne ya ce a kori Malam Iliya d’azu daga dawowarsu daga meeting, wai dan ya bar bakin main gate ya tafi siyan Agwaluma.”

“Allah ya kyauta”.

Shi ne abinda Mom ta ce, sannan a hankali ta ce “wai menene ma to abunda ya taso da fad’an nasu shi da Abban??

Da fa har muna murnar almost 2 years lafiya k’alau tsakaninsu, shima kuma Abban ciwon nasa ko tari babu.”

Sai da Daddy ya d’an furzar da numfashi tukunna ya ce” wai mafarkai yake yi da Maryam! Da jariri a hannunta, tana kuka tana cewa ya zo ya taimaketa, abun ya kai 3 months ya ce kullum in ya kwanta sai ya yi shine fa ya d’aga hankalinsa.


Da farko, Dad ya samu ya fad’a mishi. Shi kuma Dad ya ce mishi ya yi ta addua kawai.

Shi ne fa tsabar ganganci kawai ya je ya tunkari Granpa da maganar.

A kan wai yana so ya je ya ganta, ya tabbatar babu yaro a tsakaninsu, saboda mafarkan da yake ta yi.”

Ba shiri Mom ta zaro ido waje sosai kafin ta yi kasa da murya tukunna ta ce” Me Granpa din ya ce?”

“Cewa za ki yi me ya yi masa, ba me ya ce ba!”

In ban da abun Abba kai da ka san mutumin nan yana ta fushi da kai for morethan 24 years ko ga miciji ba kwa yi da shi, amma shi ne za ka kwashi k’afa ka je ka tunkare sa da irin wannan zancen?

Ni wallahi Adama ni ma na fara tunanin ko dai asiri ne matar nan ta yi masa, saboda ki duba kiga yadda he’s willing to risk everything just to talk to her again. Duk da irin bak’ak’en maganganun da ta dinga rubuto masa har da fa threatening nashi da kotu fa ta yi.


Daga k’arshe fa idan ta aiko da sak’o ba ya nuna mana! Daina nuna mana ya yi ni da Dad, Allah kaɗai ya san irin maganganun da suke a ciki.

Shi kuma a wannan lokacin kullum cikin bata hak’uri yake yi yana aikawa.
Da kyar Granpa ya samu ya rabasu, shi ne yanzu yake son tada zaune tsaye, shi ko ta jikinsa da lafiyarsa ma ba ya yi, gashi yanzu granpa ya yi masa horo mai tsanani.

“Kin ga da farko ya sallame shi a duk wani company da kika sani namu a yanzu babu Abba a ciki, sannan ya hana shi share d’inshi. Kuma ya bashi notice akan ya bar masa estate d’inshi kar ya k’ara ganin shi ko y’ay’ansa.
Yace kuma duk wanda ya bashi hak’uri sai ya had’u da tsananin b’acin ranshi, hatta Gramma.”

“Ya subahanallah”

Shi ne abunda Mom ta fad’a sannan a hankali ta ce “bara inje wajen Zainab.”

“To” kawai ya ce mata ya juya ya nufi dining area ya nemi guri ya zauna ya fara zuba abinci, kana ganin fuskarsa ka san yana cikin matsananciyar damuwa.

Fitowa ta yi tana zancen zuci ta k’arasa bakin gate sannan ta fita ta k’aramar k’ofa, ta nufi d’aya daga cikin gidajen tana d’an sauri, tana isa tayi knocking, kamar kowanne gida nan ma mai gadi ne ya zo ya bud’e mata, ya gaidata ta amsa sannan ta shiga.

Tana shiga ta hango wata k’atuwar moving van ga jakankuna a ajiye a waje da boxes, sannan ana ci gaba da fitowa da wasu. K’ara saurin tafiyar tata ta yi ta nufi hanyar k’ofar shiga main parlourn wadda ke nan a wangale ana ta shige da ficen kwashe kaya.

Da sallama a bakinta ta shiga, tana shiga ta hango wata farar mata zaune a kan 2sitter na d’aya daga cikin jerin kujerun falon, matar ta zabga uban tagumi, kana ganin ta ka san tana cikin damuwa sannan tayi nisa a tunani.

K’arasawa Mom ta yi kusa da ita sannan ta dafa ta, ganin kamar ma ba ta san ta dafa tan bane ya sanya ta kira sunanta “Zainab!”

Firgigit!! Ta yi ta juyo, suna had’a idanu da Mom kuwa kamar jira take yi ta fashe da kuka, sannan ta kamo hannayenta duka biyun kafin ta fara jujjuya kai ahankali tana kallonta ta ce, “Adama ina ta kiranku yau kwana biyar wayanki ba ya tafiya, komai ya zo mini k’arshe kashina ya bushe!! I never saw this coming!!

Shi kenan na san yanzu zai yi finding out kum…”

Mom ba ta bari ta k’arasa ba ta yi saurin zare hannunta wanda ta rik’e ta yi amfani da shi wajen toshe mata baki sannan ta juya tana kallon falon tana rarraba ido cikin fargabar kar wani ya jiyo so.

Ganin da ta yi ba kowa a falon masu kwasar kayan ma duk sun gama na k’asa sun yi sama ne ya sanya ta kamo d’ayan hannun na ta da har yanzu yake cikin nata ta mik’ar da ita sannan ta ja ta suka nufi ɗaya daga cikin ɗaku nan parlour.

Sai da Mom ta tabbata ta saka key, tukunna ta juyo ta ce “Yanzu menene abun yi?”

Share kwallarta Zainab ta yi sannan ta ce, “Granpa ya kore mu shi yasa kika ga ana ta kwash…”

“Na sani” Mom ta katse ta, sannan ta ce “Daddy ya fad’a mini komai.”

Shiru Zainab ta yi, sannan ta jingina da bango ta d’aga kanta sama ta rufe idanunta a hankali ta ce “in dai muka bar gidan nan, kin san cewa babu abunda zai hana Abba bibiyar Maryam ko? Saboda ya kasa yarda da takarda har yau, kin san cewa ko a kwanakin baya dama na gaya miki Ina ganin kokwanto a fuskarsa, ita kuma mayyar gashi yanzu har a mafarki zuwar masa take yi.”

Bud’e idanunta ta yi ta kalli Mom sannan ta ci gaba da cewa, 4 days ago fa yana tashi yace shi wajenta zai je, ya gaji da wannan mafarke-mafarken, da ya je wajen granpa suka yi fad’an nasu da suka saba, dan bai samu an goya masa baya ba shine tun a chan ya zube, sai kwasar shi aka yi , akai asibiti da shi. Kwanan mu d’aya da wuni bai san inda kanshi yake ba ana fama.”

Shiru ta yi kafin ta ci gaba da cewa “Adama granpa shi kad’ai yake iya takawa Abba burki akan Matar nan yanzu ya bashi freedom!! Saboda wannan abun fa da aka yi da Granpa da mutane ne suke ganinshi as punishment amman a wajen Abba freedom ne.

Can u imagine in 2 weeks time fa Granpa ya ce “mu bar gidan nan amman Abba a jiya da sassafe ya kira masu penti aka fara pentin gidanshi na kundila yanzu kinga yau da safe ya ce mu fara parking, na tabbatar ko kammala pentin ba a yi ba. Atleast ai ya jira ya dawo daga asibiti ko?
Ya samu ya d’an warware may be b4 then ma granpa ya sauk’o.”

Murmushi Mom ta yi kafin tace
“Haba Zainab, ke har yanzu ba ki san waye uncle d’inki ba ne? If there’s one thing that I’m sure of shi ne Granpa ba zai goge decision d’inshi ba sai dai in ya sassauta, yanzu mafita itace abar nema ba wai wannan dogon labarin ba, dan ba ke kad’ai ba hatta ni da Mammy sai mun raina kan mu idan zance ya fito…

Na san granpa Hates Maryam with passion, but what we did is something da bai kamata a ce mu bari a kama mu da laifinshi ba!.”

Ajiyar zuciya Zainab ta sauk’e kafin ta juyo ta kalli Adama sannan ta kama hannuwanta biyu ta ce” Ki taimakeni
at any cost kar mu bar gidan nan, you always come out with the perfect solution, do something. Har yau ban samu soyayyar Abba ba, I’ve been trying my best wajen ganin na yi winning nashi kuma na san I’m almost there but in dai matar nan ta dawo cikin rayuwarsa komai lalacewa zai yi.”

Shiru Mom ta yi tana d’an tunani ta kusan 5minutes sannan ta yi murmushi tace mata “kawo kunnenki kiji wata magana” Matsowa ta yi sannan ta fara rad’a mata maganar.

Da farko juyowa ta yi ta kalleta da alamun mamaki mamaki sai kuma ta juya ta ci gaba da sauraronta ahankali ta fara murmushi.

“Ummi! Ummi!! Ummi!!!” Suka ji murya ana kwala kira a parlour.
Da sauri Zainab ta juyo tace ina ga ga su Shuraim sun dawo d’azu suka tafi asibiti.” Har ta kai bakin k’ofa ta murza key d’in za ta fita sai kuma ta juyo ta kalla Mom ta ce mata,

“Kin tabbata babu matsala?”

Murmushi mom ta yi sannan ta d’aga mata kai, alamar ‘eh.’


Juyawa tayi ta fita itama ta biyo bayanta suka fice a d’akin.

Wani Yaro ne yake shigowa cikin parlourn fari tass da shi kyakkyawa.

Suna had’a ido da Zainab ya kalli sama yana kallon d’ayan Yaron da ba zai wuce 10 years ba yanata hawa Bene yana kwala kiran “Ummi!!”.

Da d’an k’arfi ya ce “Sudais!” Da sauri wanda aka kira da Sudais d’in ya juyo yana kallon d’an uwanasa wanda juyowar da ya yi ne zai sanya ka fahimci ashe twins ne dan komai nasu iri d’aya ne.

Nuna masa Zainab ya yi sannan ya ce “Ga Ummin nan.”

Da saurin sa kuwa ya sauk’o ya zo ya rungumeta kafin ya d’ago kai ya ce mata “Ummi Abba ya dawo, Dr ya ce ya warke! Suna waje shi da ya Arshaad yanzu zai shigo da shi.”

bai gama rufe bakinsa ba kuwa Arshaad ya shigo shi da wani mutumi kyakkyawan gaske, dogo d’an kakkaura amman bashi da k’iba kwata kwata, fari tas da shi, kyakkyawar fuskarshi cike da tsananin kyau haiba da kwarjini. Abba ya rik’e hannun Arshaad d’in na dama shi kuma Arshaad d’in ya ruk’o kafaɗarshi da dayan hannun for support suna tafiya a hankali, kana ganin mutumin ka san bashi da lafiya.

A hankali suka k’arasa Arshaad ya kai sa har kan d’aya daga cikin kujerun parlourn ya zaunar da shi tukunna ya juyo ya kalli su Ummi ya gaida su.

Sai da suka gama gaisawa sannan Ummi ta k’araso kusa da su ta ce “Abba ya jiki? Yaushe aka sallameka? Mai yasa ba ka kira ni ba?”

D’an gyaran murya Arshaad yayi, sai da ta d’ago ta kalle sa sannan a hankali ya ce, “Ummi Dr yace kar a dame shi fa, and yana buk’atar hutu,sosai!.”

Juyawa ta yi ta kalla gefe ta d’ayan staircase d’in yadda ake ta sak’k’owa da kaya ana shige da fice kafin tayi murmushi ta ce “To Arshaad yanzu daka ka wo shi ka ga alamun rashin hayaniya anan d’in? Kalla fa parking aka hau yi yau d’innan gadan gadan, nima ina dawowa daga asibitin na tarar da su suna jirana a gate da na
tambaya suka ce wai Abban ne ya ce su zo su fara kwashe kaya suna kaiwa sabon gida, yanzu saboda Allah idan bai ji da lafiyarsa dan kanshi ko ni ba, ai ya duba Yaran nan”. Ta yi maganar tana nuna su Sudais tare da share kwallar da ta zubo mata.

A hankali Abban ya yi d’an tari sannan ya gyara zamanshi tukunna ya ce, “Arshaad.”

“Na’am Abba.” Arshaad d’in ya fad’a cikin girmamawa ya d’an rankwafo ta saitin shi.

Sai da ya kuma yin tari sannan ya ce “ka duba moving van d’in dake a waje akwai boxes da Ghana most go a ciki ka d’auko empty ones d’in da yawa, ka shiga parlourna da d’akina duk wani abu ka had’a su ka tattare, sannan ka rubuta sunan items d’in da suke ciki a jikin kowanne box da makar saboda kar ya bada wahalar tantancewa idan anje chan. Ka yi sauri idan ka gama za su shiga yanzu su kwashe furnitures, naga har sun kusan gama can side d’in.”

Ya k’arashe maganar yana d’an tari.

“To Abba”

Shine abinda Arshaad ya ce, daga haka ya nufi waje domin d’auko boxes d’in.

Juyawa Abba ya yi ya kalla su Sudais sannan ya ce “kuma ku je ku d’auko ku had’a naku kayan.”

Har ya gyara zaman ya d’an jingina ya lumshe idanunsa, sai kuma ya d’ago ya kalli Ummi sannan a hankali yace mata, “za ki bi mu ko a nan za mu barki!”

Yunk’urawa ta yi za ta yi magana ranta na sake b’aci, da sauri Mom wadda ke a bayanta ta rik’o hannunta ta d’an matse alamar ta yi shiru.

Shurun kuwa ta yi sannan Mom ta yi gaba ta ce, “Abba sannu da jiki, Allah ya sa kaffara ne. Bara muje saman in taya ta had’a kayanta. Idan kana buk’atar wani abu muna sama sai ka kiramu a waya.”

D’aga kan shi ya yi alamar ‘to’ sannan ya mayar da idanunsa ya lumshe ya koma ya jingina a jikin kujerar.

               

<< So Da Buri 3So Da Buri 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×