Skip to content
Part 44 of 72 in the Series So Da Buri by Bulama

Tun Asuba Hudan ta sauk’o daga fushin ta fara kula Sakina, dan ita ta tasheta ma sallar Asuba.

Sakina kuwa har suka yi wanka suka shirya, aka je aka yi breakfast aka dawo bata kula Hudan. Ko tayi mata magana ma sai dai tayi mata banza:

Hankalin Hudan bai tashi ba, sai da taga Sakina ta saka kayanta wadanda tazo dasu chap ta shirya, tace mata “sai sunyi waya”. Da sauri ta shiga gabanta ta tsaya dan har ta kusa k’ofa,
kafin tace “Ban gane ‘sai munyi waya’ ba! Me hakan yake nufi?” Ba tare data kalleta ba tace “Tafiya zan yi”. Cikin rashin jin dad’i Hudan tace “Akan Ya Arshaad kika yi fushi dani haka har kika yanke hukuncin tafiya ki bar ni??
Kin san kuwa me yayi min?”

D’ago dara daran idanuwanta Sakina tayi, kafin ta ce “Nabsani Hudan, sanin abunda ya had’akun ne ma har yasa kike fushi dashi hakan ne zai sanya in tafi. Jiya baki b’ata min rai sosai ba
amman da na san dalilin fad’an naku wallahi ba ki ji yadda raina ya b’aci ba.” Cikin takaici da son fahimtar da ita Huda ta ce “Sakina Jalila fa yaje.”

Cikin katseta Sakinar ta ce “na fad’a miki fa, na sani. Jiya mun yi chatting da shi sosai ya fad’amin komai! Haba Huda, kamar baki san wacece Jalila ba? Dan ta fad’a miki magana sai ki hau ki zauna?? Kishi ne ya rufe miki ido ko rashin wayo? A tsakaninki keda Ya Arshaad bai kamata a samu haka ba. Jiya cemin yayi kawai ba kya son shi, maybe akwai wanda kike so yanzu saboda he can recall yadda kika yi calling off engagement d’inku saboda Ya Junaidu kawai don ba kya son ki b’ata mishi rai! Amman shi yanzu lokaci d’aya kin murzawa idonki tuka kina ta zuba mishi rashin kirki! Ba abunda yafi b’ata mishi rai irin yadda ana fad’a miki kika hau kika zauna, kamar daman tun farko kina zarginshi. Anyways ya ce yana neman alfarma a wajenki, anjima zai san yadda zai yi ya kawo Jalila nan, akawo AlQurani suyi alwala shi da ita kowa ya rantse akan gaskiya yake fad’a!
But ya ce b4 then dan Allah ki d’au waya ki kira Aaima ki tambayeta waye Auwal ya halin shi yake!”

Tunda Sakina ta fara magana jikinta yayi sanyi sai yanzu take ganin rashin kyautawarta.

Ganin Sakina, tana shirin zagayeta ta fita ne yasa ta kuma tararta ta tare hanyar kafin tace “To ki yi hak’uri ki fasa tafiya, haba Sakina, ko ke ce kika ji haka fa dole kiji haushi”

Da sauri Sakina tace “Hudan zan tafi! Dan ba zan iya tsayawa inga wai Ya Arshaad yana dafa Qur’ani yana rantse miki akan ba shi ne ya yiwa Jalila ciki ba! So that ki yarda kuyi getting back together. Haba Huda! Ya Arshaad ne fa, wallahi sam bai chanchanci haka daga gareki ba! But ba zan hanaki ba, ki barshi yayi dan na san tunda kin riga kin saka haka a ranki to in ba rantsuwar yayi miki ba ba zaki tab’a yarda ba! Amman wallahi kinji dai na rantse miki ba ruwan Ya Arshaad a lamarin nan!
Shi wannan Auwal d’in shine yayi aika aikar shi kuma za ki ce na gaya miki, Ya Arshaad ya fad’a min baki tab’a ganinshi ba sai ranar amma yana fad’a miki magana kika hau kika zauna shi kuma da kika sanshi for almost 4 years kika k’i yarda dashi.

Hudan Ya Junaidu, kwatar ki yake yi a hannun su Jalila idan suna kimar ki amman kin ce ba za ki tab’a manta alkairinshi gareka ba Ya arshaad fa?
Za ki iya gaya min irin tarin alkairan da yayi miki? Ba ke ba har ni kaina da nake kusa dake sai da alkairinshi ya shafe ni.”

Ahankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Sakina ranar nan fa a gaban ki Mama tace min taji Yaro yazo yace wai Jalila taje inji Arshaad.”

Murmushin takaici Sakina tayi kafin tace “kuma a same day da time ne ke da Ya Arshaad d’in kuka yi dogon video call ba! Ba ma voice call ba video call and a d’aki muka ganshi throughout bai fita ba har kuka gama, ba a mota ba!. Kinsan wani abu Huda?
Bata jira jin amsarta ba tace “wallahi duk makirci ne, so suke yi kawai su shiga tsakaninku! That Auwal shi yayi planning komai, ban san mecece agenda d’inshi ba, but na san shine master mind! Ban ganshi ba amman na tsane shi!.

Ni dai shawarata a gare ki itace ki bud’e idonki da kyau, ki fahimci gaskiya tun kafin dare yayi miki!
Arshaad ya sanki ya soki tun kina Hudan ki! Idan kika ce za ki juya mishi baya yanzu gaskiya baki kyauta ba!.
Ban hanya in wuce, dan ba zan iya ganin wannan abun takaicin ba.”

Rugumeta Huda tayi kafin tace “Shikenan ya wuce na hak’ura! Dan Allah karki tafi.”

“No, Hudan seriously ki bari yayi miki clearing confusion d’inki, saboda kar ki dinga ganinshi da abun dan na sanki da taurin kai! Kar ki je an kashe case but still kina zarginshi so just ki barshi su zo d’in.”

A hankali ta ce “komai ya wuce, ki cire hijabin please haba mana”!Ta k’arashe maganar kamar zata yi kuka.

Sai yanzu Sakina tayi murmushi kafin tace “Shikenan na faasa tafiya amman ki barsu kawai suzo d’in ayi a gama”

D’aga mata kai Hudan tayi. A hankali Sakina ta koma ta zauna akan gado, bayan ta cire hijabin.

Da kad’an kad’an Hudan ta dinga janta da hira har ta samu ta sake ta daina fushin. Nan take bata labarin Ya Junaidu, amman the good news is that
DNA d’in su Baba bai yi matching da gawarwakin ba both wanda aka yi a Lagos da wanda suka taho da sample d’in nan Kano aka yi.

Hawaye Hudan ta share kafin tace Yanzu Ya Junaidu ya b’ata kenan?”
A hankali Sakina tace “mu yita addua kawai Allah ya baiyyana shi” “Ameen” ta ce.

Ba abunyi dan haka daga kallo sai chatting da hira.. Yau su biyu tol suka yi lunch, su Shuraim suna school Abba kuma ya d’an fita wasu ayyuka, Arshaad bai lek’o ba Aslam ma haka.

Sai bayan Magrib Arshaad ya kira Sakina yace mata “suna k’asa shi da Jalila, su sauk’o!” Jalila tunda take bata tab’a jin farin ciki irin wannan ba! D’azun tana d’aki Gwaggo Asabe tazo ta ce mata “taje, inji Arshaad, yana kiran ta.” Kasa b’oye farin cikin ta tayi a gaban Gwaggwo Asaben har da su fesa turare da shafa jambaki, daman already idanunta da kwalli fuskarta kuma da powder! Ita dai Gwaggo Asabe tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, Allah yasa dai ba wannan Yarinyar Arshaad zai kwaso musu ba, ita tunda tazo gidan gaisuwa bata tab’a had’asu ba, gashi bata son aiki, hatta d’akin da take ciki sai dai tazo ta kira aje a gyara mata.

Doguwar riga y’ar kanti mai kyau ce a jikinta, dan haka ta d’auko d’an k’aramin mayafi tayi d’auri sannan ta d’auko wani ta yafa shima d’an mitsitsi daga nan ta d’au wayarta tazo ta wuce ta fita ta bar Gwaggo Asabe da baki a sake. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e, kafin ta lek’a da d’an k’arfi tace mata “yana chaan waje a bakin mota”
Don har tayi nisa.

“Ok”
Kawai Jalila tace
tayi gaba abunta.

A bakin motarshi ta ganshi a tsaye. Bai yi wani kwalliya ba
hasalima Jallabiya ce a jikinshi bak’a amman sai da numfashin Jalila ya kusan d’aukewa dan yayi mugun tafiya da imaninta!
A k’asan ranta tace
“Ma shaa Allah”
Tanajin tsananin tsantsar k’aunarsa tana sake ratsa dukkannin ilahirin jikinta,
itafa ko da ace Arshaad zai dinga yi mata dukan tsiya kullum! Muddin zai yarda ya aure ta su zama k’ark’ashin inuwa d’aya, ta na amsa sunan matarshi to
wallahi zata iya zama da shi!.

Tsabar kallon da take yi mishi har tuntub’e tayi ta kusan fad’uwa wanda hakan ne ya janyo hankalinshi gareta dan shi bai ma san ta fito ba!.

Suna had’a ido ya tamke fuskar shi kamar bai tab’a dariya ba.

A take taji gabanta ya fad’i amma sai ta dake ta k’arasa inda yake
still tanata satan kallonshi….

Sai da ta d’an risssina tukunna tace mishi “Ina wuni” cikin wani kalan yauk’i da kissa.

Sake had’e rai yayi, ya bud’e mata murfin motar tukun yace “lafiya, shiga mu je!”

A take tsoro ya rufeta, D’an bata san mai ya shirya mata ba
Tana shiga, ya rufe ya zagayo ya zauna mazaunin drivern.
Sai da taji tashin motar tukun ta bud’e idanunta dan tun lokacin da ya rufe mata motar ta wani lumshe ido tana murmushi saboda ba k’aramin dad’i taji ba.
D’an juyowa tayi ta kalleshi
fuskar shi yanda kasan wanda bai tab’a dariya ba!
A hankali ta zaro wayarta ta turawa Auwal message
saboda
gaskiya in dai daga ita sai Arshaad ne a waje tou za a iya samun matsala dan tabbas tsaf! Zata Fallasa komai kuma ta san Auwal uban ta zai ci idan tayi hakan.

Suna parking a cikin gidan dai dai message d’in Auwal ya shigo wayarta…
Sai da su Hudan suka sauk’o tukun ta fahimci inda suka zo dan haka tayi mishi reply ta ajjiye wayar.

Tunda ta sauk’o take maka mata harara!!
A kujerun tsakiyar parlourn suke dan haka suma suka nufi wajen suka zauna.
A hankali suka gaidashi ya amsa
Sannan Huda ta kalli Jalilan tace “Ya Jalila ina wuni”
Wani uban tsaki Sakina taja ta d’auke kai.

“Hmm”
Kawai Jalilan tace, wallahi ba don Arshaad yana wajen ba da sai ta tashi ta bugewa Sakina baki, dama a k’ule take dan ita kad’ai ta san tashin hankalin data shiga tun saukowarsu…..
Ajiyar zuciya ta sauk’e
kafin ta kalli Hudan tace “lafiya”
Kawai! Amman a k’asan zuciyarta ji take yi kamar ta mutu dan tsananin bak’in ciki! Wani irin tuk’uk’i ne yake taso mata saboda abunda idanunta suka yanzu nan ne gidan Mahaifin Huda??
Ba abunda yafi d’aga mata hankali daman tuntuni irin labarin da taji Gwaggo Asabe tanayi da wata mai aiki dattijuwa akan ‘Mahaifin nata ya bar gidan saboda Babansa yace ya zab’a ko shi ko ita!!’
Ita a tunaninta bashi da wani kud’i sosai dan tama d’auka gidan haya suka je suka kama suna zaune
Ashe shima mugun mai kud’i ne.
Ta tabbata Hudan y’ar masu kud’i ce kenan yanzu? Kuma Babanta yana matuk’ar sonta!

Muryan Arshaad ce ta katse mata tunani jin yana cewa
“Jalila ga Al Qurani, izu sittin.” yayi maganar yana nuna mata kan center table kafin yaci gaba
“Idan baki da alwalla kije kiyi kizo yanzu!
Zan rantse akan ‘cikin jikinki ba nawa bane ba! Sharri kika yi mini’ kema kuma zaki rantse akan ‘gaskiya kike fad’a (cikin nawa ne).
Tsakanin ni da ke duk wanda yayi karya Al Qur’ani ya ci shi!.”

Wata zazzafar zufa ce ta keto mata, tana shirin yin magana taji ance
“Sannu Ya Sheik! Akaramakallahu.”
Suka ji muryarshi yana takowa cikin parlour…
Cikin gadara Auwal ya k’araso wajen, kafin one by one ya kalle su! Da kyar ya iya janye idanuwanshi daga kan Sakina! Sannan ya d’anyi murmushi yace “Ai ya kamata ni ma a gaiyyaceni meeting d’in ko?”
Ya fad’i hakan yana mai neman kujera ya zauna kafin yace
“Ya sheikh!! You were saying??”

Banza Arshaad yayi da shi ya tashi ya matsa yana k’ok’arin d’aukar Qur’ani n Hudan tasa hannu ta d’auka
a hankali tayi k’asa da kanta ta fara magana
“Ya Arshaad dan Allah kayi hak’uri akan abunda nayi maka, na yarda da kai please ba sai ka rantse ba!”
Wani farin ciki ne ya lullub’e Arshaad da Sakina a take.
A hankali shima, yace
“Thanks for trusting me Hudan, but i’ve to do this, please don’t stop me, okay?”
Cikin katseshi tace
“Nima please kar kayi haka, wallahi i trust you, in kuma kak’i yarda har kayi, to
it means stilll baka hak’ura ba kenan da abunda nayi maka.”
This time around murmushi yayi, kafin yace
“Tou kawo, bani”
Yayi maganan yana mik’a mata hannunshi
Tana shirin yin magana, suka ji Auwal ya kwashe da dariya, cikin dariyar yace ,
“Yayi Romeo and Juliet!!
Hey, look here”
Yayi maganan referring to Hudan, kafin yace
“Ki yarda da shi ko kar ki yarda da shi wannan matsalarku ce!!
Ba wai dama na fad’a miki dan wani abun bane, that very day
kin shigone a time d’in da case d’in yake goin that’s why har kika san maganar!
Anyways
Jalila it’s up to you, sai ki san abun yi…
Tunda gashi yanzu ya nace akan ba nashi bane!
I think su Granpa ne kawai zasu iya kwatar miki hakkinki dan ni kam daga yau na cire hannuna a case d’innan naku, in shaa Allah.”
Ya k’arashe maganar yana mai bud’e hannayenshi biyu ya kai bayan k’eyarsa ya sak’ale sannan yayi resting gaba d’ayansa akan kujerar ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya.

Wani tuk’uk’i ne ya turnuk’e Sakina, bata san lokacin da ta fara magana ba!
Kamar yadda ya yiwa Huda itama hakan tayi mishi
Hey! You look here, Auwal kake ko wa?
Waye ne ya gayyatoka nan?
Wa ya kira ka?
Waye ya kasa da kai?
Wa yace maka ana son jin opinion d’in ka a cikin maganar nan?
Hakanan kawai ka kama ka shigo tsulum! Ka tarar da mutane ko sallama baka yi ba
ka hau magana kamar wani kwarkwar!.
And let me tell you something abunda kayi yanzun, ya tabbatar da you got something to do with her and the baby!
Kuma da kake wani cewa ‘zaka kai magana sama’ Ai da kai! Da mu! Da ita munafukar taka duk munsan gaskiya dan
haka ina mai shawartarka da ka tabbatar ka d’auko fad’an da ka san zaka iya k’arasawa, in ta kwab’e!!
Ke kuma!”
Ta juyo kan Jalila,
sannan tace “ki karb’a ki rantse a gaban kowa, sannan ki yi Allah ya isa a duk wanda ya cutar dake haka, a tsakanin Ya Arshaad da wannan Auwal d’in.

Hudan Dan Allah ki bawa ya Arshaad, yau zan ga k’aryar iskanci.”

Tunda Sakina ta fara magana Auwal yake kallonta ya kasa d’auke ido, k’arshe ma murmushi ya fara yana jin inama kar ta daina.

Muryar Jalila ce ta katseshi jin tana cewa “Tou uwata! Ke har kin isa ki gaya min abunda zan yi?”

Da sauri Arshaad ya juyo yace “in baki da alwala kije kiyi kizo yanzu” Yayi maganar babu
alamun wasa a tattare da shi.

Gaba d’aya jikin Jalila ya jik’e da gumi, tun lokacin da aka fara maganar, tsabar tsoro!

“Ko bakya ji ne?”
Arshaad ya fad’a cikin b’acin rai dan takaicin Yarinyar yake ji ba kad’an ba, ji yake yi kamar yaje yayi ball da ita.

Auwal ta d’ago ta kalla, taga yayi mata wani kallon data fassarashi da warning!! Ganin kowa ita yake kallo yasa ta cire mayafinta ta ajjiye ta wuce tana cewa
“ina ne toilet?”
Wata k’ofa kurkusa Arshaad ya nuna mata yace “ta shiga”.

Tana shiga ta turo k’ofar ta jingina tana haki, kamar wadda tayi y’ar tsere!
Tunda take bata tab’a shiga tashin hankali irin na yau ba…ko hauka take yi ba zata tab’a dafa Qur’ani akan k’arya ba, akan gaskiyar ka ma ba a cika son kana dafawa ba, balle k’arya!
Da albarkar ka ma ya ka k’are
ballantana babu!
Kuma ita a halin yanzu
tana buk’atar albarkarta fiye da ko yaushe, da kusanci da Ubangijin ta! Tana so ta rok’esa arzik’i da soyayyar Arshaad
dan muddin taci gaba da ganin Huda a cikin wannan daular alhalin ita bata da shi, to wallahi ta san zuciyarta sai tayi ajalinta….

Ta dad’e a cikin band’akin sosai, har sai da Sakina taje tayi mata knocking tukunna ta bud’e, tana bud’ewa ta zabga mata harara kafin tace
“Banza y’ar karere kawai, sarkin zak’ewa!”

Dariya Sakina tayi kafin tace
“Ai gara ni y’ar karere ce
Kuma kirana aka yi takanas! Nazo ba abun kunya ne ya zaunar dani a gidan ba.”

Jalila bata ita take ba, dan haka tayi shiru kawai ta fito suka k’arasa parlourn
tana tunanin next stage!
Gabanta in banda fad’uwa ba abunda yake yi..
Ana tsayawa Sakina ta amshi Al Qur’ani n ta ajjiye akan centre inda yake tun farko, kafin ta kamo hannun Jalila ta kaita wajen tace “Bismillah!”
Fusge hannunta Jalila tayi
tana hararar ta
Kallonta Sakina take sosai da mamaki akan fuskarta kafin tace
“Da alama dai taimama kika yi ko?
Dan banji alamun danshin ruwa a hannunki ba, ga d’aurin vail d’inki shima rad’au!! Powder ki kuwa kamar ma k’arawa kikayi.”

….Gaskiya In Sakina bata daina shiga huruminta ba wallahi zata illatata a wajen nan!! Wanne irin iskancine wannan??…
Jalilan ta aiyyana hakan a ranta.

Muryar Hudan taji tana cewa
“Ya Jalila idan kin san baki yi alwala ba karki tab’a Qur’anin nan fa, Dan Allah.”

Takaici kamar ta shak’eta haka Jalila taji, a ranta tace
“Y’ar ‘Yaa Jalilan’ uwa!”.

Muryar Arshaad taji yace “Ba kiyi alwalar ba?”

Cikin rawar murya tace
“Eeh bbb ban dd’akin babu ruwa”

Da sauri Hudan tace
“Zo muje d’akina, kiyi a chan”

Sakina ta yunk’uro za tayi magana taji Arshaad yace
“Muje in kunna miki famfon, yana da wuyar sha’ani dama.”
Ya fad’i haka yana wucewa gaba.
Jikinta har karkarwa yake yi haka ta wuce, ta bishi….
Suna shiga ya kunna mata shower ya kunna famfon sink, da wani famfo a gefe ya nuna mata yanda zata matsa abun tsarkin jikin toilet sannan ya fito ya bata waje ya bar ruwan yanata zuba bai kashe ko d’aya ba.

Alwalar tayi ba yadda ta iya, ta kashe famfunan, ta tsaya tana kallon fuskarta a mudubi.

Jin yayi knocking yasa gabanta mugun fad’uwa!
Ita kam yau ta ga talatar kanta, gashi ba daman tace tana fashin sallah!
Da kyar ta iya daurewa ta fice, k’irjinta na dukan uku uku.

Suna k’arasowa, Sakina ta mik’a mata vail d’in da ta cire a jikinta d’azu ta ajjiye
tace “Bismillah”
Fisgewa tayi tana hararar ta.
Murmushi Sakina tayi kafin tace
“Yarinya yau ko idanunki zasu fad’o k’asa sai kin rantse!”

A nan fa ake yinta, ga Jalila ga Al Qur’ani a gabanta ga jama’a kowa ya zuba mata ido… Parlourn yayi shiruuuu.

Ba abunda yafi bawa Arshaad mamaki irin yanda Auwal ya d’auke wuta diff!!! Don gaba d’aya kamar babu shi a wajen..

Shi kam Auwal yana chaan ya sha’afa da kallon Sakina kamar ya samu tv, sam! Bai damu da kalar harar da take zabga masa a duk sanda suka hada ido ba! Babu abunda yafi tafiya da imaninshi kamar idanuwanta waenda idan ta kalleshi dasu yake ji gaba d’aya kamar an zare mishi lakka bayan fad’uwar gaban da yake tsintar kanshi a ciki..duk wata hayaniyar shi yau ya ji babu ita, yanaso yasa baki a lamarin su Jalilan amman ya kasa, don bashi da wani sauran energy, gaba d’aya jikin shi yayi lakwass!!!.

Sakina kuwa so take ta gama da Jalila ta koma kanshi idan bai daina yi mata wannan kallon k’urillar ba!.
Hudan tana lura dasu, dan haka ta gama aiyyanawa a ranta suna komawa d’aki zata zaiyyanewa Sakinan waye shi!!
Kar ma ta soma bashi fuska dan ita tun zuwan su Munjibir park ta gama aminta da Auwal ba mutumin kirki bane ba!.

…duk sunyi shiruuu, kowa da abunda yake tunani a ranshi.

Nishi suka fara ji sama sama,
da sauri duk suka juya kanta..
Wani lumlumshe ido take yi tana layi, kafin ta tafi luuuu ta fad’i akan kafet d’in!
Da mugun sauri Sakina ta d’auki robar ruwan dake gefenta ta nufeta, ta na zxuwa ta bud’e murfin ta kelaya mata
ruwan mai mugun sanyi dan har da k’ank’ara k’ank’ara ma a ciki!!

Ai kuwa a firgice Jalila ta bud’e idonta tana wani mugun tari dan ruwan har cikin hancinta ya shige sosai….
Da kyar ta samu ta seseta kanta ta fara k’ok’arin mik’ewa,
tana mikewa kuwa ta d’aga hannunta zata zabgawa Sakina mari shi kuma Arshaad a take ya rik’e hannun da sauri.

Wani kalan shock taji a jikinta da wani sanyi a zuciyarta wanda ya sanyata kasa yin motsi!
A hankali ta lumshe idanunta tanajin yanda laushin hannun nashi yake ratsa jini tsoka da b’argonta.

Muryarsa ce ta dawo da ita duniyar su, jin cikin fad’a fad’a yana cewa
“Jalila kin fara isata wallahi ranki zai yi mugun b’aci!
Inada abun yi amman kin tsaya sai b’ata mana lokaci kike yi!!
Sannan meye na yunk’urin marin nata da kika yi?
Ina taimakarki tayi?
Kar ki kaini bango, ranki zai b’aci wallahi kinji dai na rantse!!.”
Ya fad’i hakan cikin tsananin b’acin rai sannan yayi wurgi da hannun nata, ya wuce ya k’arasa ya durk’usa a wajen, ya fara kokarin dafawa….

Kuka kawai yaji Huda ta saka dan haka da sauri ya sago ya kalle ta.
Cikin kukan tace
“Ya Arshaad da Allah fa na had’a ka, nace maka komai ya wuce amman still kak’i ka yarda ka hak’ura, itama Ya Jalilan ku barta kawai, ni na fahimci gaskiya, dan Allah ku daina , Al Qur’ani fa ba abun wasa bane ba..”
Tana gama fad’an haka ta juya ta haye sama da gudu,,tana kuka.

Mik’ewa Arshaad yayi ya dafa kanshi, ya kusan one minute a haka kafin ya juya yana kallon Sakina yace
“Kice mata nace idan cikin ya kai 5 ko 7 months in shaa Allah za aje ayi dna test, plss kar tace a’a,,for me.”
Yana gama fad’in haka bai jira amsar Sakina ba ya juya ya fice.

Haushin su ne ya hana Sakina ci gaba da zama a inuwa d’aya dasu, dan haka ta juya ta haye sama itama.

Da k’arfi Jalila ta sauk’e ajjiyar zuciya, bata gama dawowa dede ba taji Auwal ya fincikota da mugun k’arfi, cikin b’acin rai yace
“Wanne shirme da iskancine ya sa kika biyo shi in the first place??? Mahaukaciya mara kamun kai kawai!! Daga ji ance tazo a tafi ta shige mota ta biyo mutum zungui zungui. Wallahi yau da wani abun ya fito, toda da hannun nan nawa zan illataki, mahaukaciya kawai.”
Ya k’arashe maganar yana sakin ta sannan ya juya yayi hanyar waje.
Da sauri ta mik’e ta bishi…..

Ba k’aramin artabu suka sha ba a wajen ma, daga k’arshe dai ya hak’ura ya mik’ata gida, yanata faman zazzaga mata ruwan bala’i!
Daga nan yace “yayi grounding d’inta! Ko wajen umma kar ta yi gangancin tambayarshi
Daga yau babu inda zata sake fita har sai yayi sorting out ma kanshi solution!”
sannan yace “ko hanya tabi in dai ta hango Arshaad to ta chanja!
Don ya lura sam Arshaad d’in bai hak’ura ba, ita kuma wawuya ce, so kasancewar su tare is very dangerous for him.”
Ita dai Jalila da “to” kawai ta bishi amman a yanda take jin Arshaad a ranta ai ko labari taji ance zai bi ta waje to fa ita mai iya zuwa ta tsayane ta jira wucewarshi.

A gate d’in estate d’in ya tsaya yace “ta fita!”
Allah ya so ta mai gadin yaga motarshi kuma ya ganeta dan haka aka barta ta shige.

Ko da Aslam yazo, Hudan Sakina ta bawa ta kai masa ruwan karatun…
Dinner kam dama a k’oshe suke, gaba d’aya kunyar Arshaad take ji bataso su had’u, iyakar yadda Ya Jalila tayi ta acting ya ishi yasa ta gane gaskiya….ita sai yanzu ma take ganin shiriritarta da ta yarda da su!
A gefe guda kuma na zuciyar ta tausayin Jalilan take ji.
Yayinda gaba d’aya hankalinta kuma yau ya d’unguma ga son ganin Mama
dan har yau Ummu tak’i d’aukar wayarta, wayar Sakina ma ta daina amsawa!
Tanaso ta tambaya amman kuma bata son zuwa k’asan dan haka ta yiwa Abban message.

Ba a fi mintuna uku ba, taga reply dinshi kamar haka
“Ok, no problem, but let it be tomorrow.”

Taso zuwa yau d’in, amman ta tura
“Thanks Abba ”
Kawai, ta mik’e tayi sallah..
Yau basu wani zauna hira sosai ba,,ta dai fad’awa Sakina halin Auwal tace “Don taga yanata kallonta kar yazo mata da shirme”
Dariyan takaici Sakinan tayi kafin tace ,
“First, kin dai san akwai wanda naki dating, right?
Second, ga abunda ya yiwa Jalila sannan ya k’ulla makirci wai Ya Arshaad ne.
And third, wallahi ni bana son irin waennann mazan kwata kwata yana yinsa bai yi min ba at first sight!”.

Ajiyar zuciya Hudan tayi kafin tace “Duk cikin su Ya Arshaad shi ya fita daban i don’t know why.”
Murmushi Sakina tayi kafin tace “d’an halak, gashi yana kiranki.”
Tayi maganan tana mik’a mata wayar ta dake a hannunta.
Karb’a tayi ta amsa
bayan sun gaisa ta fara son sake bashi hak’uri amman sam yak’i yarda, a cewarshi bata laifi a gurinshi……..
Tun Sakina najin hiran su sama sama har bacci ya kwasheta bata san lokacin da suka gamaba.
Ranar ansha soyayya abun ba a magana dan sai wajen 2 tukunna suka yi hanging up, suka kwanta.

Bata samu magana da Sakina ba, kamar yadda ta yanke zata nemi shawarar ta jiya,
sai da suka sauk’o yin breakfast…
Suna zuwa suka tarar ba kowa dan haka suna zama Huda tace
“Daman akwai maganan da nake ta so muyi in mun gama shiryawa”

“Ok, akan me?”
Sakina ta fad’a tana mai d’an juyowa ta bata dukkannin attention d’inta.”

A hankali Hudan tace
“Ya arshaad ne, daman already ya yiwa su Abba maganan!
So yanzu jiya yace, wai ya nake gani,,jiya sun yi magana da Dad wai sun tsaida in anzo saka rannan za asa two months ne ba wani lokaci za a dauka mai tsawo ba!”

“Woow”
Sakina tace tana d’an zaro idanuwanta, kafin tace
“Amma hakan bai yi wuri ba kuwa?”

Da sauri Huda tace “nima dai abunda na gani kenan!
Amman dana nuna mishi tun kafin ma In furta sai naga kamar bai ji dad’i ba.
Wai shima yana so ya tafi wani course, so kafin a juya sabon session yake son samamun admission sai muje chan ni Ina degree shi kuma yana course din, nashi.”

Dai dai nan suka ji sauk’owar Abba, dan haka
a hankali Sakina wadda duk jikinta yayi sanyi jin za a rabata da best frnd d’inta
tace
“Anjima ma ji me su Mama za suce, in munje.”

Cikin girmamawa suka gaisheshi ya amsa da kulawa yana ce musu “ai da sun fara kawai”

Sai da suka kammala ya kalli Hudan yace “ki cewa Arshaad idan ya dawo a office ya zo, ku zo tare Ina son ganin ku!”

Da “to” ta amsa, shi
kuma ya tambaya ko “akwai abinda suke buk’ata zai fita shima” a hankali tace “a’a” sukai yi mishi a dawo lafiya, ya wuce.

Gidan shiru, daga su sai masu aiki…
Tun lokacin da Abba ya fita take nazari a kanshi, kamar akwai abunda yake damunshi, dan har sai da ta yiwa Sakina maganar…
Murmushi Sakina tayi kafin tace “Hudan he just knew you fa, kuma yanzu ana shirin aurar da ke, dole yaji ba dad’i mana.”

Jikinta itama duk sai yayi sanyi, ba abunda yafi d’aga mata hankali, irin barin k’asar da Ya Arshaad yace za suyi, ta san aure dolene dama wata rana za tayi shi, but bata tab’a kawowa nan kusa ba, kuma ba a k’asar ta ba.
Haka dai ta wuni ranar sukuku kana ganinta tashi d’aya zaka fahimci akwai abinda yake damunta!
Ko da Sudais ya shigo musu shi da Sakina suka yi ta shirmen su tana jin su k’arshema kwanciya tayi ta lumshe idanunta kamar mai bacci
Sakina kanta k’arfin hali kawai take yi tana daurewa, dan bataso itama ta zama moody kamar Hudan ta sake d’aga mata hankali.

Kafin Magriba Arshaad d’in yace mata zai dawo, so tana gani 6 yayi ta mik’e ta isa parlourn Abba.
Knocking tayi aka bata izinin shiga, a hankali da sallama ta tura k’ofar ta shige ciki.

Aiki ta sameshi yanayi tuk’uru
ga takardu da computer a gabanshi takardun duk a zuzzube.
Suna had’a ido yayi murmushi ya ture kayan aikin gefe ya bata dukkannin attention d’inshi bayan ya nuna mata gefen shi inda yake zaune a 2 sitter yace “ta zauna.”

Bayan sun gaisa ba tare da b’ata lokaci ba yace mata “Dad d’in Arshaad jiya ya kirashi akan maganarsu …..
Yayi mata bayani dai dalla dalla kamar yadda Arshaad yayi mata jiya”
Kafin ya k’ara da cewa
“Kina son shi!
In ba kya sonshi ki fad’amin, ba zan bari ki auri wanda ba kya so ba!”
Just say watever it is that you feel towards him ko friendship ko love ko ma meye just feel free to tell me”
Ya k’arashe maganan yana kallonta da dukkan hankalinshi.

Shiruuu, tayi tana d’an jin kunyar cewa Abban tana son shi k’iri k’iri, dan haka tace
“Abba mun ma shirya mun daina fad’an, duk abunda kuka yanke dai dai ne.”

Ya fahimceta sarai amman yace “Kina sonshi kenan? Za ki aureshi?”
A hankali ta d’aga kanta, sannan tayi saurin rufe idonta da tafun hannunta.

Murmushi yayi,
bai ce komai ba, daga nan
d’akin ya d’au shiru.
A hankali Hudan ta aro jarumta kafin tace
“Daman Abba akwai wata magana danake ta so in rok’e ka”
Kallonta yayi kafin yace
“Un hm, Ina jinki”
A hankali tace “akan su Ummi ne
Abba dan Allah ka..”
Tun kafin ta k’arasa yace
“Maganan ya fita a hannuna tun tuni, so karki sake min maganan bana son ji.”
Ganin da tayi kamar ranshi ya b’aci ne yasa tace
“Sorry Abba”
A hankali ya sauk’e ajjiyar a zuciya kana yace
“It’s okay”
Dai dai nan suka ji ana knocking!
Izinin shigowa ya bada, hakan ya sa ya turo k’ofar a hankali ya shigo…
K’amshin turarenshi ne yasa ta ganeshi!
Me kuma ya zo yi?
Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta.

Bata gama wannan tunanin ba, ta ji muryar Arshaad yana sallama alamun tare suka shigo.

Rashin nutsuwar da takan tsinci kanta a ciki ne ya ziyarceta a take, lokaci guda!.

Akan kujerun suka nemi wajaje suka zazzauna.
Sai da suka gama gaisawa da Abban tukun ta juya ta gaidasu
A hankali Aslam yace
“Lafiya Alhamdulillah”
Arshaad kuma yana d’an murmushi ya d’aga mata gira d’aya yace “fine” a hankali.

Murmushi tayi itama ta maida kanta k’asa.

A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi kafin ya bud’e yace “Abba, Arshaad yace wai akwai meeting inzo kana son ganinmu”
Murmushi Abba wanda ya fahimci Arshaad d’in
yayi kafin yace
“Ni shi kad’ai na kira, sai dai kuma na lura har kunyar surukai ta fara shiga tsakaninmu tunda gashi sai da ya nemo d’an rakiya.”
Murmushi Arshaad d’in yayi ya sunkuyar da kanshi k’asa yana danna wayarshi dan gaskiya Abban ya fad’a sam bai san daliliba amman wata kunyarshi yake ji kwana biyun nan.

D’an murmushi kad’an Aslam d’in yayi yana mai sauk’e ajiyar zuciya.

A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya shima kafin yace
“Mun gama magana da Huda saura kai”
Har zai fara magana sai kuma ya juyo yace
“Daughter akwai wani abun da kike son sanar dani ko shikenan?”

A hankali tace “ba komai Abba duk na fad’a
kawai dai maganar zuwa wajen Mama ne, k’arfe nawa?”
Murmushi yayi yace “bayan isha zan kaiki ku shirya ko?”
Da “to” ta amsa tana murmushi kafin ya sallameta tayi musu sallama, ta wuce.

D’an gyaran murya Abba yayi kafin yace
“Arshaad!”
Jin yanda Abban ya kirasa yasa Arshaad d’in d’agowa yana kallonshi with full attention.

“No need na In tsaya tamabayar ka ko kana son Hudan tunda gashi duk ka fad’a mana ko? But inaso In sake tabbatarwa tunda kaga shi aure ba abun wasa bane, sannan kuma inaso ka tsayar da kanka da hankalinka waje guda kafin a gama magana, dan naji Dad yana cewa 2 months kawai za a saka bikin saboda tafiyarka!
So kaga kar aje abu ya taho kuma kuzo ku fara inda inda, bayan ba wannan lokacin.”

D’an tari kad’an Aslam yayi, kafin ya mik’e tsaye yace
“Abba Ina zuwa, i’m thirsty”
Bai jira jin me zasu ce ba ya fice daga parlourn ya sauk’a chaan k’asa.

Yana fita Abba ya ci gaba da cewa
“Sannan magana ta biyu!
Why do you hide Hudan away from me??
Meye shirinka?
Bana so ka b’oye min komai”

A hankali Arshaad ya lumshe shanyayyun Idanunshi, kafin ya bud’e su ya d’aura akan Abban sannan ya fara magana “Abba ba 2 months ba, ko nan da 2 days ne aka yanke ranar aurenmu, I’m ready in auri Hudan dan ita nake so, so na tsakani da Allah,
Ita nake son aura in rayu da ita har abada, na yanke wa kaina wannan decision d’in 3 years ago and I don’t think akwai rana d’aya dana tab’a jin tunanin sauya decision d’ina.

Magana ta biyu kuma


Tabbas na fahimci wacece Huda, tun ranar da muka had’u da Mama a graduation d’inta saboda naga pictures d’inta (Mama) da yawa a locker d’inka da sunan ta and everything a time d’in da kace in tayaka, parking.

But I’m really sorry Abba i was selfish back then, shiyasa na k’i fad’awa kowa har ita (Hudan) dan na san no mattarr how much I love her itama take sona muddin iyayenta (b’angaren uwa) suka fahimci waye ni to ba zasu tab’a yarda da auren mu ba duba da issues d’in da suke tsakanin families d’in
kuma kaima it can cause problems for you daga Granpa dan na lura maganar kad’ai idan akayi ran kowa sai ya b’aci a estate d’in.
Shiyasa na rok’i Baban Sakina akan ya b’oye identity d’ina har iya lokacin da za a d’aura mana aure, daga nan zan san yanda zan yi In shirya ku kaida su Madu, tunda kuma ga auratayya a tsakani, dole a na san za a hak’ura a sauk’o a yafewa juna…

Na san nan ne side d’in Mahaifinta mun fisu k’arfin da iko da ita amma da nayi lissafi tabbas naga akwai possibility d’in suci galaba a kanmu, ni kuma issue ko case ne kwata kwata bana so har in samu cikar buri na shiyasa nayi k’ok’ari wajen ganin na danne duk wani abu da ka iya zama mini matsala wajen ganin na mallaki Huda a matsayin matata.
I know I was wrong!
Ban san taya zan fara baka hak’uri ba, but I did everything out of love! Dan to be honest a yanda nake jin k’aunar Huda a raina Abba wallahi I don’t think I can go on living idan aka yi tunanin raba ni da ita!

Please try to understand and forgive me.”

Ya k’arashe maganar cikin tsananin kalar tausayi kamar wanda zai fashe da kuka.

Shiruuu, Abba yayi yana nazari
kafin yace


“Arshaad na san menene so, tbh a lokacin da nake tare da Maryam, ake k’ok’arin rabamu!

Hakan nima nayi na zama selfish har naga mun mallaki juna…

Amman abunda kai kayi is morethan selfish, Arshaad banji dad’i ba, ka k’i ka baiyanar mini da y’a ta.”

Shiruu, Abba ya d’anyi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yaci gaba da magana
“But, zan iya yafemaka!

Zan yi k’ok’ari In manta da abunda kayi after all everyone deserves a second chance sannan naji reason d’inka and its not all bad.

But Arshaad don’t ever try something like this again saboda i as selfish back then just like you and abun bai yi ending well ba!

Although I was happy for good 10 years, but har yau Maryam is not in good shape with her parents because of my decision.”

A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “And another thing thankyou so much!

Hudan ta fad’a min yadda ka dinga d’awainiya da su har makaranta, Allah ya saka maka da alkhairi.”

A hankali Arshaad yayi murmushi kafin yace “ba komai Abba, thankyou”

Murmushi Abban yayi kafin yace
“A matsayina na Mahaifin Hudan! Na baka ita Halak Malak! Allah ya nunamin ranar da zan aura maka ita.
Dan Allah Arshaad ka kula min da ita.”

Ya k’arashe maganar, cikin nauyi da karyewar zuciya.

Zamowa Arshaad yayi daga kan kujerar da yake kai kawai ya hau godiya, yana yi masa alk’awarin in shaa Allah zai bata dukkanin kulawar data kamata.

Sai godiya yake yi, har sai da Abban ya sallameshi tukun ya mik’e ya fita still yana godiya.

Murmushi Abba yayi bayan fitar Arshaad d’in, ba abunda ya zo kanshi sai lokacin dasu Kaka suka bashi Maryam! Yadda Arshaad yayi exactly shima hakan yayi.

A hankali yayi murmushin da har sai da y’ar kwalla ta zubo daga idanunshi! Yana tuno ta (Maryam) da moments d’insu.

Chaan, ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, a hankali yasa hannu ya sharce kwallar shi, sannan ya ce
“Astaghfirullah”.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 43So Da Buri 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×