Yau saura sati biyu auren su Hudan, sai shirye shirye ake yi.
Yayin da jikin Mama yayi sauk’i sosai abun har mamaki yake bawa jamaa kamar ba wadda ta karye ba, follow up kawai take zuwa abunta.
Abba da kanshi yaje ya siyowa y’arsa kayan d’aki na gani na fad’a, hatta cokali bai bari ba sai da ya siyo mata komai bayan ya tambayeta taste d’inta, wasu kuma yana daga chan d’in yake turo mata Sakina ta tayata zab’a. Sannan ya had’a mata gara nan ma na gani na fad’a.
Lokacin da bikin ya rage saura sati d’aya already kayan gara da kayan d’akin amarya suna gidanta. Duk da ba wai zama za suyi anan d’in ba, kai ta
kawai za a yi gidan daga nan su wuce karatunsu amman hakan bai sanya an k’i yi mata kayan d’aki ba saboda
time to time za su ke zuwa hutu.
Shima Arshaad a nasa b’angaren hakan bai hana sa siyan gida ba! Da a cikin estate d’in zai zauna amman da yake Granpa ya san Hudan zai aura haka nan k’iri k’iri sai ya hana sa gida!
Da farko Granpa d’in cewa ma yayi ya bar mishi estate d’inshi, tun kafin auren! Da kyar Aslam ya lallab’a shi
ya hak’ura amman duk da haka sai faman neman fad’a yake yi kuma fa sai da Dad ya tambaye shi tun farko lokacin kafin ma a saka rana amma sai ya nuna irin shi ba ruwan shi d’innan su yi abunda suke so. Yanzu kuma da bikin ya taho sai neman rigima yake yi yana neman abokin fad’a!
Shiyasa kowa ya sha jinin jikinshi dan duk wanda yayi rashin sa’a ya yarda ya samu matsala da Granpa a wannan yanayin da yake, tou tabbas kashin shi ya bushe! Wannan dalili yasa Arshaad ya sayi gidanshi da kanshi daman kuma shi har ga Allah ya ma fi son ya yi komai da kanshi, dan da kyar ma ya yarda ya bari Daddy ya bawa Mommy mak’udan kud’ad’e take had’a mishi zazzafan lefe. Gida kuwa da Abba yace zai siya mishi yi yayi kamar zai yi kuka, shi kuma Abban ya dage!
Sai da Mommy ta saka baki tukunna Abban ya hak’ura ya bar Arshaad d’in ya sayi gidan shi mai hawa biyu d’aki bakwai da parlour hud’u har da d’an k’aramin bq a gefe a nan cikin Nasarawa sai dai da d’an tafiya tsakaninsu da gida da estate.
Su Ummu da Mommy ne suka je suka yi mata jerenta tsaf! Wanda yanzu kawanchen Mama da Mommy ya dawo sabo fil! Dan har gida Mommy taje ta dubo ta, duk da Dad ba wani son yawan fitar tata yake yi ba amman indai abu ya shafi Maryam to ya kan bari saboda Mommyn tana yi musu campaign a lamarin Abba, sai ita kuwa Mama duk maganganu da Mommy take mata akan Abban amsa d’aya zuwa biyu take bata kullum ‘Allah ya zab’a mafi alkhairi’ ko kuma ta ce ‘ita fa ta riga ta hak’ura da Abba har abada! Ba akan dalili d’aya ba sai akan dalilai barkatai’.
Amman duk hakan bai sanya Mommy ta hak’ura ba, haka nan suke fama kullum.
Yau sauran kwana uku d’aurin auren!
Su Hudam basu samu komawa wajen Mama ba sai a yau d’in. Kafin su wuce Abba ya nemi ganinta. Kamar ko wanne uba haka nan ya zaunar da ita yayi mata nasiha mai ratsa jiki! Yana hawaye tana kuka haka su Sudais suma da suka zo yi mata sallama. A haka dai ba dan suna so ba suka yi sallama Abba ya sanya mata albarka.
Mommy da kanta ta kaita har gidan Shuwa gaban Mama Hudan tayi mamakin ganin baki y’an Maiduguri da suka zo dan gidan a cike tap! Suka tarar anata hada hada. A yau d’in zasu fara event! Dan haka suna isa suka tarar har mai kwalliya ta k’araso
tana jiransu, wadansu a cikin friends d’in su ma duk sun zo, da yake mai kwalliyar da tayi mata ita ce za tayi musu saboda Arshaad Maiduguri style yayi duk shi ya biyawa friends d’inta kud’in makeup da anko.
*****
Tunda Mommy ta warke kullum itake ce take yiwa Aslam girki. Wani special kulawa take bashi amman ta rasa dalilin damuwar shi dan ko jiya ma sai da Doc ya zo ya duba shi kuma ya tabbatar musu jininshi ya k’i sauk’a instead ma k’ara hawa yayi! Sannan ga zazzab’insa shima ya dawo.
Gaba d’aya hankalinsu duk a tashe yake, dan sun rasa gane kan Aslam kwata kwata.
Arshaad tun yana kula shi, yana tambayarshi meke damun shi yana lallab’a shi, har ya zo ya hak’ura kawai ya watsa shi a kwandon shara Dan Arshaad d’in gani yayi kamar ma Aslam d’in haushinshi yake ji! Idan ma yana waje Arshaad d’in ya shigo kawai sai dai ya tashi ya fice ya bar mishi wajen, ko magana baya so ta had’asa da shi! Kamar ma wanda yake k’ok’arin yin gaba da shi ta k’arfi da yaji! Shiyasa Arshaad d’in kawai ya rabu da shi amman a chan k’asan zuciyarshi mamakin abubuwan da Aslam d’in yake mishi a wannan lokacin da ya kamata yafi kowa taya shi murna, yake yi.
Hatta Dad Abba da Daddy sun lura da hakan, basa son shiga tsakaninsu tunda sun fi kusa shiyasa kawai suka zuba musu ido a ransu suna mamakin mai ya had’a best friends haka??
Da yamma, Mommy na d’aki tana jera kaya a wardrobe Dad ya shigo. A bayanta ya tsaya yayi hugging d’inta.
A hankali tayi murmushi kafin ta juyo still yana rik’e da ita tace “ina wuni Dad” Murmushi shima yayi mata yana jin tsananin k’aunarta tana nunkuwa a cikin zuciyarshi, a hankali yace “bayan wadannan akwai wasu kuma da kike buk’ata??” A hankali ta girgiza mishi kai alamun ‘a’a’.
Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya jawo hannunta suka nufi gadon dake d’akin.
Sai da ya zaunar da ita shima ya zauna a daff da ita tukunna yace “Aisha, magana nake so muyi dake ta gaskiya da gaskiya”. Da sauri ta mik’e tana k’ok’arin kawar da kanta daga gareshi kafin tace “Not again Dad, na gaya maka ban tuna komai ba, please Dad ka bar maganar nan.” Mik’ewa shima yayi ya sake rik’o hannunta kafin yace
“Look at me kice mini ‘wallahi Dad ban tuna komai ba‘.” Hannunta ta fara k’ok’arin kwacewa a cikin nashi ta hade rai sosai cikin fushi ta ce “Tunda ba ka yarda da ni ba, shikenan!”
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
“Jiya da yamma kin manta wayarki a d’akina kin tafi kitchen, naje kai miki wayar saboda a nata kira. I didn’t mean to eavesdrop but i have no choice! Naji komai maganan ku da kuka yi ke da Asabe!. Mai yasa kika b’oye min?”.
Gabanta ne ya yanke ya fad’i! A hankali ta tsaya tayi tsit ta nutsu ba tare da tace komai ba, sannan ta kasa d’agowa ta kalleshi.
Hannu yasa ya kamo hab’arta ya juyo da fuskarta ya d’ago fuskar, da sauri ta runtse idanuwanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin a hankali yace “Maimaita min abinda ya faru that very day da kika fad’o, waye ya turo ki?! Ina so inji daga bakinki, don’t lie, kin san naji komai. Kawai i want you to tell me.”
A hankali ta ce zan fad’a maka amman sai ka yi min rantsuwar ba zaka fad’awa kowa ba sannan ba zaka nuna ko da a fuskarka ne ba.” Cika fuskarta yayi cikin fad’a yace “Ba zan iya ba Aisha! Ya zama dole in fad’a sanann in nuna fushi kuma in d’auki mataki! Dole ne in hukunta mai laifi! Kin san irin ciwon da kika yi kuwa? Kin san irin wahalar..”
Cikin katseshi tace “to kaga dalilin da ya sanya na b’oye maka ko?” Cikin karyewar zuciya taci gaba da cewa
“I have lost a lot, shekaru sun jaa.
Na ci burin yiwa y’ay’ana tarbiyya especially ma Aaima da ta kasance mace amma kalli fa duk na yi missing
Mai ya rage yanzu?. Ni za kayi wa abun nan ko? A kaina kake so ka hukunta me laifin ina? To ni d’in nace ‘na yafe, har abada har gaban abada!’
Meye kuma na dawo da abunda ya riga ya wuce??. All i need to do now shine ibada dan kwata kwata ban gamsu da sallolina da kuka ce ina yi ba, Nafilfili da ibada su kawai nake buk’atar inyi a halin yanzu, ba wai case da holding grudges ba! I want peace.”
A hankali ganin ya d’an nutsu yana kallonta kawai, ta kamo dukkannin hannuwanshi biyu ta rik’e ta ce
“Dad, duniyar ma duk nawa take?
Idan fa muka yi hak’uri ma duk mutuwa za muyi! Yanzu idan ka ce zaka d’auki mataki wallahi square one zamu koma, mutane ba za su tab’a duba laifin da aka yi mini ba instead gani za suyi kamar ka fifita ni ne wanda fifita Aslam da Granpa ya yi tun farko ni na tabbatar shiyasa aka zamo silar zabge min kusan rabin rayuwata haka nan na yi ta a wahala! Please dan Allah let it go, for me.”
Mommy ta dad’e tana kwantar mishi da hankali, da nuna mishi ita kwanciyar hankali kawai take buk’ata yanzu, tukunna da kyar da mugun kyar ya yarda da buk’atarta akan ba zai yi komai ba, kuma ba zai nuna ba ko a fuska! Tukunna a hankali ta hau fad’a mishi abunda yaji tana fad’awa Gwaggwo Asaben.
In banda ajiyar zuciya ba abunda Dad yake sauk’ewa a jejjere, Ji yake kamar ya mutu dan tashin hankali da takaici
gashi ta saka shi yayi mata alk’awari.
A haka Aslam ya shigo ya samesu.
Tabbas ya lura akwai abunda suke tattaunawa but yadda Dad yayi ta k’ok’arin ganin ya danne ne yasa kawai ya basar dan ya fahimci koma menene to bai shafesa ba.
Gaidasu yayi ya nemi waje ya zauna a k’asa kan kafet yana kallonsu k’aunar iyayen nashi tana sake shigar mishi zuciya yana jin wani farin ciki yana taso masa ta k’asan zuciyarshi just by looking at them.
Suma d’in shi suke kallo wanda tashi d’aya in ka kalle shi zaka hango tsananin damuwa da k’uncin da yake a ciki.
“Ya baka shirya ba? Yanzu muka gama waya da Arshaad, yace yanzun za a tafi gudun kar ayi dare, kai da Aaima kawai ake jira. Na kira Aaiima tace min ta shirya tun d’azu, a tunanina kun wuce ma.”
Ajiyar zuciya Aslam d’in ya sauk’e kafin a hankali yace “Am, daman sallama nazo in yi muku.”
Da mamaki suke kallonshi. Bai jira jin me za su ce ba yace “Ina so zan wuce Uk! Akwai ayyukan da nake so In k’arasa a chan.
K’uraaa mishi ido kawai yaga sun yi, har ya fidda ran za suyi magana yaji Mommy tace “Mai yasa? Ka fad’i mini gaskiya dan na san akawai dalili Aslam”
Murmushi kawai yayi kafin yace
“Please ku barni in tafi, dan Allah”
Mik’ewa Dad yayi ya nufi hanyar fita kawai ba tare da yace mishi komai ba, ya fice.
Hannu Mommy ta mik’a mishi,
a hankali ya sa hannun nashi cikin nata ya mik’e ta dawo dashi kan gadon inda Dad ya tashi.
Cikin kulawa ta kallesa ta ce, “Aslam meye damuwar ka? Ko har yanzu kana jin zafin abubuwan da nayi maka ne?”
Ta fad’i hakan muryanta na d’an rawa kamar wadda zata fashe da kuka.
Da sauri ya ce “Mommy please mana, ki daina tunanin hakan sam a haka bane, ai ba laifinki bane ba.”
Cikin katseshi tace “To yaya ne?
Menene? Talk to me dan Allah!
Ko kanada wadda ta fini? Talk, kai kanka za kaji nauyin zuciyarka ya ragu. Waye ya b’ata maka rai?
Ko kana da masaniya akan abunda ya faru ranar dana fad’o? Fad’a kuka yi da Granpa? Ko Daddy ko wani? Ko Arshaad ne? Ko company d’in ne?
Naji Dad ya ce it was successful kun bud’e kai da Abba, akwai wani abun ne?” Duk ta rikice tambayoyi kawai take jero mishi barkatai.
A hankali ya lumshe idanunsa, sannan ya d’auko Dayan hannun shi ya d’aura akan hannayen nasu! Ganin haka yasa itama ta d’auko Dayan free hand d’inta ta d’aura akai ta bashi dukkannin attention d’inta a hankali tace “Talk, I’m your mother, I can help you.”
Bud’e idanuwanshi da suka yi jaa yayi, a hankali ya fara magana “I know I’m trying to be selfish here, but.”
Wata k’akk’arfar ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e bayan ta gama sauraran tilon d’an nata, a hankali ta janyo shi jikinta ta rungume, ta fara hawaye, cikin karyewar zuciya ta ce “I’m soo sorry son, ba zan iya taimakonka akan wannan al’amarin ba!.”
Murmushi yayi wanda yafi kuka da ihu ciwo a hankali ya zaro ta ajikinshi kafin yace “I know, kawai ki tayani addua, thats all I need maybe zan samu sauk’in rad’ad’in da nake ji, please Mommy.” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, kafin ya ce
“Maybe i’m not destined to be happy, a duniyar nan!! Haka Allah yake son ganina, if not why? Ta yaya zan kasa cire.”
Da sauri ta sa hannu ta toshe mishi baki, tausayinshi yana sake shigar mata zuciya. Ahankali yasa hannu ya zare hannun nata sannan yace, “Pls Mommy ku barni In tafi, dan Allah.”
Tana shirin bashi amsa, Dad ya shigo.
Kallonsu ya yi kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru ya juya kawai, ya ce
“Ku zo duk ku biyun gidan Granpa, yana son ganinmu, an dawo da su Adama!” Yana gama fad’in haka ya juya ya fice.
Sanye take cikin bridal gown, peach colour anyi kwalliya da white stones masu shek’i da d’aukar ido a gabad’aya k’irjin da kuma half d’in k’asan rigar ta tsaye har ta bayan side d’in inda yake flowing. Ta d’aura jewelry’s white,
yayin da takalmi, tauban, mayafi da head d’inta suka kasance peach.
Fuskarta ta sha casual makeup simple!
Dan cewa tayi itama ayi mata casual d’in inyaso ranar wuni, traditional day d’in da Shuwa, da su Mama za suyi, sai ayi mata bridal d’in.
Tayi masifar yin kyau kuwa gashi kwalliyarta ta tafi da shigarta matuk’a.
Bridesmaid d’inta su 10 har da Sakina 11, Khadijah bata zo yau ba tace sai gobe zata fara zuwa saboda tana laulayi kuma jikin ya d’an motsa.
Kusan duk Sakina ce ta gayyatosu (bridesmaids d’in) Y’an makarantar su nti kuma aka ci sa’a suka karb’i gayyatar aka shirya anko da su kasancewar ta fad’a musu da wuri. White gown ne a jikinsu, sai peach head, takalmi da jewelry’s sai vails d’insu white. D’inkin su iri d’aya sak dan saboda ma gudun samun mishkila dama tailor d’aya ne yayi d’inkunan ( bama anan ba ) Makeup d’insu komai iri d’aya.
Tana tsaye Sakina tana yafa mata mayafi Mama ta shigo, suna had’a ido kawai suka fara hawaye a tare!
Sakina wadda itama taji idonta ya cicciko ne tace “Mama dan Allah ku daina” sai kuma ta fara kuka itama, a haka Ummu ta shigo ta samesu, itama tana ganinsu ta hau kuka.
Da kyar friends d’insu suka lalllashesu aka d’an yi musu hotuna suka yi abunda ya kawo su, suka juya suka fita. Sai da aka sake gyarawa Hudan da Sakina makeup d’in su, Allah yaso mai makeup d’in bata riga ta tafi ba.
Ana gamawa, mai makeup d’in ta fara had’a kayanta, tana shirin tafiya kiran Auwal ya shigo wayar Sakina. Taso tayi ignoring amman kawai sai fa daure ta d’auka, albarkacin biki dan ta lura yafi kowa zak’ewa, so dole ta san sai ta had’u da shi one way or the other sannan ta lura da yanda shi kuma Ya Arshaad ya sakar mishi komai , it’s like ya ma manta da abunda yayi mishi akan Jalila, a k’asan ranta kuma sai tace “Ko da yake ba’a shiga tsakanin y’an uwa dama m, blood is thick!”
Da wannan tunanin ta d’auka wayar ta kara a kunnenta tace, “Assalam akaikom”.
Yana zaune cikin motar shi, a Ahankali ya lumshe idanunta da jin muryarta!
Sai da ta cire ran za ayi magana tukun taji a hankali taji yace “Sakeena..”
Da sauri cikin fad’a fad’a ta ce “Menene!!?” Dan jikinta ya fara yi mata abunda yake mata a duk lokacin da suke tare wanda ta tsana fiye da tunani.
Murmushi yayi kafin yace “Mun iso,
ku fito mu wuce, ko?” Bata bashi amsa ba ta kashe wayar.
After kamar 10 minutes haka suka fara fitowa.. Tunda suka fara fitowa camera man da mai video coverage suke d’auka. Sakina da k’anwar Ashraff saurayin Sakina da Hudan ne suka fito a k’arshe.
Motocine a jere tun daga farkon layin har zuwa k’arshe! Gabadaya irin su d’aya bak’ak’en benz! Sai ta tsakiya da aka d’ora wata y’ar k’aramar peach flower a gaban glass d’in ce kawai ba bak’a ba instead ita fara ce ta sha tint!
Amman itama k’irar ragowar motocin ce kawai kalar ne ya bambanta, kana gani ka san itace ta Amarya da Ango
dan haka su Sakina suka ruk’ota suka nufi motar da ita.
Suna zuwa bakin motar Arshaad yasa hannu ya bud’e seat d’in baya inda yake zaune ta gefe. Wata zazzafar suite ce a jikinshi white, hatta neck tie d’in shi white ne da takalmi, sai wani d’an kyalle da ya d’an d’aura a jikin aljihunshi na suite d’in nasa d’an mitsitsi peach.
Lokacin da yace mata kar su damu ya gama order da had’a komai kayan da za ayi using, aranta ta gama aiyyanawa ‘ba wani kyau za suyi ba’ dan tayi tunanin maza ba su iya zab’e ba amman yau kam ta tabbatar Ya Arshaad k’arshe ne wajen zab’a, had’a kaya da colours.
Murmushi Sakina tayi
kafin tace “Ango irin wannan kyau haka?”
Dariya ya d’anyi sannan yace “Ai ban kaiki ba. K’anwar Amarya”. Yana mata magana idanunshi na kan Hudan!
Da kyar ma ya amsa gaisuwarta ita da k’awarta. Lura da Sakina tayi hankalinshi baya kansu yasa ta saka mishi Hudan a motar ta rufe a ranta tace “Gata nan ai sai ka cinyeta da kallo”. Tana d’an murmushi.
Ba dan hancinta ya jiyo mata k’amshin turaren Auwal ba da ba abunda zai hanata afkawa kanshi In ta tashi juyowa domin barin wajen. A hankali ta d’an juyo jin k’amshi da mutum a bayanta daff! Suna had’a ido kuwa ta zabga masa wata uwar harara. A wajen k’anwar Ashraff kawai ya samu gaisuwa, bai damu ba ya amsa ta kafin ya juya ga Sakina yace “Kin yi kyau over!” Yad’an yi mata alamar perfect da hannunshi yana murmushi. White suite ce shima a jikinshi da d’an ratsin black, yayi masifar yin kyau sai dai askinsa da yayi yau d’in ne ya b’ata mata rai.
Hannu yasa ya bud’e gaban motar, kafin yace “Bismillah” yana kallonta still da murmushi akan kyakkyawar fuskarshi.
A hankali ta d’auke idanunta daga kanshi, daman tun d’azu da ta sunkuya suna magana da Arshaad ta ganshi zaune a mazaunin driver! A tunaninshi zata yarda ta zauna kusa dashi kenan, tab! Ai ko hauka take ba zata yarda ta zauna kusa da shi ba
ita da take k’ok’arin ganin ta kauce mishi ta kowacce hanya, besides Ashraff ma yana jiranta tare za su tafi..’ Da wannan tunanin ta kamo hannun k’anwar Ashraff ta saka ta a cikin gaban motar ta rufe, ta yi gaba abunta.
Guiwa a sace Auwal ya bita da kallo har ta isa inda motar Ashraff d’in take a chan gefe bama a cikin convoy d’in nasu ba, ta shiga. Da kyar ya iya dedeta kanshi ya juya yaje ya shiga ya kunna motar dan har an fara yin gaba…
Suna isa inda za ayi event d’in
ya bud’e motar shi ya fito. Sai hotuna ake d’auka amman shi bai damu ba, neman ta kawai yake yi. Ganin ba ita ba dalilin ta yasa ya zaro waya ya hau kiranta! Kowacce mota ta k’araso, har ta masu d’aukar hoto amman tasu bata iso ba. Arshaad ne ya d’an kira sunan shi dan haka ya juya, da hannu Arshaad d’in ya yafito shi, yana zuwa yace “Ana ta hoto babu kai, me kake nema?” D’an murmushi kawai yayi ya tsaya aka yi musu, daga nan aka fara k’ok’arin shiga hall d’in. K’awayen Amarya, a baya Abokan Ango a gaba
Auwal da Jamil su ne daf da Ango da Amarya dan sune suka saka suit kamar Angon ragowar mazan kowa kayan shi ya saka.
Shi dai Auwal har aka shiga bashi da nutsuwa dan haka Amarya tana zama ya juya ya fita yana mai cewa Jamil yayi jawabin da da shine zai yi, yana da uzuri.
Arshaad bai yi mamakin rashin ganin Aaima da Aslam a wajen ba! Amman tabbas ranshi ya sosu, baya son b’ata wannan ranar ta musamman dan haka ya kawai sai ya basar ya ci gaba da huld’ar gabanshi.
Tsarin wajen ba k’aramin had’uwa yayi ba, Tebur da kujeru uku a zagaye wajen guda ashirin! Sai chan wajen sit d’in Amarya da Ango gefen dama da hagun su kuma akwai kujeru goma goma da dogon tebur a lamun nan ne wajen zaman best friends dan har ma sunje sun zazzauna matan masu anko mazan kuma waenda suka zo tare.
Kwata kwata friends d’insu da suka tarar a wajen ba sufi ashirin ba!
Cool music ke tashi ba wani hayaniya.
Cocktail ne da cake da sweet da hot chocolate da kuma menu mai d’auke da abubuwa daban daban akan tebur d’in, sai waiters a gefen tebles d’in a tsattsaye su wajen 30 da uniform, duk
abinda kake buk’ata sai ka kira ka gaya musu a menu d’in aje a kawo maka in ka gama su d’auke.
After kamar 20 minutes da fitar Auwal, motar su Sakina ta shigo wajen. Ranshi a mugun b’ace ya k’arasa inda motar take! Bai yi wata wata ba yasa hannu ya bud’e side d’inta ya kamo hannunta ya fito da ita. Da kyar ta iya tsayawa ta gyara mayafinta wanda yake k’ok’arin zamewa. Ko lura da guy d’in da ya fito shima ya zagayo inda suke Auwal d’in bai yi ba ya fara magana “Ina kuka tsaya?? Kin san mintunku nawa kuwa?
Almost 30 minutes kowa ya k’araso banda ku, Ina kuka biya haka?” Ya k’arashe maganar cikin tsananin b’acin rai, kamar wani ubanta
Kallon shi take yi kawai. Sai da ta barshi ya kai aya tukun ta fara k’ok’arin wuce shi ba tare da tace uffan ba!. Tafarfasar da zuciyar shi keyi ba kad’an bane dan haka cikin zafin nama ya sake sa hannu ya fincikota ya dawo da ita unintentionally ta bugu da jikin motar.
Da sauri Ashraff ya k’araso inda suke ya juyo da shi ya cukumi wuyan rigar shi! Cikin tsananin b’acin rai yace “Meye ne matsalar ka? Who the hell are you? A iya sani na bata da yaya!
Ka fito kawai ka fara yiwa mutane hauka. Ka godewa Allah ni ba mahaukaci bane Irin ka dan wallahi da sai na gyara maka zama a wajen nan!” Ya k’arashe maganar yana sakin mishi kwala da k’arfi. Auwal ya taso kenan yana shirin yin magana a zafafe
Idanuwansa suka sauk’a kan Sakina wadda ta fara hawaye.
A take yaji duk jikinshi yayi sanyi.
Tun lokacin da ya tura ta jikin mota har yanzu bata motsa ba tana a yanda take sai dai hawayen da ita kanta ta rasa na menene waenda suke zuba
akan k’uncinta.
Kamar an tsoma shi a ruwan sanyi haka yaji, ya kasa motsawa zuciyarsa na dukan uku uku, gashi tak’i yarda ta kalli inda yake.
A hankali Ashraff ya k’arasa inda take ya fara yi mata maganar da Auwal d’in baya jin me yake cewa.
Goge hawayenta tayi ta gyara tsayuwarta. Sannan Ashraff d’in ya bud’e bayan motar ya d’auko k’aton cake d’in da suka tsaya karb’a. Daga nan suka zo suka wuce shi ba tare da sun ce mishi komai ba!.
Sam ya kasa motsi ya kasa yin komai.
Kawai iya hawayen da ya gani daga idonta ne ya kashe mishi guiwa ya sanyaya mishi jiki. Yafi 10 minutes a wajen kafin da kyar ya samu ya wuce ciki, yana zuwa ya nemi waje ya zauna. Ba abunda ya iya ci a wajen yana nan zaune a wajen shi kad’ai amman dukkannin hankalinshi na a kan Sakina wadda itama ya lura bata da sukuni ga Ashraff a gefenta wanda yake ji kamar yaje ya rufe da duka, sai wani shishshige mata yake yi.
Su y’an matan wajen a tunanin su tsabar kyau da had’uwar sa ne yasa yake shan k’amshi yak’i shiga mutane
basu san shi kuwa zuciyarshi ce take shirin tarwatsewa ba! Gashi ank’i a tashi daga wajen.
Sai after kamar 2 hours tukunna aka ce Amarya da Ango su yanka cake!
Bayan sun yanka Huda na k’ok’arin durk’usawa ta bashi yayi saurin tarota ya karb’a shi ya durk’usa ya bata!
Ai kuwa aka hau tafi ana ta videos da pictures. Daga nan masu bada gifts suka bada aka yi addua aka tashi a lokacin already Auwal ya dad’e da komawa cikin mota su kawai yake jira.
Suna fitowa kowa ya fara kama gabanshi.
Bai yi tunanin Sakina zata shigo motar ba! Dan haka ya fara k’ok’arin tada motar bayan su Hudan sun shigo, Arshaad ne yace “Wait Auwal, bara mu d’an jira Sakina”. Yana juyawa yaga sun yi sallama da k’awarta da wanda ya gansu tare sun tafi.
Sai da taga wucewarsu, tukunna ta zo ta shiga a lokacin ita kad’ai ce ma ta rage a harabar wajen.
Har suka isa gidan su Mama bai ko kalli inda take ba. Motar shiruuu sai hirar su Arshaad da suke yi k’asa k’asa ba wanda yake jin me suke cewa.
Sallama Sakina tayi da Arshaad
Hudan kuma ta cewa Auwal sun gode, daga nan Arshaad ya dawo gaba su kuma suka wuce cikin gida.
Dad, Mommy, Gramma, Aslam Arshaad sai Aaima kawai Granpa ya buk’aci gani tunda a ganinshi ya riga ya cire Dad da Abba da su Hudan a cikin zuriarshi.
Mammy da Mom kawai suka tarar a parlourn dan Ummi kusan a sume ma aka kawota, shiyasa Granpa ya kira Doc akai d’akin Gramma ma da ita domin bata taimakon gaggawa.
Aaima tana shigowa da suka had’a ido da Mammy sai tayi kanta ta gudu ta rungume kawai tasa kuka. A hankali Aslam yaje ya gaida Granpa tukunna ya dawo wajensu ya gaidasu yana mai shafa kan Aaima alamun lallashi, haka itama Mommy bayan ta je ta gaida Granpa d’in ta dawo wajensu. Gaba d’aya hankalinsu yana ga Aaima, wani abun mamaki kwata kwata basu lura da Mommy ba har sai da muryarta ta yiwa dodon kunnuwansu dirar mikiya! A firgice duk su biyun suka d’ago suna kallon ta! Itan ma su d’in take kallo da murmushi akan fuskarta
especially ma Mammy wadda bakinta yake rawa ta kasa furta uffan! Mom na shirin yin magana Granpa yayi gyaran murya.
Duk nutsuwa suka yi suka maida hankalin su a kanshi bayan sun d’an gyaygyara zama. Kallonsu yayi d’aya bayan d’aya, kafin yace “Ina Muhammad?” A hankali cikin girmamawa Aslam ya ce, “Yana wajen event d’insu an fara yau”
Da mamaki Mom da Mammy suka kalleshi, suna shirin yin magana suka ji Aslam d’in ya sake cewa “Ni da Aaima ma da yanzu zamu wuce
to kuma sai kiranka ya riskemu”.
“Call him! Ka ce ya bar duk abunda yake ya zo yanzun nan!” Cewar Granpa.
A hankali Aslam ya ce “Granpa plss…”
Cikin d’an fad’a fad’a abunda bai tab’a yi mishi ba yace “Call him now!!”
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“Ok, Granpa.” Sannan ya zaro wayar shi ya hau kiran Arshaad. Har ta tsinke ba a d’auka ba, ya sake kira nan ma ba a d’auka ba, zai kira a karo na uku Granpa ya d’aga mishi hannu, yace
“Leave him” Daga nan ya fara magana
“2 months ago! Adama, Rukayya da Zainab Sun yi wa wannan family d’in babban laifi wanda hakan ya kai ni ga yanke hukunci a garesu mai tsauri!
Dalilin tara ku a nan da nayi shine
Inaso In jaa muku kunne akan
‘magana ta riga ta wuce!’. Mazajen su Adama da ita Ummi basa kusa dan haka kai Yahaya kai ne zaka sanar da sak’ona gare su! Ba na so ko da wasa inji makamanciyar maganar nan ta sake tasowa! Sun yi laifi an hukuntasu magana ta mutu!! Duk kuma wanda ya k’etare umarnina ko a fuska ya nuna musu wani abun yi zai gamu da fushina tabbas. Su Yusuf kar suga wai basa tare da ni, muddin suka yi wani abun da bai kamata ba a matayensu to tabbas zan yanke musu hukunci mai tsanani! Ka gaya musu hakan.
Ku kuma” Ya juya kan su Mammy
“Wannan hukuncin da na yanke muku kuka yi going through for the past 2 months ba komai bane! Ku k’irga azabar sau ashirin tou tabbas ita zaku fuskanta muddin kuka bari naji wata matsala daga gareku.
Sai magana ta biyu! Duk da Muhammad ya b’ata min rai a yanzu, hakan ba zai saka In chanja abunda na shirya ba. A kwanaki yayi laifi wanda ya kai ni ga rage mishi matsayi Auwal ma haka. Tou yanzu Alhamdulillah naga progress da ci gaba a tare da su, dan haka ranar Monday. Auwal ba dan halin ubansa ba sai dan kwazon shi zai koma assistant md, tunda Aslam ne md yanzu shi kuma Muhammad ya koma matsayinshi, treasurer.
In shaa Allah Nan da shekara d’aya za a fidda wanda ya chanchanci a malllakawa MT gabad’aya na uk da na Abuja da na nan Kano, a tsakanin su uku.
Yahaya In Zainab ta warke ka mik’a ta gidan Mijinta inda ya k’aura ya koma, amman yanzu ka fara kai Adama tukunna ta samu ta huta, Mammy kema ki wuce d’akinki. Allah ya bamu alheri.” Yana gama fad’in haka ya mik’e, ya shige d’akin shi.
Shiruu, d’akin ya d’auka. Da kyar Mammmy ta iya mik’ewa dan jikinta ba energy ta isa inda Mommy take tana zuwa kawai ta fad’a jikinta ta fashe da kuka tana cewa, “Alhamdulillah!! Na ji dad’in ganinki a haka y’ar uwa ta, Alhamdulillah Alhamdulillah”. Mom ita ma rarrafawa
tayi inda suke, ba yabo ba fallasa ta d’an rungume Mommy kafin tace
“Alhamdulillah, Allah ya k’ara mike lafiya”
Ba wadda Dad ya k’urawa ido irin Mammy! A hankali yace musu “ku taso mu tafi” kawai, ya mike. Aaima ce taje ta kansu ta taya su mik’ewa, dan ko kuzarin kirki babu a jikinsu! Duk sun yi bak’i sun rame sun kod’e sun k’anjame! Banda kuka ba abunda take yi.
Aslam tare suka tafi da Mommy kamar yadda suka zo tare. Dad kuwa sai da ya fara kai Mammy gida ita da Aaima
tukunna ya wuce da Mom dan kaita sabon gidan da su Abba suka koma.
Side d’in Daddy ya shiga tana biye da shi a baya. A zaune suka samu Daddyn a parlourn k’asa yana shan coffee da suit d’inshi a jikinshi ko takalmi bai cire ba da alama yanzu ma ya dawo daga aiki dan ga suitcase d’inshi a gefe.
Sallamar Dad ce ta jawo hankalinshi gare su, mik’ewa yayi yana d’an murmushi da muryarshi dake nuni da a matuk’ar gajiye yake yace “Yaya ina wuni, ai da ka kirani na zo.” Muryarshi ce ta mak’ale sakamokon ganin Mom wadda ta fito yanzu daga bayan Yayan nashi.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, yana kallanta. Rabonshi da ita wata d’aya kenan, tun last zuwanshi da yaje tayi ta kuka ya yanke shawarar sai dai ya kira police d’in ya had’asu dan ba zai iya jurar ganinta a wannan halin ba
Muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi, a hankali yaji tace “Ina wuni”, Jinjina kai yayi kafin a hankali yace , “Alhamdulillah”
Sannan ya koma ya zauna ya shiga gaida Dad wanda ya nemi waje shima ya zauna.
A k’asa kan kafet Mom ta zauna tana ta sun sunkui da kai! Tausayinta fal zuciyar Mijinta dan ya hango tsantsar nadama da shiryuwa a matar tashi, daman chan shi ya san sharrin shaid’an ne! Ba abunda yafi d’aga mishi hankali irin bak’i da lalacewar da tayi, in shaa Allah nan da 3 days zai shirya musu fita suje ayi mata checkup.
Muryar Dad ce ta katse shi jin yana cewa, “Abba ya dawo kuwa??
Ina son ganinku ne tare.”
“Eh to i don’t think so but bara in kirashi” Daddyn ya fad’a yana mai zaro wayarshi daga aljihun wandonsa.
Da kyar ya iya kai wa 2 yau a waje, duk da tarin aiyukan da suke a kanshi haka nan ya baro su birjiki! Ya dawo gida. Yana d’aki shi kad’ai sallah kawai yake iya fita yayi. Anya bai yi gaggawar aurar da Hudan ba kuwa?
Kar yaje garin gudun b’atawa su Yaya da Daddy rai ya cuci kanshi fa!
He just knew her amman har ya d’auketa d’ungum ya bama wani
kuma bama a Kano kusa da shi da anytime yaso zai je ya ganta za su zauna ba! A Uk za su zauna, sai
after 4 ko ma 5 years tukunna za su dawo!. Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya
A ranshi ya raya zai nemi Alfarmar Arshaad akan su d’an zauna anan gidanshi for some time, ko da ace duniya za tayi mishi kallon the most selfish father ne!! Tsaki ya jaa tunawa da yayi Arshaad d’in har ya biya mak’udan kud’i na course d’inshi da zai yi da kuma karatun da Hudan zata fara. Yana wannan tunanin yaji kira ya shigo wayarshi. D’auka yayi ba tare da ya kalla sunan ba ya amsa ya kara a kunnenshi, sai da Daddy yace “Abba”
Tukun ya fahimci wanene dan haka ya gyara zama yace “Ina wuni, ya aiki?”
Amsawa Daddy yayi daganan yace masa “yazo ya samesu ga Dad ya zo yana son ganinsu”.
“Ok” kawai yace, sannan ya kashe wayar ya mik’e ya fice jikinshi duk a sanyaye.
Ko mintuna hud’u cikakku bai rufa ba, ya k’arasa parlourn. Waje ya nema ya zauna suka sake gaisawa. Ba tare da b’ata lokaci ba, Dad ya fad’a musu sak’on Granpa! Shi Abba wallahi har k’asan zuciyarshi yama manta da wata halitta wai ita Ummi! A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, ya koma ya kwantar da kanshi a jikin saman kujerar ba tare da yace da su komai ba! Dan in ya cewa Dad zai iya yin abunda Granpa yace a yanzu dai tou gaskiya k’arya yake yi, sai dai maybe ko in gaba.
Mom ce ta katse mishi tunanin shi ta hanyar cewa “Abba Ina mai baka hak’uri game da kuskuren da muka aikata maka! Bisa ga biyewa son zuciyoyinmu, ka yafe mana dan Allah.”
Shi sai a lokacin ma ya gane ita ce a wajen.
Mik’ewa kawai yayi ya cewa su Dad
“Bara inje in sha magani In d’an kwanta kaina yana min ciwo, sai da safe.” Daga nan kawai ya nufi hanyar fita, inda ace Mom ta san tunzura shi d’in da maganar ta tayi, da ba zata soma ba! Kawai wani sabon haushin su ne ya sake lullub’e shi.
Hudan is soppose to get married at this age duk wani uba zai so hakan
amman dalilin su ya sanya har yake having second thoughts akan abunda ya san shine farin cikin ta, yakamata ace yana taya ta murna yana sopporting d’inta d’ari bisa d’ari amman because of them gashi har yana son aikata abunda za aganshi kamar selfish, kuma ya san inba da kyar ba, su Yaya za su iya jin haushin sa wanda hakan abunda bai tab’a
faruwaba ne.
Daddy yana shirin yin magana da sauri Dad ya dakatar dashi ta hanyar d’aga mishi hannu! Har Abba ya fice ba wanda yace komai.
Yana fita shima Dad d’in ya mik’e yayi musu sallama ya fice.
Mik’ewa Daddy yayi daga inda yake ya koma k’asa wajen Mom. Tun kafin yace wani abun ta fad’a jikinshi ta fashe da kuka tana rok’on shi akan “yayi hak’uri shi da y’an uwanshi, in shaa Allah ba zata sake ba! Sharrin shaid’an ne dan Allah kar ya dinga kallonta da abun ya taimaka mata ya goge komai a ranshi…”
Lallashinta ya shiga yi yayi hugging d’inta yana jin tausayin ta na sake shiga zuciyarshi.. Da kyar ya samu tayi shiru daganan yace “tazo taje tayi wanka ta huta” Dan da gani tana buk’atar ta tsaftace jikinta da kuma hutu ba na wasa ba.
Hatta kujerun personal parlour d’inta na chan sama, sabbi dal Daddy ya saka mata. Bedroom ma ya saka mata sabbin furnitures duk don ya dan rage mata zafi.
Har k’asa kuwa ta durk’usa ta kama k’afafunshi tayi godiya sannan ta sake bashi hak’uri. Shi kam Daddy tausayinta kawai yake ta ji, yaga duk tayi sanyi ta koma kalar tausayi, sai wani nan nan yake yi da ita.
Ko da Auwal ya dawo bai san da labarin dawowarta ba, gashi kuma ranshi a mugun b’ace yake ga gajiya, dan haka direct side d’inshi ya nufa, yayi wanka yayi sallah ya bi lafiyar gado, da kyar sai da yayi da gaske tukunna hoton Sakina da Ashraff yabar idanuwanshi sannan ya samu bacci ya d’auke shi.
Auwal yana ajjiye Arshaad ya shiga gida shima. A mugun gajiye yake dan haka tun a hanyar shiga ya zare suite d’in shi ya rik’eta a hannu kafin ya fara k’ok’arin zare necktie d’in! Kana ganinshi ka san bacci kawai yake buk’ata. Ko kallon cikin parlourn bai yi ba ya nufi side d’inshi….
“Ango!!” Yaji muryar Mammy.
Da sauri ya d’ago yana kallon setin inda yaji muryar tata ta fito, “ai kuwa ita d’in ce” ya fad’i hakan a ranshi.
Da murna ya k’arasa inda take zaune ita da aiima. Ita kam ko wankan ma bata samu tayi ba! Tana nan a yadda ta fito a cell! Yo ina zata iya wanka, ko sama bata samu ta hau ba tun da Aaima ta fad’a mata mummunaan labari take zaune take jiran dawowar Arshaad.
Huggin d’inta yayi kafin ya d’ago yayi kissing forehead d’inta tukun yace
“Welcome home Mammy, we miss you.”
Murmushin takaici tayi kafin ta mike tsaye, cikin tsananin b’acin rai tace
“Ba kayi missing d’ina ba Arshaad, da kayi missing d’ina to da ba zaka yi min yaji ka daina zuwa inda nake ba”
Kamar zai yi kuka yace, “Mammy bana son ganin b’acin ranki, abunda kike so inyi ne ba zai yi ba, kiyi hak’uri please.”
Cikin katseshi tace “Ka san cewa Aslam baya yin kwana uku bai lek’o mu ba?
Haka Auwal shima! Daddy kuwa kullum sai ya kira waya an had’ashi da Adama, Ummi kam daman kowa ya san Mijinta ba zuwa zai yi ba tunda shi ne ya kulle mu! Kai fa? Arshaad da kai da uban ka laifin me nayi muku, a rayuwa?
Anya ni na haifeka kuwa Arshaad?”
Da sauri ya matsa sosai inda take idanuwanshi har sun cicciko kamar zai yi kuka ya d’aura hannunsa ya rufe mata baki kafin yace “Mammy pleas…”
LBai k’arasa ba ta buge hannun
cikin tsananin b’acin rai tace “Kar ka yi mini ‘please’ bana son ji! Kun riga kun nuna min matsayi na da kai da ubanka! Naji nagani kuma na fahimta,
akwai lokacin da na ware muku kai da shi zan waiwayeku amman ba yanzu ba dan wallahi sai kun san kun wulak’anta, hak’urina ya k’are a cikin gidan nan! Amman yanzu akwai boss d’in da ya kamata mu fara kashewa ni da kai a yau kafin komai.” Bata jira jin me zai ce ba taci gaba “Naji labarin za kayi aure! Jibi ko? To wallahi bari kaji
In dai sunana Rukayya, kuma nonona ka sha to wallahi muddin ka auri wannan Yarinyar ni kuma a ranar zan tsine maka.”
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Ita ce kalmar da Arshaad yake ta nanata wa a ranshi! Ya kasa motsi ya kasa cewa komai. A ranshi ya ce
“Wannan shine abunda nake gudarwa since day 1, ya zan yi da Mammy, ya zan yi da zuciyata wadda na san muddin aka fasa aurena da Hudan tabbas tarwatsewa za tayi”.