Skip to content
Part 57 of 73 in the Series So Da Buri by Bulama

Da kyar Aslam ya iya mik’ewa bayan fitar su Auwal.

A hankali yana jin yadda zuciyarshi take bugawa da mugun k’arfi ya isa bakin k’ofar d’akin da ya ga su Sakina sun fito daga ciki.

Da kyar ya iya d’aga hannunshi ya fara knocking.

A hankali kamar mai kuka yaji tace
“Sakina shigo mana”. Dan ita har ga Allah ta yarda da Sakina wadda tace mata ‘bara su je su yi siyan baki ta dawo ai ita a nan ma zata kwana yau’.

A hankali ya lumshe idanuwasa ya bud’e kafin ya murza handle d’in ya tura k’ofar ya shiga da sallama.

Da sauri ta d’ago jin muryar Namiji!…
Duk da su Sakina sun ja mata mayafinta kafin su fita amman tana iya hango shi!

Har yanzun shadda ce a jikinshi abunda bata tab’a ganiba kenan. Sai taga yayi mata mugun kyau! Tsayi kamala surar jikinshi ta cikakkaen lafiyayyen Namiji ta fito sosai. A take zuciyarta ta hau bugawa da sauri da sauri.

Takowa yake yi izuwa bakin gadon wanda hakan da yake yi ji take kamar a kan zuciyarta yake yin tafiyar. Duk taku d’aya sai taji tamkar numfashinta zai d’auke ne! Hakan yasa ta fara ja da baya. Yana matsowa ita kuma tana ja baya. Aslam shi bai ma lura da yadda take ja da bayan ba har sai da yaga sun kai edge d’in gado tana neman mik’ewa, dan shi har ga Allah ba abunda idanuwanshi suke gane mishi sai ita, ruhinta! Shiyasa sam bai lura da movement d’inta ba. Yana isowa dab da ita, ya jaa ya tsaya a bakin gadon.

Ita kuma sai k’ok’ari take ta mik’e amman k’afarsa da side drawer sun tokare ta gashi har ta kai jikin fuskar gadon so ba daman ci gaba da matsawa.

A hankali taga yana d’an sukuyowa, ji take yi kamar ta bud’e murya ta kurma ihu! Ko kuma ta tashi ta yi tsalle ta fad’a tsakiyar gadon daga nan ta samu ta sauk’a ta d’ayan side d’in.
Ita har ga Allah tun farkon had’uwar ta da shi, sam! Bata k’aunar zama a kusa da shi (Aslam) Saboda muddin suna tare no matter how she tries kwata kwata zuciyarta bata barin wannan mahaukacin gudun data rasa dalilinsa! Gashi bata san dalilin da ya sa yaketa matsowa kusa da ita ba.
Ita fa yanzu abunda ya kamace su shine su nutsu su yi tunanin ya za suyi da rayuwarsu da wannan auren da aka k’ulla musu shiyasa duk a rud’e
sannan a rikice take kuma gashi yanzu ya zo ya sake rikitata.

Tana cikin wannan tunanin ta ji fuskarsa daff da tata! A hankali taji yasa hannu ya yaye lullub’in laffayar fuskarta.

Had’a idanu suka yi! Da k’arfi zuciyoyinsu suka buga a tare!

Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin ya sak’ale kwayar idanuwanshi da tata sannan ya ce “Assalam alaiki, Maryama.”

Da mugun k’arfi ta runtse idanuwanta sannan daidai nan hawayen da bata san dalilinsu ba suka b’alle mata a take.

A hankali ya hau yi mata kallon k’urilla. Cikakkiyar minti d’aya ya d’auka yana kallon fuskarta
kafin da kyar ya samu ya iya kokawa da zuciyarshi ya d’auke idanunsa yana mai lumshe su.

Wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauk’e wadda itama bata san lokacin da ta sauk’e tata siririyar ajiyar zuciyar ba
sakamokon numfashinsa mai d’umi da dad’in shak’a da ya ziyarci hancinta wanda har zuciyarta sai da ta amsa!
Hakan ne kuma ya haifar mata da sauk’e ajiyar zuciyar da bata shirya wa ba…

A hankali ta ji sauk’ar wani lallausar tafin hannu kamar na jarirai mai mugun taushi a kan kumatunta!
A mugun zabure ta bud’e idanuwanta da suka k’ank’ance suka yi jaa ta zuba masa su. Bai damu da kallon da take yi masa ba! Kallonta kawai yake yi yana goge mata hawayen nata.

Idanuwansa da ya zuba mata ya kafeta da su ne ya sanya ta runtse nata idanuwan jikinta na wani mugun rawa!.

Wata ajiyar zuciyar kawai ya sake sauk’ewa…yana gama goge hawayen ya mik’e da sauri dan ba k’aramin kokawa yake yi da zuciyarsa ba tun lokacin da ya shigo!

Sai da ya lumshe ido na some seconds tukunna ya bud’e ya ce “Ki taso mu je kici abinci”. Kafin ya rufe bakinsa tace
“N na na k’oshi” Tana mai jan numfashi har yanzu jikinta bai daina rawa ba.

Bai ce mata komai ba, ya sa kai ya fice a d’akin. Minti kad’an ya dawo da ledojin da Auwal ya shigo da su. Gefenta ya nema waje ya zauna a bakin gadon! A hankali ya bud’e ledojin ya d’aura akan stool kafin yace
“Oya, gashi ki ci. Akwai wani abun da kike buk’ata?”

Da sauri ta girgiza kai alamar ‘a’a’.

A hankali ya mik’e yace
“Sai da safe”

Tun kafin ya rufe bakinshi tace
“Allah ya kaimu”. Don so take ya fita.

Shima lura da hakan da yayi ne dama ya sanya kawai ya mik’e d’in.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kamar zai ce wani abun sai kuma kawai yace
“Allah ya tashe mu lafiya”
Yana mai juyawa ya fita daga
d’akin gaba d’aya”

Yana fita ta sauk’e wata wawiyar ajiyar zuciya. Har ta d’an zauna sai kuma ta mik’e da sauri ta isa bakin k’ofar ta murza key ta zare ta taho da shi ta ajjiye a kan side drawer tana ta tunani. Ta dad’e bata sha mamaki irin na yau ba! Yadda yake yin abu kan sa tsaye sannan kamar bashi da wata damuwa abun yayi mugun d’aure mata kai! Duba fa yadda ya wani zauna a kusa da ita sannan har da wani share mata hawaye. Ita tana tunanin sai ta yi kusan kwanaki ma bata ganshi ba daga nan ya bata takarda yace taje ta auri Arshaad d’inta Amman kalli abunda yayi tun yau. Ba abunda yafi d’aure mata kai irin siyan bakin da aka yi
sai kace waenda suka yi auren soyayya…

Harga Allah yunwa take ji sosai ma kuwa amman d’aurewar da kanta yayi ne ya sanya ta mayar da kajin cikin ledarsu ta had’a da ledar drinks d’in ta saka a d’an k’aramin fridge d’in data gani a d’akin.

Da kyar ta lallab’a ta yaye laffayar jikin ta ta ninke, ta shiga toilet ta d’auro alwala tazo ta nemi waje ta zauna dan already sun yi sallolinsu Magrib da Isha ita da su Sakina.

A ranta ta gama ayyanawa
tabbas idan aka yi d’an kwana biyu taji Aslam bai yi mata wata magana ba
to ita kam zata tareshi da zancen ya saketa! Idan ma Mahaifiyar Ya Arshaad ta hana aurensu to zata hak’ura ta rungumi k’addara tayi facing karatunta idan Allah ya fito mata da wani ta yi aurenta
amman ita kam ba zata iya zama da wannan murd’ad’d’en mutumin da bashi da alk’ibla ba! Infact tayaya ma zata zauna da mutumin da kullum in dai suna tare sai taji zuciyarta tana barazanar fashewa haka kurum salon yaje ya fasa mata zuciya a banza ya yiwa Mama da Abba da su Sakina asara, Inaa ba zai yiu ba!

Da wannan tunanin ta kwanta akan lallausan gadon tana mai lumshe ido.
Nan kuma ta fad’a tunanin Arshaad!
Tana yi tana istighfari amma sam ta kasa dainawa. Tabbas sai ka rasa abu kake gane yawan son da kake yi mishi!
A lokacin da take tare da Arshaad bata san tana sonshi haka ba sai yanxu da ta san In ba da kyar ba to ta rasa shi kenan har abada! Dan muddin Mahaifiyarsa bata basu go ahead ba to ita kuma tayi alk’awarin ko sonshi zai kasheta ba zata tab’a aurensa ba tare da albarkar ta ba! Besides sai ma ta fara nemo mafita akan wannan auren!
She has to do something fast
saboda taga take taken Aslam kamar shi zai iya hak’ura ya zauna da ita don ya faranta ran su Abba Kuma ta tabbata idan hakan ta faru to haka za su k’are rayuwarsu ba soyayya
tunda ita dai zuciya d’aya Allah ya bata kuma ta riga ta damk’awa Ya Arshaad shima kuma Aslam d’in ta tabbata bai ya k’aunarta sai dai ya kawai ya zauna da ita saboda ba yadda ya iya to Ina riba? Garama shi Namiji ne anytime idan ya had’u da wadda yake so zai aura ita fa? An cuceta an cuci Ya Arshaad d’inta..how she wish she can see him now tana so
taga halin da yake a ciki, bawan Allah d’azu ba kalar zargin da batayi mishi ba ashe fin k’arfinsa aka yi. Bata san lokacin da wani mugun kuka ya kufce mata da k’arfi ba.

Tunani da kuka basu barta ta rintsaba sai around 2:00am tukunna bacci ya kwasheta wanda bata yishi cikin dad’in rai ba. Kafin asuba ta farka
sakamokon mugun ciwon kan da ya rufar mata, da zazzafan zazzab’i
ko idanuwanta bata iya bud’ewa sosai in banda rawar sanyi ba abunda take yi.

Tana ji ana kiran sallah
k’ok’ari take yi ta samu ta tashi amma sam ta gagara.

A b’angaren Aslam shima bai samu yayi ishashshen bacci ba
kusan kwana yayi yana nafila.
A nan kan daddumar ya samu bacci ya saceshi. Kiran sallar farko da aka maka a masallacin cikin estate d’in ne ya farkar da shi, dan haka ya mik’e ya shige bathroom. Sai da yayi wanka ya d’auro alwala sannan ya fito ya d’an
kimtsa ya zura jallabiya ya gabatar da fajr nafl, ya zauna karatu.

Yana idarwa ana tada sallah
dan haka a gurguje ya fice ya nufi mosque.. Ya so ya duba Huda
amman gudun kar ya makara yasa ya fita da niyyar ana idarwa zai dawo ya duba ta.

Azkar kawai yayi daga nan ya fito daga masallacin. A k’ofa suka had’u da Dad
dan haka suka jera yana d’an yi mishi nasiha har suka iso gidan, Jan hankalinshi yake sake yi akan ya rik’e amana dan Allah kar ya wulak’anta matar da suka zab’a masa, ya
taushi zuciyarshi ya bata dukkan hakkin ta da kulawa wata rana zai k’aunaceta in sha Alla…

Shi dai Aslam da ‘to’ ‘in sha Allah’ kawai yake ta binshi dan ya rasa dalilin da yasa zuciyarshi taketa faman azalzalarshi akan yaje ya dubata.
Sam ya kasa sukuni ballantana ya samu ya bawa Dad d’in hankalinshi..

Da kyar ya samu Dad ya barshi ya wuce side d’inshi, bayan yace mishi “ya tabbatar sun je sun samu Granpa”, saboda ta watsapp yaji yace mishi zai nemeshi tun jiya amman har yau shiru, kar aje ko fushi yayi shi kuma har ga Allah baya so ya je ya sameshi gudun rigimarshi yake kuma bai san a wanna mataki ya saka maganar auren Aslam d’in ba gara idan Aslam d’in yaje da kanshi maybe abun yazo da sauk’i.

Da ‘to’ Aslam ya amsashi, sannan suka yi sallama ya wuce side d’inshi
yana dariya da mamakin Dad d’in
k’iri k’iri ya hango tsoro a tartare da shi, wato sun yi abu amman kuma suna tsoro shine bara su tura shi.
Da wanna tunanin ya Isa bakin k’ofar d’akin da Huda take ciki ya d’anyi knocking sannan ya murza handle d’in da niyyar turawa amman k’ofar sai ta k’i motsi, a hankali yad’an sake yin knocking amman still yaji shiru.
Yayi mata knocking yafi sau biyar amma yaji shiru dan haka ya d’an sassauta murya ya matsar da fuskarshi jikin k’ofar ya fara kiran sunanta.

A take gabanshi ya yanke ya fad’i! Dan in dai kunnuwanshi sun ji mishi dede to kamar sheshshek’a da jan numfashi yake jiyowa yana tashi daga d’akin!

Da mugun sauri ya koma d’akinsa ya d’auko spare key sannan yazo ya zura ya murza ya tura da sauri ya shiga.

A k’udundune ya hangota a kwance tana rawar sanyi. Da sauri ya k’arasa ya d’agota ya zaunar sannan ya fara shafa goshinta wanda ya ji ya d’auki zafi ba na wasa ba. A firgice yake kallonta, gabad’aya ta jik’e da gumi kamar an watsa mata ruwa, pillow ya jawo ya kwantar da ita sannan ya mik’e ya nufi toilet ya jik’o towel ya fito.

Hannuwanta da tafin k’afarta sai saman goshinta ya shiga shafawa towel d’in amman kamar k’ara mata zazzab’in ma yake yi dan haka kawai yamik’e ya je d’akinsa ya d’au waya ya kira Doctor tukunna ya dawo ya ci gaba da goga mata… ji yake kamar yayi kuka gani yake yi duk laifinshine dan inda a d’aki d’aya suke da tun farkon zazzab’in nata zai yi noticing ya san abun yi…..

A hankali ya ga tana bud’e idonta, da sauri ya matso yace “sannu ya jikin?”

A hankali ta shiga motsa bakinta a lamun magana take son yi..

Hannunshi yasa a a gefen kumatunta yana kallonta kafin yace “me kikeso? Tell me.

Yanzu Doctor zai zoo kin ji, sannu” ya k’arashe maganar a hankali yana kallon bakinta da take k’ok’arin yin magana..

Murmushi ya ga ta fara kafin yaji tace
“Ya Arshaad! yaushe ka zo? Ina ka tafi ka bar ni?”Tana mai kallon cikin idanunsa.

Da sauri sannan da mugun k’arfi Aslam ya runtse idanuwanshi.

Magana take yi amman ba ya fahimta, babu abunda yake iya ji sai Ya Arshaad’ d’in da take ta ambata a duk k’arshe ko farkon maganarta!

Ya so ya zauna ya cigaba da shafa mata jik’akk’en towel d’in a samu fever d’inta ya sauk’a amman sai ya kasa!
A hankali ya mik’e tsaye daga kan gadon yana ganin dishi dishi…,

Ji yayi kawai ta fashe da kuka
sannan ta fara k’ok’arin ruk’o hannunshi, cikin kukan tace “Dan Allah kar ka tafi, mu zauna a cikin mafarkin nan da nake yi ni da kai har abada, kar ka tafi ka barni
bana so in farka idan kuma zan farka to sai ka yi min alk’awarin zaka dawo gar….”

Wucewa yayi da sauri ya fice a d’akin ya barta nan tana ta faman surutai..

Da kyar ya iya kai kanshi d’aki
yana zuwa ya dafa bango da d’ayan hannunsa d’ayan kuma ya dafa goshinsa yana jin yadda zuciyarshi take harbawa da tafarfasa tamkar zata fashe! Sunayen Allah ya hau karantowa sannan ya fara k’ok’arin controlling kanshi. Tabbas ya san zafin zazzab’i ne ya sanya ta take
hallucinating amman hakan bai hanashi jin kamar zai mutu ba!
Da kyar ya samu ya zaro waya ya kira Mommy yace mata “ta zo Hudan bata da lafiya”. Daga nan ya lallab’a ya koma bakin gado ya zauna ya jingina bayanshi a fuskar gadon ya lumshe idanuwanshi.

Kamar yadda su Umma suka tsara!
Yau da sassafe k’arfe 7:00 na safe Anty Zainab ta biyo mata suka kama hanya.
Tafiyar awa uku ce ta kaisu d’an k’aramin k’auyen da za su je wanda tsaf In ka tsaya zaka iya k’irga gidajen wajen kaff d’insu. Wani gida isolated a chan nesa suka nufa, a dai dai hanyar gidan akwai wata y’ar majalisar wasu matasa a k’asan wata k’atotuwar bishiyar mangoro dai dai suna zuwa za su wuce wani a cikinsu yace
“Ga wasu b’atattun yau ma sun zo”
Sarai sun ji saa ba wannan ne a gabansu ba dan haka suka wuce suka yi cikin gidan….

Sai da suka d’an jirashi ya karya sannan ya samu damar ganinsu. Suna shiga suka nemi waje suka zauna.

Da kyar Umma ta iya ce mishi “Ina kwana” Bata jira amsawar shi ba
ta hau zuba. Har da cewa da ya san ba zai yi aikin ba tun jiya da bai ce ta k’ara mishi kud’i ba! Sai da Anty Zainab ta d’an zungureta tukunna aka samu ta yi shiru.

Gyaran murya Anty Zainab d’in tayi sannan tace “Ni a ganina yanzu aikin gama ya riga ya gama, tunda har ta tare. Yanzu abunda muke so shine a tabbatar da auren Jalila da shi Arshaad d’in sannan a san yadda za a yi a taimakawa Jalila ta fitar da Huda daga gidan!”

Shiruuu, mutumin ya d’ab yi ya lumshe idanuwanshi. Chaan! Ya bud’e, ya kalleta yace “Na riga fa na yi abunda zan yi! Kun tabbatar anyi auren ita Huda da shi Arshaad d’in kuwa? Dan ni gaskiya bincikena bai nuna min an yi ba.” Da sauri Umma tace “Shirme kenan! To bari kaji.
Jiya ma a gidanshi ta kwana k’arshen magana kenan. Kuma na tabbatar idan aka bincika ma yanzu haka ciki gareta!
In dai binciken tsakani da Allah za a yi”.

Murmushi kawai yayi kafin yace “shikenan. Ku d’an jira ni”. Daga nan ya mik’e ya fita. Kamar minti biyar haka ya dawo…

Wata bak’ar laya kawai ya mik’o musu bayan ya zauna Anty Zainab ce tasa hannu ta karb’a dan ita Umma in banda tura baki da kumbure kumbure ba abunda take yi. Sai da ta karb’a sannan ya ce “Ku nutsu! Ku bani dukkan hankalinku! Dan kunga wannan abun da na baku shine kankat! Amman muddin kuka yi ganganci aka samu matsala
to abun zai dawo kanku ne!
Kun amince?”

“Eh” Suka had’a baki duk su biyun.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya sake cewa “Shawara itace. Ku sake bincikawa ku tabbatar an yi auren
dan in dai basa tare kuma
aka yi wannan aikin mai zafi to
idan ya tafi bai same su ba kan ku zai dawo! Bi ma’ana auren d’aya daga cikinku ne zai mutu.”

Murmushin takaici Umma tayi
kafin tace “Mallam”. Yace “Na’am” tace “fad’a mana yadda za ayi amfani da ita kawai! Maganar tare kam Huda da arshaad suna tare.”

“To shikenan. Aikin ba mai wani wahala bane ba, ita wannan abar dana baku cikin dare za a tashi a k’ona ta k’urmus! Shikenan Ko wanne irin kalar aure aka k’ulla musu sai sun rabu! Rabuwa ta har abada, idan har kinga sun dawo sun zauna to sai dai in za a iya maida layarnan ta koma dede yadda take kafin a k’onata!. Sannan shi kuma wannan” yayi maganar yana basu wani turare kafin yace “Ita Jalilar za ki bawa ta shafa a jikinta, ta tabbatar shi Yaron ya shak’a da Mahaifiyarsa da Mahaifinsa da duk wani wanda zai iya shige mishi gaba wajen auren, in sha Allah ba za ayi awa 24 ba za a d’aura musu aure.”

Sai a sannan Umma tayi murmushi tace “sun gode” Daga nan suka d’anyi wasu maganganun ragowar matsalolinsu….

Sun d’an jima tukun suka mik’e suka fara shirin tafiya. Har suka fita Malamin nan yana ta nanata musu “su tabbatar sun yi conforming auren Huda da Arshaad kafin su yi amfani da layar na”.

Zuciyoyinmu fess haka suka fito
Umma ta karb’a kayan ta danna a jaka
suka wuce.

A gigice Mommy ta shiga d’akin Huda!
Hakan yayi dai dai da k’arasowar Doc shima. Aslam bai bari Mommy ta gansa ba, suna zuwa k’ofar d’akin shi da Doc d’in ya fara jiyo muryarta a rikice tana yiwa Huda magana dan
haka yana nunawa Doc d’akin ya juya ya koma d’akinsa.

Sai da ta sha allurai sannan aka jona mata drip tukunna ta fara gane waye a kanta.

Mommy kuwa da ta samu Huda ta d’an farfad’o sai ta hau fushi da Aslam.
Bawan Allah shi kam bai ma san tana yi ba yana d’aki yana fama.

Ita da Gwaggo Asabe ne suka yi jinya, kafin dare ta d’an warware amman ba sosai ba Sai a sannan ta samu ta kira su Mama….Lokacin ita d’aya ce a d’akin Gwaggo Asabe ta tafi kitchen
Ita kuma Mommy taje shiryawa Dad table. Ba yadda bata yi dasu ba akan su turo mata Sakina bata jin dad’in zaman ita d’aya amman sam suka k’i
suka ce “in ita bata da hankali to su suna da shi” K’arshema fad’a suka rufeta da shi Mama tayi ta gama ta bawa Ummu itama ta yi nata ta mik’awa Shuwa! Haka nan ta hak’ura ba yadda ta iya. Bata ce musu bata da lafiya ba dan karsu d’aga hankalinsu.

Mommy a d’akin suka kwana tare da
Ita da Gwaggo Asabe. Ita Huda har mamakin tattali da k’aunar da Mommy da Gwaggo Asabe suke nuna mata take yi, ko tari tayi nan
da nan hankalinsu zai tashi,
ba abunda yafi d’aure mata kai irin yadda Mommy take cika bathtub da ruwan d’umi tace ta shiga, a ranar sai da tayi mata sitbath yafi sau biyar!.
Ita dai abun mamaki yake bata har ga Allah, gashi duk da ba wai son Aslam take yi ba amma sai ta tsinci kanta da mugun kunyar Mommy da Gwaggo Asaben, sam ta kasa sakewa a d’akin.
Da kyar ta d’an samu bacci kad’an, daga nan ta farka idonta ya bushe, sam ta kasa komawa dan haka ta mik’e tayi alwallah ta fito ta d’au hijabi a cikin akwatin kayanta da tazo dashi ta tada sallah.

Shima Aslam bai samu wani isheshshen bacci ba, so
yake yaje yaga jikin nata
amma d’azu k’iri k’iri Mommy ta hanashi shiga d’akin da suka had’u a k’ofa! Kuma tak’i kulashi. Kafin ya kwanta ya kirata yafi sau nawa amman tak’i d’auka, dan haka shima da yaga ya kasa baccin sai ya mik’e ya fara jero nafilfili. A Daren ranar ne kuma Umma ta k’ona layarta! Bayan ta yiwa Jalila waya tayi mata kwatancen mansion d’in da suke ita kuma tayi
mata alk’awarin ‘gobe da safe zata zo mata ta sak’on da zai saka ta auri Arshaad’ Sannan tace mata “ta kwantar da hankalinta zata fitar da Huda a gidan in shaa Allah”. Sai a sannan Jalila ta d’an nutsu dan tun jiya da taji a wajen Umman an kai Huda gidan Arshaad shikenan ta birkice ta susuce ko bacci bata yi ba sai kuka take ta yi duk ta fita hayyacinta.
Ba k’aramin dad’i taji a ranta ba kuwa.
Haka ta kwanta zuciyarta fess
tana kwanciya bacci mai mugun dad’i yayi awon gaba da ita! Wanda ta dad’e bata yi ba.

Washegari da sassafe y’ay’an Gwaggwo Asabe su biyu suka iso, da y’an yaransu k’anana. Yadda Gwaggo Asabe take da kirki haka suna y’ay’anta. Sai a sannan Huda ta d’an sake ta d’anji sauk’i dan
a cikin wuni d’aya suka saba
ta sake sosai da su, hakan
kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa su Mommy ba.

Da yamma jikin nata da d’an kwari dan haka Mommy tace “ta shirya ta fito main parlour kar zaman d’akin ya gundureta.

Suna zaune da yamman
Huda na gefen Mommy akan kujera 3 seater a zaune ana hira a main parlour Aslam ya fito! Mommy tana ganinshi ta kauda kai gefe ta had’e rai.

Dariya Gwaggo Asabe tayi
tana tuna yadda d’azu ma yazo tayi hakan, ba yadda basu yi da ita ba amman tak’i kulashi k’arshe sai hak’ura yayi ya tafi kamar zai yi kuka..
Ita kam Huda rabon ta da shi tun ranar da aka kawota shekaran jiya
da yayi mata sai da safe ya fita bayan ya kawo mata kaji.

Gefen Mommy yazo ya zauna ya kamo hannunta ya b’ata rai kamar zai yi kuka. Bata kula shi ba bata kuma kwace hannunta ba amman ko kallon inda yake bata yi ba.

Yaran Gwaggo Asabe Karima da Laurat ne, Suka hau tsokanarshi dama sun saba. Daga nan kuma aka hau gaggaisawa Karimar Yaranta uku maza itace Babba sai Laurat tana da twins y’an biyu mace da Namiji.
Aslam yana mugun son Yara dan haka ya sake yayi ta wasa da Yaran sunata yi mishi surutunsu na shirme.

Da ido Gwaggo Asabe tayiwa Huda sign bayan sun had’a ido. Duk sai taji kunya ta rufeta, ita tama manta ashe basu gaisa ba! A hankali ta d’an kalleshi kafin tace “Ina wuni”
Sai da ya ajjiye k’aramin Yaron Karima akan kafet sannan ya juyo yana kallonta yace “Alhamdulillah, ya jikin?” Sunkuyar da kanta tayi kafin tace “Alhamdulillah”

Hannun Mommy da yake a cikin nashi yad’an damk’e kafin yace “Mommy bara mujewa Granpa”

Bata kula shi ba. Hakan yasa ya mik’e tsaye yana mai sakin hannun nata yana murmushi kafin ya cewa Huda
“D’auko hijabin ki mu je”

Juyawa tayi ta d’an kalli Mommy.

Muryar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa “ku je mana. Yi maza ki d’auko hijabin.”

Ko da ta fito parlourn bata same shi ba, Gwaggo Asabe ce tace mata “yana compound” “To” tace sannan tacewa Mommy “yace za mu fita” Sai a sannann Mommyn tace, “A dawo lafiya” Tana ji gabanta yana fad’uwa!
Dan bata san ya had’uwar Huda da Granpa zata kasance ba.

Su Karima ta juya ta cewa “sai ta dawo” da Gwaggo Asabe sannan ta sa kai ta fita.

A tsaye ta hango shi chan bakin gate dan haka ta k’arasa. Tunda ta taho ta lura da irin kallon da yake yi mata
har ta k’araso inda yake ta tsaya.

Sai da suka yi kusan 1 minute ba wanda ya motsa a cikin su
kafin yace “Jikin da sauk’i sosai ko?”

“Um” Kawai tace mishi
dan ita haushima ya bata meye nashi na wani nanata tambayar! Bayan already ya riga ya tambayeta tun a ciki.

Yana so ya tambayeta ko akwai abun da take buk’ata amman ya lura kamar bata son yawan maganr tasu dan haka ya rabu da ita kawai, ya ce “muje” yana mai juyawa.

A jere suke tafiya gwanin burgewa. Har suka k’arasa gate d’in gidan Granpa. Cikin girmamawa mai gadin ya bud’e musu gate d’in suka wuce bayan ya gaidasu.

A k’asa Aslam suka tsaya ya kira Granpa ya bashi izinin hawa tukunna suka hau! Gaban Huda na dukan uku uku..

A chan sama suka sameshi,
Parlournsa! Yana zaune a kan kujera ya baza takardu yana dubawa…

Tunda suka shigo ya d’ago ya kafe Huda da ido! Hudan kasa k’arasowa tayi sakamokon yadda fad’uwar gabanta ya tsananta saboda yadda taga Granpa ya kafeta da ido. Har Aslam ya kusan k’arasawa inda yake sai kuma yaji kamar bata tare da shi dan haka ya juya. A chan farkon parlourn ya ganta tsaye ta sunkuyar da kanta.

Granpa ya kalla sanan ya juya ya kalleta, d’an lumshe idanunsa yayi ya bud’e tukunna ya koma ya je inda take a tsaye, bata yi auni ba kawai taji ya kamo hannunta!

Da sauri ta d’ago zata yi magana taga ya tsareta da kyawawan idanuwanshi,
a hankali taji yace “Muje mana” still yana kallonta sannan da kyar ya samu ya iya zare idanuwanshi a nata ya juya ya fara tafiya…

Tsintar k’afafuwanta kawai tayi suna takawa suna binshi. Sai da suka k’arasa gaban Granpa sannan yace mata “ta zauna” Shima ya ja ya zauna a kan kafet.

A hankali yace, “Granpa Good afternoon.” Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya ce , “Ya aiki? Ya sabon company?”

A hankali Aslam d’in yace mishi
“Alhamdulillah, komai Alhamdulillah.”

Juyawa Granpa yayi ya kalli Huda kafin yace mata. “You can leave now!
Na riga na san an yi aurenku da Aslam ba tare da consent d’ina ba! So ki je kawai ki jira sakamokon ki.”

Da sauri Aslam ya d’ago idanuwanshi ya zuba mishi, zai yi magana Granpa ya d’aga mishi hannu, cikin d’an karaji ya cewa Huda. “Leave! Kar In sake ganin ki a nan.”

Jikinta na wani irin mahaukacin rawa ta mik’e, da sauri Aslam shima ya mik’e ya kamo hannunta sannan
ya juyo yace “Granpa matata fa na kawo maka..”

Cikin katse shi yace, “Aslam ba zan tab’a yarda da wannan auren ba!
Tun jiya nake expecting d’inka,
i have a lot to discuss with you.

Despite da fact that an yi auren ba tare da consent d’ina ba. I can’t believe Yahaya da Aisha suna da guts d’in kwasota ita da y’an kawota su kawo mini cikin estate! Ranar ina ji har wajen 12am ana yi min shige da fice a estate.

You are very naive Aslam ba ka san halin mata ba. Ni na san Maryam itace zata k’ullawa Yakubu shi kuma yayi taking advantage d’in innocence d’inka ya mak’ala maka useless daughter d’insa.”

Da k’arfi Aslam ya ce “Grandpa!!!!”

K’ura masa ido Granpa yayi na kusan 1 minute haka shima Aslam d’in! Shi kanshi Granpa yayi mugun mamakin b’acin ran da ya hango a cikin idanuwan Aslam d’in…
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya janyo sandarshi ya dogara ya mik’e tsaye ya tako gaban Aslam wanda yake rik’e da hannun Huda yace “Allah ya isa tsakanina da Maryam!”

Wani mugun kuka Huda ta fashe dashi ta fara k’ok’arin zare hannunta a cikin na Aslam amman gam! Ya rik’eta
as if his life depends on her hands…

Sam Granpa bai damu da
kukan nata ba yaci gaba da magana
“I loose Yakubu because of her
and now I think I’m going to loose you
duk a ta dalilinta! In banda tsabar rainin hankali taya ya za a d’aura maka aure da y’arta tashi d’aya babu shirin babu sanarwa a cikin rana d’aya? Ya akai aka fasa d’aurawa da Muhammad? Anyways ba ni da intrest d’in sauraron bayanin kowa, zab’i ne kaima zan baka kamar yadda
na bawa Yakubu. Mun riga mun gama magana ni da Maryam 30 years ago akan babu ita babu family d’ina!
So ba zan tab’a chanja decision d’ina ba Ni matter who gets in the way
Idan zan zama ni kad’ai a duniyar nan to zan rayu muddin kuka ce bayan maryam za ku bi ba zan damu ba
I can survive alone.

Yusuf da Yakubu sun zab’a abunda suke so, yanzu kai ya rage! Duk da kuwa Ina matuk’ar jin ciwo da zafi saboda Aslam kaine backbone d’in family d’ina kai ne na fi ji da a kaf cikin zuri’ata! Na san ka san da hakan
amman hakan ba zai hanani ce maka
‘Ba zan tab’a accepting matarka a estate d’innan ba! Sannan within 4 hours ka fitar min da ita tun kafiin bad luck d’in Maryam ya shafi zuriata’ ba.”

Nannauyar ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin ya ce “Granpa! Gaskiya d’aci ne da ita.. Abunda kake yi is not right. No matter how yo try fa
wallahi ko ta ina aka bi aka zagayo sai an samu jininka a jikin Huda! Da ita kanta Anty maryam d’in you can never change that.”

Da k’arfi Granpa ya ce “Shut up!!”

Bai yi shiru ba yaci gaba “Idan kace babu ruwan ka da Anty Maryam ba zaka tab’a cewa ba ruwan ka da Huda ba tunda jikar ka ce y’ar gidan Abba!
Ba yadda zaka yi dole fa tana cikin zuriarka itama.”

Cikin b’acin rai yace “Aslam I’m warning you, keep quite!!!”

Still bai yi shirun ba ya ci gaba “You need to wake up! Ka cire hatred a cikin ranka, Anty Maryam ta rigada ta shigo cikin rayuwarka cikin zuriarka cikin family d’inka ta yi dumu dumu babu yadda za kayi idan har kuwa kace zaka tsameta to tabbas zaka yiwa wannan family d’in babban gi’bi! The sooner you accept that the bett…”

Tassss! K’arar marin da Granpa ya d’auke Aslam da shi ya karad’e ilahirin makeken parlourn.

Tsit!! Haka parlourn yayi shiruuu, hatta kukan Huda d’aukewa yayi.

Shafa wajen da aka mare shi yayi kafin ya d’ago da jajayen idanuwanshi yace “kar ka damu Nan da 4 hour zan fitar da matata daga eatate d’inka in sha Allah Granpa.”Yana gama fad’in haka ya juya ya ja hannun Huda suka nufi k’ofa. A bakin k’ofar suka ci karo da Gramma da wasu books a hannunta..
Kallon ta kawai Aslam yayi, ba tare da yace komai ba ya kauce ya ja Hudan wadda take ta faman kuka suka fice
dan sam ya kasa ma yin magana kuma ga dukkan alamu Gramma ta ji komai.

Basu tarar da kowa a main parlour ba dan Magariba har tayi, sai da ya kaita d’akin da aka ajjiye ta tukunna ya cika mata hannu yace, “D’auki abunda kike buk’ata mu tafi”. Cikin kuka tace
“Ina?” Kallonta yayi ya d’auke kai yace
“Ki d’au abunda kike buk’ata nace!”
Still tana kuka tace “Ya Aslam ba inda zan bika fa! Infact kawai ni ka maidani wajen Mama! Kar kaje kaima ka samu matsala da Granpa.” Ba tare da ya kalleta ba yace “Hudan for the last time! Ki d’au abunda kike da buk’ata
If not zan jaki mu tafi empty handed.”
Ya k’arashe maganar yana mai juyowa ya kalleta. Kallon shi tayi still shima itan yake kallon cikin muryar kuka tace “Babufa inda zan je da kai!
Ka maidani gidan Mama in yi rayuwata a chan”

Cikin b’acin rai ya k’araso inda take kamar zai maketa yace “Ba ki da hankaline? Da auren nawa akan ki zan maidake gidan Maman da suka kawoki nan shekaran jiya jiya?!”

Cikin kuka tace “Ai ba auren gaskiya bane ba! Besides daman ni ina so ince maka ka sakeni! Ya Aslam baka sona nima bana sonka! Ba zan iya wannan zaman ba. Su kansu su Abba a wannan karon basu k’ulla abunda zai yiu ba!
So kawai mu nemawa kanmu mafita kayi hanyar ka in yi tawa, ka samu ka zauna lafiya da Granpa.”

Aslam bai san lokacin da ya kamo kafad’unta ya manna ta da bango ba
cikin tsananin b’acin rai yace . “Ni kike cewa in sakeki! Eh?” Ya k’arashe tambayar cikin tsawa. Daidai nan Mommy da Dad suka shigo. Da sauri Mommy ta k’arasa ta kwace Hudan wadda ta fara galabaita daga ruk’on da yayi mata tana jera mata sannu. Cikin tsananin b’acin rai ta d’ago bata yi wata wata ba ta d’auke shi da wani gigitaccen mari. Daidai nan Abba da Daddy suma suka k’araso, har da
Auwal wanda ya tuk’o su.

Da sauri Abba ya k’araso yana cewa
“Haba Mommy, me yayi haka?”
Daddy ma k’arasowa yayi yana tambayar “me yake faruwa?”

Bata amsa kowa daga cikin su ba ta wuce ta fita daga d’akin.

Ganin Aslam d’in yak’i kula su ya sa Abba ya k’arasa wajen Huda da take ta faman kuka ya janyota ya rungume ya shiga lallashinta. Da kyar aka samu tayi shiru.

Tukunna Dad yace “Gramma ce ta kira ku kuma?” “Eh” kawai Abba yace
still yana rik’e da Huda.

Daddy ne ya dubi Dad kafin yace
“Bara mu tafi da su kawai Za mu san abun yi daga nan”

Da sauri Aslam yace “A’a Dad.
Ina da gida a nan. Za mu tafi kawai kar ku damu.” Dafa shi Abba yayi, sai da ya juyo ya kalleshi tukunna yace mishi
“Muje ko Aslam, kar ka yi gardama.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 56So Da Buri 58 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×