Lumshe idanuwansa yayi kawai ya bud’e daga nan ya juya ya fita ba tare da yace musu komai ba. Direct sama d’akin Mommy ya wuce.
A tsaye ya sameta tana ta faman safa da marwa. Tana juyowa suka had’a ido, cikin b’acin rai tace “Juya ka fita Aslam, ba na son ganinka!
Juya ka fita na ce. Anya Aslam kana son Yarinyar nan kamar yadda ka fad’a kuwa?”
Bai fitan ba, ya k’araso inda take kawai yayi hugging d’inta.
Sai da ta tsorata da jin yadda jikinsa yake rawa. Da sauri ta sa hannu ta d’ago sa, suna had’a ido yace
“Mommy cewa fa tayi in saketa!!”
Kallonsa tayi na some minutes kafin tace, “Shiyasa kake neman illatata?
Are you okay kuwa?.
Na san Huda matarka ce but duk da haka duba da abunda ka yi mata shekaran jiya ana kawota sannan kasa kai ka fita ba tare da ka bata kulawar da ta kamata ba! Sannan d’azu kalli fa yadda ka buga ta da bango kuma kana ganin yadda ruk’on da kayi mata yake neman cutar da ita but baka damu ba!
A gaskiya Aslam hakan ya sanya na fara kokwanto fa, dan inda ace son gaskiya kake yi mata ai at least ka iya jira ku d’an saba tukunna kafin komai
amman ga wahalar biki da ta zuciya sannan kai kum…” Da sauri yace “Haba Mommy” Sai kuma ya sunkuyar da kanshi k’asa yana ji kamar k’asa ta tsage ya shiga. Kamar zai yi kuka yace
“Wallahi ba abunda nayi mata. Ba ma a d’akin na kwana ba ranar..” Kasa ci gaba da tsayawa a gabanta yayi dan haka kawai ya juya yace “Mun tafi” daga nan yayi sauri ya fita.
A hankali Mommy ta fara smiling..a take ta ji zuciyarta ta yi sanyi. Tabbas soyayyar shi ga Huda da ta dasawa aya gaskiya ce! Dan haka ta bisu da fatan alkhairi, amma duk da haka zata kora mishi warning akan kar ya sake attempting abunda ta ga yayi mata d’azun.
A mota ya tarar da su Dad dan haka shima ya wuce tasa ya shiga suka nufi gate Gwaggo Asabe da su Karima suna d’aga musu hannu har suka fice.
Kamar su jawo Huda su hanata tafiya haka suke ji amma duba da yadda su Dad d’in suke kamar a d’an firgice yasa suka bari akan za su tambayi Mommy idan ta sauk’o.
Ba yadda Aslam bai yi ba akan su bari Huda ta zauna a side d’in Daddy ba amman furr suka k’i amincewa. Gashi daga k’arshema Dad d’in cewa yayi shima sai dai ya koma gidan da zama dan ba zai barta ita kad’ai ba. Kamar yayi kuka, saboda duk sun bi sun d’aureshi da jijiyoyin jikinshi ta ko’ina, haka nan ya hak’ura kawai akan zai zauna a nan d’in ba dan yana so ba sai dan babu yadda ya iya.
Jalila, tana garden lokacin da suka shigo. Ganin motoci ya sanya tayi sauri ta shige kitchen ta lab’e a jikin window tana hangen su tana jin su. Allah kuwa ya taimake ta suka yi parking a kusan windown side d’in kitchen d’in Daddy,
dan yana kusa da main k’ofar shiga side d’in Abba.
Tabbas! Idan har kunnuwanta sun jiye mata dede tou kuwa Huda da Aslam mata da miji ne! To amma tayaya hakan ta faru? How??… Gabad’aya kanta ya kulle. Tana cikin wannan taradd’ad’in ta ji Auwal ya shigo suna magana shi da Mom, da sauri ta koma jikin k’ofar ta lab’e.
“Wai nan suka dawo?” Taji muryar Mom. “Yeah, Granpa ya sake yin what he is really good at!” Taji Auwal d’in ya bata amsa.
Da sauri Mom tace “To kuma ai Daddy ya ce min shekaran jiya da safe sai da suka tura mishi sak’o bayan d’aurin auren Huda da Aslam d’in, ya ce musu ‘okay’. Mai ya faru yanzu kuma?”
Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e kafin yace, Mom ce musu fa kawai yayi ‘okay’ Dama ni na san akwai case a k’asa!. Mammy ita ta lalata komai wallahi, da ace ta bar Arshaad ya auri Hudan cikin sauk’i da duk haka bata faru ba. An yi miki magana kema akan ki ganar da ita amman da yake ba k’aunar Huda kike yi ba shiyasa kik’ak’i ki ce komai! Kuma still gashi dai Hudan surukarku ce kuma y’arku!
Dan abunda yayi Abba shi yayi su Dad
Kuma abunda yayi Arshaad shi yayi Aslam dan haka kinga babu riba kenan sai dai sake tarwatsa family ma da kuka yi dan yadda Granpa ya rufe ido ya gurzawa Aslam to wallahi kowa ya kuka da kanshi.” Yana gama fad’in haka ya wuce ya nufi side d’insa.
Tunda Mom take a estate d’in nan bata tab’a jin farin ciki irin na wannan ranar ba! Dan har goshinta ta saka a k’asa tayi sujjada bayan wucewar Auwal… Arshaad ya gudu Aslam kuma sun yi fad’a shi da Granpa in sha Allah
she‘ll make sure it stays like this har izuwa lokacin da za a mallakawa Auwal d’inta MT!..
A b’angaren Jalila kuwa ba k’aramin k’ok’ari tayi ba wajen hana kanta kurma Ihun murna! Bayan ta doka wani uban tsalle, sannan ta fara juyi tana tik’ar rawa.
Sai da ta lek’a taga Mom bata parlourn tukunna ta fito tab wuce d’akinta a ranta tana “Wato idan kana da uwa a duniyar nan ba wanda ya kaika gata!”.
Tana shiga d’akin bata yi wata wata ba ta d’auki wayarta ta fara kiran Umma.
Tana d’aki a zaune tana goge wa Ya Ja’afar jiki kiran Jalila ya shigo…
D’auka tayi ta saka a speaker ta ajjiye a gefe, za ta cigaba da abunda take yi.
Ko gaisuwa babu Jalila tace
“Ummana albishirinki”
Da sauri ta ajjiye towel d’in hannunta ta d’au wayar jiki na rawa tace
“Goro” Nan Jalila ta shiga zayyano mata kaff abunda taji ta gani yanzun nan Shiruuu, Umma tayi, tana shirin yin magana ta yi an shigo ana kuka.
Kamar an hankad’o Anty Zainab haka ta shiga d’akin a hargitse kamar mahaukaciya! A gigice Umma take kallon ta, sai da ta bari ta nemi waje ta zauna tukunna tace “Zainab lafiya kuwa??” Cikin kuka tace
“Ba lafiya ba! Sadiya na shiga uku!!”
Da sauri Umman tace “subahanallah mai ya faru?” Ta yi mata tambayar tana me d’aukar wayar ta kashe ta ajjiye a gefe.
Da kyar Anty Zainab ta d’an tsayar da kukanta tace “saboda Allah tsofai tsofai da ni amman wai ni Baban Khadija ya rufe ido ya dank’ara wa saki har uku! Saboda tsabar idonshi sun rufe ya ma manta da biyun da ya tab’a yi mini”.
Da mugun k’arfi gaban Umma ya yanke ya fad’i! Saboda lokaci d’aya kwakwalwarta ta d’auki chaji
Tabbas ita ce ta tafka kuskure abun kuma ya koma kan Anty Zainab! Wadda daga rakiya gashi yanzu ta janyo mata. Tana cikin wannan tunanin Anty Zainab d’in ta sauk’o ta matso kusa da ita kafin tace “Yi maza Sadiya d’au waya ki kirawo Jalila mu ji…Anya kuwa an yi auren nan? Ko dai zurma mu su Maryam suka yi?
Dan wallahi masifarnan tana fad’omin maganar Malamin nan na jiya na tuna.
Yi sauri Sadiya ki kirata mu ji, ta bincika mana sosai.. In dai maganarshi gaskiya ce to mu samu mu koma mishi
a san abun yi tun da wuri! Kin ji Sadiya! Dan Allah kirawo ta mu ji……”
Cikin In Ina Umma tace “Tt ta tam!
Amman d’azun nan ma mun yi waya da ita kuma ta tabbatar min da cewa an yi auren.”
Hannu biyu Anty Zainab ta d’aura a kai kafin tace “Innalillahi wa innailaihirrajiun Me ya faru da ni tou???”
Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e jikinta na rawa tace “To wai ke me ya had’a ku ne?”
Cikin kuka Anty Zainab tace
“Aure wai mutumin nan zai yi!
Yarinya k’arama dan tsabar cin fuska shine bai gaya min ba, sai d’azu tukunna Baaba Talatu ta kirani take gaya min, ashe wai ita sun sani ita da Shuwa shine suka b’oye min wai dan kar in d’aga hankalina inzo inyi wani shirmen, Sadiya abunda zai baki mamaki wallahi tallahi kawai zuwa nayi nace mishi ‘Ya zai yi min haka?
Me yasa ya b’oye min? Ai da ya gaya min tun da wuri’.
Kar ki k’ara kar ki rage daga
haka kawai sai ya hau masifa,
k’arshe yace In tattara in tafi ya sauk’e igiyoyinsa na aure kaff ukun da suke a kaina! Wai ya san in dai amaryar tasa tazo ba zan barta ta zauna ba.
Ko kayana bai barni na kwasa ba da magariba dan bala’i ko kwana bai bari nayi ba ya kad’oni har da rufe gidansa.
Ita kuma Baaba da na je mata daga jin magana bata tsaya taji ba’asi ba kawai
ta hau fad’a! Wai ai laifi na ne, daman shiyasa suka k’i gaya min, ai ba a kaina Miji ya fara k’are aure ba, ai yanzu gashi na janyowa su Sadik haka
yanzu zai dawo daga boarding ya tarar ba Maman shi a gidan.
K’iri k’iri Yaro ko secondary school bai gamaba amma ina k’ok’arin maidashi maraya, har su Khadija ma da suke gidan Miji sai ta shafesu…
Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, k’arshe ma ko zama bata barni nayi ba itama ta koreni!” Da sauri Umma tace “Yanzu kenan a nan za ki zauna?” Cikin share hawaye Anty Zainab tace “To ya zan yi? Ina zan je?
Port harcourt ko Ina?”
Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin tace “Ki kwantar da hankalinki, zai mayar da ke, kin ji ko, In sha Allah.”
Cikin kuka Anty Zainab tace “Baban Khadija fa babban d’an ka’ida ne ke kin sani ba zai tab’a bari mu zauna da saki ukun nan ba”
Cikin yin k’asa da murya Umma tace “Ki kwantar da hankalinki, za mu nemi mafita In sha Allah.
Sannan ko hauka muke ba zamu bar auren nan ba yasin sai dai in me taurin ruhi ce kamar Maryam wadda ta nace sai da kyar! Tukunna aka samu ta bar gidan nan, to kinga idan irinta ce ba yanda muka iya dole mu barta amman shima sai mun ci ubanta wallahi.
Maza basa kyautawa wallahi sam! Saboda Allah Ina ma lefin ya d’auko miki mai d’an shekaru. Fisabilillahi Ina Baban Khadija Ina sa’ar su Khadija?Tsofai tsofai da shi.”
Da sauri Anty Zainab tace “Kuma budurwa!”
Cikin karb’e zancen Umma tace “Ba zai ma yiu ba fa Wallahi! Dole mu san abun yi.
Ki kwantar da hankalin kar ki saka damuwa a ranki, zamu nemi mafita.
Bai isa ba wallahi, kin ji.
Su Shuwan nan suna bani mamaki, daga an yi magana suce wani wai kar mutum yayi shirme in za ai mishi kishiya waye waye
Bayan su basu san zafinta ba!
Tunda duk cikinsu babu wadda Mijinta ya tab’a yin koda budurwa ne a waje, sun kafa sun tsare nasu mazajen amman sun iya tak’ark’arewa suna yiwa mutum nasiha akan kishiya tsabar renin wayo
Su bar waenda suka san zafin kishiya
su yi magana mana ba wai su tsayayyun matan da suka kafe mazajensu ba…”
Ita dai Anty Zainab mik’ewa tayi ta isa kan gado ta kwanta ta juyawa Umma baya, dan taga abun nata kamar ya fara zama cin fuska kuma. Tana jinta tana ta bambami daga k’arshe ta yi shiru ta gyarawa Ya Ja’afar wanda yayi bacci kwanciyar sa ta lullub’e sa tazo ta nemi waje gefen Anty Zainab itama ta kwanta. Ta gama rayawa a ranta gobe zata koma wajen mutumin nan tayi masa maganar Anty Zainab asan abun yi dan gaskiya tayi mugun tausaya mata. Amman kuma abunda yasa tayi shiru bata gaya mata gaskiyar lamarin yanzu ba shine
ta lura aikin mutumin kamar yakan iya juyewa kuma waiwaye! Tunda gashi na Huda ya koma kan Anty Zainab d’in , duk da ya fad’a musu dama amma still kamata
yayi ace aurenta da Aslam ne ya mutu ba wai na Anty Zainab ba tunda de Hudan aka yiwa abun so it doesn’t matter ko waye Mijin nata ita ya kamata a sako.
Kanta ya kulle dole ta koma wajenshi amman ba zata bari suje da Anty Zainab ba dan yadda take a rikicen nan haka kurum taje ta tunzura mutumin yayi mata nata aikin aje garin gyara nata a tab’o na Jalila da bai gama had’uwa ba. Ko da ace zata gaya mata Hudan ba Arshaad ta auraba to sai ta tabbatar Mutumin ya gama yi musu aiki mai kyau! An d’aura auren Jalila da Arshaad ta kamashi sosai ta samu fada a wajenshi tukunna, saboda kar aje aiki ya had’a masa biyu yak’i concentrating akan na Jalila sosai, ko kuma kuma yaje ya gyara na Anty Zainab wani abun ya samu na Jalila….
A ranar dai haka suka yi bacci duk su biyun rabi da rabi.
Su Hudan suna shiga a parlourn suka tarar da Ummi da su Shuraim sunata shirya dining tare da masu aiki.
Ummi tana ganinsu ta k’arasa inda suke tayi hugging Hudan tana mata sannu da zuwa. Cikin girmamawa suka gaisheta ita da Aslam, ta amsa musu da kulawa, daga nan
suka gaisa da su Sudais,
murna kuwa a wajen su kamar suyi me tunba ma da suka ganta har da akwati ba’. Su suka ja mata suka kai mata har d’aki Abba yaso su zauna a sama amman Aslam yace “a barsu a d’akin bak’i” shi da cewa ma yayi ita akai mata nata kayan sama shi a barshi zai zauna a d’akin bak’i, shiyasa kawai Abban yace “a kai mata akwatin ta nan d’akin bak’in”.
Ita dai Huda so take tace ‘a barta ta tafi d’akinta’ amman bata san ta ina zata fara ba! Ta san a idon duniya da su Abba Aslam mijinta ne amman taya ake expecting tayi sharing d’aki da shi bayan ga d’akuna birjik kala kala a gidan.
Su kuwa su Daddy dama tun kafin su fita daga gidan bayan Gramma ta kirasu suka gama deciding akan zasu san yadda za suyi su taho nan gidan ita da Aslam d’in daga nan kuma su ajjiyesu shi da Hudan a waje d’aya, dan sun lura tabbas sai sun d’an taka rawa a relationship d’in nasu tukunna za a samu su ma fara magana mai tsayi da hira a tsakaninsu.
Abba ne ya umarcesu da su je su yi alwala ayi sallah kafin ayi dinner.
Hudan so take su had’a ido da shi amman bata samu wannan damar ba. Abba kuwa sarai ya ganta shiyasa ya maida hankalinshi gaba d’aya kan Dad suka shiga hira.
Ganin ta a tsaya ne ya sanya Ummi ta k’araso inda take ta rik’e mata hannu tana murmushi kafin tace “Muje to nan d’inma in rakaki. Naga kin tsaya.
Aslam muje In taka ma Amaryar taka, kunyar mu take ji naga alama”
Juyawa kawai yayi ya fara tafiya. Ita kuma Ummi ta ja hannun Huda suka nufi d’akin..
A bakin k’ofar bayan taga shigewar Aslam ta ja ta tirje sannan ta kalli Ummi kamar za tayi kuka tace
“Ummi wai nima a nan d’akin zamu zauna kuma ni da shi?”
Dariya sosai ta bawa Ummin amman sai ta dake ta d’an b’ata rai kafin tace
“Eh mana! So kike ya zauna shi kad’ai?
Wa zai dinga gyara d’akin yana wanke band’aki? Ko so kike a dinga tura mishi su Linder suna shigar masa anyhow?”
Da sauri tace “Ummi zan dinga zuwa kullum da safe ina mishi Allah”
B’ata rai sosai Ummin tayi this time around kafin tace “Zamu b’ata da ke fa! Dole anan zaki zauna Huda.
So kike idan yana buk’atar wani abu urgent sai ya nemoki kenan? Kinga, gara ki shirya fa dan hatta girki ma sai kin dinga yi masa nashi special
ko da kala d’aya ne Breakfast Lunch da Dinner Kullum! Ko kin d’auka auren wasa ne?”
Tabbas ta san da waennan abubuwan dan sai da Shuwa ta tsara mata komai amman ita dai a tunanin ta su Ummi da Abba zasu d’aga mata k’afa tunda ai ba shi takeso ba kuma sun sani. Wani k’ululun takaicine ya tokare mata mak’oshi! Tayaya ma za ace saboda zata dinga yi mishi aikace aikace da abubuwa har wani kuma sai ta zauna da shi a d’aki d’aya dole! Sai kace wani baby.
Ji tayi Ummi ta ja hannunta sun shige d’akin sannann ta mayar a k’ofar ta rufe. Sai da ta kaita kan gado tukunna tace “Ki yi sallah ku fito dinner”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin.
Naji dadin labarin sa da buri