Skip to content
Part 63 of 73 in the Series So Da Buri by Bulama

Murmushi Arshaad ya yi kafin a hankali yace “Ummi, na same ku lafiya?”

Sai a lokacin Ummin ta yi laakari da yadda bashi da lakka a jikinsa da kuma tsananin ramar da yayi.

“Alhamdulillah” tace, sannan ta d’aura da cewa “where have you been?”.

Still yanzun ma murmushi ya sake yi, a hankali ya ce “Bara in d’an huta”. Ya fad’i hakan yana mai wucewa ya shige cikin parlourn, wanda sai da ya zo wucewar ne tukunna Ummi ta lura da akwatin da yake tafe da shi! Gabanta ne taji yad’an buga! Gashi babu damar ta tsayar da shi ko ta hanashi wucewa, a k’asan ranta tace “Anya kuwa zaman su Aslam da Arshaad zai yiu a waje d’aya?…” Tana cikin wannan tunanin ta jiyo ihun Hudan! Dakatawa Arshaad yayi ya juyo ya kalleta kafin yace “Kamar muryar Huda..”

Shiruuu, Ummi ta d’anyi, chaan kuma ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya
tace “Eh, suna nan, Granpa refuse to accept them” Ya bud’e baki kenan zai yi magana suka sake jiyo ihunta a karo na biyu. Ita Ummi har ga Allah tayi tunanin wani abun ne ya sameta dan batayi zaton Aslam d’in ya dawo ba! Shiyasa tayi saurin nufar d’akin, ba tare da b’ata lokaci ba shima Arshaad ya bi
bayanta da sauri.

NOW.

Wardrobe d’in a setin k’ofar yake a ta tsaye! Shiyasa suna shiga suka gansu…

Da mugun sauri Arshaad ya juya Ummi kuwa da kyar kunya ta barta ta iya jan y’an k’afafunta ta bar wajen.
Ko kyallin Arshaad bata gani ba, ga de akwatinsa nan a tsakar parlourn inda ya barshi…

Wucewa tayi sama da sauri dan ji tayi kamar za a bud’e k’ofar d’akin su Hudan a fito.

Achan d’akin kuwa su Ummi suna fita Huda tasa kuka! Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin Ya Arshaad wanda suka had’a ido dashi! Shikenan ta san yanzu zai ce taci amanar sa ta gama! Bayan ko sati uku ba ayi da yin bikin ba. Shiruu, Aslam ya d’anyi yana kallonta ta rufe idonta tana kuka ta duk’unk’une a tsaye waje d’aya, ajiyar zuciya ya sauk’e…..a hankali taji kamar ya bar wajen. Addua take yi Allah yasa fita zai yi, ai kuwa a hankali taji ya bud’e k’ofar ya fita. Tana bud’e ido taga ita kad’ai, ajiyar zuciya ta hau sauk’ewa a jejjere, da kyar ta samu ta d’an nutsu tukunna ta soma k’ok’arin barin wajen. Poster da ta sub’uce a hannunta d’azu ta taka! Kalla tayi ta sake kallo kamar tanason yin nazarin wani abun chan kuma sai ta lumshe idonta ta bud’e kawai ta d’auka ta mayar inda ta ganta.

Jikinta duk a sanyaye hakan nan ta samu ta shirya da kyar ta nemi waje ta zauna.

Aslam yana fita ya fara k’arewa falon kallo kamar akwai abunda yake nema. Yana cikin kallon parlourn Idanuwanshi suka sauk’a akan trolley madaidaici. Wani yawu ya had’iye mai d’an d’aci tukunna ya furzar da iska ya nufi d’akin da yake da tabbacin Arshaad d’in yana a ciki.

Knocking ya tsaya ya d’anyi, jin shiru yasa ya tura k’ofar ya shiga… Ganin ba kowa ya sanya yayi tunanin to ko dai ba nan d’in ya shigo ba, har zai juya sai ya jiyo motsin ruwa a toilet. A hankali ya sauk’e wata siririyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya nemi waje ya zauna a bakin gadon.

Morethan 10 minutes Arshaad ya d’auka a band’akin bayan shigowar Aslam. Har Aslam d’in ya fara tunanin lek’awa a ransa yana tunanin ‘maybe ko baya ciki an yi mistake d’in barin fanfo a kunne ne’ sai kuma yaji an kashe tap d’in! Still sai da ya k’ara 2 minute tukunna ya fito ya na tsane fuskarsa da towel.

A tunanin Aslam wanka Arshaad d’in yayi amman fitowar da yayi sanye da kayan jikinshi ne ya sa ya fahimci ba wanka yayi ba sai dai ko alwallah dan gashi ya nad’e dogon hannun white shirt d’in jikinsa gashin hannunsa a kwakkwance sajensa da sumarsa suka duk a jik’e.

Murmushin da Arshaad d’in yayi masa ne ya katseshi daga nazarin da ya fad’a.

A hankali ya mik’e tsaye yana kallonshi har ya k’araso inda yake tsaye. Aslam yana shirin yi masa magana yaji yace “Sorry.. Ban san kuna tare ba Ummi and I tot wani abun ne ya sameta shiyasa mu.”

“Where have you been??” Muryar Aslam d’in ta katseshi.

“Maldives” Ya bashi amsa a tak’aice sanann ya d’an wuce sa yayi hanyar fita yana ci gaba da cewa
“Already na riga na yi arranging komai for honeymoon” Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace
“Arshaad, i.” Da sauri Arshaad yace “Let’s pray! Naji har an kusan shiga masallaci.” Yana gama fad’in haka ya bud’e k’ofar ya fice. Aslam ya dad’e a tsaye kafin ya samu ya iya motsawa daga inda yake shima ya fice.

Bai sameshi a wajen ba sai a masallacin, a gefensa ya tsaya suka yi sallar, sai da sukazo fita tukunna suka had’u da su Shuraim.

Suna ganin Arshaad d’in suka nufeshi suka yi hugging nashi cikin tsananin farin ciki..Sudais yana dariya ya ce “Ashe baka manta ba”.

Murmushi yayi kafin yace mishi “Ai na gaya maka last year daman ko Ina ina ne
zan dawo ayi celebrating this year da ni” Murmushi dukkansu suka yi suka nufi gida.

Suna shiga su Shuraim suka yi sama shi kuma Arshaad ya jaa akwatin shi ya nufi d’akin da ya zab’awa kanshi.

Bai san Aslam yana tare da shi ba sai da ya shiga d’akin ya juyo zai rufe k’ofar! tukunna
suka yi ido biyu. A bud’e kawai ya bar mishi k’ofar daga nan ya juya ya jaa trolley d’insa ya kai ya ajjiye.
Yana juyowa ya ga Aslam d’in still a tsaye, murmushi yayi kafin yace “Ka k’araso ka zauna mana”

“Arshaad listen, we have…”Cikin katseshi Arshaad d’in yace “We have to talk ko? About Huda! Aure! And everything right?” Numfashi ya fesar kafin ya cigaba “Akan me to za muyi maganan abunda ya riga ya faru ya wuce?”

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ba abun magana kam gaskiya, i just want to know how you feel about us, together, and everything sannan kai! Are you ok??”

Murmushi Arshaad yayi mai had’e da dariya kafin yace “Aslam i feel fine! Sannan I’m Ok. Tunda har ka ga na dawo. Nigeria, Kano to I’m Ok Aslam. So kawai abunda zan gaya maka shine kar ka dubani kace zaka yi affecting relationship d’inku negatively, ni ban ma san kuna gidan nan ba da a hotel zan zauna zuwa
jibi inzo a yi birthday da ni daga nan in nemi inda zan je saboda. I still can’t face Mammy!
Sannan ba zan iya zama a tsakiyarsu ita da Dad suna fad’a kamar Annabi da kafiri ba. But still zuwa jibi
zan san yadda zan yi in sha Allah.”

Da sauri Aslam ya matso inda yake yace, “No, you don’t have to. Kar ka je ko ina…”

Cikin katseshi Arshaad yace “I’m sorry to say this amman after yadda kake feeling guilty right now akan halalin ka saboda ka san na ganku i definitely need to go! Kuna buk’atar air, in fact
your relationship is somehow complicated dan haka kuna buk’atar time da space
In other for you two to build a healthy and happy marriage. If I can’t help banga dalilin da zai sa in zauna a tsakiyarku ba ina sakaku kuna feeling somehow. Zan iya rantse maka akan cewa
I have moved on! And na manta da komai na cire Hudan a raina completely but na san ba lalle ka yarda ba, itama ba lalle ta yarda ba, za ku dinga gani kamar ko in kun yi abu zai sa inji ba dad’i ko wani abu makamancin haka wanda hakan zai sa ku kasa sabawa da kuma sakewa da juna, ni kuma har ga Allah ba zan so hakan ba, therefore i think i need to stay away for some months ko a year haka. Maybe nima idan na tashi dawowa In dawo da tawa bride d’in” Ya k’arashe maganar da d’an murmushi a kan fuskarsa.

A hankali Aslam ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin yasa hannu ya janyoshi jikinshi yayi huggin nashi.

K’arar wayarsa ce ta sanya shi cika Arshaad d’in yad’an matsa sannan ya zaro wayar ya d’auka yasa a kunnenshi yace “Auwal” D’an jimm! Yayi, chan kuma yace “what for?” A hankali kuma sai yayi murmushi yace “Bara mu fito, Arshaad is home ma.”

Bai jira jin me Auwal d’in zai ce ba ya katse kiran ya d’ago yana kallon Arshaad kafin yace
“Mu je, Auwal ne” Bai musa shi ba ya bi bayanshi suka fita.

A babban parlourn suka sameshi, zaune cikin d’aya daga cikin set d’in kujerun dake a parlourn.
Yana hango su ya taso, duk da halinda yake ciki hakan bai hanashi k’arasawa yayi welcoming Arshaad warmly ba.

Aslam ne ya katse su ta hanyar cewa “Mai ya faru ne? You sound worried! Yanzun ma kuma you look worried”

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Tana Ina please? Bani da energy…..”Gaba kawai Aslam d’in yayi
shi kuma ya bishi a baya. Suna zuwa k’ofar d’akin nasu ya murza ya shiga Auwal d’in kuma ya tsaya a waje.

A zaune ya sameta, ta rafka uban tagumi…sanye cikin doguwar rigar da ta fitar d’azun zata saka.

A rayuwarshi blue is one of his favorite colours, gashi blue d’in mai d’an duhu wanda ya taimaka wajen fito da ainahin kyawun farar fatarta..Yanayin dim light d’in dake kunne a d’akin ne ya taimakawa stones d’in jikin rigar tata wajen yin kyalkyali na musamman mai d’aukar ido da hankali…Normal d’aurin d’ankwali tayi irin na ture ka ga tsiya wanda ya fitar da uban tulin gashinta da ta tufke ta nannad’eshi a k’eyarta.
Ba komai a fuskarta ko mai bata shafa ba amman kalar kyan da tayi masa yau dole ya bada tukuici!.

A hankali k’asa k’asa yadda ta tabbatar ba zai ji ba tace “Ni fa bana son kallo” Tana mai d’auke kanta daga gareshi had’i da d’an turo baki.

Murmushi kawai yayi sannan ya tako gabanta ya tsaya yace “Saboda me yasa bakya son kallon?”

Runtse idanuwanta tayi, a ranta tace “Wannan ko maciji albarka”

Batai auni ba taji yasa hannunshi a nata ya mik’ar da ita tsaye yana kallon rigar jikinta kafin ya maida idanunsa a kan d’ankwalin, murmushi yayi yace “D’aurin masifaffu dama yafi yiwa masu tsiwa kyau.”

Haka kawai sai ta tsinci kanta da kasa d’agowa da kuma kasa cewa komai, still bata san daliliba amman maganar tasa ba k’aramin dad’i tayi mata ba! A take taji haushin shi da fushin da take yi da shi suna d’an raguwa…

Ya jima yana kallonta kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace “Ki je Auwal yana parlour yana jiranki, muryarsa har rawa take yi, da alama emergency ne.”

Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya dan ta san me ya kawo shi.

Sai da ya sake cewa “Ki je” Tukunna ta iya jan k’afafuwanta ta d’anyi baya kad’an ta yadda ta tabbatar ba zata gogeshi in ta zo wucewa ba sannan ta wuce.

Har ta kusan k’ofa taji yace “ungo” Tana juyowa ta ganshi a kusa da ita yana bata hijab d’inta.

Tsayawa tayi bata matso ba balle yayi tunanin zata saka.

A hankali ya matsa inda take yana kallonta itan ma shi take kallokafin ta yi k’asa da kanta kamar d’azu.
Yanayin yadda ta yi d’aurin tabbas in ya saka mata a haka zai iya shak’eta shiyasa yasa hannu ya zare d’ankwalin ya rik’e a hannunsa

So yake ya saka mata hijabin amman kyau da shek’in da gashin yayi da kuma yanayin parking d’in da tayi ne ya yi mugun tafiya da imaninshi dan haka ya tsaya ya shagalta da kallo.

A hankali yaji tace “Bara in je, ka ce ce emergency ne” Ba tare da ta d’ago kanta ba.

Wata nannauyar ajiyar zuciya taji ya sauk’e kafin a hankali ya ware hijabin kamar baya so..sai da ya nemo fuskar hijab d’in tukunna ya ajjiye d’an kwalin nata a gefe ya sa hannuwanshi duka biyu ya bud’a ya kawo dede setin fuskarta yace “Raise your face” Tana d’agowa suka had’a ido yana kallonta itan ma shi take kallo ta cikin hijabin. A hankali ya matsar da hijabin yasa mata a fuska sannan ya d’an jashi ya zauna dede kafin ya ida warewa ya sakar mata shi ya rufe ilahirin jikinta. Tana shirin wucewa taji yayi cupping fuskarta yad’an matso kusa da ita. A zabure ta d’ago tana kallonshi shima ita d’in yake kallo kafin ya lumshe idanunsa a hankali ya kai lips d’insa dede goshinta ya sakar mata light peck d’in da ya sanya ilahirin jikinta d’aukar rawa! A hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya sannan ya matsar da bakinsa a dede setin kunnenta yace “You look beautiful tonight” Yana gama fad’in haka ya cikata ya wuce toilet dan yana buk’atar yad’an watsa ruwa kafin lokacin dinner, garin yau akwai zafi sannan shi kanshi kwana biyun nan yana saurin jin zafin yanayin dauriyace kawai yake yi.

Da kyar ta samu k’irjinta ya d’an ragu da bugawa sannan ta d’an dedeta kanta ta fita wajen Auwal.

Tare ta tadda su a parlourn shi da Arshaad. Gaba d’aya sai ta tsinci kanta da diriricewa kamar mara gaskiya, ta tsaya.

Tun sanda ta fito Arshaad ya ganta, ganin duk ta rikice ta kasa k’arasowa ne yasa yace
“ko In baku guri ne?” Ya fad’i hakan da d’an k’arfi ta yadda ya san za ta jiyo sa.
Da sauri ta d’ago ta kalli inda suke, suna had’a ido ya sakar mata lallausan murmushi sannan ya sake maimaita tambayar tasa.

A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta fara takawa ta isa inda suke ba tare da ta sake yarda sun had’a ido da Arshaad d’in ba.

Murmushi kawai yayi ya zaro wayarsa a aljihu ya shiga daddanawa.

Tana zama Auwal ya juyo gaba d’ayanshi gareta ko gaisawa bai iya tsayawa sun yi ba yace
“Dan Allah da gaske gobe za a kawo kud’in auren Sakina?”

Ba k’aramin tausayi ya bata ba dan har wata kwalla taga ta taru a idanuwanshi..

A hankali tace “Ya Auwal duk abunda kaga Allah bai yi ba muddin ka yi addu’a to ba alkhairi bane, ka kwantar da hankalinka zaka samu wadda ta fita in sha Allah.”

Cikin katseta yace “Da gaske ne kenan” A hankali muryarshi na d’an rawa.

D’agowa tayi da niyyar sake bashi hak’urin ya rungumi k’addara
kawai taga hawaye bibbiyu suna zubo masa! Da sauri ta runtse idonta tace
“Ya Auwal dan Allah ka daina mana, ka rungumi k’addara kayi adduar Allah yasa hakan shine mafi alkhairi”. Bud’e baki yayi da niyyar yin magana sai kuma ya kasa,
da sauri ya tashi ya fita a side d’in gaba d’aya ba tare da ya sake waiwayon su ba.

Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali tana jin tsananin tausayin Auwal a ranta.
Kamar ance ta d’ago, tana d’agowa suka had’a ido da Arshaad, murmushi
ya sake sakar mata kafin yace “Abun tausayi, ko?” Sunkuyar da kanta tayi
a hankali ta d’aga kan alamar “Eh”

Yana shirin yin magana Ummi ta sauk’o! Har ga Allah haka kurum sai ta tsinci kanta da rashin jin dad’in ganinsu a zaune su biyu. Tana zuwa ta nemi guri ta zauna kusada Huda ta kamo hannunta k’asa k’asa tace
“Huda tunda ba ku kad’ai bane a gidan, ku dinga saka key a k’ofar ku mana. Wallahi ban san ta ina zan fara kallon Aslam ba”

Da sauri Huda ta sunkuyar da kanta k’asa sosai wanda hakan har sai da ya sanya Ummi ta d’anyi murmushi.

Sarai Arshaad ya ji abunda suka ce amman bai nuna musu ba! Hasalima chatting d’insa kawai yake yi yana murmushi.

Ganin hirar tata ba zata yiu da Hudan ba yasa ta juyo ga Arshaad tace
“Ka je wajen Mammy?” Sai da yad’an k’ura mata ido, kamar ma bai ji abinda tace ba
tukunna yad’an gyara zaman shi ya maida wayar aljihu kafin yace “A’a,
direct daga airport nan nayo”. A hankali tace “Bata da lafiya”

Bata ida rufe bakinta ba yace “I know!”

Ta lura da yadda yanayinsa ya chanja amman hakan ba zai hanata yi masa nuni da gaskiya ba dan
haka tace “Arshaad no matter what, ko me tayi maka. Mahaifiyarta ce! She’s sick! Very sick! She needs you!
Aiima bata nan ita kad’aice.

Ajiyar zuciya ya sauk’e yana kallon Ummin ido cikin ido yace “Abba baya nan ne?”

“Eh, yayi tafiya shi da Daddy business trip sannan za su bud’e
branch d’in construction company d’insu shi da Aslam a UK sun ma bud’e
It was successful sannan trip din nasu was also successful
shiyasa jibi za mu yi double celebration in sha Allah.”
Ummin ta zayyano mishi dan so take su yi magana kar
ya samu question d’in da zai sake jifanta da shi as an excuse.

“Ma sha Allah, Allah ya k’ara d’aukaka” Yace, daga nan ya mik’e.

Itan ma mik’ewa tayi tace “We are not done”

Sai da ya lumshe idanuwansa ya bud’e kafin ya kalleta yace “Ummi ko In koma inda na fito ne?
Although i came for Shuraim and Sudais but it’s like bakya murna da ganina!”

Da sauri tace, “Arshaad ba haka ba…”

Cikin katseta da d’an b’acin rai yace “To na rok’eki da girman Allah ki daina yi min maganar Mammy
Ummi kina so inje In zauna Ina ganin suna fad’a kullum ita da Dad ko yaya?”

Tausayin sa ne ya fara rufeta dan haka ta k’arasa inda yake ta kamo hannunshi ta rik’e a nata tace
“Ba haka bane son, ka fahimceni”

Kamar zai yi kuka yace “Me kike so inyi yanzu?”

Har ta bud’e baki za tayi magana sai kuma tace “Ba komai, nothing”

A hankali ya zame hannunsa a cikin nata ya juya ya shige dakinsa.

Ta d’an jima a tsaye kafin ta sauk’e ajiyar zuciya ta juya ta nufi kitchen ta fara setting dining table.

A hankali itama Huda ta mik’e ta k’arasa ta shiga tayata. Sai da suka gama tukunna Huda ta wuce d’aki, ita kuma Ummi ta zauna anan kan dining d’in ta rafka tagumi.

A gaban dressing mirrow ta sameshi yana taje gashinsa. Sanye cikin pyjams dark ash da suka yi mishi kyau matuk’a!.

A hankali ta k’arasa bakin gado ta zauna ta d’auki wayarta da ta mak’ala a charge ta danna kiran Sakina
Bayan ta zare wayar a charging. Tana d’auka tace “Yanzu Ya Auwal ya tafi”

“Um”. Kawai Sakinar tace, a hankali.

Ajiyar zuciya Huda ta sauk’e kafin tace “Yayi matuk’ar bani tausayi, har da kuka fa yayi.
Da kin sani baki gaya mishi yanzu ba”

Shiruu, ta ji Sakinar tayi kafin chan tace “Ya dameni da kira da massages! At least yanzu zan huta
sannan i don’t want him to have any false hope.” Cikin son kawo k’arshen maganar Auwal d’in tace
“Za ki zo goben?”

Sai da ta kalli Aslam wanda yanzun yake zaune akan sofa yana k’ok’arin kunna computer tukunna tace
“Ya hanani” Da d’an k’arfi ta yadda ta san zai ji.

“Ki lallab’ashi” Shine kawai abunda Sakinar tace. Har zata kashe wayar sai kuma tace
“Jiya su Shuraim ma sun biyo nan daga school, sun kawo mana invitation d’in birthday d’insu
Su Mama dai ba zasu zo ba amman ni da Sumayya za mu zo goben In sha Allah.”

Cike da murna Huda tace “Allah ya kaimu da rai da lafiya. Ku zo da sassafe dan Allah ayi shirye shiryen komai da ku”

Murmushi kawai Sakina tayi tace “Ai inaga 3 hours ma kawai za mu yi, za mu zo 2 mu tafi 5 haka, ba lalle ma mu samu event d’inba kawai dai za mu zo ne dan naga sai wajen 10 ma tukunna za a fara, so kawai za mu d’an lek’o.”

Da sauri Huda tace “To ku kwana mana” Dariya Sakina tayi tace “Bara in yi sallah. Sai anjima”
Dan so take ta kashe wayar sakamokon kanta da yake mata tsananin ciwo da kuma rud’anin da zuciyarta take ciki! Dauriya ce kawai take yi da har aka samu take iya yin magana.

“Okay, ki gaida Ummu da Sumayya” Hudan tace daga nan suka katse kiran.

Ita bata ma san Aslam ya fita ba sai da ta d’ago tukun taga ba ya nan “Hmm, mutum sai basirar iya san’da kamar munafuki”. Ta fad’a a ranta.

Tana mik’ewa tayi haramar kimtsawa domin ta gabatar da tata sallar dan taji an shiga masallaci.

Tana idarwa ta fita da sauri ta d’ebo abinci a plate ta d’auko ruwa ta shigo har da d’an gudu dan taji kamar mutum zai fito a kitchen.

Da wuri tayi ta cinye ta sha ruwa ta yi brush, ko plate d’in bata d’auke ba ta kwanta ta k’udundune a cikin bargo! Ala dole Ita tayi barci kenan saboda gudun kar ma wani ya shigo yace ‘taje tayi dinner’
Saboda ita har ga Allah kunyar had’uwa da Arshaad take yi after what he saw daga zuwanshi gidan
bata jin zata iya sakewar had’a ido dashi balle zama waje d’aya.

Kusan kamar 40 minutes wayarta ta fara k’ara! Dan haka ta tashi ta d’auka, tana ganin sunan Abba ta d’auka da wuri cike da zumud’i tace “Abba, Ina wuni, kun taho ko?”

Murmushi yayi yace “A’a tukunna, yanzu dai muke shirin isa airport. Gobe around 7:00am in sha Allah za mu k’araso saboda muna da transit”

“Okay, Allah ya kawoku lafiya”

Murmushi yayi yace “Ameen princess, Ina Aslam?”

Sai da ta d’anyi shiruu, tukunna tace “Yana waje, suna dinner”

Da sauri yace “ke fa?” A hankali tace “yanzu na gama a d’aki”

Zai yi magana ya ji tace “Ya Arshaad ma ya dawo.”

Shiruuuu, taji Abban yayi kafin yace “Okay, sai mun k’araso goben in sha Allah”

A hankali tace “Safe fligh Abba”

Murmushi yayi yace “Thank you princess” Daga nan suka katse wayar, tana shirin ajjiyewa
Aslam ya shigo! Hannunsa rik’e da plate a da ruwa. Ta ji shigowar tasa amman bata d’ago ba, har ya tako ya zo inda take ya zauna a gefen gadon kusa da ita.

Sai a sannan ta d’ago tana kallonsa da plate dinsa, a ranta tace “shima a nan zai ci abincin yau ko me?”

A hankali taji yace “Kin ci abinci kena?”

D’agowa tayi tana kallonshi taga yana kallon plate d’in gefenta wanda ta ajjiye akan side drawer.
A hankali ta d’aga masa kai alamar ‘eh’.

Shiruuu, suka yi chan taji yace “Ya za muyi da wannan??”

D’agowa tayi taga shima itan yake kallo! Da sauri ta sunkuyar da kai dan yau wani kalar kallo taga yana yi mata wanda ya sanya kwata kwata bata son had’a ido da shi.

Shirun ne ya sake biyowa baya kafin ta ji ya bud’e plate d’in da ya rufa a kan na abincin ya fara tab’a spoon d’in. Bata gama tunanin me yake yi ba taji yace “Haa” Tana juyowa taga ya d’ebo fride rice d’in wadda taji hanta ya kawo kusa da fuskarta. Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya sannan ta kawar da kai tace
“Na k’oshi” ji tayi kawai ya kamo hannunta ya d’an matse a cikin nasa a hankali ya sake cewa
“Haa” Yana sake matso da cokalin.

“Ya subahanallah! Wannan wanne irin mutum ne?” Ta yiwa kanta tambayar a cikin ranta.
Ji tayi ya murza tafin hannunta da nashi hannun still a hankali taji ya sake cewa “Haa” Da sauri ta juyo ta bud’e bakin ta lumshe idanunta numfashinta na fita da sauri sauri.

Murmushi yayi ya saka mata cokalin a baki ita kuma ta karb’a ya juye mata
tukunna ya zare.

A hankali ta shiga taunawa, har yanzu idanuwanta a lumshe suke.

Kamar wanda ya samu tv haka ya nutsa ya maida hankalinsa wajen k’arewa kyakkyawar fuskarta kallo.

Sai da ya ga ta had’iye tukunna ya mayar da cokalin ya fara k’ok’arin d’ebo wani,
da sauri ta d’aura hannunta a kan nasa ba tare da tayi laakari ba, tace “Nafa ci abinci
Mai yawa. Please Ya Aslam kar in yi amai” Sannan ta fara k’ok’arin bud’e kyawawan idanuwanta da suka taru da kwallah.

Tana gama bud’ewa taga ya ajjiye spoon d’in ya na k’ok’arin bud’e robar ruwa…
Ba yadda ta iya haka ta yarda ya bata a baki ta sha tukunna ya mik’e ya d’auke plate d’in da ta ajjiye a kan side drawer ya had’a da wanda ya shigo da su ya fitar.

A yadda ya fita ya barta a haka ya dawo ya sameta, bai kalletaba bai ce mata komai ba ya nemi waje ya zauna ya ci gaba da aikin da yake yi d’azun kafin ya fita sallah.

Ya d’an jima yana aikin, kafin yaga ta taso ta k’araso ta zo inda yake. A hankali ta zauna a gefensa tace
“Ya Aslam” “Um, Anty Huda”. Ya ce ba tare da ya kalleta ba, yana mai ci gaba da typing d’in da yake yi.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace “zan je dan Allah, goben.”

“No” Yace, still bai kalleta.

Turo baki tayi kafin tace, “Na dawo fa d’akin”

This time around dariya yayi kafin ya rufe computer gaba d’aya sannan ya juyo gareta yace
“Ki yi hak’uri, baza ki je ba.”

Kamar da wasa kawai sai yaga ta fashe ta kuka!

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya matso ya kama hannunta yace “Mama ce tace kar a barki ki sake fita sai nan da wata d’aya. Idan kina son fita ki kira Hajiya Shuwa idan ta barki sai ki je.”

Da mamamki take kallonsa tana rage sauti da yawan kukan nata. Jinjina mata kai yayi alamar tabbatarwa.

A hankali ta shiga share hawayenta tana sauk’e ajiyar zuciya a hankali.

“Yanzu zaki kuma yin wani yajin kenan? Tunda dai kinga ba damar fita gobe. Ba ni zan barki ba Hajiya da Mama ne”

A hankali ta girgiza kanta tace “Ka yi hak’uri, a kan abinda nayi”

Murmushi yayi yace “Ai kuwa na hak’ura! Tunda har kwalliya da turaren wuta aka saka duk dan saboda ni. Ko ba dan ni akayi ba??”

Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kanta k’asa.

A hankali yana kallonta kafin yace “Je ki kwanta. Gobe tashin asuba ne, ko?”

Ba tare da ta d’ago ba tace “Kaje ka kwanta kai, ni a nan zan kwana. Da bananan ai a gadon kake kwana.”

Sai da yad’an k’ura mata ido tukunna yace “A nan d’in nake kwana. Har gyara miki gadon nake yi kullum thinking you will come back . A haka bacci yake d’ibana kullum.”

Shiruuu suka yi duk su biyun kafin yaji tace, “Ka fini tsayi, ina gani kullum kujerar bata isar ka, ka je ka kwanta don’t be stubborn”

Dariya taji yayi kafin yace “In da acting stubborn nake miki yanzu ai da na san tuni kin fita a d’akin nan da gudu”

Bata fahimci kan zancen nashi ba dan haka kawai ta basar da zance ta sake cewa
“Ya Aslam barci nake ji, ka je ka kwanta.”

A hankali yan kallonta yace “Are you sure? In je in kwanta ba damuwa?”

Da sauri ta d’ago ta d’aga mishi kai sannan tace “Sai ka fi sakewa achan da kyau”

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Thank you Hudatie”

Haka kurum ta tsinci kanta da murmushi dan ba kad’an ba sunan ya yi mata dad’i matuk’a.

Murmushi shima yayi kafin ya mik’e ya fara d’ibar throw pillows d’in kan sofar, iya yadda hannunshi zai iya d’iba ya kwasa ya nufi gadon. A ranta tace “Ikon Allah! Neman magana yake yi wannan ko mee?
Bayan pillows d’in da suke kan gadon wajen guda 4 masu laushi mai kuma zai yi da throw pillows??”
Tunaninta ne ya katse ganin yana jera throw pillows d’in yana raba gadon gida biyu da su.

Tuni! Kwakwalwarta ta bata me yake shirin yi dan haka tana gani ya gama ya tunkaro ta ta mik’e ta fara magana ba tare da ta kallesa ba “Ai ni nace maka anan zan kwanta Allah kar ma kayi tunanin haka!
Idan kuma neman maganata za ka yi to wallahi zance na fasa sai da ka dawo ka cigaba da kwana a sofa kuma ko zanga k’afafuwanka suna lankwashewa kana tafiya da kyar ba zan sake y……” Dip! Maganarta ta d’auke sakamokon d’aukarta da yayi tashi d’aya in a bridal style.

Ba tare da ya kalletaba ya fara tafiya da ita towards the bed.

Tsoro da mamaki da kuma yanayin da ta tsinci kanta a ciki ne suka sanya ta kasa magana ko yunk’urin zamewa.. In banda kallon gefen fuskarsa ba abunda take yi har ya isa bakin gadon ya sunkuya ya kwantar da ita rigingine a kan gadon ya d’aura mata kanta a kan pillow ya zame hannuwansa. Ba tare da ya d’ago daga sunkuyon da yayi a kanta ba fuskarsa dan da tata ya d’ago da idanuwanshi ya sanya su cikin nata
a hankali yace “Sleep here. Dan Allah” Sannan ya mik’e tsaye ya zagaya d’ayan side d’in ya kwanta.

Sai a lokacin ta samu ta sauk’e wata siririyar ajiyar zuciya mai vibration kamar mai jin sanyi.

A hankali taji yace “Ki yi addua, good night”.

Ita dai Hudan a yadda ya barta nan rigingine tana kallon sama a haka ta farka ta ganta lullub’e da bargo, daga cikinta zuwa k’asa..ba ta san lokacin da barci ya kwasheta ba. Ko ba a fad’a mata ba ta san Aslam d’in ne ya lullub’eta. Kiran sallar da ta ji ne ya sanya ta fahimci tabbas yau ta d’an makara dan kamar ma har an shiga masallaci, ta ji. Addua ta yi tukunnan ta d’an juya ta kalli side d’in da ya kwanta. Ga mamakinta sai ta gansa kwance a kan gefen damanshi yana facing d’inta. Bacci yake yi peacefully kamar kuma da murmushi a kan fuskarsa. Kamar yadda ya rufe mata rabin jikinta haka nan shima ya rufu da bargon.

Jin an tada ik’ama yasa ta d’an matsa kusa da shi ta fara kiran sunanshi.

A hankali yake bud’e idanuwansa, kafin ya k’arasa bud’e su tarr a kan fuskarta!
Murmushi ya sakar mata a hankali taji yace “Lucky Morning”

Shiru tayi taana kallonshi shima itan yake kallo chan ta d’auke idonta da sauri tace
“Zaka makara fa, har an shiga sallah.” Da sauri ya mik’e ya d’an dafe kansa yana mutstsika idonshi kafin ya sauk’a akan gadon ya fad’a toilet. Ko da yaje har an tafi ruku’u dan haka raka‘a d’aya ya samu. Haka nan suka dawo tare da su Shuraim da Arshaad Sudais yana cewa Arshaad “Ya kamata ya yiwa Ya Aslam bulalar makara sallar asuba yau”

Murmushi kawai Arshaad d’in yayi ba tare da yace musu komai ba ya wuce d’akinsa. A shirye ya tarar da Huda, suna gaisawa ta fice zuwa kitchen don had’awa Abba abunda ta san yafi so.
A kitchen d’in ta tarar da Ummi don haka suka taru suka had’a masa lafiyayeyyen breakfast..

6:30am, Aslam ya fice tare da Sudais suka tafi d’auko su bayan shi da Hudan sun yi wishing d’insu ‘Happy birthday’ sun basu gifts d’insu shi da Shuraim.

Kafin 8:00am suka dawo, Daddy direct side d’insa ya wuce Abba ma suka nufi side d’inshi shi da su Aslam.

Da gudu Hudan taje ta yi hugging d’inshi tana murna haka ma Shuraim, daga nan
aka shiga gaggaisawa.

Ummi, ba kad’an ba tayi matuk’ar jin dad’in yadda Abba ya yi mata faram faram!
Dan haka ta samu kwarin guiwa ta hau gabatar masa da abinci kala kala ita da
Hudan. Cike da farin ciki yake karb’a yana ci dan Huda da Shuraim da Sudais ke bashi a baki one by one duk da Sudais yana ta yi musu kwange. A haka suka ciyar da Mahaifin nasu cike da tsananin so da k’aunar juna. Sai da ya k’oshi aka tattare wajen ya fara shirin mik’ewa tukunna Arshaad ya fito.

Cike da kulawa Abba yayi welcoming d’insa daga nan ya wuce sama bayan ya bawa Ummi briefcase d’insa yace ta kai masa dakinsa Shuraim kuma ya ja masa trolley d’inshi.

Bai tarar da Shuraim a d’akin ba, sai Ummi ita kad’ai ya tarar ta juya baya tana k’ara turaren wutan da ta saka tana d’an fifitawa…

D’akin ya sha gyaru ba kad’an ba gwanin sha’awa. A hankali ya k’arasa inda take tsaye yayi hugging d’inta ta baya.

A mugun zabure ta juyo dan sam! Ko da wasa bata yi expecting haka daga Abban ba.

D’an guntun murmushi ta gani kwance a kan fuskarsa, a hankali yace
“Ko ba a shirya yi min wannan tarbar ba?”

Ummi bata san lokacin da ta fashe da wani kuka ba, ta fad’a jikinsa cikin kukan tace
“Abba ka yafe min dan Allah kayi hak’uri ka yafe min”

Hugging d’inta yayi a hankali dede setin kunnenta yace “Shiii, komai ya wuce.
Ki manta da komai! Just think about me”.

Ana cewa mutum yana kasa dai na murmushi bata tab’a yarda ba sai yau da ta faru a kanta.
Shi kanshi Abban ya lura da tsananin farin cikin da take ciki!

Yaso ya gaya mata cewa Maryam ce ta rok’esa akan ‘ya yafe mata ya zauna cikin kulawa da ita’ dan shi bai iya kwana kwana ko b’oye b’oye ba amman yadda ya ganta cikin tsananin farin ciki ne ya sa ya fasa gaya mata ya kuma yi alk’awarin rufe maganar tsakaninshi daga shi sai Maryam d’in. Tabbas shima yana cikin farin ciki ba kad’an ba dan yanzu Maryam ta kan kulashi, jiya har Friday massage ta mayar masa
bayan tayi mishi replying nashi message d’in da ‘Ameen, jazakallahu khairan’.

A hankali ya lumshe idanuwansa yana adduar ‘Ubangiji ya sake mallaka masa ita a karo na biyu’.

Har Ummi ta gama drying gashinta ta fita dan ana buk’atar ta urgent a k’asa
bai sani ba. Sai da ya tashi shiga toilet tukunna ya lura bata nan.

Shirye shiryen birthday ake yi na y’an gata! Gaba d’aya compund na mansion d’in ake decorating, an kwashe motocin duk an fitar wasu kuma an kaisu baya.

Hudan bata tashi sanin abun na gaske bane sai da taga ana rubuta ‘Happy birthday Sudais&Shuraim’ da grass carpet tun daga farkon mansion d’in har wajen k’ofofin shiga mansion d’in sannan ta sama ma fitilun da ake decorating da su sunan su ne aka rubuta ‘Happy birthday Shuraim and Sudais’

Gurin zaman su ma ya sha decoration ba a magana ga cake d’insu anata jerawa
guda biyu iri d’aya each one ya kai kusan hawa biyar.

Compound d’in kuma inda guests za su zauna kujeru ne guda biyu da table a tsakiya shima ya sha decoration. Irin haka wajen guda 70 a daban daban.

Abinci kuwa sai shigowa ake yi da su kula kula drinks da ruwa ma ba a magana cupcakes desert soaked cakes abun dai sai wanda ya gani.

Tun 3:00pm Aka fara kawo Yara, friends d’insu maza da mata y’ay’an masu kud’i
masu fad’a a ji, daga yanayin motocin da drebobin da suke kawo Yaran za ka gane abun na manya ne.

K’awar Ummi d’aya ce tak! Ta zo. Dan mutum d’aya kawai ta yi inviting saboda
yawancin k’awayenta ta lura a yanzu halayyarsu ba d’aya ba so ta san tasu ba zata ci gaba da zuwa d’aya ba.
Mammy kam kaff sister’s d’inta sai da suka zo tare da y’ay’ansu, Mom itama tayi gayyata sosai
amman kuma tunda suka zo ko Ummin ba su lek’awaba sun mak’ale a side d’in Mom wadda suka ja gefe Ita da Mammy sunata k’usk’us! Daga ganin fuskar Mammy ka san ba alkhairi dan ko kallon mutum ma da kyar take iya yi In banda cika da batsewa ba abunda take yi.

Har aka kira isha su Sakina basu zo ba gashi sai kiran su take yi basa d’auka!
Haka nan ta mik’e tanata k’unci ta gabatar da sallar isha ta mik’e ta fad’a toilet.

Fitowarta a toilet kenan. sanye cikin bathrobe gashin kanta wanda ta wanke kuma ta nad’e da towel..
Kusan tare suka bud’e k’ofa suka shigo cikin d’akin ita da Aslam wanda ya shigo rik’e da wani k’aton box!
Had’a ido suka yi dan haka ta sunkuyar da kanta k’asa tana gyara zaman bathrobe d’in jikinta.
A hankali ya tako yazo inda take nan tsaye tak’i gaba tak’i baya, yace “Mu je ki shirya”
Da sauri ta d’ago tana kallonshi kafin tayi k’asa da kanta tace “To ka fita mana”

Dariya yayi ya juya ya ajjiye kwalin a kan dressing mirrow ya kwashi kayanshi da zai saka yace
“Ki jirani i have a gift for you, kar ki fita please”.

Ajiyar zuciya ta sauk’e a hankali tana kallonshi ya zo ya wuce ya shige toilet d’in.

A hankali ta sunkuya ta bud’e wardrobe ta jawo akwatinta ta d’auki mai ta shafa ta mayar ta day inner wears d’inta ta saka ta maida bathrobe d’in sannan ta d’au turaren jiki da misk ta shafa.
Powder eye liner da mascara ta fitar ta ajjiye a gefe sannan ta fidda wata doguwar riga b’aka da mayafinta.
Sai a lokacin ta lura bata da takalmin da zata saka sai dai tayi using wanda take yawo da shi a cikin gida saboda duk takalmanta na lefe da wanda take da su gaba d’aya suna gidan Ya Arshaad.
Shiruu, ta yi ta shiga tunani.

A hankali taji ya bud’e k’ofa ya fito dan haka ta d’aga kai tana kallonsa.

Ba yau ta fara ganinshi da suite ba amman ta yau special ce dukda bai d’aura suite d’inba amman kyawunshi ba k’aramin fitowa ya sake yi ba! Wandon dogo ne Baki kamar pencil wanda ya yiwa dogayen k’afafuwansa tsananin kyau! Rigar kuwa longsleeve ce itama baka yayi tucking cikin wandon.

“Na yi kyau har haka ne?” Taji muryarsa ba tare da ya kalletaba.

Da sauri ta sauk’e idanunta k’asa, ta shiga kiciniyar mik’ewa sai dai kuma har ya k’araso yazo ya tsaya a wajen bata mik’e d’inba!

Murmushi kawai yayi ya bud’e wardrobe wajen kayansa ya d’auki agogo da belt sannan ya zaro suite d’in da zai d’aura akai da necktie ya wuce gaban mudubi. Sai a lokacin ta samu damar d’aukar y’ar mitsitsiyar hair dryer d’in da take buk’ata ta mik’e ta nufi bakin gado da kayan da ta ware…

Tsaff ya shirya ya shafa mai kad’an ya fesa turarurruka ya gyara gashinsa, sannan
ya d’auki kwalin ya nufi inda take zaune har yanzu ko kwance kan bata yi ba ballantana ta busar
Ita ala dole jira take sai ya fita tukunna.

Yana zuwa ya d’aura mata akan cinyarta ya nemi waje ya zauna a gefenta.

D’agowa tayi ta kallesa, da gira yayi mata alamun ta bud’e! A hankali ta shiga warware bow d’in da yake nan a saman kwalin wanda an yi amfani da igiyar ne wajen d’aure kwalin, tana kwancewa ta d’an d’aga ta zareshi gaba d’aya a jikin kwalin ta ajjiye kafin ta kama gefe da gefen ta d’aga shima ta ajjiye murfin a gefe.
Bata san lokacin da tace “woow!” Ba.

Wata had’add’iyar riga ce a ciki, duk da a nunke take ta fahimci princess gown ce dan gata a jikin wata a gefe an manna da alamun anaso masu siya su san yanda take ba tare da sun bud’e ledar sun warwaretaba.
Gefe guda kuma y’an kunne ne masu kyau da bracelet da anklet, sai takalmi shima an yi mishi gurin ajiyar sa daban mai matuk’ar kyau kalar y’an kunnen da kayan RED!.

Chan k’asa kuma wani d’an k’aramin lipstic ne an yi rapping d’inshi da leda garai garai da alamun gift ne shi aka bayar.

Banda murmushi tana kallo tana sake kallon katon kwalin, ba abunda take yi.

A hankali ta ji yace “Do you like it?” Murmushi tayi mai d’an had’e da dariya kafin ta juyo ta d’aga masa kai tace “Yes, na gode sosai”

Kallon idanunta yake yana hango farin cikin da take ciki a hankali ya jinjina kai ya d’an motsa bakinsa yace
“Welcome”. Sannan ya mik’e ya karb’a dryer d’in hannunta ya bud’e ya mak’ala comb d’in ya jona a socket. Har zai kunna sai kuma ya koma gaban dressing mirrow ya d’auko hair cream ya dawo. Takalmansa sau ciki ya cire ya bar iya safar ya hau kan gadon ya tsugunna ata bayanta sannan yace “ta mik’o mishi dryer”
Juyowa tayi da d’an mamaki a fuskarta kafin tace “Me zaka yi?” Tana d’an zaro ido.

“Bani sai ki gani, ko?” Ya fad’i hakan yana k’ok’arin b’alle murfin hair cream d’in da ke hannunsa.
“Ko kina buk’atar cuddling ne sannan ki mik’o?” Ya fad’i haka yana zare towel d’in da ta nad’e gashin da shi.

Tun kafin ya ida rufe bakinsa tayi sauri ta mik’a masa dryer.

Karb’a yayi yana dariya k’asa k’asa sannan ya d’an d’ebo man ya mulke mata jik’ak’k’en gashin nata da shi ya fara busarwa yana tajewa.

Hudan, ba k’aramin mamaki ta sha ba game da yadda akai ya iya gyaran gashi dan
har wani massage yake mata da taji tana shirin fara barci.

Gyaran gashin yake yi amman cikin nutsuwa da aji. Kasa hak’ura tayi tace
“A ina ka koyi gyaran gashi?”

Sai da yayi murmushi tukunna yace “Internet. I always dreamt of making my wife’s hair..gashi
is one of the things da nayi ta adduar Allah ya sa matata ta kasance tana da shi, I love it!
Sai gashi Allah ya amsa adduar tawa.” Ya fad’i haka yana me kashe dryer dan har ya gama.

Dariya Huda ta fara ganin yadda ya dawo gaban gadon yana haki kamar wanda yayi race.

Hararar ta yayi ya b’ata rai tukunnan yace “ba thank you sai dariya ko?”

A hankali tace “thank you”

Sai da ya gama hutawa tukunna ya tashi ya d’auko rigar ya cire a leda ya ware ta
ya kama hannunta ya mik’ar. Da sauri tace “Ya Aslam kai fa kai kad’ai ka shirya”

“Bari tou In cire nima sai ki tayani, ko?” Yayi mata tambayar yana k’ok’arin kwance belt d’in wandon jikinsa.

Da sauri ta rik’e hannunsa tana turo baki sannan ta sunkuyar da kanta k’asa.

Zip d’in rigar har kusan chan k’asa ne dan haka ya zuge shi duka tukunna ya kawo ta wajen kanta ya zura mata sannan ya saki rigar.

Ganin yana k’ok’arin sa hannu ya kwance mata bathrobe d’in ta ciki yasa tayi sauri ta matsa ta kwance ta zame hannuwan kafin tayi k’asa da ita duka sannan ta jaa hannun rigar ta saka threequater hannun
ta fara k’ok’arin zuge zip d’in. Ganin bazata iya ba ya sa duk turjewarta haka ta tsaya ya ja mata…..
Kwalliyarma da kyar ya barta ta shafa powder ta saka mascara da eye liner amman y’ankunne bracelet anklet takalmi da red lipstic duk shine ya saka mata!
Tayi kyau kuwa sosai…,

A hankali ya ajjiye lipstic d’in yana kallonta. Ganin kallon yayi yawa ya sa ta wuce taje ta d’au ribbom d’inta ta yi parkin, ta d’auko wani tauban cap na chantily mai stones red ta saka ta d’auko vail black medium ta rufa a kafad’a.

Aslam, gaba d’aya jikinsa yayi sanyi dan Huda ba k’aramin tafiya tayi da imaninsa ba..duk
inda tayi kawai binta yake yi da idanu.

A hankali ya d’au wayarsa ya k’arasa inda take ya jaa hannunta suka nufi gaban dressing mirrow suka tsaya. Ta tsaya a gabanshi shi kuma a baya ya rik’e waist d’inta yayi musu hoto.. Sun yi kyau kuwa ba kad’an ba
kuma sun fito sosai.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya gyara mata mayafin nata ta hanyar maidashi saman kanta kafin yace
“Can we talk?” ya fad’a hakan yana me juyo da ita suka yi facing juna kafin ya d’aura hannayensa a kan kafad’unta ya fara magana, “Next week, in shaa Allah inaso mu wuce UK!

Mun riga mun gama magana da su Abba tun last 2 weeks jiya kuma har su Ummi na gayawa a wajen dinner, yanzu ke kad’ai ya rage baki sani ba. Za ki bini?” Ya k’arashe maganar a hankali.

“Um um” Tace tana mai ja da baya ta d’an sunkuyar da kanta kafin tace “Mai yasa za mu tafi?
Me su Ummin suka ce?”

Sai da ya lumshe idanuwanshi ya bud’e kafin yace “Arshaad is morethan comfortable!
Infact da farko shi ne ma daa zai tafi saboda yace zaman mu under same roof ba zai yiu ba, sai da na yi masa bayani d’azu akan already daman akwai plan d’in tafiyar ta mu tukunna shi ya yarda zai zauna a nan.”

Sai da ta gama jin bayanin nasa tukunna tace “Nifa ba saboda Ya Arshaad bane nace A’a ba.”

A hankali ya ce “mai yasa to ba zaki bini ba?”

Cikin tarar numfashinsa tace “Ya Aslam kamata fa yayi mu yi focusing akan yadda zamu warware wannan auren! Kar mu bawa su Abba false hope d’in wata rana za mu so juna..” Ta k’arashe maganar tana jin wani nauyi yana sauk’a daga zuciyarta.

Janyo ta kawai taji yayi yai huggging d’inta…Sun d’an jima a haka kafin a hankali yace
“Za mu tafi UK next week. It’s an order”

Shiruu, tayi tana mamakin yadda k’irjinsa yake bugawa da kuma yadda gaba d’aya jikinsa yake karkarwa,
gashin sai sake rik’eta yake yi da kyau kamar wanda akace za’a kwace ta.

So take ta motsa ta gaya mishi itafa ba inda zata je amman kuma kamar wadda aka rufe waa baki, kwata kwata sai ta kasa.

Sun jima a haka suka ji ana knocking.

Mommy, tunda tazo take baza ido, so take kawai taga ta Ina za su fito. Duk da Aslam yana zuwa kullum wajen ta idan ya tashi a office wani lokacin ma kafin ya fita sai ya je amman so take yi kawai ta gansu especially Hudan…Hak’urinta ne ya k’are dan haka ta cewa Ummi “ta je ta kira mata su, da wurwuri
take son tafiya su fito su gaisa kafin ta tafi.” Dariya Daddy yayi yace “A’a Mommy ki dai fad’i gaskiya…y’ay’anki kawai kike son gani. Tun d’azu fa nake ganin ki kinata zullo kina lek’en ta Ina za su fito”
Ai kuwa gaba d’aya aka saka dariya banda Mammy da Mom Arshaad kam murmushi kawai yayi.

Mik’ewa Ummi tayi zata wuce daidai nan su Shuraim suka sauk’o. Suite d’insu milk masu asalin tsada sai belt da takalmi brown. Ba k’aramin kyau suka yi ba. Wajenta suka fara zuwa suka yi hugging d’inta! Bata san daliliba kawai sai taji hawaye ya zubo mata. A hankali ta dafa kawunan su ta ce “Allah ya yi muku albarka”. Daga nan tayi saurin wucewa dan bataso tayi kuka.

Nan suka k’arasa inda Dad Mommy Abba Arshaad Mammy Mom da Daddy suke.
Aka fara hotuna bayan an yi wishing d’insu Happy Birthday kowa ya basu gifts d’in da ya shirya musu.

Knocking kawai Ummi tayi ta juya dan ta raba kanta da shiga d’akinsu Aslam ita kam.

Bata yi minti d’aya da zama ba suka fito.. Kowa a parlourn zuba musu ido kawai yayi, ba
k’aramin kyau da dacewa da juna suka yi ba. Kallo d’aya Arshaad yayi musu ya d’auke kai da sauri
Mammy kam tana ganin fitowarsu ta juya kan ma gaba d’aya ta sake tamke fuska.

Ba yadda Hudan bata yi da shi akan ya saki mata hannu ba amman fur!! Ya k’i. Haka nan duk sai taji kunya ta lullub’eta especially da suka had’a ido da Mommy wadda take ta zuba murmushi kamar an mata albishir da gidan aljannah. Suna k’arasowa ta mik’e ta kamo hannun Hudan ta fara k’ok’arin janta dan ta zaunar da ita a gefenta.

D’agowa tayi suka had’a ido da Aslam! Sai da ta d’anyi dariya tukunna tace “Cikata mana, ko?”

Shima kuma sai yaji kunyar Abba da su Dad ta rufeshi dan haka a hankali ya cikata ta zaunar da ita itama ta zauna Aslam ya zauna a gefnta. Tun kafin ta fad’a Shuraim ya shiga yi musu hotuna. Abba da Dadddy da Dad ma suka shiga, haka ma Ummi. Ranar dai anshan hotuna kala kala bibbiyu uku uku,
daga nan su Shuraim suka fita saboda friends d’insu duk suna waje.

Sai wajen 9 su Sakina suka zo, murna a wajen Hudan ba a magana.
Suna gama gaisawa da su Abba suka fita compound suka nemi waje suka zauna.
Basu dad’e da zama ba aka fara gudanar da program of event.

Suna cikin hira su biyu dan Sumayya har ta yi k’awa wata Khairat sun ja gefe anata iyayi da manyance, suka ji an jawo kujera an jona da table d’insu an zauna a gefen su. Tana d’agowa suka had’a ido
a take gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa! So take ta cire idanunta a nashi amman ta kasa…..

“You came.” Yace yana mai kallon cikin idonta.

A hankali tace “Yes”. Sai kuma ta mik’e da sauri tace “Hudan muje ki rakani bathroom”
Tana mik’ewa ta yi gaba.

Da sauri ya kalli Hudan yace mata “A minute please” Sannan ya mik’e ya bi bayan Sakina wadda tayi hanyar falon su Hudan da sauri.

Kwarewa Mammy ta yi, da sauri ta kamo hannun Mom! Tana juyowa ta nuna mata su, tace
“Kinga Auwal da Cousin d’in Huda wadda suka zo d’azu Hudan take ta murna d’innan.”

Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yadda Auwal yake kiranta yana d’an gudu
amman ko alamun zata juyo ma bata yi ba…

Tana shiga shima yana shiga! Sai a lokacin ta lura da Huda bata biyo su ba. Da sauri ta had’e hannuwanta biyu waje guda alamun rok’o, tace “Dan girman Allah Ya Auwal ka rabu da ni! Ka fita a harka ta.
Me kake so in yi maka? An saka ranar aurena! Nan da 5 month in sha Allah Ina gidan wani me kuma zaka ce min yanzun me kake buk’ata a….” Maganarta ce ta katse sakamokon hawayen da ta ga sun tsinke masa lokaci guda kamar fanfo sai kace wani k’aramin Yaro.

A hankali ya durk’usa a gabanta ya had’e hannuwanshi duka biyu shima, yace “Sakina dan girman Allah
ki san yadda za kiyi da ni! Wallahi ban san halinda nake ciki ba, ba laifina bane ba, na san na takura ki da yawa amman ba laifina bane ya kamata ki gane. Ya kike so in yi? Wallahi na yi na yi In cire ki a raina amman kullum sonki da k’aunarki k’aruwa kawai suke yi! Ki taimaka kar ki auri wani wallahi zan iya mutuwa.

Na ji zan baki time zan baki space amman kar ki auri wani na dan girman Allah.
Sannan ki san yadda za kiyi da ni, ki yi min abunda zan ji kin fita a raina. In kikayi min haka kin gama min komai.

Na san ba a neman aure cikin aure amman na kasa hak’ura da ke! Ba zan iya ba ki san yadda za ki yi dani dan Allah.

I know I’m not making any sense here I can’t loose you kuma tunda kince bakya so na
i can’t force you to love me so I can’t love you, saboda ni happiness d’inki shine abunda nake so
amman fa kar ki ce za ki auri wani. Wallahi rabona da bacci tun shekaran jiya! Inaga haukacewa zan yi, bana gane komai bana gane kowa sai ke! Ki fita a raina sai in barki Ki fita a zuciyata sai in.”

Kukan da ya taho mishi fiye da na farkon da yake yi ne ya sanya ya kasa ci gaba da magana.

Ita kanta Sakina kukan da take ta k’ok’arin rik’ewa ne ya samu nasarar kufce mata.

“Innalillahi wa innailaihirrajiun!!” Suka ji muryar Mom da Mammy a bayansu har da wata k’awar su,
suna salati suna tafi.

Da sauri Sakina ta share hawayenta ta d’an matsa saboda Auwal d’in ya tashi ya basu damar shigowa
amman ko gezau bai yi ba.

Wani kallon tsana Mom take watsa mata, kafin cikin tsananin b’acin rai tace
“Yanzu ku jinin Madu ashe ba zaku tab’a jin tsoron Allah ba? A haka za ku k’are?
Wato Maryam ta yi shine kema zaki biyo ki haukatamin d’a?? To billahilazim na fi k’arfinki!
Duk surk’ullen da kika je kika yi ki koma ki je ki wargaza tun kafin In tashi biyowa ta kanki!.

Saboda Allah Mammy ku kalli yadda Yarinyar nan ta maida Auwal! Auwal fa!!!
Wai yau shine a gaban mace yake kuka haka wiwi da hawaye kamar wani sakare?

Wallahi Allah sai yayi mana hisabi da mu da family d’in Madu ranar gobe k’iyama.
Wanne irin jarababben abu ne yake yawo a jininku sai kace mayu?” Tayi maganar tana kallon Sakina cikeda tsana wadda itanma ta zuba mata nata dara daran idanuwan da suka rine sukai jaa.

Za tayi magana kenan Auwal ya mik’e da kyar ya juya gareta yace “Haba Mom,
abubuwan da suke kai na already sun yi yawa. Dan Allah kar ki zo kiyi haka
kar ki saka ta k’ini completely! Ki koma waje dan girman Allah. Magana muke yi, maganar da ta shafemu iya mu biyu tak! Ba wanda ya gayyotoki ke da k’awayen ki nan”. Ya k’arashe maganar tari yana kufce masa…”

A rikice tace “Auwal na rantse da Allah zan yi maka abunda baka tab’a zato ba!
Karankatakaf fad’in duniya ace ka rasa macen da za ka so sai jinin Maryam Jikar Madu da Shuwa?
Kasan su waye su kuwa?”

Kuka kawai Sakina ta saka ta fara ja da baya…Da sauri Auwal ya juya ya fara binta yana magana yana tari
“Ki tsaya.. Don’t mind her.. let’s talk…Dan Allah..

Sai a sannan Mom ta samu damar shigowa ita da su Mammy. Kamar ma tangad’i Auwal d’in yake yi dan haka suka samu suka wuceshi suka yi kan Sakina!

Mom tana zuwa, ta shak’ota tace “You must mind me!
In dai kina da hankali kuma kin san darajar uwa a wajen d’anta
to ki sani ba zan tab’a barin Auwal ya aurenki ba wallahi!
Dan haka ki hak’ura. Ina fatan Huda ta zame miki lesson a rayuwa amma idan
mahaukaciya ce ke to ki so Auwal ki aureshi dan Allah, wallahi nayi miki alk’awarin sai na lahira ya fiki kwanciyar hankali”Tana gama fad’in haka tayi cilli da ita wanda har ya kaita ga kaiwa k’asa.

Kasa motsi Auwal yayi dan zuwa yanzu ya fara ganin dishi dishi, tabbas ya san halaiyyarsa da kuma Granpa su suka hana Sakina yarda ta auresa amma ya san tana sonshi wanda hakan ne ma yasa ta sanya aka kawo kud’in aurenta da wuri! Duk ya fahimci hakan. Yanzu kuma ga Mom! Ya tabbatar ta gama wargaza masa d’an guntun chance d’in da yake hangowa…. Duk da baya ganinta amman yana iya jiyo setin inda take kuka, dan haka ya fara yunk’urin d’aga k’afarsa domin ya k’arasa wajenta.

Yana motsawa kuwa kamar jira ake jiri yace bismillah! Gabad’aya ganinshi ya d’auke in banda duhu babu abunda yake gani, ga wani mahaukacin juyawa da kanshi yake yi. Da sauri yasa hannu ya dafe kan nashi yace “wash!!”Da d’an k’arfi. Sai a lokacin hankalin Mom da Mammy da k’awar tasu waenda suka k’arasa suka cigaba da tsigale Sakina suna kiranta da ‘talaka, kwadayayyiya’ Ya koma kan Auwal.

Da sauri Mom ta nufesa ganin yana shirin zubewa k’asa amman kafin ta k’arasa har ya fad’i k’asa sumamme..

Dede nan su Daddy Abba da Ummi suka shigo dan dama Ummi kamar ta d’an jiyo hayaniya sama sama…

Ba karamin tsorata Mom tayi ba ganin Auwal a k’asa kamar matacce.

A haukace ta juya ta koma kan Sakina da take nan durk’ushe tana kuka, ta sake shak’ota ta mik’ar tsaye ta hau magana kamar tab’b’abb’iya “Waenna irin mutane ne ku? Baku da tausayi ne? Dolene sai an so ku?
Wallahi na rantse da Allah ko a Birnin sin kika yi mishi asiri yau sai mun je yanzu ba sai gobe ba kin warware shi.” Ta fad’i haka tana k’ok’arin fara janta.

Sakina kam banda tari ba abunda take yi gaba d’aya ta fice a haiyyacinta dan ba k’aramar shak’a Mom tayi mata ba.

“Adama!!!!” Suka ji muryar Dad cikin tsawa a bayansu.

Juyawa Mammy da k’awar tasu suka yi ita kuma Mom ta cika wuyan Sakina ta durk’ushe a wajen ta fashe da kuka.

Dede nan Aslam da Huda suka shigo! Da gudu Hudan ta k’arasa inda Sakina take…

Cikin tsananin b’acin rai Daddy ya k’arasa inda suke ya d’agota ya fara magana “Baki da hankali ne?
Me yake damunki? Wachche irin kwakwalwa ce da ku ne wai? She’s our guest for crying out loud!!
Ga babanta chan a waje ya dawo d’aukar su a haka kikeso a fitar mishi da ita ko yaya?”

Cikin kuka Mom tace Kallafa Auwal” Ta nuna masa Auwal wanda Abba da Aslam suka ciccib’a za su fitar,
cikin kukan taci gaba da magana “Asiri tayi mishi. Irin wanda Maryam ta yiwa Abba bani da tantama!
Daddy a k’asa fa nazo na tarar da Auwal durk’ushe gaban wannan k’ask’antacciyar yana rok’onta ta soshi ta aureshi yana kuka kamar k’aramin Yaro In ba aikin asiri ba tayaya zaka yi tunanin Auwal zai so wannan k k’ask’antacciyar?”Tayi maganar tana nuna Sakina a wulak’ance.

“Tayaya aka yi na so ki har na aureki?” Muryar Daddy ta katse mata maganar da ta yunk’uro za ta ci gaba.
Da sauri ta juyo tana kallonshi cike da shock!

Cikin tsanannin b’acin rai yace “Adama na gaji na gaji da rashin tunanin ki da shirmen ki da son zuciyarki!
Na gaji wallahi.. Tsabar idonki ya rufe daga ganin gaskiya you don’t even realize the fact that Auwal ya nutsu tunda ya had’u da Yarinyar nan. Kar ki bari In chanza miki wallahi ba zaki ji dad’ina ba dan kin kaini bango!.” Ya k’arashe maganar cikin tsananin fushi.

Dede nan Aslam wanda ya dawo daga kai Auwal ya dafa Daddy yace
“Daddy dan Allah ka yi hak’uri.” A hankali Arshaad wanda ya shigo yanzun
shima ya k’araso inda suke yace “Akwai mutane a gidan Daddy, Abba kai yake jira ku kai Auwal asibiti suna mota.”

Kallon Mom yayi wadda ta k’ame tun lokacin da ya fara magana..
Kamar zai ce mata wani abun sai kuma kawai yayi tsaki ya juya ya fita ranshi a mugun b’ace.

Yana fita Mammy ta k’araso ta dafa ta tace “Zo mu je”
Daga nan ta ja hannunta suka nufi wani d’akin a nan k’asan ita da k’awarta..
Suna shiga kamar jira Mom take ta fashe da kuka tace
“Akan Yarinyar chan Daddy ya gaya min wannan maganar??
Waenna irin mutanene su Maryam wai ni Adama…”

Cikin katseta Mammy tace “Saboda haka baki ga ta zama ba!
Ko kuma ince ba muga ta zama ba har sai mun cire ta a zuciyar auwal!.
Sannan akwai wani abunda ya faru na tashin hankali d’azun nan nima na gani
amman kar ki damu dama na gama tsara mana mafita tun kafin in zo
Sannan itama wannan sai mun yi da gaske tukunna zamu cireta a rayuwar Auwal.

Da sauri Mom tace “Kina ganin ciretan zai yiu? Kina gani fa Arshaad bake kad’ai ba har ni d’innan gaba yake yi da ni. In ba asirin aka karya ba ba zamu samu sukuni ba.”

Ajiyar zuciya Mammy ta sauk’e kafin tace “Adama Allah ya jefomu cikin wasu kalar family masu zuciya mai naci dan haka sai mun yi da gaske saboda su na fahimci weakness d’insu mace ce! Ki duba kiga har shi kanshi Granpa d’in duk abun shi kina ga yana yiwa matarsa?”

Cikin kuka Mom tace “Kullum addua ta d’aya kar Auwal ya fad’a kaidin mace kamar iyayensa
sai gashi rana d’aya ya fad’a, ni Adama ya zan yi? Shi kad’ai gareni! Ita kad’ai fa yake gani
ko maida hankali kwana biyun nan na lura ba yayi akan aiki ashe ita ce sila! Kiji Daddy tsabar rashin sanin ciwon kai wai har da ik’irarin Auwal ya nutsu! Shi a ganinshi nutsuwa ce wannan
an haukatamin kwakwalwar d’a amma shi yana ik’irarin ya nutsu…” Ta k’arashe maganar tana durk’ushewa a wajen.

A hankali Mammy ta k’arasa ta hau lalalshinta, sai da taga tayi shiru tukunna ta matsar da bakinta dede kunnenta ta shiga rad’a mata waensu maganganu.

Aslam da Hudan ne suka raka su Sakina har bakin mota bayan sun lallasheta ta yi shiru da kyar!
Har da Arshaad. Sanann suka tsaya suka kira Sumayya a wajen k’awarta suka wuce tare.

Hudan maganganu ne fal a ranta take so tayi da Sakina amman ganin halin da take ciki kawai yasa suka yi musu godiya ta bari akan In komai ya lafa za suyi chatting.

A parlourn suka tarar da Mom Mommy da Mammy da Ummi. Dad ya had’asu gaba d’aya da alamun fad’a yake yi musu. Suna shiga Aslam ya cewa Hudan “taje ta had’o masa Coffee mai zafi please”
Daga nan ya wuce ciki bayan ta amsa masa da “to” ita kuma ta nufi kitchen d’in direct.

Arshaad ma ya wuce d’akinsa.

Arshaad yana shiga d’akinsa Mammy ta mik’e ta nufi d’akin dan they have to talk, ta lura in ta biye shi gaba zai yi da ita. D’azu sau biyu tana zuwa d’akin nasa bata sameshi ba.

Tana shiga su Dad suka gama zaman nasu suma aka mik’e kowa ya kama gabansa.

Ta gama had’awa kenan ta d’auko flask za ta juye wayarta ta fara k’ara!
Tana dubawa taga sunan Sakina dan haka tayi saurin amsawa ta kara a kunnenta.
Ko sallamarta Sakinar bata amsa ba tace “Hudan d’anyi sauri ki fito kinga akwai sak’on da zan baki ashe na manta.”

“Ok”. Hudan tace sannan ta kashe wayar ta ajjiye flask d’in ta rufe had’in nata ta fita.

Tana fita wani mutum ko wata mata ta/ya shigo ta k’ofar baya sanye cikin bak’ak’en kaya kamar irin na leda d’innan na tare ruwa an rufa har hular saman fuska.

Ta chan ciki a fuskar da mask bak’ik’irin, baka ganin komai hatta idanuwan a rufe suke da bak’in glass.
Tafin hannu da k’afa kuma duk da bak’ak’en socks.

Wani ruwa aka zaro a cikin syring aka bud’e had’in coffe d’in da Hudan ta gama had’awa aka b’alle kan syringing kamar za a matsa sai kuma aka tsaya aka yi shiruuu! Da alama mutumin ko matar is having second thoughts.

Ahankali aka ja wani d’an siririn tsaki aka mayar da murfin aka rufe aka ajjiye syringing a gefe kamar ana tunani…

Motsin mutum ya ji ko ta ji dan haka aka yi saurin d’agowa ana kallon k’ofar bayan ta inda aka shigo
ai kuwa aka ci sa’ar ganin giftawar inuwar mutum!

Lalle kuwa ko waye ya gifta to ta/ya san ya ganshi ko ya ganta! Dan haka da sauri aka
bud’e k’ofar bayan aka bi Inuwar da aka gani amman ko da wasa babu alamar mutum a wajen…
Har bayan compound sai da ya/ta zazzagaya amman ba kowa. Ya/ta dad’e a tsaye tana/yana tunani kafin chan ya/ta nufi hanyar kitchen d’in da niyyyar d’auke syringing da ta/ya manta akan kanter kitchen d’in kusa da tray da coffe d’in da ya/ta had’a.

Tana/yana zuwa tayi/yayi saurin ja da baya sakamokon hango Huda da Ummi a cikin kitchen d’in!
Hudan tana juye coffe d’in a cikin flask Ummi kuma ga wani abu a hannunta tana sha suna d’an hira.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 62So Da Buri 64 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×