Skip to content
Part 65 of 73 in the Series So Da Buri by Bulama

39 DAYS AGO!

Gandun Albasa. Gidan shiru, gaba d’ayansu suna zaune kowa yayi jugum!
Kamar a nan ake zaman makokin.

A hankali Shuwa ta juya ta kalli Ummu kafin tace “Gaskiya fa Mama ta fad’a Ummu, ku je kawai ke da Sakina. Ai ta ce ta kirashi ko?”. A hankali Mama ta d’aga kai alamun ‘eh’. Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin tace, “To shikenan Hajiya. Sakina taso mu je,
Babanku yana waje.”

A hankali Sakina ta d’an kalleta sai kuma ta d’auke kai tace “Ummu, dan Allah ki je kawai ko da Sumayya ne
ba na son zuwa gidan wallahi”. D’an k’ura mata ido Ummu tayi kafin tace
“Taso mu je! Ba na son shirme. Ba zaki yiwa su Abba da Aslam gaisuwa ba ko me??”. A hankali Mama ta ce “Ummu barta kawai ku je ke da Sumayya.” Shiruu Ummun tayi kamar za tayi magana sai kuma tace “Sumayya mu je”. Ta fad’i hakan tana mik’ewa ta d’au mayafinta ta nufi k’ofa da alamun ranta ya b’aci.

Suna fita ita da Sumayya Hajiya Shuwa ta mik’e ta fita tsakar gidan don yin zagaye saboda kumburin da k’afafuwanta suke yi idan ta zauna shiru.

A hankali Mama ta mik’e ta koma kan kujerar da Sakina take zaune 2 seater..

Tana ganin ta dawo kusa da ita ta tashi ta zauna da kyau sannan ta d’an sunkuyar da kanta a hankali tace “Bara inje d’aki in kwanta”. Tana shirin mik’ewa Mama ta kamo hannunta ta rik’e.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta sunkuyar da kanta k’asa.

Sai da Mama ta gama k’are mata kallo ta gama nazartar ta tukunna tace
“Nima b’oye min za ki yi?”

Da sauri Sakina ta d’ago tana kallonta kafin ta juyar da kanta tace
“Me ne zan b’oye miki Mama?”
Tana k’ok’arin danne kukan da taji ya taho mata.

A hankali Maman ta sa hannunta ta juyo da fuskarta sannan ta ce
“Tun ranar da kikace kin bawa Ashraff go ahead ya turo Sakina har yau ban ga walwala a kan fuskarki ba! In akwai wani abun ki yi magana a samu a gyara Idan mai gyaruwa ne. B’oye b’oye ba abunda yake janyowa sai dana sani a rayuwa. D’azu Ina jinki a band’aki ke kad’ai kinata kuka!
Meye ne yake damunki? Ko na tashi daga Mama na koma wata daban wadda ba zaki iya gayawa damuwarki ba?”

Duk k’ok’arin Sakina na ganin ta tsayar da kukanta kasawa tayi, tashi d’aya ta hau ambaliyar hawaye ta shiga kuka tsakaninta da Allah..

Janyota Mama tayi zuwa jikinta ta rungumeta. Sai da tayi me isarta
tukunna ta yi shiru da taimakon lallashin Mama, kafin a hankali ta fara magana. “Daman akan Ya Auwal ne cousin d’in su Hudan.” Tun ranar da suka fara ganin juna har kawo yanzu
ba abunda Sakina ta b’oyewa Mama…

Kallon ta Maman take yi tana sake wa kafin a hankali ta ce “Sakina wa ya gaya miki ana aure saboda a yakice soyayyar wani daga cikin zuciya?”
Bata jira jin me zata ce ba tace “to bari kiji in gaya miki.

Shekarata goma sha takwas tare da Ya Usman matsayin mata da miji amman har yau ba abunda ya shiga zuciyata game da shi ta fannin soyayya sannan ba abunda ya ragu a cikin soyayyar Abba a zuciyata.”

Da sauri Sakina ta d’ago tana kallon ta sai kuma ta fashe da kuka ta ce
“Mama dan Allah kar ki yi min fatan in yi dakon soyayyar Ya Auwal haka har k’arshen rayuwata! Wallahi tallahi In dai yadda nake ji akanshi haka zan ci gaba da ji har abada bayan bana tare da shi tabbas mutuwa zan yi”. Ta k’arashe maganar tana kifewa akan cinyar Mama tana sakin wani sabon kukan.

A hankali Mama take shafa kanta.
Sai da taji ta d’anyi shiru tukun tace
“Sakina ba zan b’oye miki ba, kin yi mistake!”

A hankali ta d’ago tana kallon Mama da dara daran idanuwanta da suka rine sukayi jazir.

Jinjina kai Maman tayi alamun tabbatarwa.

Cikin share hawaye Sakina ta ce “Mama kin ji fa abunda Mom da Mammy suka yi min still in aureshi?
Daman ni saboda family d’insa shiyasa na k’i tun farko bana san issues sannan…” Sai da ta d’anyi k’asa da kanta kafin tace “Sannan womanizer ne shi ne ya yiwa Jalila ciki fa”

Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace, “Sakina Ubangiji ya halicci bayinshi kowa da irin yananyin tashi k’addarar! Idan Allah yayi wannan ce k’addararki kina ganin kina da wayon da za ki kufce?.

In dai Auwal yana sonki tsakani da Allah to zai daina abubuwan da yake yi, za ki iya gyarashi besides ai Auwal d’in ya shiryu ke kanki kin ce Arshaad tun ba yau ba ya cewa Hudan ya ga changes a tare da shi sannan kin ce Mahaifinsa shima yace ya shiryu!
Ni a ganina zaki iya sake gyarashi tunda yana son ki wanda Allah kad’ai ya san d’umbin ladan da za ki samu.
Tabbas ban so ki aura irin Miji mai halinshi ba ko da ace ya shiryu amman in dai haka Allah ya tsara yana sonki
kema kuma kina son abunki to ya za ai?. Kuma Mahaifinsa ma baya k’in ki yana son ki wanda shi ne yake da say a gidan! Tabbas Mom matsala ce amman ni a ganina zugar Mammy ce yadda
kika ce tanata kuka ta rikice a lokacin da ya suma na tabbatar inda ba a kawo kud’in auren ki ba to da tuni yanzu tazo nan gidan saboda farin cikin d’anta dan tana tsananin sonshi
wanda hakan shi zai sakata ta sauk’o ta so ki. In sha Allah.

Yanzu kam ba abun yi sai dai hak’uri.
But by any chance kar ki sake yunk’urin toshe hanyar da za ku bi ku mallaki juna ke da Auwal! Ko da wasa, tunda kuna son juna.”

Kukan da Sakina take ne yasa Mama ta janyo ta jikinta, a hankali ta shiga lallashinta kafin tace “Ki yi hak’uri
Allah ya zab’a miki mafi alkhairi.
Ku yi ta addua. Allah ya zab’a mafi alkhairi.”

Da kyar Mama ta samu ta lallab’ata ta yi shiru dann ita kam ta san inba wani tsananin rabo ba to Auwal yayi mata nisa! Ta riga ta datse duk wata igiyar da zata k’ullasu su kasance tare k’ark’ashin inuwa d’aya da hannunta.

A Cikin kwanakin da ba su kai wata d’aya ba da Anty Zainab ta yi da Sadiya tabbas ta fahimci ba zaman amana take yi da ita ba!

Mamaki k’arara take yi game da yadda Abotar tasu take k’ok’arin juyewa ta koma wani abun na daban.

Haka nan ita za ta yi musu girki da kud’inta saboda duk wani ragowar gari ko abun dafawa da suke da shi Umma ta tattare tace “babu ya k’are!”
Sai ta fita aiki ita da Jalila su dafa su ci. Tun bata gane ba har tazo ta fara fahimta. Ga shegiyar k’azanta daga Umma har Jalilan sannan wani lokacin Jalila har yada mata da magana take yi wai ‘anzo an zaune musu a gida!’ Sannan Ya Ja’afar kwata kwata basa kula da shi dan wani lokacin wandonshi har tsutsa ne suke binshi
gashi kullum cikin datti kacha kacha
especially gashin kansa sak mahaukacinsa!

Haka nan zata tartare kitchen da band’aki dan idan zai yi tsutsu ba za su gyara ba! Sannan ta gyara Ya Ja’afar ta fita aiki ta je ta dawo ta dafa kuma su ci tare.bAna cikin haka Junaidu ya dawo. Ranar suna zaune a d’aki suna d’an tab’a hira kawai suka ganshi ya shigo! Da farko Umma tsorata ta yi dan ihu ma ta yi, fahimtar da tayi ba ita kad’ai ce take ganinshi ba yasa ta tashi ta k’arasa ita da Jalila inda yake.
Sai da suka d’an tab’a fuskarshi da jikinshi suka tabbatar da shi d’inne tukunna suka rungume shi a tare suka fashe da kuka. Tabbas shima yayi matuk’ar kewar gida shiyasa bai san lokacin da hawaye suka wanke mishi fuska ba. Da taimakon Aanty Zainab aka samu suka yi shiru ita ma ta rungume shi tana d’an nata hawayen sannan suka nema waje suka zazzauna.

Tun daga lokacin duniya ta dawowa Umma da Jalila sabuwa!…. Hankalin Junaidu ba k’aramin tashi yayi ba ganin halin da Ya Ja’afar ya ke ciki.
Bai yi k’asa a guiwa ba haka suka kinkimeshi shi da Jalila suka sa a mota suka nufi asibiti. Bayan y’an dube dube Likita ya basu sunan asibitin da ya kamata a kaishi.

Ba abunda ya fi bawa Jalila mamaki irin kyan asibitin da mak’udan kud’ad’en da Ya Junaidun ya bayar
daga nan suka amshi Ya Ja’afar d’in.
Kusan kamar gidan mahaukata haka wajen yake amman ana basu kulawa da treatment mai ma’ana.

Suna dawowa washegari ya fara da case d’in Baba shima wanda tun ranar da ya dawo yaje ya ganshi a gidan Kaka don tun dawowarshi a wajen Baba Talatu yake.

To anan ma an kashe kud’i wajen bincike da ragowar abubuwa, duk kuma tare ake zuwa da Jalila wadda babu abunda tafi sakawa ido irin aljihun Junaidun dan haka tana dawowa gida take sayarwa da Umma Jarida! Nan kuwa suka maidashi atm. Tun abun yana burge Anty Zainab har yazo ya fara bata tsoro saboda yadda Junaidu yake wasa da kud’i ya kamata a bincikesa.

Ita kuwa Umma ba abunda ya dameta, da Anty Zainab tayi mata maganar ma cewa tayi “Kar su yi mishi magana
yayi tunanin zarginshi suke yi ya rage basu kud’in”. Tun daga nan Anty Zainab taja bakinta tayi shiru bata k’ara magana ba.

Su Umma duniya ta dawo sabuwa! Hatta shinkafa basmati ake ci a gidan
Kaji kuwa ba a magana. Wani zubin ma da daddare sai dai a siyo tsire ko pizza da fresh milk aci a kwanta.

Har gidan su Kaka da Abba Madu junaidu bai bari ba alkhairi na yau daban na gobe daban.

Tabbas zama da Sadiya sai mutum mai d’ankaren hak’uri! Dan wannan duniya da jin dad’in da ta samu
sai ta mayar da Anty Zainab kamar wata bola! Idan an kawo kaji sam ba zata bari ta tab’a ba ma, ita da kanta za ta gyara ta soya su d’ibar mata dan wulak’anci a nata kason kai da k’afa suke fitowa, sam basa la’akari da ‘shi Junaidun nephew d’inta ne itama’.
Idan ya zo fita suka ce suna buk’atar kud’i har da na Anty Zainab yake ajjiyewa amman sai su hanata!
Abubuwa kala kala haka ta dinga fuskanta wanda daman ance ba a gane asalin halin mutum sai an zauna tare ko an yi yunwa. Gashi wani abun mamaki, sam Umma tak’i yarda su koma wajen malaminsu tare! Kullum sai sun bari ta fita aiki sai su je ita da Jalila, idan ta dawo sai ta tarar sun je sun karb’o mata sak’o. Gashi kullum ita ke bada kud’i su basa bada ko sisi
wannan watan tun kafin wata ya zo k’arshe an bita bashi ba dan Khadija da Yayarta sun aiko mata kud’i ba to da bata san ta ya zata dinga zuwa aikin ba ma.

Haka kurum yau taji bata yarda da bayanin su Umma ba dan a gaskiya so take a san yanda za ai ta koma gidanta! Shiyasa tana tashi a aiki ta wuce wajen mutumin da kanta.

Hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba da taji bayanin mutumin tabbas ashe shiyasa ko waya idan tace su kira a gabanta sai suce an sace wayar mutumin bashi da waya yanzu.
Jiki ba kwari haka ta yi mishi sallama dan ita kasa ma yi mishi bayanin komai tayi ta mik’e kawai ta tafi.

A tsakar gida ta samesu. Suna gashin zabi akan abun gashi, gaba d’aya gidan ya d’au k’amshi.

A hankali ta k’arasa ta zauna a kan tabarmar da suka shimfid’e a tsakar gidan ta kalli Jalila ta ce “Auta dan Allah d’an kawo min ruwan sanyi a fridge d’in Junaidu in akwai”Ba tare da ta kalletaba tana chattn a wayarta tana nan kwance akan tabarmar bata motsa ba tace “Babu!”

Ajiyar zuciya Anty Zainab ta sauk’e kafin tace “Je ki duba”. Ta yi maganar cikin d’an tsare gida.

Banza Jalilan tayi da ita.

“Hmmm” Umma wadda take zaune akan kujerar tsugunno a gabn abun gashin tace sannan ta juya ta kalli Jalilan tace “Auta dan Allah je ki duba mata mana.”

Tsaki tayi ta ajjiye wayar sannan ta mik’e ta wuce d’akin.

Tana wucewa Umman ta juya ta ci gaba da abunda take yi, ba tare da ta kalli Anty Zainab d’inba tace a “Zainab y’ay’an yanzu fa sai hak’uri, in ba da Allah ka had’a su ba ba zuwar maka aike suke yi ba.”

Murmushin takaici Anty Zainab tayi kafin tace “Y’ay’an da aka b’ata dai!
Y’ay’an da son zuciyar iyayensu take kaisu ga halaka”.

A zabure da mamaki Umma ta juyo tana kallonta sai kuma ta kwashe da dariya ta rangad’a gud’a! Kafin ta ajjiye brush da man hannunta ta juyo gaba d’ayanta ta gyara zamanta
ido cikin ido ta kalli Anty Zainab d’in kafin tace “Kin san Allah! Bar ganin wai kin san cikina na san naki Bar ganin mun yi Abotar sama da shekaru talatin da ke! Billahil Azim kin ji rantsuwar y’ar musulmi ko? Yanzun nan zan murzawa idanuna toka in gurza miki rashin mutunci, har makofta sai an jiyo mu.” Ta k’arashe maganar tana d’aga murya.

Cikin tsananin b’acin rai Anty Zainab tace“Murzawa ido toka kuma na nawa Sadiya? Banda tsantsar son zuciya da son kai da rashin sanin ya kamata mai kuka sani?”

This time around mik’ewa tsaye Umma tayi cikin kad’a hannuwa tana gyara d’aurin zaninta tace “Oya oya Zainba shiga d’aki yanzun nan ki d’auko kayanki ki yi waje! Tun kafin mu kasa sheda juna ni da ke.”

Daidai nan Jalila ta k’araso wajen da gorar ruwan sanyi a hannunta, ba tare da ta san dalilin hayaniyar da ta tarar ta d’an fara tasowa ba tace “Ko baki ji abunda aka ce miki ba ne? ‘Out’ ta ce!!!!”

Anty Zainab d’in bata kulata ba dan ba saar yin ta bace ba, ta kalli Umman tace “Ko baki koreni ba Sadiya na gama zama da ke, dan ba zan tab’a zama kina yi min zagon k’asa ba, amman kafin In tafi ina so ki san na san abunda kuka yi ke da y’arki. Yau naje wajen Malam yanzu haka ma daga chan na ke” Bata damu da yadda maganar tata ta girgiza su ba taci gaba da magana “Sadiya da kika san ba zaki bari ayi min abunda nace ba ai da kin fito kin fad’amin na chanza shek’a, tunda na san dalilinki na hana ayi aiki na saboda kina gani ata dalilin aikin Jalila ne na samu matsala so kar azo a gyara nawa azo ita kuma Jalila ta rasa Arshaad ko? Haka ne ko ba haka ba?
Haba Sadiya!! Wacce irin zuciya ce da ce? Wacece Ummul aba’isin fad’awata wannan matsalar tsofai tsofai da ni?
Ko kina tunanin ban san abunda nake yi ba? Sarai fa na fahimci komai
kuma duk dan kar ku ji ba dad’i shiyasa na ja bakina na yi shiru.

Abun naki ma ni sai na ga kamar har da mugunta saboda a ganina. Idan kin ce nace na hak’ura da Baban su Khadija bana son komawa gidansa a bar aikin mene kuma zaki d’aura da cewa a yi abunda ba zan koma ba? Haka muka yi da ke? Haka alk’awari ya ce Sadiya saboda Allah?” Anty Zainab ta k’arashe maganar tata tana fashewa da kuka saboda wani takaici da dana sanin biyewa Sadiya da ta dinga yi tun Yarinta da ya lullub’eta lokaci d’aya.

Da kyar ta samu ta lallashi kanta ta share hawayenta sannan ta d’ago ta kallesu! Su na nan a tsaye sun yi cirko cirko tace “Bari ku ji in gaya muku..
Wutsiyar rak’umi ta yi nesa da k’asa! Ba na duba bana buga k’asa dan bin malaman ma ke kika saka ni amman wallahi tallahi ku rubuta ku ajjiye in dai Arshaad kuke jira ya dawo ya auri Jalila to kuwa zata k’are ne a haka har abada babu Miji! Ku d’auki maganata as curse a matsayina na k’anwar Mahaifinta, bi’ma’ana baki ne na yi mata.”

Wani wawan tsalle Umma tayi ta dira kan Anty Zainab ta shak’o wuyanta wanda sai da ta kaita k’asa Ba su yi wata wata ba suka rufeta da duka ita da Jalila.

Tun Anty Zainab tun tana daurewa har ta ware murya ta hau zunduma ihun neman agaji.

Da kyar mak’ofta suka kwaceta a hannunsu bayan sun shishshigo..Still inbanda zage zage da tujara ba abunda Umma da Jalila suke zubawa. Wata mata ce tace mata “Ta zo su wuce ta kaita wajen Talatu ta d’an kimtsa daga nan sai ta wuce gidanta saboda gaba d’aya jikinta sun yi mata jjina jina.”

Ba wanda ya iya tanka musu dan an san halinsu, haka nan matar ta kama Anty Zainab wadda take tafiya da kyar ta jata sukai waje Mutane ma aka fara watsewa.

Wani tsohone ya kasa hak’ura ya juyo ya kalli Umma yace “K’anwar Mijinki ce fa! Kuma k’awarki tun kuna Yara saboda Allah idan ke kin daketa ai bai kamata ki bar y’arki ta d’aura ko da yatsa a jikinta ba. Wannan rashin sanin ya kamata har Ina? Ki bi duniya a sannu fa, Sadiya.”

Yunk’urowa ta yi zata yiwa tsohon rashin mutunci wasu samari biyu da suma basu kai ga fitaba suka yo kansu d’ayan ya ce “Kun san Allah In rashin d’a’a ne mu har certificate muke bayarwa! In kuma kanku na hayak’i to ku tanka mu gani”

Shiruuu, suka yi ba wadda tace uffan.

Girgiza kai kawai tsohon yayi ya juya ya fita.

“K’ananan marasa kunya kawai” Samarin suka ce kafin su juya su fita, daga nan aka watse aka barsu su biyu suna huci.

Su Baaba Talatu suna tsakar gidansu na ciki wajen d’akinta a kan darduma gaba d’ayansu hankalinsu a mugun tashe dan yanzun nan aka shigo da results d’in tests d’in da aka yi wa Baba! Suna a haka aka shigo da Anty Zainab. Da sauri Ya Jamilu ya mik’e ya k’arasa kusa da matar yana tambayarta “lafiya?” Dan su da farko ma basu gane Anty Zainba d’in ba
saboda gabad’aya fuskarta jini ne.

Tiryan tiryan matar ta koro musu bayani tun daga kan ihunta da ta jiyo da yadda idanuwanta suka gane mata Sadiya da Jalila a kanta suna jibgar ta.

A hankali Shuwa ta mik’e ta k’arasa ta kamo hannun Anty Zainab ta cewa matar “an gode”

Matar tana fita Baaba Talatu ta rarumi mayafinta! Da sauri Kaka ya mik’e yace “ina za ki je”

Fashewa ta yi da kuka cikin kukan tace “Kar ka hanani. Na rok’eka da girman Allah kar ka hanani ci ma Sadiya yau!
Duk abubuwan da take yi bana magana yau kam ta kaini bango wallahi.”

Kallonta kawai Kaka yake yi kafin cikin b’acin rai yace “Laifin waye Zainab taje gidanta ta zauna?”
Ta bud’e baki kenan zata yi magana ya d’aga mata hannu yace. “Dan Allah ki barmu mu ji da Usman yanzu! Shuwa ku wuce ciki ki taimaka mata ta gyara jikinta ku kyale Sadiya kawai! Kuna ganin halin da Mijinta yake ciki ai amman wani lokacin sai ta yi kwana biyu ma bata lek’o shi ba! Ku zuba mata ido ita da y’arta zan samu lokacinsu kwanan nan.”

A hankali Shuwa ta jaa Anty Zainab suka shiga ciki Baaba Talatu ma tabi bayansu tana sharar kwalla. Kaka kuma da Ya Jamilu suka koma inda Baba yake zaune yana ta faman zubar da hawaye.

Sai da aka had’a da allurai da magungunan bacci tukunna Anty Zainab ta samu ta iya runtsawa a ranar. Washegari kuwa sai da Shuwa ta yiwa su Khadija da gaske tukunna suka hak’ura amman da cewa suka yi sai sun je sun samu Sadiya da Jalila sai dai a tashi gidan wallahi! Daman chan ita Khadija basa shiri da Jalila kwata kwata.

Da yamma bayan su Khadija sun wuce, Mama da Shuwa suna zaune suna kallo Baaba Talatu ta shigo. Yanayin ta kad’ai yasa Shuwa ta fahimci abunda ya kawota a hankali ta lumshe idanuwanta ta bud’e sai kuma kawai ta mik’e ta bar wajen.

A hankali Baaba Talatu ta k’arasa inda Mama take ta zauna sannan ta amsa gaisuwar da Maman take yi mata da fara’a, sai da suka gama gaisawa tukunna ta mik’a mata takardun hannunta da ta shigo da su.

Kallonta Maman tayi kafin ta kalli takardun sai kuma tasa hannu ta karb’a ta fara karantawa.

Tabbas ta sha wahala a hannun Baba
amman ba k’aramin tausayinsa ta ji ba. A hankali tace “Allah sarki Ya Usman” wasu hawaye suna zubo mata.

Hannayen ta duka biyu Baaba Talatu ta kamo kafin tace “Dan Allah dan Annabi Maryam Ina neman alfarma a wajenki…Usman bashi da lafiya dududu sauran mishi bai kai shekara ba! Ya nemi a maida aurenku
dan yana so ya mace a matsayin Mijinki. Na san Usman bai kyauta miki ba! Na’am ya yi laifi amman a halin yanzu bashi da maraba da babu. D’an lokacine wanda ba zai ma kai shekara ba kawai za ku yi tare. Dan Allah Maryam.”

Kasa magana Mama tayi. Sai da Baaba Talatu ta sake cewa “Maryam”. Tukunna ta juyo a hankali tace “Baaba dan Allah dan Annabi kar ki rok’eki abunda ba zan iya ba! Ki yi hak’uri amman a gaskiya wannan alfarmar taki ta yi tsauri da yawa.”

Bayan kwana biyu, Baaba Talatu ta sake dawowa. Sun dad’e suna magana da Mama.

Haka kurum kamar almara Mama ta samu su Madu tace “ta amince da auren Baba! Tunda ya rok’i yana neman alfarmar ya mace a matsayin Mijinta to zata yi mishi hakan a matsayinshi na wanda take kallo kamar d’an uwa”

Ba yadda ba su yi da ita ba amman fur!! Tace “Ya Usman kamar d’an uwa yake a wajenta dan haka zaata zauna da shi na shekara d’ayan ba komai.”

Ba dan sunso ba suka amince saboda sun riga sun yi alk’awarin ba za su sake tilastamata ko su sakata tayi abunda bata so ba.

Sai dare Shuwa taje ta sameta,
cikin son fahimtar da ita ta shiga yi mata nuni da yadda Abba yake ta faman zirya…

A hankali Mama ta yi murmushi kafin tace “Hajiya ni fa dama na gama yanke shawarar ba zan koma gidan Abba ba”

Da mamamki Shuwa take kallonta.

A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Jin ku kawai nake yi Hajiya,
amman yanzu tashi d’aya in na koma cewa za ai kamar Ina jira matarshi ta mutu ne. Sanann ko baya ga hakama
na riga na gama deciding in dai ba Mahaifinsa bane ya amince da ni to ba zan tab’a komawa ba, ina so Mahaifinsa ya nema mishi aurena kamar yadda ko wanne uba yake yi wa d’ansa sannan ya yi welcoming d’ina cikin zuri’arshi, ya karb’eni a matsayin surukarshi kamar yadda ko wanne uban Miji yake yi wa matar d’ansa, na san hakan ba zata tab’a kasancewaba
ni kuma In ba hakan yayi ba to ba zan koma ba! Kinga kuwa babu batun maida auren mu ni da Abba dan na san Mahaifinsa ba zai tab’a amincewa ba sannan ba zai yi waennan abubuwan da nake kwad’ayin inga yayi min ba.

Shuwa za tayi magana Mama tayi saurin d’aura hannunta a kan bakinta
ta ce ‘dan Allah ta yi shiru, a bar maganar’. Saboda ita kanta daurewa kawai take yi.

CONTINUATION!.

Driving Aslam yake yi cikin nutsuwa, har suka isa MT estate ba wanda yace k’ala! Dan kowa akwai abunda yake tunani.

A cikin gidan Granpa ya yi parking, da sauri driver d’inshi ya k’araso ya bud’e mishi motar ya fito cikin kamala suka nufi cikin gidan direct. Ba kowa as usual, har chan sama suka wuce tare. A hankali Granpa ya d’an kalleshi ya ce “ka fad’awa su Yusuf Ina buk’atar ganin kowa da kowa anan after isha”

“Okay Granpa” Aslam d’in yace daga nan Granpa ya nufi personal parlourn shi wanda zai sadashi da bedroom d’insa.

Da mugun sauri Aslam wanda yake ta faman kame kame ya na rarraba ido ya fad’a d’akin Gramma.

A zaune ya tadda su suna hira su biyu.

Da sauri duk suka d’ago suna kallon k’ofar ganin yadda ya afko.

Dariya Gramma ta yi kafin tace “K’araso mana”. Sannan ta mik’e tace
“Granpa ya dawo ko? Arshaad yace tare kuka fita”

“Eh yana d’akinsa” ya bata amsa sannan yad’an russuna ya gaida ta cike da ladabi.

Sai da ta k’arasa bakin k’ofar tukunna ta d’ago kansa ta amsa sannan tace “Sannu da zuwa, ya hanya?”

A hankali yace “Alhamdulillah”
Yana d’an satar kallon inda Huda take zaune ta sunkuyar da kanta.

Murmushi Gramma tayi sannan ta sa kai ta fice ta ja musu k’ofar dan ta lura idan ta ci gaba da zama a d’akin Aslam na iya zuwa ya rungumo matarshi a gabanta.

A hankali ya ke takawa har ya k’arasa inda take ya tsugunna a gabanta.

Da sauri ta lumshe idanunta ta fara k’ok’arin nemo nutsuwa da lakkar jikinta dan ta gaza samunsu. A hankali ya kamo hab’arta ya d’ago da fuskarta
yana kallon yadda ta runtse idon da k’arfi!. Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “I miss you.. Sosai!!!”

Bata bud’e ba kuma bata yi magana ba, tana nan a yadda take.

A hankali ya fesar da numfashi yace
“Ko you still need more time?”

Sai a lokacin ta bud’e idanunta da suka d’an tara hawaye tace “Moree time for?”

Ba tare da ya bari ta jaa numfashi ba yace “Us! More time for us, ranakun da na baki sun yi miki kad’an ko? I was so eager to see you amman ke naga ko murna ma ba ki yi da ganina ba”. A hankali yana kallonta yace “ko arzik’in sannu da zuwa ma ban samu ba.
Ya fad’i hakan yana d’an cika hab’arta sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar ta.

Da sauri ta yi k’asa da kanta tana jin yadda k’irjinta yake dukan uku uku.
A hankali ta ji ya ce “Umm??” Cikin wani kalar yanayi da siga.

Sai da ta sake yin k’asa da kanta tukunna tace “Ina wuni, ya hanya? Ya aiki?”

Ajiyar zuciya ya fesar kafin yace
“Lafiya, hanya Alhamdulillah. Aiki kuma, was terrible! Na d’an samu matsala har ya kai ga an rufe company d’ina na chan.”

Da sauri ta d’ago ta kalleshi kafin tace “Subhanallah. Garin yaya?”

Ya ji dad’in yadda ta damu da alamarin ba kad’an ba. A hankali ya d’anyi murmushi cikin son kawar da zancen company d’in yace “Don’t worry, ba komai. Ai inada wani ni da Abba. Daman bawa ya kan samu abu
at any time kuma ya kan rasa, wannan yana daga cikin k’addarar bawa, fata kawai shine ya zamo mai yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau”
A hankali ya sa hannu ya kamo nata yace “wata biyu baya!, Ubangiji yayi mini kyautar da sai da na suma tsabar farin ciki! Ya bani abunda na riga na fidda rai da samu, Amma yanzu a ce dan na rasa company sai in damu?”
Yayi mata tambayar yana wani sassanyan murmushi.

A hankali k’irjinta yana wani mahaukacin racing tun da ta fara jin bayaninsa, ta d’ago tana kallonshi.
Har yanzu murmushi yake mata.

Wasu hawaye ne suka zubo mata dan ta so ta fahimci inda ya dosa! Cikin son fahimtar da shi da kuma kawo k’arshen bagwaren relationship d’in nasu a hankali tace, “Ya Aslam shike nan yanzu Granpa zai sake cewa ni bad luck ce kenan”. Sai kuma ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara share hawayenta.

Shi da farko ma bai fahimceta ba saboda yadda ya shagala da kallon lips d’inta, sai da yaga ta fara kuka tukunna yad’an dawo dede sannan ya fahimceta! Dariya ma shi ta basa
dan haka a hankali yayi y’ar dariya kafin yad’an matse hannunta wanda yake a cikin nashi yace “In ya fad’i hakan, sai yaya?”

Da sauri ta d’ago tana kallon yadda yake mata wani murmushi mai tsada!
Cikin zubar hawaye ta ce “Masoya ma wasu in sun lura zaman su tare zai na causing problem hak’ura suke yi da juna, ballantana kuma mu. Tun kafin abu yayi nisa azo tun Granpa yana magana shi kad’ai har kowa ya fara gara kawai mu rabu da juna Ya Aslam ka samu wadda kake so ka aura
nima in.”

Da sauri ya d’aura d’ayan hannunshi akan lips d’inta yace “shhh…” Bai jira jan lokaci ba yace “Ni already na samu wadda nake so Hudatie, bana jin kuma zan sake son wata a gaba sai dai wani ikon Allahn. Tunda Allah ya bani ke ya gama mini komai.” A hankali ya cire hannunsa a lips d’inta ya yi cupping fuskarta a cikin palms d’insa biyu ya d’ago da kan da take ta k’ok’arin b’oyewa yace “open your eyes”.
Gam!! Haka ta sake runtse idanuwan nata k’irjinta na dukan uku uku da wani kalar mahaukacin sauri.

Cikin matso da fuskarsa daff da tata ta ji yace “Open your eyes before i kiss you!” Da sauri ta ware idanuwan nata tarr! Ta zuba su a cikin nasa. Kallonta yake yi itanma shi take kallo ta ji yace
“I love you”.

Da sauri ta runtse idanunta sai kuma hawaye sharr! Kamar an bud’e fanfo.
A hankali cikin kuka still yana rik’e da face d’inta tace “Ya Aslam dan Allah kar ka yi haka. Za aga kamar daman chan muna son juna. Za a ganmu kamar butulu. Ba sona kake yi ba,
idan muka rabu ka had’u da true love d’inka zaka fahimci hakan. For now dan Allah let’s just end this relationship.” Muryartace ta mak’ale sakamokon had’e bakinsu da yayi waje d’aya! Wani Irin salo ya shiga aika mata da shi wanda ya kusan tarwatse kwakwalwarta. Sai da ya ji tana shirin sume masa tukunna ya janye a hankali ya bud’e rinannun idanuwanshi, yana maida numfashi, a hankali yace
“Those this feel fake?”

Fashewa tayi da kuka ta fara k’ok’arin kwace fuskarta amman yak’i bata dama. Instead ma kawai sai ya janyo ta izuwa jikinshi yayi hugging d’inta ya shiga shafa bayanta alamun rarrashi
yayin da zuciyoyinsu suke bugawa a tare da mugun k’arfi.

Jin yanda take kuka sannan ta ma k’i ta saurareshi yasa ya cikata a hankali yace “ki gayawa su Shuraim Granpa yana son ganin kowa after sallar isha.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan yaga kamar tana buk’atar fitar tasa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< So Da Buri 64So Da Buri 67 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
0
Free daily stories remaining!
×