Tunda Baba Bashir ya shiga gida yake ta faman kai kawo, ba wai tunani yake akan wa Mama zata aura tsakanin Baba da Abba ba a’a tunani yake yi ta yadda zai fahimtar da Baaba Talatu dan already ya gama deciding tunda dama Mama tace ‘saboda Granpa yasa ba zata koma ba’ Gashi kuma yanzu Granpa d’in ya zo da kansa to kuwa in sha Allah ba zai yi k’asa a guiwa ba sai yaga an d’aura auren Mama da Abba. Kawai shi yanzu damuwar shi Baaba Talatu ce dan ko jiya da kyar tayi bacci! Halin da Baba yake ciki ya tada mata hankali ba kad’an ba so take kawai taga farin cikin shi ta ko wacce hanya tsananin tausayinsa take yi.
Ya dad’e yana nazari kafin ya d’au hanyar d’akin da Baba yake jinya dan yana ganin gara su fara maganar da shi tukunna. Yana zuwa ya d’aga hannu kenan zai tura k’ofar ya ji suna magana shi da Ya Jamilu.
MT ESTATE.
Kamar yadda Granpa ya buk’ata, ana fitowa a masallaci su Abba suka bi bayanshi zuwa gidansa..
A nan parlourn suka tarar da Mommy Mammy Gramma Huda da Aaima. Ko ciki bai shiga ba ya nemi waje ya zauna a kan cousion ya fara bin ahalin nashi da kallo one by one waenda suke nan jere a gabanshi wasu a kan kujera wasu a kan kafet. Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya kalla Aslam yace ‘ya bud’e taro da addua’.
Cikin nutsuwa ya jagoranci adduar suka yi suka shafa tukunna Granpa ya gyara zama yace “Abubuwa uku! Zuwa hud’u ne suka sanya na taraku a nan. Na farko Aisha,. Kafin Zainab ta cika ta rok’eni akan in tayata neman yafiya da gafarar ki! Sannan nima in nema yafiyarki dan tabbas an zalinceki a baya, da fatan za ki yafe mana.”
Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e a hankali tace “Komai ya wuce. Na yafe na manta da komai Allah Ubangiji ya ji k’an Zainab ya sa tana aljanna Firdausi.
A hankali duk suka ce “Ameen”.
Sai da Granpa yad’an lumshe idonshi ya bud’e tukunna ya kalla setin da Abba da Daddy suke yace
“Yusuf, Yakubu, kuna iya dawowa estate anytime from now. Komai ya wuce.”
A hankali Dad wanda tunda suka zauna yake ta k’ok’arin ganin bai bari kwallarshi ta zubo ba ya sa hannu ya goge hawayen da suka samu nasarar zubo masa.
Ahankali kamar had’in baki su duka ukun suka ce “Alhamdulillah”. A fili, kafin Daddy ya ce “mun gode Granpa Ka yi hak’uri ka yafe mana.” D’an guntun murmushi yayi kafin yace “Ni za ku yafewa, Ina neman…..”
Da sauri Abba ya katseshi ta hanyar cewa “Dan Allah kar ka rok’emu yafiyar komai, kai Mahaifinmu ne kuma d’an Adam ajizi ne, kasancewarka Mahaifin mu ya sanya tun kafin ka yi mana wani abun ma mun riga da mun yafe maka! A Yanzu ba abunda muka fi buk’ata kamar yafiya da albarkar ka saboda tabbas na san mun kwashi zunubi ata dalilin k’ok’arin mu na ganin mun nuna maka daidai.
Ka yi hak’uri Daddie a ko da yaushe zan baka hak’uri ne in yi ta baka hak’uri har k’arshen rayuwata”
Ya k’arashe maganar hawaye suna tsilalo masa.
Mik’ewa Granpa yayi ya k’arasa inda yake ya kamo hannunshi ya mik’ar da shi tsaye sanann yace “Magana ta uku, na amince maka ka auri Maryam! Na yi accepting d’inta, sannan ina yi maka albishir d’in d’azu mun je ni da Aslam na nema maka aurenta da kaina kuma an baka! Ka zab’i gida d’aya a cikin gidajen estate d’innan ko wanne yayi maka ka gyara mata dan iyayenta sun ce anytime from now za su nemeni akan batun d’aurin auren.
Sannan Aslam shima ya zab’i d’aya su zauna shi da matarsa Huda! Allah yayi muku albarka.”
K’ok’ari Abba yake ya rik’e kukan da ya taho mishi amman sam ya gagara! Dan haka kawai ya rungume Granpa a jikinshi ya sa kuka kamar wani Yaro. A hankali Granpa yake murmushi mai had’e da dariya
kafin yace “So kake ka k’arasa ni ne, Abbana.”
Wannan karon hatta Gramma sai da ta sa kuka…
A tsakaninsu, Abba Dad Mommy Daddy Gramma sam aka kasa samun wanda zai lallashi wani.
A hankali Daddy shima ya taso yazo ya rungume su su biyun duka, haka shima Dad yana hawaye yace “ba za ayi babu ni ba”. Ya k’araso shima yayi joining hug d’in yana dariya.
Gramma ce ta ce “Kar fa ku kadashi k’asa”. Tukunna suka cikashi suna murmushi, Dad ya ja mishi k’aramar kujera mara nauyi ta study ya zauna akai, tukunna suma suka zauna.
Sai da parlourn yad’an yi shiru tukunna, Granpa ya ci gaba da magana “I was wrong!
Duk tsahon wannan lokacin ina kan ba dai dai ba. Allah ya ji k’an Zainab. Ita ta fara nasarar nuna min gaskiya sanann bayan dogon nazarin da nayi na fahimceta.”
Shiruu, ya d’anyi kafin ya cigaba da magana. “Na san dukkan nin ku anan kun san yadda nake jin Zainab a raina, ba abunda yake d’aga min hankali irin in na tuna she was killed! Sanann by an insider.”
Tsit!! Parlourn ya d’auka ko k’arar numfashi bakaji.
Kafin Granpa ya ci gaba da magana, “Tun ranar da ta rasu nayi alk’awarin sai na yi punishing killer d’in no mattaer how smart he or she thinks they are! Dole zan yi bincike in nemo su kuma zan hukuntasu
dan ba zan yarda jinin Ummi ya tafi a banza ba.
30 days guda aka yi ana binciken caterers da waiters d’in da suka yi serving da girkin abincin birthday
and an gano basu da hannu a ciki, sannan an binciki masu gadi kuma an bincika akan
ko sun ga wani abun shima bamu samu komai ba shiyasa nace muku its an incider! Therefore bincike zai fara daga yau yanzun nan! Ku yi hak’uri amman dole kowa ya amsa tambaya sannan ayi investigating d’inshi including me. Daga nan banaso inga k’afar kowa a mansion d’in chan inda incidence d’in ya afku
har sai an gama komai.. Menwhile, Aslam” Granpa ya kira sunan Aslam yana kallon sa.
A hankali ya d’ago idanuwanshi ya kalle shi sannan yace, “Naaam Granpa”. Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Ka je first building by your left akwai bak’i a parlourn k’asa, ka taho da su nan.”
A hankali cikin girmamawa Aslam d’in ya mik’e ya fice. Ba a yi 20 minutes ba suka shigo shi da wasu maza
su biyar!!
Da kyar suka had’iye yawun da ya tokare musu mak’oshi, In banda “innalillahi wa innailaihirrajiun” ba abunda suke maimaitawa a tare!
Gaisawa bak’in suka yi da Granpa kafin yace “Bismillah, you can start.” Ta kan Granpa suka fara…
Tambayoyine suka yi masa, akan relationship d’inshi da marigayiya sannan when last ya ganta?
Akwai misunderstanding d’in da ya tab’a had’asu? Akwai wani secret ko, magana da ta tab’a gaya masa?
Ta tab’a gaya mishi sun yi fad’a da wani ko wata a cikin estate d’in? d.d.s. Daga nan suka d’auko wani abu kamar na tomb print amman babba suka ce “ya d’aura hannusa akai duka gaba d’aya biyun”.
Hakan yayi, sai da hoton palm da yatsunsa suka fito a kan fuskar computer da suka jona a jiki tukunna sukayi gaba. Gramma ce next suna gamawa da ita sai Daddy sai Dad sai Aslam, Sudais Shuraim Arshaad Aaima tukunna Mammy sai ta kusan kuka dan yana yin yadda suke tambayar tasu ko kana da gaskiya sai ka rikice, kafin wani ya rufe baki wani ya jeho maka wata. Da akazo kan tambayar ‘ta tab’a fad’a mata sun yi fad’a da wani?’ A take ta hau zuba tana bada labarin yadda Abba baya sonta sannan ta tab’a ce mata sun yi fad’a da huda! Yana yin maganar tata yasa kawai d’ayan ya tsayar da ita ya d’anyi y’an rubuce rubuce akan takardar ta, yace “shikenan. Ta d’aura hannayenta”.
Successful suka yi suka gama da Abba da Huda, sannan d’ayan ya kunna computer ya ajjiye a gabansu,
ga mamakinsu sukaga Mom da Auwal suma ana yi musu nasu binciken exactly kamar yadda akayi musu.
Ana gamawa suka yiwa Granpa sallama suka fice. Suna fita tun kafin Granpa ya fara magana Arshaad ya kalli Granpa d’in yace ‘Please idan an gama yana so zai wuce, Yanada aiyyyuka da ya tara da yawa.’
Sai da Granpa yad’an yi shiru, tukunna yace “Ok, you can go.”
Yana fita aka yi addua aka watse kowa ya kama gabanshi.
A hankali Granpa ya tura k’ofar d’akin Gramma ya shiga, yana lura da ita tun d’azu kamar jikin ya motsa dan bata da lafiya dama gashi ta hanashi ya fad’awa kowa. Yana shiga da Hudan ya fara tozali tana daddanawa Gramma d’in k’afa dan zuwa yanzu kam ta gagara b’oye mata ciwon nata.
Hudan tana ganinshi ta sauk’e k’afar Gramma dake a kan cinyarta sannan ta mik’e ta d’an russunar da kanta ta wuce ta fita.
Sai da ya ga fitarta tukunna ya juyo ya fara takawa inda Gramma take nan kwance akan gadon ya zauna a inda Hudan ta tashi ya d’auki k’afafun nata ya d’aura akan cinyarsa! Tana k’ok’arin mik’ewa ya ce mata
“Stay still”.
A hankali ya shiga matsa mata kamar yadda yaga Hudan tanayi. Sun d’an jima a haka kafin chan yace
“K’afar dai? Ba kya feeling kwata kwata?”
A hankali tace “Ina ji, ba kamar d’azu ba. Da k’afafuna na fita meeting na shigo nan fa d’azu”
Ta fad’a tana d’an murmushi alamun so take ya bar maganar.
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “Maijidda, ko wanne family fa suna da nasu issues d’in!
Ba a kan mu farau ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki. Kin dai ga yadda d’azu jinin ki ya hau da muka gwada a d’akina, gashi har ba kya feeling side d’in jikinki! Kar kije ki samu stroke fa, ki yi hkr ki rungumi k’addara komai zai dawo normal.”
A hankali ta mik’e ta zauna sannan ta sauk’e k’afafuwan nata k’asakafin tace “Daddie dole in damu.Ace wai a cikin zuriata an samu killer! Taya kake so in kwantar da hankalina? Bayan ban san k’arshen wannan musibar ba. Suma fa y’ay’a za su haifa, kuma mugun hali da bak’ar zuciya jini yake bi, sannan Ina
tsoron idan zance ya fito kar zuriar Ummi suma su zuciya su yi tunanin d’aukar fansa bayan sun girma duk da kuwa ba Mahaifiyar tasu aka so a kashe ba.” Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta cigaba da cewa
Daddie dan Allah idan result ya fito, aka kawo, muka ga wanda muke zxargi d’inne. Dan Allah karka baiyyana sunanshi a gaban kowa dan Allah.”
Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace “That! I cant promise you Maijidda.
Saboda dole In cire rotten seed a cikin family d’ina. An yi masa laifi tabbas amman hakan ba zai sa In hak’ura in bar killer d’in Ummi ya tafi free ba! I’m sorry amman inaso kar ma ki sake yi min maganar nan dan Allah, saboda itace alfarmar ta biyu da na ce miki daman ba zan iya yi miki ba bayan mallakawa mutum d’aya a cikin su MT.”
A hankali Gramma ta sa hannu ta share hawayenta…
Ajiyar zuciya ya sauk’e sanann ya d’an matsa ya rungumota izuwa jikinsa ya shiga lallashinta da kwantar mata da hankali.
Sai da yaga ta d’an dawo dede tukunna yace “Yarinyar nan har yau tana nan? It’s like a nan take dan tare nake ganinku”
Murmushi Gramma ta d’an yi kafin tace. “Ai har nan surukarta ta zo sata tafi da ita amma tayi ta kuka.
Ranar ina jinta tana waya kamar da y’ar uwarta ne na wajen Maman ta wai ‘In ta biyewa Aslam suka shantake da juna mutane za su ga kamar daman chan tana sonshi!’ Wai ‘za ayi mata kallon butulu’.
Murmushi Gramma ta sake yi kafin taci gaba “Ni wallahi dariya ma ta bani”.
Girgiza kai Granpa yayi kafin yace “Dariya ko abun haushi? Wanann ai shirme ne! Ita zata ke maida hannun agogo baya.” Yana gama fad’in haka ya mik’e yace “Zan yiwa Aslam magana ya zab’i gida zuwa gobe ya zo ya d’au keys, da sassafe ki shiryata ki kaita gidanta in yaso aa gyara a yi mata jeren suna ciki.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, da alamun ransa shima duk a dagule yake.”
Ajiyar zuciya Gramma ta sauk’e kafin ta mik’e ta d’auki wayarta ta danna kiran Mommy…
Washegari da safe, kamar yadda Granpa ya buk’aci Aslam yazo ya karb’a keys haka aka yi…
Yana zuwa bayan sun gaisa ya cewa Granpa d’in ‘kawai ya zab’a mishi duk wanda yake ganin yayi
Ya gode Allah ya k’ara arzik’i.’ Murmushi Granpa yayi yace “okay”. Sannan ya mik’e ya shiga ciki.
Makullin d’aya daga cikin gidanjen da ba’a tab’a bud’ewa ba ma ya d’auka ya fito. Ya na fitowa ya gaya mishi gidan da number ya mik’a mishi. Karb’a Aslam d’in yayi ya sake yin godiya, yana shirin mik’ewa Granpa d’in yace “Ku yi sauk’a. Gidan sabo ne, ba a tab’a shiga ba. Sannan yanzun nan Gramma za ta kawo maka matarka In yaso sai a gyara gidan tana ciki kawai ayi furnishing.”
A hankali Aslam yad’an russunar da kai yace “na gode”Sannan ya mik’e ya fita.
Da murmushi Granpa yake kallonshi har ya b’acewa ganinsa. Ya so bashi dariya yadda yaga kamar ma yau d’in kunyar sa yake ji, zai so ya ganshi tare da Abba yau d’in yaga ya zai yi. K’arar wayarsa ce ta katse masa tunani. Ganin number yasa ya d’aga ya kara a kunnenshi ya yi shiru.
“Assalama alaikom”. Baba Bashir yace.
Ba tare da ya fahimci waye ba yace “Ameen Wa alaikummussalam”
Ajiyar zuciya Baba Bashir ya sauk’e kafin yace “Kaka ne. Daga b’angaren Maryam Madu, yanzu
Arshaad yayi min texting numberka”
“Okay, okay” Granpa yace yana gyara zama kafin yace “Ya iyali?” “Alhamdulillah” Kaka yace sannan ba tare da b’ata lokaci ba yace “Na kira ka ne domin in sanar da kai cewa a duk lokacin da kuka shirya kuna iya zuwa a d’aura aure.”
Sai da Granpa ya lumshe idanuwanshi ya bud’e tukunna yace “Weekend Saturday!
Rana ita yau, in sha Allah za mu shirya komai…mu zo.“
“Okay Na gode” Baba Bashir yace. Murmushi Granpa yayi yace, “Mune da godiya, sai mun
had’u”
Daga nan suka yi sallama suka tsinke kiran.
Ajiyar zuciya Baba Bashir ya sauk’e. Yana ajjiye wayar ya juya da niyyar fita su ka yi kicib’is da Baaba Talatu!
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara k’ok’arin wuceta domin ya fita.
Da sauri ta tareshi ta hanyar shiga gabanshi, ta fara hawaye sannan tace
“Mai yasa za ka yi haka? D’an shekara d’ayan da zai yi da mu shi kake neman maidawa sati d’aya?
Dan na tabbatar muddin aka d’aura auren Maryam a gaban idonshi to tabbas a ranar zai cika!.
Ka barsu mana, ita kanta Maryam d’in ta amince ta tausayi masa.. Nan da shekara d’aya ma fa ba zaka sake ganin Usman a doran k’asa ba.”
Sai da Kaka ya runtse idanuwanshi tukunna ya bud’e yace “Ke mahaifiyarsa ce, ki daina yi masa baki haka
Usman ba inda zai je in sha Allah.. Bari kiji in gaya miki d’azu na je akan In fahimtar da shi ya hak’ura kawai tunda har ga Granpa ya zo da kanshi, ina zuwa k’ofar d’akin nasa kin san me na ji suna tattaunawa?”
Cikin share hawaye Baaba Talatu tace “Amman dai ko meye ne ka ji ai a ganina bai shafi..”
Cikin d’an fad’a fad’a yace “Ki amsani kawai! Kin san me na ji suna tattaunawa?”
A hankali ta girgiza kanta alamun ‘A’a’ Sai da Kaka ya had’iye wani k’ululun takaici, kafin yace
“Akan maganar k’aryar takardun da suka yi na ji suna magana! For your information
Usman garr!! Ya ke babu mutuwar da zai yi in sha Allah. So yake kawai Maryam ta koma gidansa
ya cigaba da azabar da ita.
Wallahi Talatu kunyar Yarinyar nan nake ji. Ban tab’a b’oyewa Madu wani abu ba amman tabbas zan b’oye masa wannan maganar idan shekara ta zagayo aka ga Usman bai mutuba mu ce. Ikon Allah ne! Dan ban san ta ina zan fara ce masa Usman da Jamilu sun yi k’aryar ciwo da mutuwa a Usman d’in dan kawai su yaudaremu ya aure masa y’a ya ci gaba da azabtar da ita, ba. Ki dubafa ki gani, tsabar ya san bai kyauta ba
ya ma kasa fitowa a mutum yayi bikon ta dan bai san ta Ina zai fara ba! Sai da ya had’a da k’aryar ciwon mutuwa. Wanne irin deceiver ne wannan Yaron????
Kiga fa duk abunda ya yiwa Maryam amma tashi d’aya ta hak’ura ta ji tausayinshi zata koma ta yi jinyar sa har ya koma ga mahalliccinsa alhalin shi yana nan yanata yaudarar ta da mu kanmu..”
Cikin katseshi Baaba Talatu tace “Ai dan ba ka san ya muka yi da Maryam d’in bane, ba ka
san ya akai ta yarda ba! Ba ka san me na ce mata tukunna ta yarda ba…..”
Cikin tsananin b’acin rai ya d’aga mata hannu ya ce “Talatu!!!!”
Jin yadda ya daka mata tsawa ya sanya ta nutsu ta sha jinin jikinta.
A fusace ya fara magana “Ban damu da in san me kika ce mata tukunna ta yarda ba,
tunda dai har ta yardan to ta yi proving kanta ba as selfish kamar ke da d’anki ba!
Abu d’aya nake so in yi miki gargad’i akai ko kuma ince In umarceki ki yi…Ina so ki tsame hannuwanki lamarin nan…ko da wasa idan kika sake yunk’urin had’a Maryam da Usman su koma su yi zaman aure wallahi!! Kin ji dai na rantse sai na datse igiyoyin aurena kaff! Da su ke a kanki!”
A zabure ta ware idanuwanta tana kallonshi.
“Tabbas!” Kaka yace cikin gasgasta maganar tasa sannan ya ci gaba. “Tunda na lura son kan naki ya yi yawa.. Tun farko kike gwada son kai har yau kin k’i ki saduda Talatu. Usman d’a ne haka itama Maryam y’a ce! Amman wani abun takaici tunda kike Talatu not once kika tab’a duba farin cikin Maryam kullum kawai ke Usman! Baki damu da kowa ba sai d’anki. Kamata yayi ace yanzu kin nuna masa tsananin b’acin ranki
kallafa k’aryar mutuwa yayi amman kina k’ok’arin yin burus da al’amarin saboda…”
Shiru yayi sakamokon ido biyu da suka yi da Baba.
A hankali cikin mutuwar jiki ya k’araso cikin d’akin ya durk’usa a gaban Kaka da Baaba Talatu ya fara hawaye a hankali ya ce “ku yi hak’uri, na san na yi, laifi amman ku yafe min, dan Allah kar ka bari su Abba su ji wannan maganar, tunda har ita Maryam d’in ta yarda zata koma kawai ku kyaleta, daga baya duk abunda…”
Marin da Kaka ya d’auke sa da shi ne ya sa ya yi shiru! Cikin tsananin b’acin rai ya ce “Usman inaso ka tattara kayan ka ka koma inda ka fito! Kuma kar ka kuskura ka dawo, har a gama d’aurin auren Maryam a kaita gidan Abba! Dan na lura imaninka ya fara rawa so zaka iya yin komai. Ka tattara ku koma kai da Jamilu har a k’are tukunna ka dawo.
And one more thing.. Ko ka san cewa y’arka ciki ta yi? Kuma Sadiya ta tura ta gidan su shi Yaron ta zauna
ta yiwa kowa k’aryar tana gidan Hansai?? Baka sani ba ko? Bada ban cikin ya zube ba
na tabbatar da sai ta haifi shege a cikin zuriata!. Saboda kawai Yaron ya kasance mai kud’i
shiyasa tsananin buri irin na Sadiya ta gwammaci jikata ta je ta haifa shege dan kawai ta dinga turo mata da kud’i!
Kana nan sake da baki kana k’ulla ta yadda zaka dawo da Maryam instead of ka tsaya ka kula da iyalinka Usman!!
Kaf y’ay’anka da matarka babu wanda za a kalla a nuna a yi alfahari da shi! Dan shi
kansa Junaidu abun a bincika ne! Amman daga kai har Jamilu da ya kamata ace kun tashi kun tsaya akanshi kun yi bincike, kun zauna kuna k’ulla makirci da k’arya kamar mata! Kun zuba mana ido ni da Madu tsofai tsofai da mu mu za mu yi komai. To Ina so ka sani nima yanzu ta kaina nake yi, abunda kawai zan yi focusing akai bayan d’aurin auren Maryam shine ibada. In samu in gyara tsakanina da Ubangijina kafin In koma gareshi. Duk wanda yaga zai gyara iyalinshi to ya gyara wanda kuma ya ga ba zai gyara ba shi ya sani kar ya gyara ya zauna ya ci gaba da shirme yana biyewa so da buri.
Abu d’aya zan yi maka na taimako da ga shi ba k’ari! Kasancewar Jalila y’a mace kuma yanzu na san tunda zance ya fara fitowa in an kwana biyu ba lalle ta auruba, dan haka zan rufa mata asiri.
In nema mata miji kamar yadda na yi da farko. A yanzu Mati ya riga ya cike ta hud’u if not wallahi da tun a jiya da Zainab ta bani labarin ta da tuni na aura masa ita. Dan haka yanzu zan bada sanarwa this time around ba a fili ba a b’oye saboda kar Sadiya tace na yi talla da y’arta kamar farko. Duk wanda ya zo ya ce yana so daga nan zuwa ranar asabar rana ita yau, to za a had’a a d’aura aurenta, tare da na Maryam da Abba, in sha Allah.” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan yana so ya sanar da Madu an saka rana.
A ranshi ya gama rayawa ‘Ko Madun bai yarda ba wallahi sai dai kawai ya ga ana d’aura aure ranar Asabar! Ai Maryam bazawara ce yanzu sannan ba Yarinya bace ba, kowa ya san Abba take so ba Usman ba dan haka Madu bashi da hurumin yi mata dole’.