Kai kana ganin fuskokinsu ka san suna cikin tashin hankali ba na wasa ba.
Kallo suke suna sake kallan pictures d’in amman ba ta inda za su ce ba Ashraff bane ba.
A hankali Sakina ta mik’a mata wayarta sannan ta ce “yana Ina?”
Ta yi mata tambayar tana k’ok’arin mik’ewa tsaye.
Cikin ruk’o hannunta Aaima ta ce “Ya tafi”, Sannan ta d’aura da cewa
“Mai aiki nasa taje har chan waje ta shigo da shi parlourn Mammy.
Abunda ya bani mamaki ya kuma d’aure min kai shine
yadda ya nuna kamar irin kwata kwata babu alamun yama tab’a ganina d’in nan
sannan kuma he looks calm and innocent!
Kasa hak’ura na yi bayan mun gaisa na ce mishi “Sageer”.
Amman sai na ga yana kallona da mamaki!
Ganin da nayi ban ma san abunyi next ba yasa kawai na ce masa ‘ya tafi, dan Allah yayi hak’uri wani abun ya taso min urgent!’
Cikin fahimta ya nuna min ba damuwa ya mik’e ya tafi.
Sakina kaina ya d’aure saboda a ganina inda ace Sageer d’in ne to da ko a idanunsa zan fahimci firgici!
Da d’an alamun wani abun dole zai nuna amman kuma ko twins banajin za su iya zama super identical haka kamar shi da sageer.
Hatta fa yanayin magana kallo tafiya komai nasu iri d’aya ne..”
Cikin katseta Sakina ta ce “Kar ki damu Aaima, ba wani Sageer sunanshi Ashraff!
Shine!
Raina miki hankali kawai yayi. Ga Abokin sa nan ma Abbakar a wanann hoton.”
Da sauri Aaima ta karb’i wayar ta kalla sai kuma ta ce “Ai shine Saddik d’in”
“Hmm! Kawai Sakina ta ce tana mai dialing numbershi a wayarta.
Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin tace, “Kuma kin san abunda zai sa ma mu sake gasgata shi d’in ne.
Ranar farko da suka fara zuwa a ranar da ya had’u da Suhaila da ya ce mata ‘I’m Sageer by name’
Sai da Abokin nashi ya juya a zabure yana kallonshi sai kuma na ga ya fara murmushi yana girgiza kai.”
Dede nan Ashraff ya amsa call d’in Sakina. Daman a handsfree ta saka. “Hello baby”
Suka ji ya fad’a.
Sai da Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta ce “Ashraff ko Sageer?”
“My god!! Waye ne Sageer d’innan ne? Kin san i was just about to call you sai kika kira…
That cousin of yours she looks confuse! Tana ganina ta ce min Sageer itama. Ask her ta yi miki bayani please dan i d..”
Cikin katseshi ta ce “Dakata Ashraff! Ba ita bace confused, ni ce! Bayani kuma ba ita za ta yi min ba kaine!.
So I’m all ears. Ina so inji ta yadda ka chanja sunan ka da kuma yanda kake planing zaka yi da mu, Ni da Suhaila da kuma d’an cikinta”
“Oh Noooo! Innalillahi wa innailaihirrajiun. Sakina haba mana. Tana ina ita cousin d’in taku?
Bata wayar please. Wallahi daman yadda na ga tayi na san akwai matsala, waye Sageer? Wacece Suhaila? Ciki kuma a Ina?. Sakina na riga na gaya miki y’an mata biyu kawai na yi dating b4 you and duk na nuna miki pictures d’insu, please Sakina kar ki biye mata i think akwai confusion a lamarinta amman wallahi ni ban san wani Sageer ba, bata wayar please”.
Fashewa kawai ya ji Sakinar ta yi da kuka, cikin kukan ta ce “Haba Ashraff! Despite abunda ka yi da k’aryar da ka yi still kana so ka ci gaba da b’oye b’oye? Wat have i ever done to you to deserve this?”
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” kawai ta ji yanata maimaitawa kafin ya ce “Shikenan Sakina,
na gane! Yanzu na fahimci komai. Kina neman hanyar da za ki zillemun ki auri Auwal d’in da kike ta tunani kullum ko? Ko kina tunanin ban saniba ne? Idan ba kya sona ki fito fili kawai ki gaya min ki daina yi min kwana kwana! Bawai ku had’a baki ba ku k’ulla min sharrin abu mai muni haka ba. Wallahi tallahi kin ji de na rantse miki ni ban san wani Sageer ba ban san wacece Suhaila ba, sanann wallahi Sakina da gaske nake sonki ba yaudara a ciki! Ke kad’ai ce a cikin zuciyata”. Ya fad’i haka yana me fashewa da kuka kamar k’aramin Yaro sai kuma ta ji ya kashe wayar, kiit!.
Ashraff, yana kashe wayar ya kira Saddik yana d’auka bai jira jin me zai ce ba
ya ce “Saddik, I’m doomed.” Sanann ya hau koro mishi bayani hankalinshi a mugun tashe.
Shiruu Saddik d’in yayi bayan ya gama ji kafin ya ce “Listen closely Ashraff..”
Gaba d’ayansu hankalinsu a tashe yake, bama su san ta Ina za su fara ba.
Aaima ce ta yanke shawarar kiran Suhailar dan haka ta d’au waya ta shiga sunanta ta danna call.
An fi thirty minutes tukunna aka samu layinta ya fita daga busy ta amsa kiran Aaiman.
Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin ta ce “Da wa kike waya haka?”
Sai da ta d’anyi jimm! Tukunna ta ce “Wata friend d’ita ce”
Shiruu, Aaiman ta yi tana tunanin wacece k’awar Suhaila haka da bata san ta ba. Sanin ba wannan ne a gabansu ba ya sa kawai ta kawar da zancen ta hanyar bata labarin Sageer Ashraff from A -Z kafin ta ce “Yanzu ko gidan su idan kinaso zamu iya zuwa dan Sakina ta ce ta san gidan kuma zata bamu adress har number Mamansa.”
Cikin katseta Suhailan ta ce “Mun gama case d’in Sageer fa! Ki manta kawai please, kar ki
sake yi min maganarsa”
A rikice Aaiman ta ce “Kin gama case d’insa da cikinsa a jikinki??”
“Please Aaima” Shine kawai abunda Suhaila ta ce.
Aaima za ta yi magana kawai ta ji ta katse kiran.
Kasa cire wayar daga kunnenta Aaiman ta yi, da kyar ta d’ago tana kallonsu still da wayar kare a kunnenta.
Kirane ya shigo wayartata dan haka ta d’an zabura saboda a kunnenta wayar take har yanzu.
Tana ganin mai kiran nata ta d’auka da sauri ta ce “yauwa Khadija kin san me yake faruwa?
Yanzun nan….”
Cikin katseta Khadijar ta ce “Sageer, yanzun nan ya kira Suhaila. Suna fara magana ta tashi ta shiga bathroom, haka kawai na ji inaso in yi mata lab’e saboda na san kusan wata nawa ana neman shi
sai yau kawai muga ya kirata.
A yadda na fahimta Its like akwai wadda zai aura a yanzu! Wai family d’insu sun zab’a masa
shiyasa ma ya d’auke k’afa amman yayi mata alk’awarin aure nan da wata biyar muddin ta yi shiru.
Ban gama dawowa daga mamaki ba na ji conversation d’in ku a waya yanzu.
Meyene yake faruwa?”. Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e rai a b’ace ta ce “Wato shine Ashraff d’in ta tabbata kenan!…” Nan ta d’an yi briefing Khadija a kan case d’in sannan ta ce “Khadija Suhaila tana son, Ashraff
ba zata tab’a iya k’etare umarninshi ba! Dan haka yanzu aiki yana a hannunki.. Ki taimaki y’ar uwar ki
tunda ni dai kinji yadda muka yi da ita. Zan turo miki number Mamansa yanzu daga nan ki kirata ki yi mata bayanin komai! Lokacin b’oye b’oye ya wuce dole iyaye su shiga case d’innan.
Mugun tantiri ne Ashraff d’innan wallahi! Kin san yadda ya nuna kuwa kamar bai sanni ba amman kalli har ya kirawota munafuki d’an iska! Kuma wallahi k’arya yake yi, shi ya ga Sakina ya ce yana sonta ba wani had’asu da akayi. Infact Families d’insu ma basu san juna ba sai ata dalilin ita Sakinar da shi Ashraff d’in.
Wanne irin rashin wayone haka Suhaila take yi! Dan bayan soyayya tabbas akwai dak’ik’anci a cikin lamarinta, saboda Allah ace wai Mutumin da yayi maka wannan abun tashi d’aya ya dawo ya kalallame ka kuma ka yarda? Duk da ban san me ya ce mata ba amman ai ya kamata ta tambayeshi dalilin da ya sa ya bamu fake adress ko?”
A hankali Khadija ta ce “Tabbas”, Sannan ta ce. ‘Ta tura mata number Maman ashraff d’in ta kirata yanzu ba sai anjima ba kafin Suhaila ta dawo d’akin.”
Da “to” ta amsa sannan ta katse kiran kafin ta kallesu ta ce “Yayar Suhailan ce, Itama ta san da zancen.
Ina number Maman nashi?”
Kamar yadda Sakina ta fad’a haka ta bada number Maman Ashraff bayan sun kwantar mata da hankali da kyar! Dan da cewa ta yi sai ta je ta sameshi a duk inda yake! Hudan ma harda y’ar kwallarta ganin yadda Sakinar duk ta firgice ta fita haiyyacinta tana ta kuka wiwi. Gaba d’aya sun gigita da lamarin Ashraff.
Suna zaune a d’akin wata maid ta shigo musu da abinci kala kala.. Aaima da Huda ne suka d’an ci
Sakina kam har yanzu hankalinta a tashe yake, ashe ita ta yi gudun gara ne ta tadda zago
ba tare da ta sani ba…
Sai bayan sallar Magrib tukunna Junaidu ya kirata ya ce “taje yana waje, su wuce.”
Aaima ce ta rakata har bakin mota bayan sun sha kukan su ita da Huda sannan sun d’an yi mata y’ar guntuwar Nasiha suma, dan itama Aaiman ba komawa za ta yi ba sunyi sallama kenan saboda
ta san Huda tsaf sai ta rik’eta kamar yadda ta kanainaye Sakina.
Duk da halinda Sakina take ciki sai da ta fahimci kallon da Aaima da Junaidu suke yiwa juna!
Tun d’azu dama da za a kawo Huda ta d’an lura yanzu kuma ta sake tabbatarwa dan har tana yiwa Junaidun magana ma bai sani ba.
Kasa hak’ura tayi bayan sun d’au hanya ta ce “Ya Junaidu ko dai In had’aku ne?”
Wani lallausan murmushi ta ga ya yi kafin ya ce “A’a fa Sakina,
tuwon girma ai miyarsa nama! Idan na d’auko wannan ina da wajen ajjiyeta ne?”
Da sauri Sakina ta ce “Ya Junaidu, ranar nan fa na ji Kaka yana cewa Gidajen ka wajen biyar a Kano kawai ga motoci ga filaye.”
Dariya ya yi this time around sanann ya ce, “Ki bar maganar nan. Although har ga Allah i felt something
towards her very strong amman tunda na rasa Huda, i don’t think zan yi aure idan ma zan yi d’in to
gaskiya ba nan kusa ba.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e tana kallon yadda fuskarsa ta chanja lokaci guda.
Daga haka motar ta d’auki shiruuu kowa da abunda yake sak’awa a ranshi, har ya kaita k’ofar gidan nasu ya ajjiyeta.
Tana sauk’a yayi reverse ya juya dan akwai ayyuka da dama akanshi.
Tana shirin tura gate d’in gidan ta ji ya ce “Sakina”. Da sauri ta juyo! Daman taga kamar motarshi a parke d’an gaba kad’an.
Ganin sa d’in ne kuwa yasa ta had’e fuska tamau! Kafin ta ce “Naam, Sageer.”
A hankali ya k’araso inda take, sai da hasken globe d’in k’ofar gidan nasu ya haska fuskarshi da kyau tukunna ta lura da abun mamaki. Gani tayi yana kuka wiwi fuskarshi har ta kumbure da alamun ya dad’e yana yi.
Tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa “Sakina komai Aaima ta fad’a muku gaskiyane
nine Sageer! Amman asalin sunana Ashraff.. Ba zan b’oye miki ba. Har ga Allah tun farkon had’uwata da Yarinyar na ji ina sonta amman ba so na aure ba sha’awace kawai irin wadda shed’an kan saka a zuk’atan waenda ya yi nasara.
Na san Abbakar Abokina ne tun Yarinta. Muna barin gurin ya tambayeni ‘dalilin b’oye mata asalin sunana da na yi’ Ban b’oye mishi ba na fad’a mishi k’udurina a kanta! Ya ji ba dad’i kuma yaso nusar da ni amman da yake shed’an ya riga yayi galaba a kaina yasa sam ban ji ba.”
Matsowa ya sake yi kusa da ita wanda hakan yasa ta d’an ja baya. Cikin kuka kamar Yaro ya ce “Sakina na yi laifi, na san na yi laifi! Amman dan Allah ki fahimceni ki fahimci k’aunar da nake yi miki ta tsakani da Allah ce. Ki duba kiga yadda ita na fad’a mata fake adress fake suna and everything. Ke kuma na fad’a miki komai nawa! Har waya kuke yi da Mamana. Dan Allah kar ki bari a rabamu, ki toshe kunnuwanki, fight for our love! Ko wanne d’an Adam ajizi ne ni ga nawa mistake d’in, dan Allah ki fahimceni, kin ga gashi
na fad’a miki komai ban b’oye miki ba, ki yi min adalci Sakina.”
Girgiza kai kawai Sakina ta yi sannan ta share hawayenta ta ce, “Meyasa ka zab’i ka gaya min yanzu? Saboda an kira Maman ku ko? Kuma ka san dole case zai taso… Bara ka ji Ashraff, magana d’aya kawai zan iya gaya maka saboda at this stage ba zan ma iya tolerating ganinka ba! Saboda abubuwan da ka yi sunada yawa ban san ta Ina zan iya farawaba. Abunda nake so ince kuma nake so ka fahimceni da kyau
tunda naga kana da sharp brain shiine. Ba zan aureka ba!”
A gigice ya d’ago yana kallonta.
“Kwarai!! Babu wannan maganar. Ga responsibility d’inka chan ‘Suhailat’. Ka koma gareta
ka nemi yafiya ku haifi d’anku ku zauna lafiya ku reneshi a tare!” Tana gama fad’in haka ta juya zata shige gidan ya yi saurin ruk’o hannunta. A mugun fusace ta juyo bata yi wata wata ba ta d’auke shi da wani irin mahaukacin mari jikinta har karkarwa yake yi ta ce “Na rantse maka da Allah idan baka bar nan ba
zan iya yi maka illa! Dan duk abunda na raruma sai na maka ma saboda raina ya kai k’ololuwa wajen b’aci!
Audacity d’inka shi yafi komai d’aga min hankali Ashraff! Ka ma raina min hankali wallahi! How kake tunanin…..” Shiruu ta yi ta kasa ci gaba da magana chan kuma ta ce “Kaga! Just go, kama gabanka. Like i said Idan na ce zan yi maganar abubuwan da ka yi da renin wayon da ka zo da shi yanzu to
ba zan iya jurar ganinka k’alau akan k’afafuwanka ba! So just leave!!!!”
Ta k’arashe maganar cikin tsawa sannan ta juya ta tura zata shige cikin gidan
ta ji ya ruk’ota! Za ta yi magana ta ji ya toshe mata baki da hanci da wani handkerchief.
Sai dare tukunna Granpa ya tara su Dad da Gramma ya fad’a musu d’aurin auren Maryam da Abba
next week in sha Allah. A ranar Abba kasa bacci yayi yadda ya ga rana haka ya ga dare!
Daga k’arshema ma ji yayi cheecks d’inshi sun fara ciwo tsabar murmushi. Tun ba ma da ya kira Mama ta kula shi sosai ba.
Kaka ma ya samu Madu, babu alamun wasa a fuskarshi yace “In dai har yanzu
yana yi mishi kallon Mahaifi a wajen Maryam to ya sani ya saka ranarta!
Rana ita yau su Granpa za su zo a d’aura aure. Kuma dan girman Allah kar ya tambayeshi dalili ko ya yi mishi musu indai yana buk’atar Abotar su ta d’aure har k’arshen rayuwarsu.”
Murmushi kawai Madu yayi kafin ya ce “Kaka ai Abotar mu har aljannah in sha Allah
ba abunda zan bari ya shiga tsakani dan haka duk abunda ka yanke na goyi bayanka
blindfolded….duk da ban san dalilinka ba amman i trust you kuma zan yi sopporting d’inka d’ari bisa d’ari!
So dan Allah kar ma ka sako maganar lalacewar Abotar mu. Allah ya kaimu ranar asabar d’in da rai da lafiya.” Ya k’arashe maganar yana murmushi.
Duk fushin da Kaka ya kwaso daga gida sai ya ji gaba d’aya ya kau. Dan haka yad’an sake suka shiga tattauna abunda ya shafi alamuransu mostly a kan Jalila. Kafin daga baya ya nemi ganin Mama itama….
Same yada ya yiwa Madu itama haka yayi mata kafin ya d’aura da cewa “Indai ta d’auke shi a matsayin uba har yanzu tou kar ta yi mishi jayayya kawai yanaso ta amince da abunda ya zo da shi”
Daga anan ya d’aura mata da Nasiha akan ‘kar ta rik’e Abba a ranta komai ya wuce
su zauna su yi rayuwarsu kamar farko. Allah yayi musu albarka.’
A hankali ta ce “ameen” sannnan ta yi mishi godiya daga nan ta mik’e ta fita.
Wata nannauyar ajiyar zuciya Kaka ya sauk’e yana jin wani nauyi yana sauk’ar mishi
tun kafin ya kai ga sauk’ewa gaba d’aya.
Tana zaune a kan darduma ta idar da sallar isha kenan. Gwaggo Asabe ta shigo
da akwati sai kuma Mommy da ragowar masu aiki mata duk da akwatuna. Tun tana iya irga su har ta hak’ura ta tsaya kawai a tsaye bayan ta mik’e ta gaidasu cikin girmamawa. Sai da aka jere akwatunan tukunna suka yi mata sai da safe suka juya suka fita suka barta nan a daskare.
Ta fi minti uku kafin ta samu ta k’arasa bakin gadon ta zauna still idanunta a kan akwatunan.
Da sallama ya turo k’ofar ya shigo! Da leda a hannunshi.
Da sauri ta sunkuyar da kanta ta ja hular alkyabbar ta rufe fuskartata.
Murmushi yayi kafin ya k’araso inda take nan bakin gadon ya zauna ya kamo hannunta cikin nashi ya rik’e ya d’an murza kafin ya ce “Sai na yi siyan fuska shima?”
Dariya Hausar tashi ta bata dan haka ta d’an saki murmushi wanda har sai da ya jiyo sautin shi.
A hankali ya ajjiye ledojin dake nan rik’e a hannunshi kafin ya sauk’o gabanta yad’an durk’usa tukunna ya sa hannu ya janye hular alkyabbar.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “Ma sha Allah”, Sai kuma ya sake cewa “Kukan me kika yi?”
A hankali ta girgiza kanta alamun ‘ba komai’. Tana jin bugun zuciyarta yana kara tsananta!.
Cikin son ya tashi a gaban ta ta ce “Akwatunan menenen wannan?”
Murmushi yayi yad’an sunkuyar da kanshi k’asa ya ciji lips d’inshi kafin ya d’ago da kanshi yana kallonta tukun ya fara magana “Ai dama sai da na cewa Mommy ta yafe min a barni ba sai na yi ba, amman ta saka ni kashe uban miliyoyi akan lefe! Yau kusan wata biyu kenan tana ta tatsemin aljihu. Ga shi ke kanki bama ki so ba ko? Mu mayar mu karb’o kud’in mu?”
Sai yanzu ta d’ago ta kalleshi “Ma sha Allah” ta fad’a a ranta. Tunda ya shigo dama ta lura da fararen kaya ne a jikinshi kaftan, sai yanzu taga ashe har hular kansa itama fara ce tas! A ranta ta ce
“Manyan kaya sun fi yi maka kyau”
Cikin katseta ta ji ya ce “Kwalliya ya biya kud’in sabulu kenan! Tunda gashi har an saki baki ana kallona”
Ya fad’a yana murmushi gefen baki da d’age mata gira.
Da sauri ta d’auke idonta da kyar. Cikin son kawar da zance ta ce “Ya Aslam wasa wasa fa kanada rowa, tun ba yau ba na fuskanci haka”.
Dariya sosai yayi kafin ya ce “Ai kin fini rowa! Tunda gashi ana ta yi mini rowar zuciya.”
Ya fad’i maganar yana k’ok’arin yin zaman dirshen akan kafet d’in gaban gadon ( a gabanta)
Yana zama, bata san lokacin da ta yi sauri itama ta sauk’o ta zauna a gabansa ba
har guiwowinsu suna gogar juna. Sai kuma ta fara k’ok’arin janyewa. Hannuwanshi ya saka ya rik’e cinyar tata ta yadda ba zata iya motsawa ba! Yana jin wani yanayi na daban ya na shigar shi…
A hankali yana d’an murmushi ya ce “I love this respect da kike min Hudatie, Thank you.”
Sunkuyar da kanta ta yi kawai ta kasa cewa komai.
A hankali yana kallonta ya ce “Baki ce komai ba. Akan maganar mu da muka fara a d’akin Gramma”.
Da sauri ta ce “Ya Aslam dan Allah ka daina bana son maganar. Kuma ni dai ka d’auke hannunka.”
Gefe ya kalla yayi wani murmushin gefen baki.. Bata gama fahimtar murmushi da jinjina kan me yake yi ba
ta ga ya mik’e tana shirin yin magana ya sunkuya ya d’auketa!
Sai da ya k’arasa wajen sofa tukunna ya zauna ya d’aura ta a kan cinyarshi kafin ya ce “Bud’e idon sannan ki ja numfashi Matsoraciya kawai.
In kika sake yi min musu ko kika ce kar In tab’aki Allah sai na nuna miki matsayina a wajenki.”
A hankali ta bud’e idonta tana kallon k’asa.. Hankalinta In yayi dubu tou ya tashi!
Tanajin yadda jikinsa yake d’an rawa kad’an kad’an ga zuciyarshi tana iya feeling bugunta!
A hankali ta ji ya ce “Unhm ina jinki. Say something anything i told you how I feel. Let’s talk about us,
Um??” Yayi maganan yana ruk’o hannunta.
Zuwa yanzu kam Huda ji ta yi ba zata iya jurar wannan torture d’in ba dan apart from heart d’inta da yake over racing! Ta rasa fahimtar meyene game da hannun Aslam da yake sanya touches d’inshi suke zautar da ita.
D’igar hawayenta ya ji dan haka ya sauk’e ajiyar zuciya ya mik’e da ita a jikinshi ya ja hannunta…
Sai da suka je inda ya ajjiye ledojin d’azu tukun ya d’auki wata ledar bag y’ar babba mai zip lock mainkyau sosai ya bata ya ce “Gashi ki shirya ki sa wannan kayan ki yi alwalah..please ki saka rigar ciki”. Har zai juya sai kuma ya ce “If not”. Ya matso da bakinshi kusan kunnenta ya fara magana. Da mugun sauri ta juya ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta jikinta na karkarwa.
“Kisa rigar kin ji, pls” Ya fad’i maganar kamar ba shi ya gama zuba mata maganganu a kunne ba yanzun nan.
A hankali ta ce “tou” dan ita Allah Allah take ya fita ya bata guri ta samu ta shak’i isashshiyar iska.
Yana fita ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tana dafe k’irji sanann ta nemi waje ta zauna akan gadon.
Ta jima a haka kafin kawai ta mik’e ta fad’a toilet dan daman wanka take son yi tun kafin ya shigo:
Ta d’an jima tukun ta fito bayan ta yi wanka da ruwan turarrukan da Ummu ta jere mata a toilet d’in, da brush duk sai da ta yi sannan ta fito.
Rigar, dan kyau ta yi kyau sosai sai dai spaghetti hand ke gareta. Ba wani rashin d’a’a a rigar dan doguwar gown ce har k’asa Slim mai bin jiki sai wasu stones masu shek’i na azaba k’anana a saman edge d’in wuyan rigar da kuma dede k’asan boost sai kuma chan k’asan edge d’in rigar shima an zagaye da stones d’in.
Ko bra bata saka ba dan rigar irin me bra d’innan ce ta ciki.
Sai da ta saka rigar ta zuge zip d’in da kyar tukunna ta ga rashin d’a’ar rigardan kusan rabin k’irjinta a waje ne sannan bayanma gaba d’aya ashe akwashe yake dan ma Allah ya taimaka gashinta ya rufe kusan rabi.
Da sauri ta fara k’ok’arin zuge zip d’in domin ta samu ta chanza rigar kafin ya shigo.
Bata kaiga zugewan ba kuwa ya shigo! Sanye cikin jallabiyafara tass! Mai k’aramin hannu.
Suna had’a ido da shi bata san daliliba kawai sai ta fashe da kuka.
Da sauri ya k’araso gaban madubin dan shi a tunaninshi yadda ya ga ta rik’e wajen zip d’in ta na jaa
ya d’auka had’ewa ta yi da fatarta.
Sai da ya duba ya ga ba komai tukunna ya sauk’e ajiyar zuciya ya juyo da ita ya fara lallashinta yana dariya k’asa k’asa dan sai yanzu ya fahimci dalilin kukan nata.
Da kyar ta yi shiru tana sauk’e wasu tagwayen ajiyar zuciya tana nok’ewa:
A hankali yake binta da wani irin kallo kafin ya tattara gaba d’aya gashin nata ya zubo mata shi ta gefen fuskarta suka fad’a a kan k’irjinta gefe d’aya.
Tunda ya fara kallonta har ya gyara mata gashin kan nata ta sunkuyar da kanta k’asa.
A hankali ya zaro wata red rose ya sak’ala mata a jikin gashinta ta d’an saman kunnenta
kafin ya zaro wani tsadadden pendant necklace d’an mitsitsi mai shape d’in heart ya ware shi ya bud’e ya kara mata a wuyanta sannan ya matso sosai ya lek’a ta baya ya manne mata sark’a ya saketa ya gyara mata gashinta.
A hankali ya na nan a yanda yake dan baya son motsawa daga position d’insa ya ce
“Open it”. Da kyar ta iya bud’ewa hannunta na gogar k’irjinsa…Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba Right side d’in an rubuta ‘Y’ Left d’in kuma ‘M’. A hankali ta mayar ta rufe sark’ar tana d’an murmurshi.
Jin yayi shiruu yasa ta d’an motsa sai kuma ta tuna ashe a jikin madubi ta ke! Da sauri ta juya ta katseshi daga k’are mata kallon da yake.. Dariya ya yi ya ce “To ai nan d’in ma zan ganki” Da sauri ta koma ta kanannad’e shi ta baya ita ala dole kar ya sake ganinta.
Ganin tana shirin kunce mishi lissafi yasa ya ce “Tsaya In d’auko miki hijabi mu je mu yi sallah”
Da kyar ya samu ta sakeshi ya k’arasa wajen akwatunan ya bud’e wanda yake kyautata zaton akwai hijabin a ciki. Cikin sa’a kuwa ya samu ya d’auko harda darduma ya dawo ya mik’a mata hijab d’in ya ce “Ungo, saka”
A hankali ta karb’a ta saka tana sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya.. Daga nan
ya ja hannunta ya ce “mu je, i have a surprise for you.” Yana rik’e da hannunta suka fito suka nufi d’akinsa…Yana bud’ewa! A hankali ta ce “Woow..” Tana murmushi. Sai da ta k’arasa shiga cikin d’akin tukunna ta fahimci abunda ya rubuta da y’an k’ananan candles d’in da ya kunna a tsakiyar d’akin
I Love You Hudan!.
Kan gadon ma wanda ke nan shimfid’e da white bedsheets haka ya rubuta da wasu k’ananan red roses.
Murmushi kawai take yi tana kallon yadda d’akin ya k’awatu matuk’a! Ya burgeta sosai.
A hankali ta ji yayi hugging d’inta ta baya sannan ya ce “Do you like it? Ya yi kyau?”.
Murmushi ta yi a hankali ta ce “Ya yi kyau”.
Juyo da ita ya yi ya d’an b’ata yayi kalar tausayi fuska abun dariya ya ce “Ya yi kyau but you don’t like it ko?
Y?”
Sai da ta yi k’asa da kanta tukunna ta ce “Ni Ya Aslam kana confusing d’ina ne idan na ji ka ce you love m me” Ta k’arashe maganar da d’an inda inda.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya ce
“Y?”
Cikin runtse idanunta ta ce “Ya Arshaad fa k’anin ka ne! Amman kuma how kake sona
bayan ka san shi zan aura? Idan kuma ba haka ne ba to tayaya zaaka ce ka fara sona ana d’aura auren mu?
Tunda na lura tun lokaci ka fara nuna intrest.” Ta fad’a tana sake sunkuyar da kanta sosai.
Ya ji zafin zancen Arshaad da ta kawo amman sai ya basar, ya ce “Dole ki sunkuyar da kai ai”
Ya fad’i hakan yana d’an jan hancinta, kafin ya sa hannu ya sake jawota jikinshi tukunna ya fara magana “Hudan! That day da muka fara had’uwa ranar da Arshaad ya ce in zo mu je yayi min introducing d’inki mu ga juna Wasn’t the first time i saw you.”
Da sauri ta d’ago tana kallonshi.
Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi ya bud’e su sannan ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa.
“Banso gaya miki haka ba na so ace na saka soyayya ta a cikin zuciyarki a hakan in ya so daga baya ki sani
amman zancen Arshaad da kika kawo wanda na fahimci it’s like kina tuhuma ta da betraying d’inshi,
shi ya sanya zan fad’i miki. Akwai wani competition da kuka yi,Tournament, Mathematics..
I think a time d’in kina ss 2 ne.
A cikin makarantun akwai wata makaranta ta y’an labanoon wadda sister d’in wani employee d’ina
d’an labanoon ta yi representing. A chan uk yake min aiki a company d’ina, muna shiri sosai da shi.
Ke kika zo first ntic Sistern nashi kuma ta zo second Labanoon school.
Employee d’in nawa ne ya turomin full video d’in yana me tambaya ta. Dama inada sister bayan Aaima?’
Na ga resemblance d’in sosai nima amma ba wannan ne matsala ta ba dan a tashi d’aya kika shiga raina.
Sai da ta kai ta kawo bana iya bacci idan har ba hoton ki da wannan video d’in na gani ba.
Ina da waenda na sani suke koyarwa a school d’inku dan haka na sakasu suka nemo min sport, prep da duk wani pictures d’inki da wasu information a kan ki! Tabbas hankalina ya tashi sosai da na ga a scholarship kika je school d’in dan zuwa wannan lokaci soyayyarki ta riga ta yi min kyakkyawan kamu!
Sanin da na yi tabbas za asha gwagwarmaya da Granpa! Ne ya yi matuk’ar d’aga mini hankali, duk da inada tabbacin idan na lallab’ashi na shawo kanshi maybe ya iya yarda.
Har ranar graduation d’inku sai da na saka aka yi min video d’inki kina bada speech
special aka turomin ke kad’ai. Zuwa wannan lokacin na san in dai ban sameki ba tou tabbas akwai matsala, dan ni kad’ai na san me nake ji.
Na shirya akan zan dawo In karb’i adress d’inki In samu Granpa in yi mishi bayani
idan yayi aproving In je in sameki dan no matter how much i love you. I don’t think zan iya yarda in jefa ki a irin halin da Anty Maryam da Mommy suka shiga ciki, ba.
Ina shirin dawowa, Arshaad ya kirani akan wai Auwal yayi framing d’inshi har an kaishi Kotu!
Bani da kamar Arshaad shiyasa tun kafin In dawo na maida case d’in shi priority tukunna in samu Granpa
tukunna in sameki.
Ana cikin case d’in nashi kuma ya ce ‘in zo mu je In ganki’
Ba k’aramin tashin hankali na shiga ba ranar Huda! Don a take Ina ganinki na ganeki sannan kika sake samun guri kika yi bake bake a cikin zuciyata. Shiyasa In zaki tuna da kyar na iya seseta kaina na fito…..
Arshaad is my brother and best friend, that is why i did what i do to you that very day saboda a ganina ya zame min dole in yakiceki. In kuma saka miki k’iyayya ta a rai saboda gudun kar ma zuciya ta rud’eni, In so kaina in zo miki da nawa zancen saboda a wannan lokacin ina k’ok’arin tursasawa zuciyata In samu Inga na hak’ura da ke amman kwakwalwata da tunanina suna nusar da ni a kan. Ba fa zan iya hak’urin nan in barwa Arshaad ke ba!. And yadda na ga Arshaad yana sonki as his big brother hak’ura da ke is the best thing to do tunda na ga kema shi kike so! Shiyasa na yi k’ok’arin zama bad guy a idon ki har Anty Maryam (and still Ina jiye wa Abba a wannan ranar shiyasa abun ya zama biyu na aikata mata abunda na yi ranar a asibiti.)
Amman kuma sai abun ya gagara dan no mattaer how i try tun ranar da na ganki har kawo yanzun nan
I don’t think k’aunarki ta ragu dede da kwanyar zarra a cikin zuciyata! A ko da yaushe k’aruwa kawai take yi.
Har d’an k’aramin hauka na yi da aurenku ya matso! Gashi Mommy ta hanani guduwa…
Zakkah sadaka da sallar dare su suka taimaka Ubangiji ya ji k’aina ya mallaka mini ke a lokacin da ban tab’a tunani ba. Na tabbatar da ace ban aure ki ba to, It’s either in k’are a asylum ko kuma mak’abarta…”
Ya k’arashe maganar yana mai cupping face d’inta kafin ya d’ago fuskar tata yana kallonta
a hankali ya yi kisssing idanuwanta da ta lumshe sannan ya ce “I love you Hudan!
Ba wai sai da na aureki na fara showing intrest ba, noo, not at all! Tun kafin in dawo Nigeria nake
So da Burin inga na aureki. You are my happiness, my everything my whole heart kin shiga kin kanainaye
ke kawai nake gani ke nake So da Burin in mallaka in rayu da har k’arshen rayuwata. Na san ba lalle ki soni ba a yanzu but please dan Allah kar ki k’i ni Hudatie try and find a place for me in your heart i promise you won’t regret it! Just a tiny place, please my love.” Ya k’arashe maganar a hankali.
Hawaye ya ga ya fara bin k’uncinta dan haka ya jata ya yi hugging nata ya ce
“Sorry.. Amarya bata kuka Shikenan a bar maganar in dai zata saka ki kuka.
Let’s pray…….”A hankali ya cikata ya sunkuya ya d’auki sallaya ya wuce ya shimfid’e.
Nafila ya ja suka yi. Ya dad’e yana addu’oi kafin ya juyo ya dafa kanta ya yi addua. Sannan ya shiga jero mata tambayoyi game da addini. Ya ji dad’in sanin da ya ji tana da.
Daga nan ya ce “itama ta yi masa tata tambayar..”
Kasawa tayi dan haka kawai yayi murmushi ya ja hannunta suka mik’e…
Shi kansa yunwa yake ji amman a yadda yake jin sa sam! Ba zai iya jira a sha ko da ruwa ba!.
Da kyar dan sai da yayi da gaske tukunna ya zare hijabin nata.
Tabbas Hudan ta ga ikon Allah! Tsaurin ido! Tsantsar rashin kunya da kuma k’arfin hali a wajen Aslam.
Tun tana tirjiya har ta d’an fara sakin jiki dan salon nashi babu sauk’i. Kafin daga baya kuma ta ji an d’auki wata hanya daban mai cike da rad’ad’i wahala da azaba na fitar hankali’. Tun tana kuka a hankali tana d’an dauriya saboda rok’o da magiyar da yake ta yi mata har ta zo ta fara tirjiya sannan ta ware murya ta fara ihu tun k’arfinta dan taga abun nashi ba na wasan Yara bane ba.
Babu wanda Huda bata kiraba har K’asimu sai da ta kira! Indai Huda ta sanka to tabbas a wannan dare ta kira ka tana magiyar ka zo ka kawo mata d’auki.
Tun tana ganin daidai ta zo ta fara ganin dishi dishi! Tsananin azaba ta sanya daga k’arshema ta shak’i numfashi ta sume ba tare da oga Aslam ya san inda kanshi yake ba ballantana ita.