Skip to content
Part 69 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

Kamar a cikin ruwa take jinta! Sai kuma muryarsa sama sama yana d’an shafa mata ruwan a fuska yana tapping kumatunta a hankali yana
kiran sunanta a d’an rikice.

Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta samu ta bud’e idanuwanta da suka yi mata nauyi.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya ce
“Alhamdulillah!! Sannu, sannu sorry sannu”

Da kyar ta iya had’a idanu da shi, wani haushinsa ta ji a take sannan duk kyawun fuskarshi yau sai ta nema ta rasa! A hankali ta kawar da kanta gefe ta sa kuka.

Cikin rashin jin dad’i yace “Sorry mana, yi hak’uri please, na ce sorry fa”

Cikin kukan ta ce “Ka fita.”

Zai yi magana ta sake cewa “Allah ka fita!”

A hankali ya mik’e ganin kamar ma bata son kallon fuskarshi ya sanya ya ce, “Ki kirani kafin ki fito, kar ki fad’i”

D’aga masa kai kawai ta yi shi kuma ya sa kai ya fita daga cikin bathroom d’in. Duk da baya son ganin ta a wannanan halin da mood d’in amman sai ya tsinci kanshi da sakin wani k’ayataccen murmushi.

Yana fita ya ga wayarsa tana haske dan haka ya k’arasa ya d’auka da d’an sauri.

Ganin Aaima ya sa ya d’auka cike da ishashshen kuzari ya ce “Auta ya aka yi?”

Sai da ta gaidashi tukunna ta ce “Yaya na zo ne”

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya kashe kiran ya k’arasa ya zaro jallabiya ya zura akan gajeran wandon jikinsa ya fita.

Da baskets nik’i nik’i ya ganta na break fast.

Bayan sun sake gaisawa ta ce “Gashi inji Mommy”

Murmushi ya yi ya ce “ki ce mata mun gode. But akwai cook a nan itama ta huta dan na san wannan da kanta ta girka.”

“To” ta ce, ga mamakinsa sai ya ga ta wuce shi ta nufi hanyar sama. Da sauri ya ce “Ina za ki je?”

Ba tare da ta juyo ba ta ce “Zan d’an je mu gaisa da Anty Huda ne”

Gani ta yi ya biyota da sauri sannan ya kamo hannunta ya dawo da ita bakin k’ofa ya ce. “Ki bari ba yanzu ba! Bacci take yi.”

K’asa k’asa Aaima take danne dariyarta kafin ta ce “Ya Aslam akwai important maganar da nake so mu yi da ita. D’an matsa dan Allah in wuce.”

Ganin ya saki baki cike da shock yana kallonta ya sanya ta kasa daurewa ta saki dariyar da take ta k’ok’arin dannewa…

Sai yanzu ya gane me take yi mishi dan haka ya yunk’ura. Ita kuma ta juya ta wuce da gudu tana dariya.

Sai da ta b’acewa ganinsa tukunna ya girgiza kai ya mayar da k’ofar ya rufe.
Ya shiga kitchen ya d’auko plate da cups ya had’a da baskets d’in ya nufi sama.

Har Aaima ta k’arasa gida tana murmushi da mamakin yadda ta ga Aslam d’in yayi wani irin haske na ban mamaki sannan ga wani nutsatsen kyau da annuri cike da fuskarsa. A hankali ta sauk’e ajiyar zuciya a fili ta ce, “Hmm” Kawai, daga nan ta yi gaba.

Yana komawa ya tarar da Huda ta fito a wanka tana takawa da kyar za ta isa kan gadon…

Ajjiye kayan hannunsa yayi nan bakin k’ofar sannan da sauri ya k’arasa ya d’auketa chak! Yana mai cewa, “ba na ce ki jira ni ba? Taurin kai ko?”.

Bata kula shi ba, haka ya kaita kan gadon da ya shimfid’awa sabon bedsheet ya kwantar, a hankali ya yi mata light peck a goshinta kafin ya zauna a gefenta ya kamo hannunta
yana d’an matsawa a nashi ya ce “Ya Aslam bai kyautaba! He is sorry.
Yanzu kam na san kafin a samu a bani amsa ta ta jiya sai na garu. Nima dai in banda ni da karambani na ta yaya zan yi wannan aikin In sake b’allawo kaina ruwa? Ni da ban gama samun matsugunni ba…”

Turo baki tayi ta d’an juyar da fuskarta kad’an.

A hankali ya yi murmushi ya kawo hannunta setin bakinshi ya yi kissing kafin ya ce, “Thank you Hudatie, thank you so much! Ban san ta yaya zan fara yi miki godiya ba. I just want you to know that You are everything that I need to be happy and more. Tnx a lot, I love you.”

A hankali ta lumshe idanuwanta. Tabbas maganganun shi sun yi mata dad’i amman yadda take ji a jikinta ji take yi kamar ta yi ta kwarara ihu!.

A hankali ya mik’e ya d’auko baskets d’in ya kawo ya zuzzuba abincin.

Naciii da threats d’in da ya dinga yi mata ne suka sanya ta ta ci da d’an dama dan ita kam ko a mafarki bata buk’atar wata had’uwar tasu ita da Ya Aslam! Ita ta san waye shi, Ita ta san azabar da ta sha.

A hankali Sakina take bud’e idanuwanta. Da sauri Ummu ta ce
“Alhamdulillah! Ta farka.” Sannan suka yo kanta da sauri ita da Mama suna jera mata “sannu”. Daga nan suka kamata suka zaunar da ita.

Wani irin abu take ji yana yi mata yawo a cikin kanta! Daman tun jiya da ya toshe mata hanci da baki da wannan handkerchief d’in a take ta ji kamar an zuba mata tsutsotsi a cikin kanta kafin ta sume to yanzun ma tana farkawa ta cigaba da jin hakan, sosai kuma da k’arfi! Shi ya sanya ta shiga shafa kanta har ta kaiga tuje d’ankwalin ta hau jan gashinta da k’arfi kamar wata shahararriyar mahaukaciya!

Idanuwa kawai ta ga su Ummu sun zuba mata. Sai a lokacin ta lura da yadda idanuwansu suka yi jaaa
duk su biyun da alamun sun ci kuka.

Tana shirin yi musu magana idanuwanta suka sauk’a a kan Ashraff! Wanda ya tunkaro gadon shima.

Cikin tsanannin tashin hankali da b’acin rai ta ce, “Ashraff! Ashraff ne.
Kar ka k’araso, Ummu kidnapping d’ina ya zo zai yi wallahi, Ashraff ne”
Duk ta rikice ta gigice dan a tsorace take.

A hankali taga ya fara zubda hawaye yana sa hannu yana gogewa.

Gani ta yi Mama ta juya ta fita
Ummu kuma ta sunkuyar da kanta.

Bata gama tunanin abunda yake wakana ba Mama ta shigo tare da Doctor.

Yana shigowa ya nufeta ya hau dubata kafin ya ce “Me kike ji yanzu?”

A tak’aice ta ce masa “Tsana da tsoro!
Na wanchan bawan Allahn, ka ce masa ya fita Allah in bai fita ba zan illatashi”
Ta k’arashe maganar tana dukan tsakiyar kanta saboda yadda take ji abu na yi mata yawo a ciki.

Ajiyar zuciya Likitan ya sauk’e
kafin ya juya ga su Mama ya ce “Results d’in sun fito! Gaskiya ta bugu sosai a kan nata shi yasa dole za take misbehaving. Kar ku biyeta, kawai ku yi addua nima akwai magungunan da zan d’aurata a kai In sha Allah za a dace.”

Cikin tsananin tashin hankali Sakina ta ce “inna lillahi wa inna ilahirrajiun”
Tana mai d’aura hannunwanta duk biyu a ka! Za ta yi magana kawai Likitan ya kama hannunta su Ummu suka taimaka masa wajen rik’eta dan har ta fara bubbuge hannunsa tana tirjiya da surutai, bai yi wata wata ba
ya danna mata allurar da ko gama shiga cikin jijiyoyin ta basu yi ba
Jikinta ya sake gaba d’aya ta tafi luu
ta zube a nan kan gadon jinyar.

Kuka kawai Ummu da Mama suka saka hankalinsu a mugun tashe.

Da sauri Ashraff d’in ya matso ya fara lallashinsu kafin ya ce. “Akwai wani Doctor d’in da na sani a New York! Dan irin haka ta tab’a faruwa da wani cousin d’inmu. Basket ball ne ma shi wani ya buga masa a ka wanda muna a filin ball d’in fad’a ya had’osu.

Mama ni har ga Allah tsakani na da Allah nake son Sakina! Ba hauka ba
ko me ne take yi na ji na gani zan aureta in rayu da ita. A yanzu idan kuna so tsaff zan iya booking appointment da Likitan in fitar da ita domin samun lafiyarta.”

A hankali Mama ta ce “Haka kurum ta fara?”

Cikin share hawayensa ya ce
“Suna buga mata dutsen suka gudu. Ni kuma ban samu na bisu ba tunda naga kamar a buge suke sannan ga itama a kwance. Muna zuwa asibitin nan bayan taimokon gaggawa ta farfad’o,
abunda ta fara ce min shine ‘Ta bawa Aaima labarin Suhaila! Allah ya isanta, na cuceta ba zata aure ni ba’. Ganin da na yi she s not making any sense ne yasa kawai na yanke shawarar In kiraku.” Ya k’arashe maganar cikin karyewar zuciya da zubar hawaye.

A hankali Ummu ta ce “Shikenan Ashraff mun gode. Bara in kira Baban nasu na ji har yanzu shiru.”

Tana shirin fara dialing numbersa suka shigo shi da Abba! Sai da suka d’anyi kallon kallo shi da Mama
tukunna aka gaisa kafin Ummu ta hau zaiyyano musu bayani dalla dalla….

“Gaba kura baya damusa” Baban Sakina ya fad’a a ranshi dan yanzun nan yana shirin shigowa asibitin
Abba ya kirashi ya ce yana buk’atar ganinshi urgent! Shi ya sanya ya jirashi sai da suka gama tattunawa tukun suka shigo duba Sakinar dan shi Abban ma bai san tana kwance ba!
Ya zo mishi ne akan maganar Auwal. Tabbas sun san cewa bai kamata ba amman maybe a san abun yi
dan Auwal tun shekaran jiya
an kasa gane kanshi kwata kwata! He’s not even responding to treatment,
gaba d’aya jikin nashi sai a slow, hankalin Daddy a mugun tashe yake
shiyasa suka yanke shawarar zuwa su sameshi ko akwai wani taimakon da za su yi musu, duk da kuwa ba su ga way out ba amman dai gara a gwada.

A hankali Abba ya ce “Bacci take yi ne?”

“Eh” Ummu ta bashi amsa.

Yana shirin yin magana Ashraff d’in ya ce “Bara in kira Doctor d’in. Idan anyi sa a yana nan ma ko a yau za a iya wucewa…”

A hankali Ummu ta ce “Sannu Ashraff”

Yana fita Baban Sakina ya nema waje ya zauna ya dafe kanshi, bai san abun yi ba! Har ga Allah.

Cikin sanyin jiki Ummu ta yi mishi bayanin Likitan New York….

“In dai zata samu sauk’i kuma zamanta a haka zai iya janyo matsala!
Tou why not kawai ya d’aura musu aure tunda an riga an gama bincike akan shi Ashraff d’in, in ya so sai ya tafi da matarshi ya yi jinyarta a chan
tunda ya nuna zai yi d’in kuma zai biya makudan kud’ad’e a nema mata lafiya da komai” Baban Sakina ya aiyyana hakan a ranshi.

Dede nan Ashraff d’in ya dawo
ya ce “Yana nan! But zuwa nan da next week zai bar k’asar zuwa wani important aiki and ba lalle ya samu ganin mu ba idan aka kai next week d’in.”

A hankali Baban su Sakina ya mik’e ya ce “Ina zuwa bara in yi waya da brother d’ina”.

Dafa shi Abba yayi ya d’an kalleshi kafin ya juya ya cewa Ashraff d’in
“Za ka iya wucewa kawai, za mu san abun yi kar ka damu”.

Zai yi magana ya ce “ka je kawai an gode” Sai da Ummu ta ce “Ashraff ka je za mu nemeka, mun gode”. Tukunna ya juya ya fita da kyar.

Da mamaki Abba yake kallonsu yana ganin yadda duk suka rikice. Yaro k’arami ya na raina musu hankali.
Cikin son gasgata zarginshi ya nemi Ummu da ta yi mishi ishashshen bayani. Tana dire aya ya zaro waya ya danna kiran Aaima. Da kyar Aaima jikinta na karkarwa jin Abba ya ji abunda k’awarta ta aikata a school ta
shiga koro mishi bayanin tiryan tiryan. Har zuwan da Ashraff d’in ya yi estate a jiya.

Tana dire aya Abba ya kashe wayar
ya kallesu ya ce “Me kuka fahimta
a lamarin su su uku?” Bai jira jin me za su ce ba ya ce “Ni na fahimci K’arya
Yaudara da tsoro a lamarin Ashraff.
Ina so ka zo mu je mu samu Mahaifinsa a nan na tabbatar in dai mutumin kirki ne to gaskiya za ta fito k’arara! But first sai na fara kulle asibitin nan da mai asibitin tunda karb’ar cin hanci ya maida sana’a”

Bai gama rufe bakin shi ba. Likitan ya shigo! Sai da ya kallesu one by one
tukunna ya k’arasa inda Ummu take ya shiga yi mata bayani akan wasu takardu da ya shigo da su yanzu. “Case d’in Sakina fa is severe! In ba a fitar da ita a yau ko gobe ba tou tabbas za a samu babbar matsala! Shima sai yanzu ya ke ganin wannan result d’in bayan ya tsananta bincike…”

Kasa magana Abba yayi tsabar mamaki da takaici dan haka kawai ya turawa commisioner of police message
tare da adress d’in asibitin daga nan ya cewa Baban Sakina “ya zo su je..”
Suna fita ya ce mishi su wuce gidansu Ashraff.

A motar Abba ya yiwa Baban Sakina k’arin haske akan abunda ya fahimta game da Ashraff d’in kuma aka ci
sa a Baban Sakinan ya fahimceshi.

Ba Baban Sakina ba hatta Abba sai da ya cika da mamaki da suka k’arasa k’ofar gidan suka tarar da tafkeken masallacin juma’an dake a jikin gidan cike da jama’a anata shige da fice.

A hankali da kamala suka kutsa kai suka shige ciki, sakamokon hango Mahaifin Ashraff ya gilma ciki sanye cikin shiga ta alfarma.

Ba su gama tunanain meke faruwa ba
suka ji a loudspeaker ana. “An d’aura auren Ashraff Muhammad Bashir
Da Suhailat Yusuf Tanko a kan sadaki naira dubu d’ari uku lakadan ba ajalan ba.”

Kallon kallo suka hau yi kafin su hau kallon jamaar one by one. Chaan! Suka hango Baban Ashraff d’in da suka biyo cikin masalllacin, yana ta fara a yana gaisa wa da wasu Abokanayen sa na jiki jiki waenda suka samu damar halartar d’aurin auren gaggawan da aka gaiyyacesu.

Yana ganin Baban Sakina hankalinshi ya d’an tashi! Dan a iya saninshi bai gaiyyaceshi besides auren ma ai secret aka yishi to me kuma ya faru?! Bai gama dawowa daidai ba suka k’arasa wajen shi da Abba suka zauna a kusa da shi. Abba ne ya iya bashi hannu suka yi musabaha Baban Sakina kuwa da kyar ya iya ce mishi “Barkanmu..
Dan Allah d’an yi min elaborating abunda na ji an fad’a yanzu.”

Sai da Baban Ashraff d’in ya d’an kalli gefe da gefen shi tukunna ya mik’e ya ja su gefe ya fara magana k’asa k’asa
“Kasan me ya faru ne? Yaron yanzu sai a hankali wallahi….” Sai kuma ya d’an yi shiru kafin ya fesar da numfashi ya ci gaba da cewa “Shi Ashraff an d’an samu matsala ya je ya yaudari wata Yarinyar oga na wanda shi ya siya min takardar kujerar sanatan da nake mulka a yanzu! Hatta campaign shi yake taimaka min da komai. Kaga ni d’an siyasa ne In na yi mishi butulci ban kyauta ba kuma siyasata za ta samu matsala tunda party d’inmu d’aya.

Jiya Yayar Yarinyar ta kira Mahaifiyarshi directm To kasan mata abun nasu sai a hankali, a take sai ta yi mata fata fata kuma ta ce ‘ba dai Ashraff d’inta ba’.

Tofa shine Yaran su kuma suka je suka samu Mahaifinsu da Mahaifiyarsu suka fad’i komai.

Adress da sunana kawai ya karb’a ya gano Ashraff d’ana ne! Yau da safe sai ganin shi na yi.

Baban sakina ko kaine a situation d’in da nake na san dole ka yi abunda nayi.

Amman ka kwantar da hankalinka
Aure tsakanin Ashraff da Sakina babu fashi! In sha Allah lokacin da muka d’iba yana cika za a d’aura musu aure.

Jiya sai cikin dare Ashraff ya dawo gidan nan a hargitse wallahi ya bani tsoro kuma hakan ya sanya na sake fahimtar yana tsananin k’aunar y’arka dan na san tabbas labarin ta ji suka d’an samu matsala shiyasa ya damu har haka. Kar ka ce za ka yi interfering
dan Allah kar kace za ka yi komai ka barsu, dan Ashraff jiya har d’an k’aramin hauka ya yi! Idan ka ce za ka hanashi Sakina ban san ya za ai ba”.

Cikin tsananin b’acin rai Baban Sakina ya ce “A jiyan da ya dawo muku a haukace ka san me ya je ya yi?” Bai jira jin amsarshi ba ya ce “K’wamushe mini y’a ya je ya yi! Ya kaita wani asibiti suka had’a baki da mai asibitin aka manna mata ciwon hauka! Yanzu haka da ka ganmu da farko shirin d’aura musu aure shi da ita muke yi
saboda ya ce ya san wani k’warerren Likita A New Yorkm In kuma aka barta ba a kaita wajen Likitan da wuri ba
to zata iya mutuwa.”

A firgice Baban Ashraff d’in ya ce
“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun”

Sai kuma ya dafe kanshi kafin ya d’ago ya ce “Kayi hak’uri Alhaji Muhammad
Ashraff yayi laifi amman wannan yana yi maka nuni da abunda hanashi ita ka iya jawowa! Na tabbatar tsorata yayi
shiyasa yayi hakan! Yanzu ka kwantar da hankalinka zan yi mishi magana
ba zai k’araba, In sha Allah. Lokaci yana yi za a d’aura musu aure a samu a zauna lafiya”.

Shi kam Abba dariya ma Mutumin ya so ya bashi. Yana shirin yin magana ya ji Baban Sakina ya ce “Unfortunately, Alhaji ka yi hak’uri amman itama Sakina akwai wanda na ga ya fi dacewa ta aura! Za mu dawo muku da duk wasu kud’ad’en ku da kaya
dan na janye maganar aurenta da Ashraff gaskiya! Bawai saboda Ashraff ya yi aure ba..not at all. Zan yi hakan ne saboda yadda na ga kana shakkar Mahaifin Yarinyar da ka aurawa d’anka a yau na tabbar idan ya ce kar a yiwa y’arsa kishiya to ba za ka bari ba.

Cikin b’acin rai mutumin ya ce
“Wai Alhaji Muhammad ya mutum kamar ni da girma na ina yi maka magana har da magiya amma kana yi min musu???”

Ciki sauk’e ajiyar zuciya Baban Sakina ya ce “Shiyasa zan barka In bar maka d’anka dan ba zan iya musun rashin gaskiya da kai ba” Yana gama fad’in haka ya wuce inda ya ga limama, ya same shi ya gaya mishi wata magana kafin ya dawo inda Abba yake tsaye shi da Baban Ashraff ya ce masa
“Ka na da sadakin da za ka bayar na Auwal ko sai ka je banki?”

Kallonshi Abba ya yi a d’an rikice sai kuma ya sauk’e ajiyar zuciya yana murmushi kafin ya ce “akwai a mota,
bara in je in d’auko”.

Ko minti biyar bai yi ba ya dawo. A lokacin limamin har ya d’an tara jama’a an zazzauna.

Yana zuwa bayan an shirya komai ya mik’a sadaki ya yiwa Auwal wakili a take aka d’aura auren Auwal Yusuf Umar Farouk MT Da Amaryarsa Sakinat Muhammad a kan sadaki naira dubu d’ari biyu lakadan ba ajalan ba.

Ana gamawa Baban Ashraff ya juya ya fita fuuuuu! Daman tun d’azu ko zama kasa yi yayi yana mamakin tsaurin ido da taurin kai Irin na wannan talakan mutumin.

Ana shafa Fatiha Abba ya bayar aka siyo alawowi a shagon gefen su
aka zo aka rarraba aka watse. A take ya kira su Dad ya sanar da su good news.

Kasa hak’ura suka yi suka ce ya bawa Baban Sakina wayar. Shi kam har d’an kunyar irin godiyar da suka dinga yi mishi ya ji, daga nan suka yi sallama
suka nufi wajen Granpa domin sanar da shi.

Su Abba kuma suka koma asibiti wajen Sakina.

Suna shiga dede suka tarar ta farfad’o amman Mama da Ummu sun danneta
Likitan yana k’ok’arin sake sank’ama mata wata allurar yana cewa
“Ai dama na gaya muku! Ku duba fa kugani irin abubuwan da take yi
if possible a wuce da ita kawai Yau!
Tunda na ji Yaron ya san garin da Likitan, shi zai yi komai dan haka komai zai zo da sauk’i.”

Da sauri Baban Sakina ya je ya kwab’e allurar daga hannunshi! Yana shirin yin magana y’an sanda suka shigo.

Babban su ne ya k’araso ya karanto mishi laifinshi.

Tabbas Likitan ya san Ashraff zai fito da shi tunda ba a yau suka fara harka da shi ba! Yasha kawo mishi mata ya cire musu ciki amman duk da haka sai da ya ji gabanshi ya fad’i! Da kyar ya dake ya bi bayansu salin alin
bayan ya turawa Ashraff d’in message.

Suna fita Sakina ta ce “wallahi Abba k’alau nake, Ashraff munafuki ne! Shi ne ya shak’a min hanky d’insa wanda Allah kad’ai ya san girman kwayar da ya saka a jiki shiyasa nake jin k’aik’ayi a kaina kuma yanzu na daina. Dan Allah ku fahimceni Munafuki ne!
Baba dan Allah kar ku kaini wajen Likitan mahaukata.”

Matsawa inda take Baban nata yayi a hankali ya dafa kanta ya ce “ba komai
komai ya wuce, ki kwantar da hankalinki kin ji? Mun yarda da ke
Aaima ta fad’a mana komai ai”

Kallonshi kawai Ummu da Mama suke yi. A hankali cikin nutsuwa ya karanto musu yadda suka je suka tarar ana d’aurawa Ashraff aure da komai
da kuma yadda suma suka d’aura auren Sakina da Auwal a yau.

Wani sassanyan murmushi ne ya sub’ucewa Mama a hankali ta ce “Alhamdulillah”

Abba da yake kallonta ne ya ce
“Ma sha Allah.” Yana sakin nashi murmushin.

Sakina kuwa wani irin kuka ta saki.

Direct parlourn Granpa Dad da Daddy suka nufa. a nan suka iskeshi shi da Gramma yana jik’a towel yana d’aura mata a ajiki.

Ba yadda suka iya haka suka sanar da y’ay’an nasu rashin lafiyar Gramma d’in wanda hawan jinine yake neman yi mata illa tun rasuwar Ummi.

Ba k’aramin tashin hankali su Dad suka shiga ba kuwa. Da kyar! Granpa da Gramma d’in suka lallab’asu suka d’an nutsu bayan sun gama shiryawa akan za a fitar da Gramma d’in waje ta d’an huta ta samu change of environment ko da na wata d’aya ne
ta yarda.

Sai da Granpa ya tambayesu
tukunna suka tuno da zancen Auwal da Sakina, dan haka suka zaiyyano musu labari tiryan tiryan.

Mik’ewa Gramma ta yi ta zauna tana murmushi ta ce “Alhamdulillah na samu another grand in-law Allah ya sanya albarka dama inata addua wallahi saboda Yarinyar ta shiga raina tun a ranar da suka zo za a kai Huda.
Barka Alhamdulillah. Auwal sai ya warke ai yanzu Ja’iri mai ciwon so.”

Dariya duk suka yi har da Granpa kafin Granpa d’in ya ce “Yanzu abunda zai faru shine. Ku fara shirye shiryen visar har da na ita matar Auwal d’in,
Yahaya ka kirawo Kakan ta ka sanar da shi cewa Duba da yanayin halin da Mijinta yake ciki muna so mu tura mishi ita da wurwuri! At least a samu ya warke da wuri ja’irin.”

Dariya duk suka yi nan ma kafin Granpa ya ce “Sai ta wuce as soon as possible mu kuma idan mun yi welcomin Maryam sai mu wuce da washe gari ko?” Ya fad’i maganar yana dafa kafad’un Gramma.

Murmushi kawai ta yi ta sunkuyar da kanta dan duk sai ta ji ya bata kunya.

Daddy ne ya ce “Inyeee.. Grand honeymoon za.” Bai k’arasa ba
Gramma ta d’auko throw pillow ta buga mishi! Da sauri suka mik’e suka fita shi da Dad suna dariya.

A hankali Gramma ta kwanta a jikinsa tana sauk’e ajiyar zuciya kafin ta ce
“Thank you Daddie”

Murmushi kawai yayi yana me shafa kanta a chan k’asan zuciyarsa kuma yana regretting abubuwan da ya yiyyi.. ashe haka happines d’in frank family life yake amman ya dinga depriving kanshi da zuri’arsa ba tare da ya sani ba? Tabbas miskilanci da mugun hali bashi da rana.

<< So Da Buri 69So Da Buri 71 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×