Skip to content
Part 71 of 73 in the Series So Da Buri by Humaira Bulama

 A parlourn k’asa Aslam ya tadda Huda tanata faman safa da marwa…

Duk yadda taso kasa rik’e kukanta tayi dan haka kawai sai ta sake shi ta taho tana zuwa ta fad’a jikinsa.

A hankali yana sauk’e ajiyar zuciya ya shiga lallashin ta

yana rad’a mata wasu maganganu a kunne.

Cikin d’an murmushi da kuka at the same time ta kai mishi duka a k’irji.

A hankali ya ce “auch!!”

Yana shafa kanta.

Washe gari da sassafe .

Arshaad ya zo. Aslam bai tashi ma akan sallayar da ya gama karatu ba ya ga call d’insa, tunaninsa kuwa yake yi dama yana rayawa a ranshi dalilin da ya sanya bai ganshi a masallaci ba.

Yana d’auka ya ji ya ce masa

‘yana k’asa gidansa,

ya zo ya bud’e masa.’

“To” kawai ya ce daga nan ya mik’e ya cewa Hudan.

“Ina zuwa”.

ya fita.

A hankali ta bishi da kallo har ya wuce ya fice tana jin yanayin da takan tsinci kanta  a gameda shi yana sake nunkuwa.

Masu aikin su duk ba anan suke kwana ba shiyasa sai da Arshaad ya jira Aslam ya bud’e mishi tukunna ya shigo.

Da murmushi suka yiwa juna sallama kafin Arshaad d’in ya ce “sorry, na tada ku da sassafen nan ko?”

Ajiyar zuciya kawai Aslam ya sauk’e sanann ya ce

“Bismillah”

Yana me bashi hanya.

Suna zama ba tare da b’ata lokaci ba Arshaad ya ce

“Sallama na zo yi muku”

Yana d’an murmushi.

Da mamaki Aslam d’in yake kallonshi kafin ya ce

“Tun yanzu?”

Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna ya ce

“I have to, sanann inaso in fara aiki da wuri..you promised Granpa ba za mu yi letting nashi down ba

so bana son in baku kunya

da kai da shi.

Sannan tun a jiya bayan mun rabu da na kira Daddy

yake cemin akwai aiki gaskiya

a company d’in.”

A hankali Aslam ya ce

“So this is it?”

“It’s just a good bye na d’an wani lokaci, zan dinga zuwa  in sha Allah kar ka damu.”

Arshaad d’in ya fad’i hakan cikin tarar numfashin shi.

Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e ya sunkuyar da kanshi yana kallon k’asa sai kuma ya fara wani kalar murmushi tukunna ya fara magana

“This Life is very funny!

Difficult! Harsh! And way too upside down

A ko da yaushe it’s very hard ka ga mutum ya samu all that he ever wished for

ko da ace kuma zai samu d’in to sai kaga ya samu late

ko kuma ya samu opposite

ko dai ma ya rasa gaba d’aya….

Tun tasowarmu

ba ni da burin da ya wuce

Inga mun rayu cikin farin ciki gaba d’ayanmu a inuwa d’aya

Ni Kai Aaima Dad Mommy Mammy

har da su Auwal

this has been my wish since childhood

amma

It turns out

ba wai ga ni kad’ai ba ga yawancin mutane za ka ga dukkannin abunda kake so shi yake zame maka jarrabawa.

Hak’ik’a Ubangiji yana jarabtarmu ne domin ya gwada imaninmu, yana jarabtar mafi soyuwa a cikin bayinsa da abunda ya san sun fi tsananin so da kwad’ayin samu….i have accept my destiny, i have accepted the fact that

rayuwar da na so in yi da ku baki d’aya a inuwa d’aya ba zata tab’a yiwuwa ba.

Although i was and I’m broken amma

I’ll heal and embrace it with time.”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya d’ago ya kalli Arshaad wanda tunda ya fara magana ya kafeshi da idanuwa, a hankali ya ce

“Ina yi maka fatan alkhairi

Allah ya sanya albarka a cikin dukkannin alamuranka

Allah ya baka sa’a ya kare ka a duk inda kake.

Arshaad inaso ka sani

you will forever be my best friend, bani da da d’an uwa who stood by me through my worst times irinka

shiyasa nake ji a raina inama ace Ina da dama to da ba zamu so mace d’aya ba.”

Murmushi Arshaad ya yi ya had’iye wani yawu mai tauri kafin ya ce

“Na gode Aslam,

Allah ya k’addara saduwarmu.

Kar ka damu ko da ace bama kusa I’ll make sure ban baka chance d’in da za ka yi missing d’ina ba daga kai har su Mommy zamu dinga waya video call sannan zan dinga zuwa time to time

In sha Allah”

Cikin sanyin murya  ya ce

“Ubangiji ya azurta ni da family masu matuk’ar sona dole in dinga lek’o su”

A hankali yana murmushi yana kallonsa ya ce

“Especially ma you Aslam..

Ina takaicin yadda na bari soyayya da takaicin ganin an mallaka maka MT suka kaini

na kusa in halaka ka!

A tunani na…

Ina ganin maybe if I have the company zan iya mallakarta ta hanyar power!

Hak’ik’a So da Buri ya kusan kaini ga matakin da za a iya saka ni a mazaunin the most ungrateful and selfish being a duniya!”

Numfashi mai matuk’ar zafi ya fesar sannan ya ce,

“Babban darasin da na fahimta na d’auka shine

‘Wayo! Dabara da kuma k’arfin iko ba su Isa su baka abunda Allah ya riga ya k’addara ba naka bane ba!

Shi ne kad’ai mai bayarwa kuma mai hanawa a duk lokacin da ya so ya kuma ga dama, bawa bai Isa ya kwatar wa kanshi abu ba Allah kad’ai ne yake wannan, shine kad’ai yake kwata ya bawa wanda ya so ya ga dama a duk lokacin da ya so ya kuma ga dama’.”

Shiruu ya yi kafin ya sauk’e numfashi yana mai kallon k’asa a hankali ya ce

“Na yi wayo, na so kaina, na kawar da duk wani negative Abu da nake gani a kan hanyata da ka iya kawo min tangard’a wajen mallakarta, na take gaskiya, na cutar da Junaidu kaima na so in kawar da kai amma duk da haka.”

Shiruu yayi ya kasa ci gaba da magana sai kuma ya d’ago ya kallesa sosai ya ce “Aslam dan Allah please forgive m…”

Da sauri Aslam ya ce

“Arshaad mun wuce wannan wajen..

Idan akwai abunda zan rok’eka ka yi min a zaman ka na Uk shine

Ka goge komai..

Duk abunda ka ga yafaru it was already written tun kafin a haife mu dan haka ya faru ya wuce na manta kaima ka manta kar ka bari ya dame ka…

Bana duba abunda ka yi min dan bana ganin shi ma.

Iyaka abunda na sani nake gani

shine , ‘You are my best Man Arshaad’

Shine kuma abunda zan rik’e har abada.

Ina rok’on Allah ya bar mana zumunci mu.”

A hankali Arshaad ya ce “Ameen”

Sannan ya mik’e ya ce “bisssalam”

“Bara in kirata ku yi sallama”

Aslam ya ce yana k’ok’arin juyawa.

Da sauri Arshaad ya ce

“A’a barta.

Kawai ka ce mata na wuce”

Da “to” Aslam ya bishi,

daga nan ya yi mishi rakiya har bakin mota.

Already sun yi sallama da su Dad da Granpa da kowa dan haka ya shiga.

Driver na k’ok’arin ja a hankali Arshaad d’in ya kalleshi ya ce masa

“Ka kula mana da Aaima,

tana wajen Mommy.”

A hankali Aslam ya ce

“I’ll.”

Sai kuma kamar wanda baya son yin maganar ya ce,

“G’bye Arshaad”.

Yana kallo driver ya yi reverse daga nan ya ja suka fice.

Yafi minti biyar a tsaye ya zubawa inda motar ta bi ta fice ido kafin a hankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya ya juya ya shige ciki

idanuwansa jaz!

24 HOURS AGO!

Jirginsu yana Landing.

Daddy yana shirin d’aukar drop ya ji Mom ta dafa shi

ta ce “Daddy”.

A hankali ya juyo suna had’a ido ya d’an b’ata fuska ya ce

“Ke da ba y’ar gari ba Adama Ina ke ina zuwa d’aukar mu??”

Murmushi kawai ta yi ta ce

“Sorry” sannan ta wuce ta isa inda Sakina take tsaye.

Tana ta kame kame dan tun tasowarsu

Take fargabar ya zata kasance mata ita da Mom d’in.

Ga mamakin Sakina Mom tana zuwa kawai sai taga ta yi hugging d’inta.

A hankali ta ce “Welcome dota”

Sannan ta ja hannunta da d’an k’aramin trolley d’inta suka yi gaba.

Murmushi Daddy ya yi

Dan ba k’aramin dad’i ya ji ba.

Cikin sigar zolaya shima ya nufi motar da suka nufa yana jan nashi trolley d’in yana cewa

“Wato ni ko In taho ko In zauna a nan ba damuwarki bane ba ko?

Tunda kin samu y’arki”.

Murmushi kawai Mom d’in ta yi a haka suka isa bakin motar.

Suna zuwa drivern ya fito ya karb’i akwatunan ya saka a booth, suka shiga

Driver ya jasu suka wuce.

Ga mamakin Sakina sai ta ga an kaisu hotel!

So take tayi tambayar ‘Ina Auwal d’in’ dan in akwai wanda tafi buk’atar gani ta ga lafiyar shi a halin yanzu tou Auwal ne so take ta yi magana amman kuma kunyar su sai ta hanata dan haka kawai ta bi bayan Mom wadda take ta wani lallab’ata har suka isa k’ofar wani d’aki.

Wanda ya d’aukar mata akwati yana ajjiyewa

Mom ta bud’e d’akin ta ja suka shige bayan ta mik’awa Daddy makulli.

Suna shiga Mom ta rufe k’ofar kafin ta kamo hannun Sakina duk biyun ta rik’e, a hankali ta ce “Dota ki huta ki ci abinci.

Daga nan sai ki je asibiti wajen Auwal ko?”

Sai kuma ta d’an yi shiru

Chan ta ce,

“Ki yi hak’uri akan abunda na yi miki ranar birthday d’in su Shuraim, ki yafe min”.

A hankali Sakina ta ce

“Ba komai Mom ya wuce, ki daina bani hak’uri dan Allah”

A hankali Mom ta saka hannu ta yi hugging d’inta.

Sun d’an jima a haka kafin ta cikata ta juya ta fita tana cewa

“Yanzu za a kawo miki abinci, ki ci ki yi wanka

Sai mu zo mu wuce gaba d’ayanmu.”

Da “to” kawai ta iya binta dan ita har ga Allah so take kawai ta ji ance ta zo su wuce wajensa.

Ba yadda ta iya haka ta daddannna abincin ta yi wanka duk ranta a jagule.

Allah yaso su Mom basu wani d’auki time ba ta ji ana knocking..

Ta san sune dan ta gansu ta jikin d’an TVn dake jone da cctv camera d’in gaban k’ofar, dan haka gudun ma kar a sake yin wani jinkirin ta d’auko har handbag d’inta ta sak’ala akan bak’ar abayar da ta chanja dama ta yi rolling

Ta nufi k’ofar ta bud’e ta fita.

Suna ganin ta a shirye chap suka ce “su wuce kawai”.

Mom na y’ar dariya k’asa k’asa

Tana yaba tsantsar k’aunar da Sakina take yiwa d’anta.

Tana jin k’aunarta na shiga zuciyarta. Tun d’azu ta lura da yadda Sakinar take ta rawar k’afar son zuwa ta ga Auwal d’in…

Da wannan tunanin suka k’arasa mota

Drivern jiya shi ya ja su ya kaisu har cikin tafkeken asibitin.

Tunda suka fara takawa cikin asibitin gabanta yake mugun fad’uwa! Had’e da wani sanyin farin ciki da ya lullub’eta.

Suna shiga dakin ta fashe da kuka, duk da kuwa Aaima dama ta gaya mata halin da yake ciki amman bata yi tunannin samun shi da oxygen har yanzu ba.

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya k’arasa wajen ya tsaya a dede kanshi yana kallon shi.

Ya rame ba kad’an ba ya yi haske sosai.

A hankali ya shafa kanshi ya ce “Son”

Tun lokacin da suka shigo yake d’an jinsu sama sama. So yake ya bud’e idanuwan nashi amman ya kasa dan haka kurum suna shigowa gabansa ya yanke ya fad’i.

A hankali ya samu ya bud’e idanuwan nashi da suka k’ank’ance..

Suna had’a idanu da Daddy ya sakar masa d’an murmushi.

Murmushi Daddyn shima ya yi masa kafin ya ce

“I’ve a surprise for you”.

Ya yi maganan yana mai juyawa ya yafito Sakina.

A hankali ta k’arasa inda suke.

Tunda ta taho jikinshi ya bashi, yana cikin tunani.

Kawai ya ganta a tsaye a kanshi!

Mutumin da ko iya motsin kirki baya yi kawai su Daddy suka ga ya yunk’ura da sauri zai tashi sai kuma ya ce “auch!!”

Yana dogarar da guiwar hannunsa a kan gadon for sopport dan da mugun ciwo k’irjinsa wuyansa kafad’unsa da kansa suka sara!

Sai kuma ya fara juwwa.

Da sauri Daddy ya tareshi yana mai zama a bakin gadon ya maida shi kwance ya ce “careful mana”

Sai kuma yasa dariya ya ce “har ka warke kenan?”

Sai a lokacin kunya ta rufe Auwal….A hankali ya d’auke idanuwansa a kan fuskar Sakina ya mayar ya lumshe…..

Tsananin farin ciki ya ji da ya ganta by surprise dan ji yayi kamar an tsundumashi a aljannah!

Sai kuma a take batun Aurenta da Ashraff ya fad’o masa dan haka take lokaci guda ya ji wani tsananin tashin hankali.

Sannan k’irjinsa ya hau zafi.

Muryar Daddy ce ta katseshi jin yana cewa “Auwal ba komai mutum yake sa rai kuma ya samu ba!

Kar ka ga ka mallaki Sakina ka yi tunanin duk wani abu idan ka sa rai nan gaba zaka samu.

Ubangiji shi ya baka ita ba wai saboda nacin ka da rashin lafiyarkaba.

An d’aura muku aure jiya kai da ita sakamokon matsalar da ta b’ullo a alamarin Aurenta da Ashraff.

Amana ce Yarinyar nan.

Mahaifinta yayi mana kawaici da mutunci.

Dan Allah kar ka bamu kunya.”

Tunda ya fara magana Auwal ya k’ame! Ya kasa motsi sam!

Ji yake yi ma kamar iskar oxygen d’in bata isarsa.

A hankali Daddy ya yi wani sassanyan murmushi ya ce,

“Dota idan kuna buk’atar wani abun ga waya chan idan Likita kuke so za ki ga digits d’in a gefe.

Idan kuma abinci ne.

Shima digits d’in suna gefe.

Mu bara mu wuce ko?

Yana da number mu duk abunda kuke buk’ata ku kira.

Allah ya yi muku albarka.”

A hankali Sakina ta ce “ameen” tana mai sunkuyar da kai.

Da kyar ya iya bud’e idanuwanshi ya ce “Thankyou Daddy”.

A hankali dan shi kad’ai ya san luguden da zuciyarsa take yi masa.

Murmushi ya yi daga haka suka juya shi da Mom suka fice tare da alk’awarin ‘zuwa anjima za su dawo’.

Bayan Itama Mom d’in ta yi musu addua sun amsa.

A hankali ta ga ya mik’o mata hannunsa yana kallonta.

Cikin nutsuwa ta k’arasa ta sa hannunta a cikin nashi.

Still yana kallon fuskarta ya zaunar da ita a gefenshi.

Da kulawa ta ce “Ina wuni”.

Tana kallon bakinshi ya amsa da “Alhamdulillah”

A hankali.

Daga nan ya ja hannun nata ya d’aura a gefen fuskarsa saman kumatunshi ya had’a da nashi hannun ya runtse.

Kafin ya maida idanunsa ya rufe…

Ko minti uku ba a yi ba ta ji yanayin rik’o da ya yiwa hannun nata ya sauya

Alamun ya yi bacci, bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba..

Kallon shi kawai take yi tana sakewa ya d’an tara k’asumba har da gemu, tabbas ta so ta tarwatsa rayuwarta da hannunta dan bata jin akwai wanda zata iya so ta zauna ta rayu ta yi farinciki da shi idan ba Ya Auwal ba. Bata tashi sanin zazzafar soyayyar da take yi mishi ba sai da ya kwanta ciwo….

Sun fi 40 minutes a haka gaba d’aya hannunta ya k’age amman bata so ta motsa gudun kar ya farka dan.

Ta lura baccin nashi mai dad’i ne yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali

Kamar ma murmushi taga yana yi.

Sai da ya yi 1 hour yana baccin tukunna ya farka. Yana bud’e ido da fuskarta ya fara tozali.

Itanma shi take kallo dan haka ya sakar mata wani tsadadden murmushi. Sai kuma ya d’an gyara ganin kamar a takure take kafin ya ce mata “call the Doctor” a hankali.

Ta fahimci me ya ce

shiyasa ta mik’e ta je ta danna kiran Doctor d’in. Bayan sun gama magana ta koma ta zauna.

Tana zama ya sake kamo hannunta yana kallonta sam murmushi ya ki barin fuskarsa.

Ba ta jima da zama ba Likitan ta shigo.

Yanayin yadda ta ganshi kwance yana kallon kowa tar hakan ba k’aramin dad’i ya yi mata ba. Jininsa ta fara aunawa cike da mamaki ta shiga dudduba shi…

Ganin no nid of oxygen d’in ne.

Ya sa ta cire ta yi mishi y’an allurai.

Daga nan ta cewa Sakina “ta k’ok’arta a samu ya ci abinci.

jikinshi is weak kuma ta cire mishi drip d’in da yake d’an rik’e shi.

Tunda ba abincin yake iya ci ba…..”

Tana gama fad’in haka ta juya ta fita tana murmushi…Irin wannan soyayyar haka tabbas saboda wannan Yarinyar ne zuciyarshi ta d’an tab’u dan gashi daga zuwanta.

Komai ya fara yin normal a hankali. Ashe dama Nigerians  ma suna irin wannan zazzafar soyayya haka?

Duk da ba bak’ak’en fata bane amman ta fahimci Hausa suke yi.

Sakina na shirin mik’ewa ya sa dukkannin d’an ragowar k’arfinsa ya jawota, bata ankara ba shiyasa yayi nasarar janyotan, ta tafi ta fad’a jikinshi.

A zabure ta yunk’ura zata tashi ya ce

“Don’t move please”

A hankali dede kunnenta.

Shiruu ta yi kawai tana jin yanda bugun zuciyarshi yake yi da k’arfin gaske….

Ganin lamarin na shirin sauya masa ya sanya ya d’an cikata.

Da sauri ta tashi ta koma gefe ta zauna dan tabbas ba zata iya had’a ido da shiba kuma.

Ya fahimci ta gano shi shiyasa kawai ya yi murmushi ya girgiza kai kafin cikin kasala da rashin k’arfin jiki ya ce

“D’an duba chan locker, ki fitar min brush da maclean da body lotion.

Sai jallabiya da k’aramin wando. Please.”

Ya fad’i hakan a hankali.

Jinjina kai kawai ta yi ta mik’e ta isa inda locker take, ta d’auko duk abubuwan da ya lissaafa mata ta dawo.

Ta ajjiye a gefen gadon kafin ta ce

“Gashi” tana kauda kanta.

Sannan ta d’an turo baki kallon nashi ya fara isarta kwatakwata ko kifta idon ma fa baya son yi!

Aranta ta ce . “Har sai ya hango muni na”.

“Um”

Ta ji ya ce,

Wanda hakan yasa ta juya ta kalleshi.

Gani tayi ya d’an d’aga hannuwanshi biyu irin yanda Yara suke yi idan suna so a d’auke su.

Bata san lokacin da dariya ta sub’uce mata ba, da sauri ta sa hannu ta toshe bakinta sannan cikin dariyar k’asa k’asa ta ce,

“In d’auke ka?”

Ta yi maganar tana nuna kanta.

D’aga mata kai yayi kawai

Idanuwanshi a kanta.

Kafin a hankali ya ce

“Allah na kasa tashi!

Jikina ba kwari ko mostin kirki fa ba iyawa nake yi ba.

So kike in mik’e in zube?”

Cikin yin kalar tausayi ta ce,

“Ya Auwal dan Allah ta yaya zan iya d’aukar ka?”

Tana maganar tana kawar da kai dan bataso su had’a ido.

Murmushi ya yi yad’an ciji lower lip d’inshi kafin ya ce,

“To shikenan naji ba zaki iyaba

Zo to ki taimaka min In tashi.”

Da sauri cikin tarar numfashinsa

ta ce “A’a gaskiya”.

This time around sai da ya d’anyi dariya wadda ta taho mishi da d’an tari, sai da tarin ya tsagaita tukunna ya ce

“Mai yasa ba za ki rik’e ni in tashi ba?

Ko ba kya so in sake…”

Da mugun sauri ta k’arasa ta sa hannunta ta toshe mishi baki, cikin muryar kamar wadda zata fashe da kuka ta ce “Wallahi idan ka k’arasa sai na tafi yanzun nan zan koma wajen su Mom”

Da kyar dan jikinshi sam ba k’arfi ya iya zare hannun nata ya ce

“Ni kuma wallahi idan baki taimakamin na tashi ba

Sai na k’arasa kuma In rufe k’ofar in hanaki fita sannan In yi ta maimaitawa.”

Kamar zata yi kuka haka ta sunkuya kansa yadda za ta iya taimaka masa.

Sai da ya gama d’aga mata gira yana kashe mata ido tukunna ya sak’ala hunnunshi a kafad’arta

Yana dariyar yadda ta chuno baki ta kauda kai gefe.

Sai da ta yi bismillah tukunna ta d’an motsa da niyyar taimaka mishi, d’an yunk’urawa shi kuma ya yi hakan ya bashi damar mik’ewa ya zauna, da taimkon Ubangiji da na Sakina da kyar ya samu ya mik’e! K’afafuwansa har d’an karkarwa suke yi.

Ita ta d’an fara motsawa yana rik’e da ita ya ce “ta d’auka kayan da ta d’auko mishi”

Hannu kawai tasa ta d’auka.

Daga nan suka d’an fara takawa.

Har Cikin bathroom d’in ta kaishi.

A bakin tangamemen bathtub d’in ya zauna.

Sai da jiirin ya d’an sakeshi tukunna ya cikata ta had’a mishi ruwan wankan tab bathtub d’in.

sanann ta matsa mishi Maclean ta mik’a masa.

Sai da ta taimaka masa ya isa wajen sink d’in yayi tukunna.

Ta fara k’ok’arin fita domin ya samu ya yi wanka.

Cikin ruk’o hannunta ya ce

“Saurin me kike yi?

Jikina fa babu kwari!

Idan kika fita na fad’i baya fa za ki dawo damu.”

A hankali ta d’an matso suka nufi bathtub d’in tare.

Sanabe! Kala Kala awajen Auwal dan

Hatta shirt d’in ma ita ta b’alle mishi mab’allin ta cire, da kyar ya yarda ya sa hannu ya cire singlet d’in!

Tun daga nan ta sunkuyar da kanta sosai ta fara k’ok’arin tafiya amman ya rik’e mata hannu.

Drama sosai suka yi.

Dan ya kafe akan wandon ma ita zata cire masa gashi ya tare hanya ya rik’eta for support ya hanata tafiya.

Ganin da ya yi ta tubure sannan tama k’i kallonshi tana shirin fashewa da kuka yasa kawai ya kama wandon ya fara ja yana dariya k’asa k’asa a hankali ta ji ya ce,

“FYI! Babu boxers a ciki.”

Da mugun k’arfi ta saka kuka ta durk’usa a wajen dede nan kuwa ta ga ya saki wando ya fad’o k’asa dan haka ta ci gaba da kuka ta k’i dagowa sam! Ta runtse idonta.

Kukan da take yi ne yasa ya cika mata hannu, ai kuwa bata yarda ta kalli direction  d’insa ba ta juya.

Ta mik’e ta fice da mugun gudu.

Banda dariya ba abunda yake yi.

A hankali ya zare boxers d’in jikinsa ya shiga cikin ruwan da kyar. Ya kwanta a ciki ya lumshe idanuwanshi yana jero wa Ubangiji kirari da godiya.

Ya dad’e a haka tukun ya ja sponge da soap ya fara wankan.

Banda dukan uku uku ba abunda k’irjinta yake yi!

Da kyar ta samu ta tsaida kukan nata.

Kana ganinta ka san a mugun tsorace take ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar ya zo fitowa ya fito mata a haka! Tunda ta lura sam babu d’igon kunya a tattare da shi.

Da wannan tunanin ta juya gaba d’ayanta tana me kallon bango. Ta jima a haka ta ji k’arar bud’e k’ofar, sake matsawa jikin bangon ta yi.

Wanda hakan ba k’aramin dariya ya bashi ba.

Tana jinshi yana yi mata dariya ta yi banza da shi.

A hankali ta ji ya ce

“Relax! Har da jallabiyata da towel a kaina na fito,

Okay?!”

Bata yarda ba sai da ya matso kusa da ita ya kamo hannunta ya d’aura akan jallabiyar jikinshi tukunna ta sauk’e ajiyar zuciya ta juyo amman still duk da haka ba ta kallonsa.

A gefen ta ya zauna da kyar yana jin tsananin jiri da rashin kuzari ya ce.

“Anya ba a sauya mini ke ba kuwa? Ina tawan ta tafi ne?”

B’ata rai ta yi ta turo baki.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an matsa ya yi peckn kumatunta ya ce “Matata!”

Yana kallonta yana murmushi.

Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba

Itama.

A hanakali ta mik’e ta yo musu order abinci sannann ta dawo ta zauna a kusa da shi.

Yana nan rik’e da hannunta tana bashi labarin Ashraff aka kawo abincin.

Auwal, ya ma manta rabon da ya ci abinci irin wannan sai dai drip most a times, da kanta take bashi!

Wani nishad’i farinciki da jin dad’i yake ji wanda ba zai misaltu ba.

Haka nan ta ciyar da shi suka yi baccin su tare suka farka.

Suka yi sallah tare!

Kafin washe gari kam Auwal ya warke ba laifi sai dai yawan baccin da yake yi da kuma rashin k’arfin jiki da y’an abubuwan da ba za a rasa ba.

Dan ko da Daddy ma ya je da daddare yana bacci.

Ba k’aramin dad’i Daddy ya ji ba da ganin shi har yayi wanka kuma babu oxygen.

Bai wani jima ba gudun kar motsin shi ya tada shi yasa ya yiwa Sakina sallama bayan ya bata abubuwan da ya tsaya ya  siya musu.

*****              

Suna gama video call d’in Daddy ya mik’e idanunshi sharkaf da hawaye zai wuce!

Da sauri Mom ta ruk’o hannunsa ta durk’usa a gabansa.

Ta lura tun d’azu da ta fara bada labarin ta’asarsu ita da Mammy Daddyn yak’i kallon direction d’inta, yanzu ma haka.

Tana kuka ta ce,

“Dan Allah Daddy kar ka yi min wannan shirun naka. Ka hukuntani! Ka yi min duk hukuncin da kaga ya dace dani amman dan Allah kar ka rik’eni a zuciya ka banxatar da ni.”

A hankali cikin share hawaye Daddy ya ce,

“Adama I love you.

Morethan you can ever imagine! Amman ba zan iya zama ince wai na yafe miki duk abubuwan da kikayi min lokaci guda kuma naci gaba da sonki ba!

Toh, wallahi k’aunarki da k’imarki tayi mugun raguwa a zuciyata…

How could you?!

Haba Adama!

Saboda son zuciya?

Adama Mommy fa kusan a kwance ta yi rayuwarta kin sani kin san matsalar.

Amman kika yi shiru!.

Sannan kika taimakawa Mammy dan ku kwantar da Aslam yayi jinya shima?

Doguwar jinya!!!

Saboda kawai kwad’ayin MT??”.

Cikin kuka ta ce.

“I was wrong!

I have been wrong for so long Daddy dan Allah ka yafe min.

Ban san ta Ina zan fara baka hak’uri ba, ka yi hak’uri tabbas na yi kuskure kuma kuskuren ya dawo mini.

Tunda gashi na rasa y’ar uwa ta d’aya tilo a duniya.”

Numfashi Daddy ya furzar kafin ya ce

“Duk son da nake yi miki dole ne in kin tab’a min family zan ji haushi Adama!

Ba zan iya kallon ki ban tuna abubuwan da kika yi ba.

Ki je wajen Inna!

Ni ban ce na sakeki ba amman kawai ki tafi wajenta zan nemeki.

Idan na huce.”

A hankali ya zaro atm ya bata ya ce

“Akwai driver da Aslam ya turo ya taho wai Auwal ya ce a kawo mishi wasu abubuwa.

Idan ya zo zan turo miki shi ku je ke da shi ku yi visa da komai. Direct ki wuce wajen Innaa.

Dan Allah ko kira na kar ki yi.

Idan na neme ki to. Idan kuma ban neme ki ba shikenan, zan aika miki da takardarki!

Allah ya raya mana Auwal…”

Yana gama fad’in haka ya juya ya fita da sauri.

A wajen ta durk’ushe tana wani irin mugun kuka.

BAYAN KWANA BIYU.

Haka kurum tunda Mama ta tashi yau jikinta a mace, Ummu na lura da ita dan tun jiya a wajen saloon taga kamar ma kuka take yi.

A hankali ta matso kusanta tace “Maama”

A karo na biyu.

D’agowa ta yi ta kalle ta.

A hankali ta ce, “Ki tashi ki cire lallen nan mana a yi miki black mai k’unshi ke take jira”.

Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e kafin a hankali ta janyo abun sakace Ummu ta hau b’alle ledar.

A take suka cire ita da Ummu ta shafa mata Mahallabiya.

Mik’ewa Ummu tayi da zummar zuwa ta kira me lallen tayi mata bakin.

Ta ji Mama ta rik’eta.

A hankali ta ce, “Abba ya fi son jan lalle”.

Murmushi Ummu tayi ta koma ta zauna ta kamo hannuwanta biyu kafin ta ce, “Kina tunawa kenan har yanzu

Alamun yana nan rad’au a zuciyarki har abada amman kuma kiketa faman k’unci tun jiya Me yasa baki da walwala?

Ko kema kukan za ki yi mana kamar y’ay’anki

Huda da Sakina?”

Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e kafin ta ce “Ba wai walwala ne bani da shi ba, dana sani nake yi.”

Da sauri Ummu ta gyara zama kafin ta ce,

“Da na sani kuma?

Na me?”

Wani d’an guntun murmushi Mama ta yi kafin ta ce

“Da na sanin kuka da sab’on dana dinga yi ina cewa ‘mai yasa rayuwarmu ni da y’ata ta zo a haka?!’.

Ummu na cire rai da Abba, na cire rai da soyayya amma gashi yanzu.

Ubangijin da nake ganin ya d’aura mana kaddara mai tauri

Zai sake mallakamin Abba.

Sannan Huda ma ta auri wanda yake tsananin k’aunarta shi da iyayensa.

What more could I ever ask for?.

Godiya da tasbihi nake ga Ubangijin talikai amman gani nake yi kamar is not enough!

Bansan ta yaya zan fara yiwa Ubangijina godiya ba.

Ki duba fa kiga yadda rayuwa ta chanja mana daga k’unci tashin hankali da bak’in ciki zuwa, Farin ciki cikar buri a lokaci daya!.

Ba abunda yake bani mamaki nake kuma gasgata Ubangiji mai kun fayakun ne.

Irin yadda komai yake tafiya smooth.

Hatta Granpa ya sauk’o sosai

Jiya fa kira na yayi a waya wai ya kira mu gaisa

Sannan ya sake ba ni hak’uri!…

Ashe dama za mu ji dad’i ni da Huda? Ashe za mu yi farin ciki?

Ashe zan sake d’and’anar soyayya?”.

Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e a hankali ta matsa kusa da ita tasa hannu ta rungumeta.

A take kuka ya taho musu a tare su biyun.

Suna a haka Shuwa ta shigo.

Murmushi kawai ta yi cikin dakiya ta k’arasa inda suke ta d’an b’ata rai.

Kafin ta ce “Yanzu dan Allah Maryam kema sai kin saka mu kuka?

Su Huda suna yi kema kina yi?”

Sannan cikin d’an fad’a ta cewa Ummu “tashi ki fita, yi maza ki fita kije kin bar Zainab da had’a abinci ke kin zo nan.

Oya Maryam kema tashi ki shirya yanzun nan za ki ga an fara zuwa”.

Bata Ida rufe bakinta ba

Hudan ta shigo ita da Mommy.

Da d’an sauri ta k’arasa ta fad’a kansu Ummu.

Tana murna.

Jujjuya kai kawai Shuwa tayi ta ce “Ni kam wannan alada taku ta turai ban santa ba!

Dan tsabar rashin man kai Huda yanzu ke da za a kai miki Maman naki inda kike shine kika fito? Kalleki ko nuna baki gama yi daga jinin amarcin ba amman dan fitina har kin fito?”

Murmushi Mommy ta yi suka gaisa ita da Shuwa kafin ta ce “Hajiya ayi mana uzuri, nima naso in hana amman ita da Mijin suka kafe!

Wai zata yi mishi kuka idan na tafi.”

Cikin d’an fad’a Shuwan ta k’arasa ta sakar mata rankwashi a kai tace “ja’ira!!

Sannnan kin zo kin wani wuce ni kin fad’a jikin iyayenki..”

Murmushi Huda ta yi ta mik’e ta yi hugging Shuwa kafin cikin dariya da zolaya ta ce “Hajiya kawai ki fito ki ce daman kishi kike yi ban kula ki ba ba wai kiyi ta kame kame ba .”

Dariya duk aka yi.

A hankali Shuwa itama tana d’an murmushi tasa hannu ta yi hugging Huda tukunna ta cika ta ta juya ta fita da sauri tana cewa “su tabbata sun sa Mama ta shirya yanzu”.

Already Maman ta yi wanka tun sassafe dan haka kayanta kawai ta shiga bathroom ta saka. Sky blue lace da white jaka takalmi da jewelry’s Ummu ce tayi mata d’auri nan take ta fito rass Amarya…

Anyi hotuna sosai.

Allah sarki sakina a video call Huda ta kirata

Ta saka fuskarta akan screen din full aka d’auki hoton da ita su Ummu suna ta yiwa shirmen nasu dariya gashi Sakina ta dage sai an yi da ita.

A masallacin unguwar kusa da gidan Madu anan za a d’aura aure dan tun kafin lokaci ya cika manyan motoci suka cika layin tap! Har layin baya

Saboda Abba gayya yayi kamar wannan ne na farko.

Lokaci yana cika dubban mutane suka shaida D’aurin Auren

Yakubu Umar Farouk Mt (Abba)

Da Amaryarsa

Maryam Muhammad Madu (Mama)

A kan sadaki naira dubu d’ari uku.

Ana shirin watsewa Kaka ya cewa Limamin ya sanar za a sake wani d’aurin auren.

Tun lokacin da Kaka ya bada sanarwar Jalila wani mai d’an kantin ana ce mishi Abdullahi ya ce yaji ya gani!

Shi da Mahaifiyarshi basu wani dad’e sosai da tarewa a anguwar ba kasancewar Mahaifinsa ya rasu kuma anata rigima tsakaninsu da dangi da iyayen uban a kan gado yasa suka baro Katsina suka dawo Kano da shi da Mahaifiyarshi da k’anwarsa Aminatu tsarar Jalila.

Da farko Hudan ya so sai da mazan layin suka zaunar da shi suka yi mishi lecture a kan ‘in dai ba gudumar late comer da heartbreak yake son yasha ba tou ya hak’ura’ Tukunna ya hak’ura ya koma kan Jalila.

Wadda sai da ya fara sonta ne ma ya lura yama fi k’aunarta akan Hudan, dan haka ya je ya sameta ya gaya mata.

K’iri k’iri ta fito mishi ta k’i amincewa da shi sannan ta wankeshi tass!! Ta yi gaba abunta.

Babu yanda bai yi ba amman ya kasa cire ta aranshi har rashin lafiya yake yi saboda Jalila tun ba ma lokacin da Auwal ya fara kwasarta ba.

Sai da ya yi k’aramin hauka.

Har gida Mahaifiyarsa ta je ta samu Sadiya amman tijarar da Sadiya ta yi mata har yamafi wadda Jalilan ta yiwa Abdullahin kuma fa idan ka ga Abdullahi bashi da laifi sam! Bak’in saurayi dogon gaske mai fad’in k’ashi

Ba shi da wani muni a fuska sam ya kammala degree d’inshi bai samu aiki ba shiyasa ya bud’e shago saboda d’awainiyar Mahaifiyarsa da k’anwarsa dole shi ne zai yi.

Yana jin labari ya tafi wajen Kaka..

Ba abunda Kaka ya b’oye masa game da cikin da Jalila tayi amman wannan Yaro ya ce yaji ya gani.

Kaka ba k’aramin farin ciki yayi ba dan bai tab’a tunanin Jalila zata samu Miji saurayi kamar Abdullahin ba amman still sai da ya sake tura Baaba Talatu wajen Mahaifiyarsa da bayani

Itama ta amince. Dan haka aka bashi Jalila ba tare da an gayawa ita kanta Jalilan ko Sadiya ba

Baba ne kawai ya sani.

Su Sadiya suna gidan Baaba Laraba sai uban hayak’i suke yi dan Malamin nasu yace in dai sun yi wannan hayak’in a anguwar in da Maryam (Mama) take tou ba za a d’aura auren Maryam da Yakubu ba.

Suna hayakin suna ta uban tari kawu nan su na ciwo suka jiyo an d’aura auren Maryam da Yakubu!

Fatali Umma ta yi da kaskon.

Kafin ta fashe da wani matsanancin kuka!.

Jalila kanta sai da ta yi kwallar tashin hankali.

Ba a yi minti talatin ba suna cikin jimami da tashin hankali suka ji ana sanarwa.

“An D’aura Auren Abdullahi Muhammad

Da Amaryarsa

Jalila Usman Bashir”.

            

<< So Da Buri 71So Da Buri 73 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×