Skip to content
Part 9 of 9 in the Series Soyayyar Da Na Yi by Habiba Maina

Zabura mamma tayi, cikin wani firgici take sai ɗan kwallinda ke kanta ne, ya faɗi. waige- waige, take ta rasa me za ta ɗauka, ɗan kwalin nata ta ɗauka ta sake ajiye wa ta ɗauko gyale ta sa gudu ta fito ta sake komawa ɗakinnata ta ɗauki purse ɗinta ta fito da gudu ji take kamar ta fire…., kwata-kwata bata sauri, ta fito a gaggauce sai karo sukayi da mahaifiyatar ta,

“Bismillahi……!” Mahaifiyarta ta faɗi cikin tsoro ta dafe kirjinta da hannun hagu ɗayan hannun nata na dama kuma na riƙe da fasash’shen glass, zuciyarta na bugawa ta ce,

“Mamma wannan wani irin fita ne da gudu? ina zaki je haka kina hanzari?”Ita ma zuciyar Tata bugun yake sai dai hankalinta a tashe, yake wadda ya kai baza ta iya yi wa mahaifiyar ta bayani ba da i-i-na ta ce,

“Ma..ma..karanta…., ki bari in na dawo zan faɗa miki.” ta faɗi da sauri sannan ta fice da gudu.

“Mamma…!
Mamma…!”

Mahaifiyar ta, take faɗi kiranta ta ke amma, inna! ta riga ta isa ga bakin gate, bata ko juyawa, ba ta ma jin kowa! ita dai burinta, ta isa ga makarantar. ganin yadda ta zo da gudu yasa me gadi Ya tashi shima da sauri ya buɗe mata kofa yana mai cewa,

“Maman baba lafiya kuwa?” Bata kula da shi ba ta fice da gudu, da idanu mahaifiyar ta bita har ficewar ta sannan tayi ajiyar zuciya ta ce,

“Ha’ah, Ni ba yanzu yarinyar nan ta shigo tana kuka a canza mata makaranta ba….? To yanzu kuma me zata je yi a makarantar?” Mahaifiyatar ta ke tambayar kanta cikin mamaki, ta ci gaban da cewa,

“To shikenan Allah ya kawo ki lafiya…, amma dai wannan yarinyar akwai abinda take ɓoyewa…, Zata zo ta same Ni.” Sannan Ta je ta zubar da glasses ɗinda suka fashe a dustbin ta juyo ta shige ciki.

*****

Umaru Shehu specialist hospital maliya suka kai shi emergency room a kaishi babu wani ɓata lokaci da zuwan su suka sami gado domin suna shiga kenan aka sallami wani mara lafiya don haka sai aka bashi gado aka kwantar da shi, Na’ima da maliya duk sun ruɗe sun rasa yadda zasu yi sai kai kawo suke, nurse’s ne suka shigo suka dudduba shi sukayi gwaje-gwajen su, sun ɗauki lokaci basu ce komai ba, babu kuma wani bayanai, babbar nurse ɗin ce da ta Dube shi sai ta girgiza kai, hakan yasa Na’ima da maliya cikin ruɗani kar fa a ce Abdul mutuwa yayi? Na’ima ce ta kasa daure yin shiru sai da ta iso tayi musu tambaya,

“sister don Allah ki faɗa mana mutuwa ya yi?”

Ajiyar zuciya nurse ɗin tayi sannan ta gyaɗa kai ta ce,
“be mutu ba, yana nan da ransa, amma ina mahaifiyar shi?” Haɗa idanu sukayi suka kalli juna Na’ima ta kasa amsa tambayar, sun rasa ma me zasu ce wa nurse ɗin, shin su faɗa mata gaskiya? ko suyi mata karya? kowa da nashi tunanin gani suke idan suka ce mahaifiyarshi na gida to za’a ce su kirawo ta su kuma basa so kowa ya sani tunda suma ce kawai, idan ya farfaɗo ai shikenan Saboda basa so bayyanar maganar ta jawo maganganu. ta ɓarin Ramlat da kuma shi Abdul. Ko wanne a cikinsu suna yi mishi kara, cikin yanayi na rashin gaskiya maliya ta ce,

“Tana gida amma mu kannen sa ne.” take Na’ima ta katse ta da cewa,

“A’a! mu course mate ɗinsa ne.” domin ta san matsalar da zasu iya shiga idan suka sa karya a cikin lamarin duk yadda sukayi dai don su boye abinda ke faruwa gaskiya sai ta fito don haka sai ta kiftawa maliya idanu da kada ta tanka akan gaskiyar da ta faɗi, ita ma bata sake cewa komai ba saboda haka nurse ɗin ta ce da su,

“To ya kamata Ku kira a gidan su ku sanar saboda yana da kyau iyayen shi su san halinda yake ciki sannan, bisa abinda muka gano akwai bayanai da muke so ayi wa iyayen nashi.” sake haɗa idanu maliya sukayi sannan ta zabura ta zo kusa tana cewa da nurse ɗin,

“Sister kince be mutu ba…, to mene ne ya ke damunsa? muma zaki iya faɗa mana, kuma ai zamu kula da shi sosai ba sai mahaifiyar shi ta zo ba, ina ganin suma ce kawai.” maliya ta faɗi ta kuma dubi Na’ima ta ce,
“ko?”

“E..eh.” cikin i-i-na Na’ima ta amsa

“Ummi…, kunce min ku course mate ɗinsa ne? to ta yaya zan faɗa muku abinda ke damun sa? in dai har yana da iyaye ba sato shi akayi ba? to muna bukatar Ganin iyayen sa a nan, idan kuma ba haka ba zaku iya canza asibiti.” nurse ɗin ta faɗi sannan ta kara da cewa,

“Yanzu dai mun sa mishi drip kuma nan da wani hours zai iya farkawa Saboda haka kafin sauran treatment yana da kyau iyayen shi su kasance a kusa da shi saboda wasu shawarwari.” tana faɗin haka ta fice ta bar su a wurin ita da nurse’s ɗinda suke Bin ta a baya.

Sinkaikai sukayi sun kasa cewa komai, komai ya ruguje musu, ta yaya zasu Fara kira a gidan su Abdul Na’ima ce ta je da sauri ta zauna kusa da shi tayi masa addu’a tana faɗin,

“Laɓɓa’asa ɗahurun insha Allah!
As’alullahal Azima, Rabbul arshil’azimi anyash’fiyaka.”

“Wish you speedy recovery Abdul, you will soon be fine! insha Allah.” maliya ta faɗi bayan dawowa da tayi cikin wani dogon tunani da ta shiga tana faɗi kamar zata yi kuka, sannan ta dawo kusa ta zauna ta ce da Na’ima,

“Nifa na rasa me muke ciki yanzu? ya zamuyi Na’ima tell me? ya zamu yi? ki dubi duk yadda muke ganin abunnan zai zo da sauki ba tare da kowa ya sani ba ashe ba haka bane kuma, wallahi Ni bana so kowa ya sani.”tana fadi tana kallon Na’ima, amsa kawai ta ke jira.

“Nima gaskiya wannan lamarin ya shammace Ni…, nifa zata nayi da Munzo kawai ɗan yayyafa mishi ruwa za a yi ya tashi ashe ba haka bane. nifa ko…? ina ganin akwai abinda nurse ɗinnan take ɓoyewa…” Na’ima ta fadi.

“Huhh! maliya tayi ajiyar zuciya ta sunkuyar da kanta sannan ta sake ɗago kai ta ce,

“nifa yanzu ba a sanar da iyayen sa abinda ke faruwa ne matsala ta ba, the problem here is that, me zamu faɗa musu idan suka tambaye mu me ya same shi?”

“Exactly! kada mu faɗa musu abinda ya faru…, shi kuma Abdul idan ya farfaɗo ya ji babu daɗi. me yuwa ya ga laifin mu. saboda da sanina ya sha ɓoye ire-iren waɗannan issues ɗin har ya wuce gidan su basu sani ba yanzu faɗa min ya ya zamu yi?” inji Na’ima.

*****

Na pep ne ya sauke mamma a bakin makarantar cikin hanzari ta cire kuɗin sa ta bashi da sauri ta nufi cikin makarantar sai cibis tayi da Shamsu kaɗan ne ya rage suyi karo cikin mamaki Shamsun ya ga mamma a zabure ya ce,

“Ramlat….! Zaki..?” ya ma rasa da tambayar da zai fara yi mata cikin tsaye ita kuma ta hanzarta tambayar shi.

“Me ya sami Abdul?” wani mamaki tambayar ya bashi ya ɗauki mintuna yana kallonta don ya ji maganar wani bumburukwai, cikin mamaki shima ya ce,

“Abdul kuma? To Me kuma ya same shi?”

“Ha’ah! This seems surprised? kana nufin lafiyar shi kalau?” Cikin mamaki Taji tambayar ta shi shima kuma da halamu shamsu bai san komai game da Abdul ba, kuma babu alama a fuskar sa cewa wani abu ya faru da Abdul, ta tambaye shi ita ma cikin mamaki kar dai plan su Na’ima suka shirya mata don ta dawo makaranta.

“Eh to gaskiya I can’t tell, because tun abinda ya haɗa ku ɗazu bayan tafiyarki gida shima ya tafi, but I don’t know where he went, we just decided to confront him Ni da su maliya should atlist to advise him about what is happening between you both, amma bamu same shi ba na kira wayar sa ma bata shiga is switched off. to daga karshe dai duk muka hakura Na’ima da maliya suka shiga ciki ban sani ba ko cafeteria suka je I don’t know, Amma wannan shine abinda ya faru.”

Yana gyaɗa kai da alamar tabbatar mata da haka, ya dakata da faɗin haka sannan ya sake tambayar ta.
“amma me yasa kike tambayar ko wani abu ya same shi?”

“There is a big problem shamsu….” mamma ta faɗi ta sake cewa,

“Wallahi bayan na huta ma a gida Na’ima da maliya suka kira Ni suna bani hakuri akan abinda ya faru, Ni kuma naga I don’t have to hide anything from them, kawai sai na faɗa musu cewa za’a canza min makaranta, bazan sake dawowa makarantar nan ba, just then Naji sun sa ihu suna hailala suna kiran sunan shi, kaman akwai abinda ya same shi. don Allah ka faɗa min gaskiya ko kana ɓoye min wani abu ne?”

Tana kallon shi har cikin idanu tana cewa,
“Bana so in zama matsala ga kowa, please shamsu tell me the truth.” tana faɗin haka cikin rikicewa kamar zatayi kuka.

“Calm down! ramlat! Babu wani abu da na ke ɓoye miki, wallahi I’m not aware of All this…, but?” bai karasa maganar sa ba sai wayarsa ta ke kara ya duba Na’ima ce take kira da hanzari ya ce,

“Yauwa ga Na’ima tana kira.” ya ɗauka ya kara a kunne,

“Hello Na’ima wai me ke faruwa ne? ina jin wani rumours akan Abdul.” ya faɗi bata bari ta ji zancen nashi ba ta ɓarke mishi da cewa,

“Shamsu! don Allah ka taimaka mana kazo ka same mu a specialis hospital yanzu-yanzu don Allah.”

“Me ya faru?” Shamsun ya tambaya amma bata bari ta bashi amsa ba ta katse wayar.

“Hello!
Hello.” shamsu yake faɗi.

“Innalillahi wa inna’ilaihirraju’un! ya faɗi da ya fahimci Na’ima ba, jinshi take ba. ta ma katse wayar. Tabbas akwai abinda ke faruwa.

“Ta tabbata akwai abinda ya sami Abdul, domin babu wani bukata da Na’ima zata neme Ni a kai, sai wanda ya shafe Ni. babu shakka! Abdul ne” shamsu yana faɗi cikin sanyin jiki.

“A ina suke?” mamma ta tambaya.

“Suna specialist hospital injita.”

“To me muke jira?! mu je mana…” Mamma ta faɗi.

“Eh babu abinda zamu jira kam, let’s go.” da hanzari suka nufi kan titi suka sami na pep suka hau.

<< Soyayyar Da Na Yi 8

1 thought on “Soyayyar Da Na Yi 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×