Skip to content
Part 11 of 11 in the Series Su Ne Sila by Aisha Abdullahi Yabo

Zaune take a tsakiyar gadon asibitin ɗaya hannunta ansa masa ankwa an haɗa da ƙarfe gado, ɗaya hannun kuma ana ƙara mata ruwa, gaba ɗaya ji take ta tsani rayuwar ta ‘me yasa ba za su barni na mutu na huta da wannan rayuwar mai ciki da duhu ba’ ta kai duban ta ga hannunta da yake da ankwa wani irin abu mai nauyi ya tokare mata zuciya, hawaye masu ɗumi suka ci gaba da zarya a kan fuskar ta. Dr Hafiz ya shigo nus na biye da shi a baya tana riƙi da fayel har suka tsaya kanta babu alamar ta san da zuwan su, kallon ta yake fuskar sa na nuna tausayin ta ‘ƙaramar yarinya kamar wannan a ce irin wannan mummunan ƙaddarar ta faɗa kanta tabbas a kwai tausayi’ ajiyar zuciya ya yi “sannu!” Kallon gefen su ta yi a tsorace ganin su sanye da kayan likitoci ta kawar da kanta tana kallon ƙofa D.S.P ne tsaye daga bakin ƙofar yana waya, ta kawar da kanta tare da yin ƙasa da idanun ta.

“Ya jikin na ki?” Shiru ta masa, nus ɗin ta ce. “Dr Hafiz ai tun da ta farfaɗo taƙi ta yi wa kowa magana tun da dare na zo na yi mata magana babu amsa haka da safe na shigo ba ta magani da na mata magana sai dai kawai ta bini da kallo, ina tsoron idan har ba wata matsalar ce ta samu ba sanadin shaƙar da tayi wa wuyan na ta ba” zuba mata idanu ya yi ba tare da ya ce komai ba ya karbi fayel ɗin ya buɗe yana duba wa D.S.P ya ƙara so wajan su yana faɗin “ai na ga kamar ta samu lafiya za a iya bamu sallama ko?”

Sai da ya ƙarasa duba fayel ɗin ya miƙa wa nus ɗin hannayen sa na cikin aljihun wando ya ce.

“AlhamdulilLah jikin da sauƙi sosai, sai dai in da matsalar take tun bayan da ta farfaɗo taƙi tayi magana dole a kwai buƙatar a yi bincike dan tabbatar da lafiyar ta ba mamaki ko sanadin shaƙar da ta yi wa makoshin ta ta hanyar rataya hakan ya janyo mata kamuwa da cutar depression”.

D.S.P ya dube ta ya na faɗin “Doctor zai iya yuwa garau take ji kawai kissa ne irin na ta tunda ta san daga nan ina za ta tafi dole ne za ta yi duk abin da za ta yi dan ɓangarar da tunanin mu domin yin hakan ya ba ta damar aikata wani abun” murmushi Dr Hafiz ya yi kafin ya ce “ba na tunanin za ta yi wani abun ku dai ƙara haƙuri idan an yi dukan auni-auni an tabbatar da lafiyarta sai a ba ku sallama ku tafi da ita ɗin”.

“Am…” Hannu Dr Hafiz ya ɗaga masa yana faɗin “ka yi haƙuri D.S.P a yi yadda na ce ba kuna tare da ita ba, ‘yansada uku ne a ƙofar ɗakin nan bayan kai cikon na huɗu ga shi duk da ba ta da lafiya kun ɗaure ta to duk ta ina za ta samu ta tsere ma ku”.

“Uhm! Shi kenan Dr Hafiz Allah ya ba ta lafiya”.

“Amin. Mu je office ina so za mu yi magana” bayan fitar su wata ‘yar sanda mace ta shigo tana sanye da kayan ‘yansada kallo ɗaya Zainab ta yi mata ta kawar da kanta ta koma ta kwanta zuciyarta a ƙuntace take jinta.

Abakin ƙofa suka haɗu da Dr Mansur “yawwa Dr Mansur yanzu nake shirin ƙara kiran ka a waya na ji ka shiru”. “Afuwan na haɗu da gosulow ne a hanya, ya jikin na ta?”

“AlhamdulilLah da sauƙi sai dai kamar ta samu matsalar depression” Dr Mansur ya fito da idanu a furgice ya na faɗin “innalillahi wa Inna ilahi raji’un!” Dafa kafaɗar sa Dr Hafiz ya yi “ka kwantar da hankalin ka ba mu tabbatar ba sai dai abin da bincike ya nuna, mu je office ɗin” cikin damuwa ya bi bayan su zuwa office ɗin Dr Hafiz.

Dr Mansur yana zaune a kan kafet falon sa abincin shi na ajiye a gaban shi A’isha ta shigo falon tana riƙi da Anwar da tashin shi daga bacci kenan yana rigima yana ganin Abban shi ya fara zillo ta a jiye shi kusa da shi da sauri ya rairafa ya hau kan ƙafar Dr yana gwaranci “Abba Abba” rungume shi Dr Mansur ya yi yana mai yin ajiyar zuciya “Anwar sarkin rigima an tashi”.

“Ya na ga ba ka ci abincin ba me ya ke damun ka kwana biyun nan duk ka yi wani iri a kwai damuwa a tare da kai”.

“Uhm! Bari kawai Aisha lamarin yarinyar nan Zainab da nake baki labari ya tsaya mun a rai wallahi gaba ke ɗaya komai baya mun daɗi” ɗauri fuska tayi “ni fa Abban Anwar ban gane ba an yi yamma da kare, na fa kula gaba ɗaya ka ɗauki lamarin yarinyar nan da girma a zuciyar ka” dariya ya yi marar sauti yana gyaɗa kai “ko dai mata sai abar ku in dai a ka zo kan maganar kishi gaba ɗaya ƙwaƙwalwar ku tamkar ta yara take komawa” kawar da kanta ta yi gefe tana tunzara baki hannu yasa ya juyo da fuskarta suna kallon juna “yarinyar nan fa da aure a kanta”.

“Amma ai mijin ya rasu ko takaba za ta yi ta gama”

“To in banda abin ki yarinyar da take da hukuncin kisa a kanta ta ina har ki ke tunanin wani abu makamanci na so zai ɗarsu a zuciyata? Kawai ina tausaya mata ne yadda AZAL ta faɗa kanta ne, sannan damuwar da ki ka ga na ƙara shiga shi ne yarinyar nan tana da juna biyu wanda ko sati uku bai ƙarasa cika ba” nan take yanayin ta ya sauya daga ɓacin rai zuwa jimami da tausayi “Allah sarki to yanzu ya za a yi kenan hakan za a yi mata hukuncin kisan da juna biyun?”.

“To hukuncin dai ya na hannun alƙali amma dai da wahala a yi hukuncin yanzu sai dai an zauna shari’a ranar Laraba wanda shi ne za a yi zama na ƙarshe akan kes ɗin ta”

“Oh ita kuwa wace irin AZAL ce ta faɗa kanta Allah na tuba ko kiyashi ka kashe ya kake ji a ranka bare kuma mutum”

“Ai kuwa dai sai dai AZAL ɗin yanayin ta kaɗai idan ki ka duba za ki yi mamaki a ce za ta iya kashe kiyashi bare har mutum, akwai rikitar wa a cikin kes ɗin”

“Allah ya kawo mata mafita amma kam akwai tausayi wallahi. Allah ya sa a sassauta mata wajan yanke mata hukuncin ko Allah zai sa ta haifi cikin”. “Amin”. “Kawo Anwar ɗin don Allah ka daure ka ci abincin”.

“Barshi kawai za mu ci tare” ya yi maganar yana ɗaukar cokali “Anwar za ka ci abinci Momy” kallon sa ya dinga yi yana dariya.

“Ina so zan shiga banɗaki” Zainab ta yi maganar cikin shaƙaƙƙiyar murya, ‘yar sandan da take karatun jarida ta kalle ta da sauri “au dama kina magana shi ne ki ka yi wa mutane shiru”.

“Ina buƙatar shiga banɗaki” ta yi maganar ba tare da ta ba ta amsar tambayar ta ba. bayan ta cire mata ankwa ta nuna mata banɗakin. ɗaukar wayarta ta yi ta kira D.S.P bai ɗaga ba jim kaɗan sai ga shi ya shigo ya na riƙi da wasu takardu “ina marar lafiyar ta ke ne?” Ya yi tambayar da ɗan tsoro a kan fuskar shi “tana banɗaki”.

“Oh! Ai na ɗauka ko ta gudu ne”.

“Haba yallaɓai akwai tsaro a kanta ko ta yi yunƙurin yin hakan ai ba za ta iya ba”

“Hakan ne gaskiya, yanzu idan ta fito sai ku zo mu tafi wajan yi mata gwaji”

“Yallaɓai in dai gwaji ne akan maganar ta lafiya lau take yanzun nan ta mun magana shi ne ma na kira na faɗa ma sai ba ka ɗaga ba”.

“To AlhamdulilLah bari kawai na faɗa wa likita a bamu sallama dama na faɗa kissa ce kawai irin na mata ba wata matsala da ta samu” daidai lokacin Zainab ta fito “ki ba ta abinci ta ci yanzu zan kira Dr Hafiz ya ba mu sallama”. “To Yallaɓai” bayan fitar D.S.P ta zuba wa Zainab abinci a filet “ga shi maza ki ci”.

“Ba zan ci ba” ta faɗa tana mai zama bakin gado cikin taɓi baki ta ce. “Ke ki ka sani ko ki ci ko kar ki ci ba abin da zai hana ki koma gidan da ke ki ka zaɓa wa kan ki kafin hukunci ya hau kan ki. Kima godewa Allah za ki ƙara samun lokaci kafin hukunci ya hau kan ki idan har ki na da rabo sai ki yi ta ibada da neman gafara kafin a yanke maki hukunci idan ba ki da rabo sai ki sake yunƙurin kashe kan na kin zo a banza za ki koma a wofi”.

Zuba mata idanu Zainab ta yi sam ta kasa fahimtar in da zancen ya dusa, “daina kallona da idanun nan na ki masu kama da na mayu!” Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ƙamshin abincin ya fara damunta hakan yasa ta kai hannu ta ɗan ture filet ɗin tana tuttushe hanci nan take ta fara jin tashin zuciya
“Abincin nan wari yake don Allah ki taimake ni ki ɗauke mini shi”

Har ta buɗe baki ta yi mata masifa sai kuma ta fasa tuna wa da irin yadda wahalar laulayi ya ke. Ɗauke wa ta yi tana faɗin “Allah ya rufa ma ki asiri amma kin tona wa kan ki da a ce ba ki aikata wannan ɗanyen hukuncin ba da tuni kina gaban mijin ki yana tarairayar ki da wannan rabo mai albarka da ki ka samu, yanzu kinga za ki ƙare rayuwar ki a gidan yari sam ba ki yi wa kanki da Babyn ki adalci ba”
Sam ba fahimtar zancen take ba tashin zuciya take ji wanda ba ta taɓa ji ba da gudu ta faɗa banɗaki tun daga bakin ƙofar ta fara harsarwa kamar za ta a mayo hanjin cikinta yar sandar ta biyo ta tana mata sannu daidai lokacin Dr ya shigo tare da D.S.P fuskar Dr Hafiz na nuna wani irin yanayi wanda mutun ba zai iya fassarar ma’anar hakan kai tsaye ba ya ce. “Ban san me yasa ka ke so lallai sai an baku sallama ba ya kamata ka fahimci irin yanayin da take ciki”

“Kar ka damu da wannan tunda muna da asibiti na tabbatar da Dr Mansur zai kula da ita” rubuta takarda ya yi ya basu daidai sanda take fitowa daga banɗaki tana dafa bango sai mayar da numfashi take sama-sama, kallo ɗaya ya mata ya kawar da kan shi ya bar ɗakin da sauri.

Tun bayan da suka koma gidan yarin za ta iya cewa ta samu sassauci daga aikin wahalar da ake sata sai dai abu mafi girman wahala shi ne ba ta iya cin abinci da zarar taga abinci sai tashin zuciya ta fara harsarwa kenan, kullum sai dare ya yi zazzaɓi mai zafi ya rufe ta, idan gari ya waye zai sauka ya barta da ciwon kai gaba ɗaya ji take komai ba ya yi mata daɗi. Zaune take gefen wata bisshiya tasa kanta tsakankanin gwauwoyin ta Lantana ta ƙaraso wajan ta ta zauna tana faɗin “sannu Zainab ciwon kanne har yanzu ko?” Kanta kawai ta gyaɗa wa Lantana “dole ki dinga ciwon kai tunda ba kya cin abinci na sha faɗa ma ki damuwa ba ita ce mafita ba addu’a kawai za mu yi AZAL ce ta riga da ta faɗa mana sai dai kawai mu nemi tuba da rahamar Ubangiji”

“Ban san ta yadda zan hana kaina damuwa ba Lantana ina cikin tsananin ruɗani a hannuna ya mut… Fashe wa ta yi da kuka zuba mata idanu ta yi idanunta sun ciko da hawaye tabbas tana tausaya wa rayuwar su amma ya za su yi da ƙaddarar Ubangiji hukunci ne na Allah, sam ba su san da zuwan gandirobar ba sai ji suka yi an lafta masu bulala zafin dukan ne yasa ta zabura da sauri nan take mararta ta riƙi hannu tasa ta dafa marar tana rintsi idanunta wani irin azababbin ciwo take ji yana ratsata ta ko ina “dan an ce a daina sa ki aiki ba yana nufin wai ki samu waje ki zauna ki na huta wa ba, maza ki ɗauki tsintsiya ki shiga cikin masu shara.!” Cikin ƙarfin hali ta tafi ta fara sharar ji take kamar mararta za ta zazzago dan azabar ciwo sai dai ina ba ta da ‘yancin nuna hakan, dama tuni Lantana ta kama gabanta.

Hayaniya ce ta kace me cikin koton tun bayan da aka tabbatar wa da alƙali da jama’ar ciki Zainab na da juna biyu Hajiya Laila da matar Alhaji Umar su ka dinga masifa “wannan zancen iska ne har ta ya za a zo mana da zancen tana da juna biyu ma mu yarda bayan mun sani ta sani tun bayan da aka ɗaura auren ta da Alhaji ko hannunta bata taɓa bari ya riƙi ba!”

“Gane mun hanya dai Hafsat ya mai girma mai shari’a wannan cikin ba na ɗan’uwana ba ne ta faɗa da bakinta cikin waye dan ba za mu taɓa yadda ta kawo mana ɓara gurbi a cikin dangi ba wallahi ba za mu yarda da shege a cikin ‘ya’yan mu ba!” Ta kai duban ta ga Zainab da tun sanda ta ji zancen tana da juna biyu ta ji wani irin shokin dukan jijiyoyin jikin ta “ke uban waye ya yi ma ki ciki!?”

“Wannan wace irin banzan tambaya ce? Yarinya kowa dai ya san aure a ka ɗaura mata da ɗan’uwan ku ba a tare kuke wuni ko kwana ba bare har ku ce za ku sheganta ɗan halak, ko ku yi shedar ba abin da yake faruwa a tsakanin ta da mijinta tunda ba a gaban ku zai zo ya yi ba!” Maman Zainab ta yi maganar a fusace idanunta na zubar da hawaye. “Kar ku wani raina mana hankali wallahi tun dare bai ma ku ba sa ‘yar ki a gaba ta faɗa ma ki a ina ta yi cikin nan dan ba za mu taɓa karɓar abin da ba jinin mu ba!” Alƙali ya dinga dukan tebur ɗin gaban sa yana tsawatar wa “ya isa kowa ya natsu a yi shiru ya isa haka!!!” Koma wa suka yi suka zauna suna hararar juna jama’ar koton a ka dinga kallon kallo ana magana ƙasa-ƙasa da ƙyar alƙali ya tsawata a ka yi shiru lauyan da ya ke ɓangaren masu ƙara ya tashi tsaye yana faɗin “ya mai girma mai shari’a ina so koto ta bani dama na yi wa wacce ake ƙara tambayoyi”

“Kuto ta ba ka dama”. “Na gode ya mai Shari’a” ya yi maganar yana ɗan sunkuyar da kai kafin daga bisani ya ƙarasa gaban Zainab “Malama Zainab shin ta ya a ka haihu a ragaya? Juna biyu ya bayyana bayan kowa ya tabbatar da cewar babu abin da ya taɓa shiga tsakan… “Objection ya mai Shari’a ya kamata a tsawata wa Barista Sani domin wannan tambayar ta saɓawa Shari’a mace da mijinta waye ya san sirrin su wannan tambayar tamkar tozarci ne da son kunya ta wacce ake zargi” lauyan gwamnati da yake kare wacce ake ƙara ya yi maganar idanunsa a kan Barista Sani.

“Barista Haidar tambayar Barista Sani tana akan daidai” koma wa ya yi ya zauna fuska babu annuri murmushi Barista Sani ya yi “na gode ya mai Shari’a” kai duban shi ya yi ga Zainab da kanta ya ke kallon ƙasa yana faɗin “za mu so ki fitar da mu duhu shin wannan juna biyun da ya ke jikin ki na waye?
Faɗar gaskiyar ki shi ne zai taimaka wajen sauƙaƙa wa shari’ar nan ta mu”.

“Ta ya za ta faɗi gaskiya tun da babu tsoron Allah a ranta, wallahi ba za mu taɓa yarda mu karɓi shege a matsayin jinin Umaru ba!” Hajiya Laila ta yi maganar tana mai kafe Zainab da idanu, alƙali ya duka tebur hakan yasa ta yi shiru tana mayar da numfashi. “Kuto na sauraren ki mene ne gaskiyar abin da da ake faɗa shin kafin ki kashe Alhaji Umar wani abu na auratayya ya taɓa shiga tsakanin ku?” Barista Sani ya yi tambayar idanunsa a kanta.

Barista Haidar ya miƙe tsaye “Objection ya mai shari’a, lauyan wanda yake ƙara yana dora laifin kisa ga wadda ake zargi, alhalin har yanzu zargi ake ba a tabbatar ba” “Barista Sani a kiyaye”.

“Na gode ya mai Shari’a” juyowa ya yi wajan Zainab wacce ta riƙi kanta ji take ɗakin na jujjuya mata luw! Ta faɗi tim! Mama tasa ihu Zainab!!” Duk da tare ta da ake hakan ta turo su ta ƙarasa gaban Zainab tana girgiza ta shiru babu inda yake motsi a jikinta “Innalillahi wa Inna ilahi raji’un! Zainab don Allah kar ki tafi ki barni na shiga uku wayyo Allah na Iya kun cuce ni ga in da kuke so ku kaita sai kusa ruwa ƙasa ku sha burin ku ya cika!!” Jama’ar Kuto a ka yi cincirindo a kan ta.

<< Su Ne Sila 10

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×