Gandurubal sam bata san abinda ke faruwa ba baccinta take ta sharƙa, iya azaba Zainab tana jinsa har bata san taya zata iya kwatantawa ba, idanunta sun firfito ba a ganin baƙin ƙwayar idanunta, numfashinta ya tsaya chak sai lilon da ƙafafunta suke yi, buɗe ƙofa aka yi ya shigo kamar wanda aka hankaɗo, wayam babu kowa akan gadon sai gandurubal da yaga tana bacci, ‘ko tana banɗaki ne’? Yayi tambayar a zuciyarsa juyawa ya yi zai fita ya ci karo da kujera ƙiris ya rage ya faɗi ji yayi wani abun ya taɓa masa kai da sauri ya kai duban shi sama “Innalillahi wa inna Ilaihi raji’un”! Ya faɗa da ƙarfi tare da riƙo ƙafafunta ƙarajin shi ne ya tashi Gandroba ta tashi a firgice tana tambayar lafi… Ganin abinda ya ke faruwa ne ya sa sauran maganar ta maƙale, yana ɗaga ƙafafunshi ya miƙa hannayen shi ya kwanci ƙullen ta faɗo jikin shi kwantar da ita yayi akan gado sam babu alamar rai a tare da ita sai salati Gandrobal take Dr Mansur haushinta ya cika shi ji yake kamar ya kama ta da dukan tsiya,”amma anyi yarinyar banza In banda taɓewa bayan nauyin kisan mutum da yake kanki kuma sai ki sake jefa kanki a wani masifar shikenan idan har kin mutu anyi mutuwar zomo anzo abanza an koma a banza?”
“Ya isa haka! Ko me ya faru ai laifin ki ne miye amfaninki kina kwance kina baccin asara har hakan ta faru duk baki sani ba, mtsw!!” Yayi maganar a fusace tare da barin ɗakin da sauri, shiru ta yi tana muzurai, jim kaɗan ya dawo tare da Nurse ya aunata ya taɓa jijiyoyin hannunta ya rataya abin awon a wuyan shi yana mai yin ajiyar zuciya gaba ɗaya hankalin shi a tashe yake, Nurse ta ce; “anya likita tana a raye?”
“Mawuyacin abu ne a ce tana da rai, amma bari mu ɗauketa zuwa babban asibiti” haka ya ɗauke ta a kafaɗar shi ya fita da ita suna zuwa wajan motar shi Nurse ɗin ta buɗe bayan motar ya kwantar da ita, Gandrobal zata shiga yana harararta ya ce; “dan Allah koma wajan aikin ki dan banga amfanin da za ki mana ba” a fusace ta juya ta bar wajan ba tare da ta ce komai ba dan iya haushi ta ji shi ta nufi ciki sai dai a ƙasan zuciyarta a tsorace take kar ace sakacinta ne wanda taga alamar ko likitan abinda ya ke gani kenan. Tare da ya bar gidan yarin ya nufi babban asibitin da yake cikin gari, a hanya ya kira shugaban gidan yarin ya masa bayani, shugaban gidan yarin ya ce za su biyo su asibitin.
Waiwaye
Kyakyawar matashiya ce sanye da kayan makaranta tana tafe a hanya ita kaɗai tana juye da ‘yan tsalle-tsallenta, yayinda jefi-jefi wasu gungu-gungu na ‘yan makaranta suke wucewa da mabanbanta uniform, “Zainab! Zainab!!” Tsayawa ta yi tana waigawa bayanta, Raliya ta ƙaraso da gudu cikin faɗa Zainab ta ce “wai dama ke ce ki ke min kiran mafarauta” tana harararta ta ce “ai dole ki faɗi hakan ni ina can ina zaman jiran ki ashe ke har kinyi tafiyar ki har sai da Maijidda Mas’ud ta ce min taga fitar ki sannan na fito.”
“To ni nasan kina jirana ne? kawai muna fitowa bangan ki ba na za ta kin tafi”
“Iskancin ki ne dai ya tashi amma ai kin san a tare mu ke zuwa muke komawa babu ta yanda za’ayi na tafi na barki, kawai dai yau ‘yan baƙin halinne a kanki.”
“To Sarkin ‘yan mita yi Haƙuri” suna tafe suna fira kasancewar babu nisa tsakanin makaranta da unguwar tasu basu jima ba suka isa gida kowa ya shige gida.
Ta samu ƙanneta Na’ila da Shahid suna cin abinci kusan a tare suka mata sannu da zuwa Kai kawai ta iya gyaɗa musu ta shige ɗakin Mama, tana shiga ta jefar da jaka da takalmi a tsakiyar ɗakin, cire Hijab ta yi ta jefar, Mama da ta fito banɗaki tana shigowa ɗakin ta ci karo da kayan ta gyaɗa kai cikin takaici ta ce; “naga sanda za ki yi hankali Zainab abinda kike ko ƙannenki basa yin hakan, dubi daga zuwanki kin fara hargitsamin ɗaki.”
Magana take cikin shagwaɓa “oh Mama ni komai nayi banyi daidai ba dawowata fa kenan.”
“Tunda dawowar ki kenan bari kiyi min jifa da kaya a tsakiyar ɗaki, idan har ba kya son faɗa sai ki natsu ki daina yin abinda kike”
“Shikenan Mama kiyi haƙuri yanzu zan gyara”
“Da dai yafi maki” Mama ta faɗa tana mai ɗaukar darduma zata fara sallah “Mama anyi abinci.”
“A’a ba’a yi ba”
“To amma naga kuma su Shahid suna cin abinci.”
“Da kinga hakan kuma kike min tambayar rainin wayo” murmushi Zainab tayi wato baƙa ce aka danƙara mata,
“Allah ya bar mana ke Mamanmu.”
“Ni dai jeki dan Allah ki barni na yi sallah ta cikin natsuwa” da sauri Zainab ta fita tana dariya Mama na gyaɗa kai “Allah ya shirya min ke Zainab yarinya in har tana gida ba za ta barka ka sarara ba.”
Zainab ta kasance ‘yar asalin jahar Kaduna ce, iyaye da kakannin a ƙauyen Saulawa Ikara. Suna zaune a Kafancan da ke jahar Kaduna ‘Ya ce ga Malam Umaru da ya kasance Manomi kuma mai sana’ar kayan Gwari a lokacin Gwari, Mahaifiyarta mai suna Maryam ta kasance mata ɗaya a gidan mahaifin Zainab, su ɗin asalin Fulani ne, Zainab ‘yar shekara 18 ita ce ‘yarsu ta biyu tana da Yaya Muhsin, wanda a yanzu ya ke karatu a A.B.U Zariya sai ƙannenta uku, mace ɗaya maza biyu, iyayenta na matuƙar sonta kowa ji yake da ita a cikin dangi kasancewar ta mai son mutane da son zumunci, ta kasance kyakyawa kamar Babanta sai dai tafi Babanta haske domin hasken Mamanta ta ɗauko, tana da ƙwaƙwalwa da anyi karatu nan take ta ɗauka, ko a aji ita take yin na ɗaya, shiyasa Malamman makaranta suke ji da ita, ƙawarta ɗaya Raliya wacce suke maƙotan juna ne, Rayuwa take cike da farin ciki duk da iyayenta masu ƙaramin ƙarfi ne amma hakan baisa sun rasa ci ko sitira ba daidai gwargwadon ƙarfinsa, makarantar gwamnati suke yi daga ita har ƙannenta, shekara ɗaya kenan da yin saukar ƙur’aninta, tana shekarar ƙarshe a sakandare.
Zainab tana da wani hali da ko iyayenta suna ƙoƙarin ganin ta daina saurin fushi idan har tayi fushi komai zata iya yi komai zata iya furtawa sai daga baya idan tayi abu yazo ya dameta koyaushe cikin faɗa da nasiha da Mama take mata kenan, sai ita ɗin tana da kirki musamman ga wanda ya iya zama da ita, ga ta mai yawan kyauta sam abun hannunta baya tsone mata idanu. Babban burin Zainab ta zama likita, ta ganta da kayan likita tana duba marasa lafiya da yi masu allura da yin tiyata wannan shi ne mafarkinta, hakan yasa ko da wasa bata kula samari duk kuwa da yanda suke tururuwan zuwa wajanta amma sam bata ba su fuska, tun Mama na mata faɗa har ta gaji ta kawo na gani ta zuba mata.
“Zainab Yaya Sanusi yana ta damuna da zancen ki ya matsa a kan yana so ya zo wajan ki” mayar da lomar hannunta ta yi a cikin flet ɗin tana faɗin “wallahi karma ki soma kina ganin kwana biyu na samu Mama ta daina min faɗan rashin kula maza ki janyo yazo ta sani gaba da faɗa.”
“Mtw! Kina da matsala Zainab, shi fa ba cewa yayi ba zai barki ki yi karatu ba, wallahi ya ce shi in dai karatu ne ko bayan auren ku sai kince kin gaji.”
“Gidan haya ce ni ƙaruwar matsala, wallahi Raliya daga ke har shi zan iya shuka maku rashin mutunci matuƙar kika sake zuwa min da zancen sa na wofi!” Shiru Raliya tayi ta cigaba da cin abincinta domin tasan halin Zainab yanzu ta biye ta har maƙota sai sun ji su, bayan tafiyar Raliya Mama tasa Zainab gaba da faɗa “wallahi Zainab ki iya riƙe fushin ki, saboda Allah miye laifin mai sonka, kawai daga an aikota sai ki hau kanta da masifa, kina jin zata ji daɗi ne ki ƙi ɗan’uwanta?”
“To ni Mama ya zanyi ne tana ta damuna da maganar ne kuma ni ba son shi nake ba, shiyasa na mata haka” zama Mama ta yi a kan kujera kafin ta ce; “ai ko ba ka son mutum ba hakan ake ba sai kibi da ita ta siyasa a rabu lafiya, amma yarinyar nan koyaushe tana tare dake tana binki sau da ƙafa ke kuma kin dinga yi mata masifa kamar kin ajiyeta ne.”
“Ki yi haƙuri Mama na daina”
“Ai fa kullum hakan kike faɗa Kuma ba dainawan za ki yi ba, ni tashi kije ki karɓo min saƙo wajan Umma Habiba” tashi ta yi tana faɗin to, bayan ta shirya zata tafi Mama ta dubeta “karfa kije ki daɗe ki dawo ki ɗora girkin dare.”
“To.” Na’ila ‘Yar shekara goma da shigowarta kenan ta ce. “Yaya Zainab na zo na raka ki?” tana harararta ta ce “na ce maki ina neman ɗan rakiya?” Komawa tayi kusa da Mama ta zauna “to mene ne idan har ta raka ki ɗin.”
“Mama yarinyar nan ta fiye son yawo wallahi, kuma tare da Raliya zamu je”
“A sauka lafiya, ki gaishe da Umma Habiban, Na’ila barta gobe idan zan tafi biki tare za mu je.”
A ƙofar gida ta haɗu da Babanta da yake tsaye da wani dattijon suna magana, cikin girmamawa ta gaishe su, Dattijon ya amsa da fara’a yana faɗin “kar dai Mai tagwayen suna ce ta girma haka?” Cikin murmushi Baba ya ce; “ita ce fa Baba, ai ka jima ba ka zo ba.”
“Wallahi kuwa kai kuma duk sanda za ka zo ba za ka zo mana da su ba kaga gabaɗaya sai a manta juna, tunda yanzu in har zata haɗu da ‘yan’uwanta duk basu san juna ba zumunci ya yi rauni.”
“Gaskiya ne Baba Insha-Allah suna samun hutu zan kawo su suyi kwana biyu” cikin farin ciki ya ce; “hakan ya yi kyau ai shi zumunci ɗan bibiya ne idan har ba a bibiya sai kaga ya yi rauni.”
“Gaskiya ne Baba, ke Zainab Baba Mashkur ne na Saulawa” da fara’a ta ce; “lah Baba an zo lafiya, ya Gwaggo Hari.”
“Tana lafiya ita kaɗai kika sani ko ita da take yawan zuwa maku?” murmushi kawai tayi, ta ma su sallama bayan ta faɗawa Baban aikinta Mama ta yi, ta tafi wajan aikan Mama, su kuma suka ƙarasa shiga cikin gidan suna firan yaushe gamo. Baba Mashkur ƙanen Mahaifin Baban Zainab ne shi kaɗai ne ya rage a cikin iyayensa maza, sai gwaggo Hari sun kasance masu son zumunci sai dai kuma suna da zafi da kafiya a kan duk abinda suka sa a gaba kusan dai Malam Umaru halinsu ne ya ɗauko mutum ne mai kafiya.
Tun a lokacin Babanta yasa a ranshi suna samun hutu zai kai su wajan dangin shi domin wasu ne suke cikin Kafancan da yawan su kuma suna Saulawa.
Suna samun hutu Baba ya ce su shirya ya kai su wajan danginsa har ga Allah Zainab bata so tafiyar ba dan ita kam bata ƙaunar abinda zai rabata da Mamanta koda da kwana ɗaya bare kuma har suyi sati ɗaya, sati ɗayanma dan ita ba jimawa za ta yi ba za su koma makaranta za su fara jarabawa, saura kwana ɗaya tafiyar da dare ta samu Baba ɗakin shi yana zaune yana saurarin labarai Mama na zaune gefen shi tana dama masa fura zama tayi gefen Babanta tanƙwashe ƙafafunta da Murmushi a fuskarsa ya ce; “Zainabu Abu mai tagwayen suna da gani akwai magana a bakin-nan naki” dariya tayi marar sauti kafin ta ce; “Baba gobe da Yaushe zamu tafi?”
“Ƙarfe goma zuwa sha ɗaya Insha-Allah za mu tafi, ko akwai shirin da ba ki ƙarasa ba ne?” Ta kai dubanta wajan Mama, “menene kuma kike kallona?” Ta yiwa Mama maganar ido “wai menene da alama kin san da maganar a faɗa min na ji.”
“A’a Malam ba ruwana shirme ne kawai irin na Zainab.”
“Faɗa min Zainabu me kike so?”
“Uhm dama Baba cewa nayi muyi sammako yanda zamu iya dawowa gobe ba sai muyi kwanakki ba” ido ya zuba mata kafin ya ce; “wajan dangin nawa ne ba kya son zama?”
Da sauri ta gyaɗa kai tana faɗin “A’a Baba Ina so sosai amma Baba har sati, to shikenan tare da Mama zamu tafi ko?” Dariya yayi kafin daga bisani ya ce; “na gane ba kya so ki tafi ki bar Mamanki ko?” Shiru ta yi “banda abunki Zainabu ke fa mace ce da watarana za ki je gidan wani a wani wajan za ki yi rayuwa ai gara ki fara sabawa da barin Mamanki gida.”
“Tab ai ni Baba shiyasa bana kula kowa, ba wani aure da zanyi muna nan tare da Mamana” tayi maganar tare da rungume Mama, Mama da tagama dama fura ta dube su tana faɗin “kai Zainab Sarkin shirme ni kam ai ba zan so ki ƙi aure ba ina so naga na goya ‘ya’yanki ko ba kya so?” Rufe idanunta ta yi tare da barin ɗakin da gudu Dukansu sukayi dariya, “wauta kamar ‘yar fari” cewar Mama, Baba ya ce; “ai kece kika sagartata inaga mayar da ita Saulawa zanyi wajan su Gwaggo Hari kinga daga nan sai ta fara koyon rayuwa ba tare damu ba” cikin fito da idanu ta ce; “dan Allah ka rufa mana asiri ai nima sai na tattara mu kuma tare.”
“Kin gani ko ai koma menene har da ke, kema ɗin ba son ta maki nisa kike ba” ta yi dariya tana faɗin “ga furan angama damawa.”
Washe-gari suka kama hanya har Raliya matsawa iyayenta tayi aka barta suka tafi tare, tabar garinsu cike da kewar Mama tare da tunanin irin rayuwar da zata yi da wasu daban da bata saba da su ba duk da ta na tare da Raliya.
Da kyau sosai