Skip to content
Part 13 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Tamannah Bhatia

Ashe da rai nake son ki jaruma ba da zuciyata ba

Komai ruwa da iska akan ki ba za na daina ƙauna ba

Idan na samu damar samun ki ba za na kula kowa ba

Ni banga kamar Tamannah ba

Balle na waiwaya baya.

In dai akan ki ne za na jure wahalar zuwa garin Mumbai

Daga an taɓa ki a jira zuwana domin akanki zan iya komai

Jimirin jiran ki na yi domin ki zo na kalle ki gimbiyar kyawu

Asali na zuciyata ke ce da kin kira ni na amsa.

Ita zuma a baki daɗi gareta zumar son ki yanzu na lasa

In dai akanki ne na yi nisa banji kira bare in amsa

Tilas ganinmu tilas barinmu domin a son ki na yi nisa

In dai akan ki ne na ko shirya har in ba da rai fansa.

Tsarin zubinki dai-dai ne

Ya kama zuciyata ne

Komai naki dai-dai ne

Ya dace da raina ne

Samun irinki ɗai-ɗai ne

Tamkar dubun mutane ne.

Ina jin kamar mafarki ne

Na san sonki ai mataki ne.

Ni banda damuwa in har zan buɗe ‘yan idanuna

In ganki gaki dab da ni ya Sarauniya Tamannah

Yau za na yo amo tun da na gane kina fa da masoya

Don yanzu na zamo a gabansu duka masoya.

Na ƙwalla shela don sanar da iya maƙiya kalamaina

Dukka a kudanci ku sani ba ya Tamannah

Idan babu ke ina ne jama’a za su samu gun ɓuya?

Kowa da nasa amma ke ce abar so ga kowa.

Yau gani a ruwa Tamannah zo ki ceci ƙalbina

Komai da mafita Tamannah kada ki yi mini bankwana

Ina ji ina gani yadda nake sonki ya fi ƙarfina

Na san a duniya ke ce kawai muradina.

Soyayya rayuwa wani sa’in sai ta zam wutar ƙauna

Ke ce kaɗai na bawa sirrin da ke a ƙalbina

Kallonki na sakani nishaɗi in ji ni kamar wani sarki

Kuma kyan idanunki na kama da a mafarki.

Samari ku yi haƙuri domin Tamannah tawa ce ni ɗai

Mata ku yi haƙuri zuciyata ta Tamannah ce ita ɗai

Soyayyarmu na da tsada ne

Ta zaga ko’ina ma ne

Ta mamaye duniya ma ne

Tamannah jaruma ta ce..

A big kudos to the most popular singer of present time in person of Hamisu Breaker.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 12Ba’indiya 14 >>

2 thoughts on “Ba’indiya 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×