Skip to content
Part 27 of 30 in the Series Tambaya by Haiman Raees

Waye?

01.

Waye zan fara da shi, in ba Allah ba 

Waye zan ƙare da shi, in ba Allah ba

Wa zan yi salati gare shi, in ba Manzo ba

Waye zan zo in yi barka, in ba manzo ba

Waye? Waye? Waye?

02.

Waye ne yayi duniya, ya ba kowa kunnen jin magana?

Waye yayi lahira, ya ba kowa damar ya sani?

Waye ne ya yi shiriya, ya ba kowa damar ya tuna?

Waye ne yake kira, yana faɗa domin a sani?

Waye? Waye? Waye?

03.

Wa ke tsara ƙaddara, idan ya so ka salwanta?

Wa ke canza ƙaddara, idan ya so ka rabauta?

Wa ke bada dukiya, idan ya so ka same ta?

Wa ke ƙwace dukiya, idan ya so ka ƙasƙanta?

Waye? Waye? Waye?

04.

Waye ko ba ka son sa, yan sonka da halinka?

Waye ko ba ka son kanka, yana sonka da danginka?

Waye ko ba ka roƙa ba, yana baka ya ƙara ma?

Waye ko ka roƙa ma, idan ya so ya hana ma?

Waye? Waye? Waye?

05.

Waye in ya ba ka, kana so dole ka gode mai?

Waye in ya hanaka, baka so dole ka gode mai?

Waye in har ka tambaya, to zai ba ka duk da halinka?

Waye kuma ko za ka mutu, ba ya ba ka ko yana da shi?

Waye? Waye? Waye?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Tambaya 26Tambaya 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×