Skip to content
Part 10 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Farida ta daukewa kowa wuta a gidan Yaya dauda . Bata tankawa kowa Bata Gaisa kowa ko da Yara kuwa duk nacin su da son shiga inda take in ma sun shiga saboda zaton ko Zasu samu Saddam da Hanan Amma Bata kula su Bata tanka su .

Tun Anty lubna Bata kula ba har dai ta Gane fushi Farida take da su .

A yau da take cikin kwanaki goma Sha Biyu Anty lubna ta aike Mata Siyama da abun Karin ta tunda jiya akayi ta Kiran ta ta fito ta karya Amma Taki fitowa shiyasa yau Anty lubna ta tura Siyama da abun Karin ta Kai mata Kuma duk gaishe ta da Siyaman take Bata Amsa ba.

Siyama ta fito tana cewa Anty lubna.

“Mama ko anty Bata da lafiya ne sai Gaishe ta nake Bata Amsa ba. Yaya dauda Yana Zaune Yana Jin su Bai tanka su ba ya ci gaba da kalacin shi.

Anty lubna ta Dubi Siyama tayi Shiru kafin tace

“Babu Mamaki Siyama wata Kil Bata da lafiya ne bari naje na duba ta don yanzu yanzu sai Allah Kuma gashi ta zabi zaman D’aka bare na iya Sanin ko tana da matsala.

Ta Mike zata nufi D’akin Farida Yaya dauda ya dakatar da ita.

“Kyale yarinyar Nan lubna lafiyar ta Lau iskanci ne Wallahi Bata san ni bane har yanzu.

“A a Daddy yanzu yanzu fa sai Allah bari na duba ta na lallaba ta ai da kuruciya a tare da ita sai ana nuna Mata.

Ta wuce Zuwa D’akin Farida tana sallama da jiran a amsa har ma abata izinin shiga Amma Taji Shiru. Ta sake rangada sallama Amma aka Kuma baiwa banza AJIYAR ta inda zuciyar ta ta ke Raya Mata Lallai Farida Bata da lafiya sallama kusan biyar Amma ba a Amsa ko Daya ba.

Sai kawai ta danna kanta cikin d’akin Bata tsaya jiran Amsawa ba inda Tasha Mamaki Domin kuwa zaune ta hango Farida tana latsa wayar da Sameer ya bar Mata tana chat din ta Amma ko ta dago Kai ta dubi Anty lubna Bata Yi ba tamkar ma Bata San da tsirar lubnar ba.

“Haba Farida yanzu Ashe da kina jina Ina ta sallama Amma kikayi shuru saboda Allah?

Nan ma Bata ko dago daga Abinda takeyi ba kanta a kan wayar ta ci gaba da Abinda takeyi.

Anty lubna tayi murmushi tana Fadin, “Farida kina bani mamaki Wallahi idan Wani ne ya fada min Cewar Zakiyi haka zan karyata shi da sauri Amma yanzu Kam kin gama shayar Dani Ruwan mamaki Amma tunda lafiya Lau kike alhamdulillah.

Ta Dan saurara ko Faridar zata ce wani Abu Amma sai taji ta shiru Bata ma dago kanta ba bare ta tanka Mata ta bawa banza AJIYAR ta Dole Anty lubna ta koma tana Mamaki.

Yaya dauda ya Dube ta Yana Fadin, “Yaya kika same ta ? Tayi murmushi tana Fadin.

“Wallahi lafiyar ta kalau daddy gaskiyar ka Farida ai tayi Nisa baiwar Allah Dole a tausaya Mata . Don Allah don ANNABI daddy ka Hak’ura da Abinda kake Shirin Yi ka mayar da yarinyar Nan ga mijin ta tunda haka take so Wallahi tana shirya Wani Abu ne Allah ma ya San hakkin ta kake kokarin kwatar Mata Amma tana Rufe idon ta tana Rashin kirkin ta don Allah kayi hak’uri ka aje naka Ra ayin kabi nata ni nake Rokon ka wannan Alfarmar ba don na Isa ba sai don girman ALLAH bana Jin Dadi idan naga tana Shirin nuna maka Kai ba komai kake a idon ta ba.

Ya Ruko Hannun lubna Yana rumtsewa a Nashi ya Kalli idon ta Yana Fadin.

“Kin Isa lubna Kuma na karbi Rokon ki Amma ki sani sai ta cike sati Biyun Da na debar mata Kuma zan Saka Musu ido in barta ita da Sameer tunda ta nuna min shi ne yafi ni a wurin ta tunda har nayi lalacewar da Farida ke fadar maganganun da ta fada na kaini Kara kotu to in Sha Allah zanyi Mata ADDU A Amma shiga lamarin ta zan barshi.

Lubna ta Rungume shi tana fadin
“Nagode da ka fahimce ni derling. Wai kasan tana zaune dafa an nake ta sallama Amma ko tada Kai batayi ta kalle ni ba? Duk maganar da nayi ko tari batayi ba. Kuma tun Shekaran jiya ta Rufe Yi maka magana Ashe Nima zan biyo Sahu Kuma kaga har gaishe ta Siyama tayi Nan ma Bata Amsa ba.

“Ki kyale ta gata ga Sameer Nan Muna Nan zakiji Abinda zai Kuma Yi Mata Haj ce kawai zata ce nayi nayi Amma ko a Gaba na Sameer zai Dake ta Wallahi zan dauke kaina nayi kamar ban Gani ba. Kuma in Sha Allah jibi jibin Nan zan mayar da ita da kaina Amma da naso Naga irin taurarin kanta.

Suna cikin maganar ne wayar shi ta dauki tsuwwa ya jawo ta yaga sunan Haj ya kashe ya Kira ta Suka gaisa tana tambayar.

“Dauda me ya faru ne ka baiwa Sameer su Saddam? Yazo mini yace kace ya kawo maka takardar sakin Auren Farida Anya kuwa ba zaka ga tashin hankalin yarinyar Nan ba? Bata da Hankali fa akan wannan mijin nata tamkar Wanda ya asurce ta.

“Haj na Gaji da zaluncin Sameer ne ga Farida shiyasa kawai nace a Hak’ura ya tafi Kuma Farida ma makaranta zan mayar da ita.

“Kar kayi haka tunda yazo wuri na ai sai dai kayi Hak’uri Kuma sai dai kaja mishi kunne Amma ni kaina zargin Nan Yana damu na dauda shine kadai matsala ta da Sameer Wallahi gidan shi Babu Rashin komai Amma Kuma wannan matsalar ta Isa tasa mace Mai zuciya Hak’ura da Auren shi kome Kuwa Ake Samu a cikin Auren.

“To Haj duk yadda kika ce haka za ayi Amma ni da gaske nake Raba Auren Nan Zanyi.

“A a kar kayi haka ai ko don yaran su tunda nace mishi sati Biyun da ka Diba Yana cika zata komo don Haka jibi ka maido ta don na tabbata yadda take din Nan idan kace haka kake nufi Babu Abinda ba zata iya ba dauda ai Kai dai ka kalli Mata a yau akan mazaje Babu Abinda ba zasu iya ba Kuma abin haushin ma sai ka ga mazajen Nasu haushi ya kashe ka.

“Lallai Haj kin San kayan ki.

“Fiye da sanin da nayi yinwar ciki na kuwa wata Kil har da wannan Damar da ya samu yasa take ganin wulakanci Amma ai ita ta jiyo Nima Allah ya sani na fada Mata tun ba yau ba Amma na Gane ba zata Gane ba kaima Rufawa kanka Asiri ta watso ta gidan ta don in ka bari aka wuce wannan takin zaka bani Labarin Abinda zai biyo baya.

“Shikenan Haj in Sha Allah zuwa jibin zan maido ta.

Sukayi sallama ya ajiye wayar Yana fadawa lubna yadda sukayi da Haj.

“Gara da ka ajiye naka Ra ayin mu bita da ADDU A Allah ya sauwake irin haka a Gaba.

Farida ta biyo bayan Anty lubna da wata matsiyaciyar harara tana Fadin.

“Sai kace mayunwaciya ba a da abun bani sai abinci an ishe ni da Yan Yan Yan . Mtsss taja tsaki tana fadin.

“Duk zaku zo ku kwashe tsiyar ku ne don ni ko na jiya da Dare ban Bude ba ma bare na tab’a haka ma wannan da kuka kawo ban ko Bude shi kuzo ku kwashe tsiyar ku.

Da Rana kuwa sai ga Fahad ya Kuma kawo Mata Abinci tayi maza ta tsayar da shi tana Fadin.

“Fahad Yaya dauda Yana Nan? Yaron yace mata Eh Yana Nan.

“Yana Nan Yana cin Abincin ne? Ya sake amsa Mata da Eh.

Yauwa kwashe wadan Nan kwanukan duk har da Wanda ka kawo yanzu mayar kace a Daina kawo min Abinci Bana so !

Yaron ya Hado kwanukan UKU rigis ga na jiya da Dare ga na safe sai kuma na yanzu da ya kawo.

Anty lubna ta Dubu Fahad din tana Jin Abunda yake fad’a Mata sakon Farida na kar a Kuma kawo Mata Abinci Bata so.

Ta juyo ta dubi dauda Wanda yayi murmushi Yana Fadin.

“To ki Daina aika Mata tunda Bata so?

“To ya za ayi Mai Rai yace ba zai ci Abinci ba saboda Allah? Ni Kam in ma Anji haushi na Kai ka janyo mini Daddy.

“To jeki kiyi mata dura tunda yarinyar goye ce.

Anty lubna ta Soma Bude kwanonin tana ganin Babu wanda ta buda daga na jiyan har na yau da safe.

Ta dauki na Ranar ta nufi D’akin Farida inda ta aje Mata kwanon tana Fadin.

“Nima laifin daudan ya shafe ni ne Farida? To kiyi Hak’uri kici Abincin Nan ta Yaya Mai Rai zaice ba zai ci Abinci ba?

“Ai ! Dama ana son Rayuwar tawa ne? Anty lubna Baki ga na Daina Yi muku magana ne bane wai ?

Wallahi ku duka haushin kowa nake ji a gidan Nan don Allah ku fita a Rayuwa ta tunda Kun nuna min ku su waye a wuri na to Abincin wofi kuke da shi da zaku bani? Ko kuwa na kawo Muku k’arar miji na baya bani Abinci? To Wallahi da gaske nake bana son Abincin ku kowa ya tsaya a matsayin sa Kuma Wallahi tallahi jibi jibin Nan ko Yaya dauda ya yarda ko Bai yarda ba sai na bar Gidan Nan sai dai ya dauki Raina tunda nayi mishi biyayya Bai San nayi Nima bani da m Kuma ban San na cikin shago ba.

Anty lubna ta kame Baki cike da Mamaki kafin tace.

“Wai da gaske kike HAUSHIn mu kike ji ? Amma kuwa da kin bani mamaki idan kika ce haka shiyasa kika ki amsa gaisuwar Siyama da Fahad? To ki sani su din Dolen ki ne Kuma kiyi saurin gyara kuskuren ki don yaro Yana Rik’e Abinda akayi mishi ne ke kina iya mantawa Amma su ba zasu manta ki ba Kinga kin Fadi idan suka Rike ki. Ni Kam dauda yaja mini na sani Amma su Bai kamata kiga laifin su ba yadda suke haba haba da ke ace kinyi musu haka don Allah ame kike kuwa a wurin su?

Jikin ta yayi sak ta Mike ta wuce Anty lubna ta leka Bata ga su Siyama ba sai ta fice inda taga Yaya dauda Yana tahowa Amma ko da wai batayi nufin kauce mishi ba sai shine ya kauce ya Bata hanya ta wuce yayi tsaye Yana kallon ta har ta karya kwana inda ta samu Fahad da Siyama ta kama Hannun su tana fadin.

“Ku taho Ya’ya na kuji na Baku waya ta kuyi Wani irin game.

Ai kuwa suka Soma tsalle Suka wuce tare Anty lubna da Yaya dauda suka bita da kallo

“Tamkar Mai aljannu?

“Ba Wani aljanu sai iskanci, Cewar Yaya dauda

Can Yaran suka wuni inda Anty lubna ta Gane ta dauki shawarar kuskuren da ta gysra mata ne akan yaran. Amma fa abinci yadda Ake Kai shi haka Ake dauko shi Bata ko budawa inda Anty lubna ke mamakin taurin Kai irin na Farida. Amma sai tayi Mata ADDU A don Babu abinda take bukata irin ADDU A .

Saura kwana Guda ta cike sati Biyu Yaya dauda ya hada ta da Daya Daga cikin hadiman gidan Wanda ya kaita kasuwa yace ta siyo Abinda Zatayi tsaraba.

Suka tafi tare da Siyama suka jido kayan tsarabar inda take ta cin magani wai an ji tsoron wutar da ta so tayarwa . Ta Kuma San Anty lubna ce ta fada mishi Abinda tace shiyasa ya yarda da komawar ta gidan.

Washe gari tayiwa Anty lubna sallama Yaya dauda ya dauko ta a mota tun daga Kaduna har katsina.

Ya zube a Gaban Haj Yana gaishe ta tana tambayar Yara yace duk suna lafiya.

“Ai da ka zarce da ita can gidan Sameer din ka hada su kaja musu kunnuwa.

“Ai Haj na Zare Hannu na Daga Al Amarin yarinyar Nan. Babu irin Rashin mutuncin da Bata Yi min saboda kawai Ina son mijin ta ya Gane tana da gata Amma Ashe har nayi lalacewar da Farida zata ce zata kaini kotu in na kashe Mata Aure. To dukkan Abinda Sameer yaga dama yayi Mata Haj iyaka ta da su ADDU A Amma wulakanci kala kala Banda lubna tana da Hak’uri da anyi Wani Abu to Amma Haj ba zan iya tsallake Abinda kika ce ba sai nayi Mata fatan Alheri Allah ta ala ya tsare faruwar Wani Abu a Gaba.

Haj ta Rik’e Baki tana Fadin.

“Yanzu dauda har ka iya kyale ta baka daka Yar banza ta fada Maka wannan maganar?

“Dole nake kyale ta Haj tunda na San Akwai Ranar da zata Gane kuskuren ta . Kuma in dai Sameer ne yadda ya tsinke iguyoyin Auren ta Biyu Daya bayan Daya to dayar ma kuwa zai tsinke ta matukar Bai daidai ta zuciyar shi ba ni Kuma nayi Mata uzurin kuruciya. Har fa yajin cin Abinci tayi Haj kuka yau kwanan mu biyar ko gaisuwa Bata hada mu ba tana Gaba Dani. Ke shekaran jiya ma sai nine na kaucewa Farida Amma da ban kauce din ba na tabbatar da zata banke ni ta wuce saboda kawai tana ganin na shiga Rayuwar ta to Haj ai Dole kuwa na kyale ta tunda in na wuce haka Babu ko shakka farida zata iya Rufe ni da Duka ko ma ta kaini k’arar da ta fad’a.

Haj kame da Baki tana kallon Farida wacce a yau din taji batayi daidai ba Amma Kuma don me za a kasa fahimtar ta?

“Kayi dauda don Allah kayi hak’uri wallahi ban San haka ba da na barka kayi Mata Hukunci irin Wanda Uban ta zaiyi Mata Kuma duk Abinda tayi Maka ba Kai din tayiwa ba sai ni da Uban ku da yake k’asa don Kai din wakilin mu ne ko Muna Raye ko mun faku . Don haka Abinda tayi ni tayiwa Nima Kuma Abinda kace shi nace Mata gata ga Sameer Nan.

Dauda ya Soma bawa Haj hak’uri tana fadin, “Haka wannan yarinyar ta koma ban sani ba dauda? Ta fada tana kwalla.

“Kar kiyi Mata kuka haj Allah ya shirye ta ai ba zamu biye Mata ba tunda nafi ta hankali zan Kuma Yi mata Adalci na Bata abinda take so tunda jini na ce.

Haj ta dauki wayar ta ta na Kiran wayar Sameer Wanda tuni Farida ta Kira shi take fada mishi ta zo katsina yazo gidan su.

Ya samu Kiran wayar Haj tace yazo ya dauki matar shi.

Yaya dauda ya fice don baya son Sameer ys zo ya same shi don kanwar shi ta gama kunyata shi don haka ya fice daga gidan.

Fitar shi Babu jimawa sai ga zuwan Sameer Wanda taho da Saddam da Hanan Wanda Suka ga Uwar su Suka Dafe ta suna murna shi Kuma Haj tayi musu nasiha da Hak’uri da kuma fiddawa zuciya zargi don matukar suka ce da zargi a zukatan su to akwai matsala.

Da sauri Sameer yace in Sha Allah haj ba za a kuma ba.

Da haka ya dauko Farida suka wuce gida Yana ta Rawar jiki don ya tabbatar da Babu yadda za ayi ya Rayu Babu farida da Ya’yan su FARIN CIKIN su don haka yana zuwa gida ya aje su ya fita ya siyo Komai na bukatar gida ya dawo aka Rufe kofar.

<< Tana Kasa Tana Dabo 9Tana Kasa Tana Dabo 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×