Skip to content
Part 11 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Gabadaya Wasila ta gigita Duniyar Alhajin naira a wannan Rana Domin kuwa ta tsaya mishi a Rai ya kasa Manta wannan Dare Nasu. Domin kuwa ta tabbatar mishi da Mata suna suka Tara ya yarda ya Kuma Gane Hakan.

Tun a Daren yake faman Kiran ta Amma da yake ta Isa gida ta Soma fuskantar calanjin daga Dan ta sagir sai ta kashe wayar gaba Daya don tana son samun ta inda zata bullo musu shi da Uban shi musamman da suka watse Mata Aiki da Zuwa gidan Anty murja suka FASA Kwai.

Hankalin ta Bai kwanta ba sai da murja tazo Gidan ta Shirya wannan karyar da wata murjar ta bayan layin su wacce Babu ita a wannan Duniyar dai ta karyar da ta Shirya

Don haka Bata shaki iskar yanci ba sai da ta kashe Bakin tsanyar inda Kuma Alhajin naira ya kafa Kiran ta…

Tana Raka murja ta tafi ta dawo ya iske wayar sai tsuwwa take ta dauka tana Fadin

“Mai Naira sai Kira kake Ina bacci kana katse min BACCI.

“Hutawa lafiya tawan ai ni ban Samu zarafin yin bacci ba jiya kin gigita Duniya ta har na kasa Samun nutsuwa ke kadai nake Gani.

“Na fa san dadin bakin ku Maza ta yuwu a bayan fage kake idan Kuma ka tusa Matar ka gaba zaka iya fada Mata Kalaman Da suka Fi wannan.

“Wallahi ban taba fada Mata Kalaman da suka fi wannan ba don kuwa ke da ita da kuna Banbanci matuka Gaya ni yanzu fa ban gaji ba zan sake bayar da kud’in da suka Fi Wanda na bayar jiya Amma fa gaskiya ki sama Mana dabara wacce Zaki kwana ko biyu ne bakya Gida don ni ko Rayuwa ta kika nema zan iya baki ita don ki nuna min Mata suna suka Tara Kuma ni saboda ciwo na na siyo magani na kome kike so kin same shi.

“Komai kace? Nifa ka San Babu abinda nake so irin kudi don da miji na Yana da kudi ba zaka tab’a Gani na ba bare ka Sanni don Haka ni kudi nake so in Kuma zaka bani zaka Ganni.

“In dai kudi ne matsalar ki to kin warke matsalar ki Yaya za ayi yanzu? Wallahi ban ki kizo yanzu kiyi min sati ba don Allah ki taimake ni kice Nazo yanzu na dauke ki.

“Sai dai zuwa anjima kazo ko Kuma in na Samu gama Abinda nake zan kira ka.

“To Ina Jira don Allah.

Ya kashe wayar ya bar wasila da tunanin ta yadda za ayi ta lalubo hanyar da zata samu barin Gidan Nan har tsayin kwana biyu. Sai kawai taga kauye ya kamata tace zata je in yaso ta Samu karyar da zata Dora ta mutuwa ko ta sabga. Don haka sai kawai ta yanke shawarar fidda Kai ta nufi gidan su tana fadawa Goggon su tana son Zuwa kauye tayi ziyarar Yan Uwa Goggon tace hakan Yana da kyau ta Kuma Yi Aikin zumunci. Don haka ta bawa Goggon waya tace ta fadawa ishaq don ya San da tafiyar. Ita kuwa Goggo Bata San kan abin ba ta karbi waya ta Rattaba wa ishaq bayani kamar duka kenan yace Babu komai Goggo Amma zata tafi da Yara don Suma suga Yan Uwa tace kwarai kuwa sagir ne kawai ba za aje da shi ba tunda shi Yana zuwa Aiki.

Wannan shine baya da k’ura in aka tafi da Yara yo me kenan? Amma batayiwa Goggon tsegumi ba don Haka Shima Bata nuna mishi ba zataje da su ba sai dai kawai yaji tayi tafiyar ta.

Alhajin Naira da ya iso majalisar tasu ya iske su gemu sun cika ana ta Shan shayin Yar butar inda gemun ya tare shi Yana Fadin.

“Yauwa Mai Naira wai Ina mutuniyar Nan take Mai boga da shawarma? Wallahi matar ta tsaya min Rai tun ban ganta ba Ina mafarkin ta ni kuwa ya za ayi na samu boga da shawarmar nan na Dan dandana kasan ni Ina Gane mace Mai test ta hanyar girkin ta ta Nan nake Gane mace Zatayi test Hannun ta a girki shine martabar ta.

“Ka bari gemu Wallahi matar Nan karshe ce ni fa Rabo na da matata an Fi wata don Sam sai naji akwai banbanci a tsakanin su Duk da dai na Gane Naman Haram ne da shaidan ke kawata shi Amma fa Babu karya matar Nan Wallahi ta Goge matuka Gaya kuma za a kwana ana harka Babu Ruwan ka da me zaije ya Dawo tunda ta Goge ta Kuma iya.

Gemu Wanda tun Ranar da yaji Mai Naira Yana bayar da Bayanin wasila da kwanan harkar da sukayi Ranshi da zuciyar shi Suka kwadaitu da son ya samu contact din ta don shi din maye ne a harkar mace bare wacce Ake ta kururutawa . Shiyasa ya kasa Manta Mai shawarma har ta Kai Yana mafarki da ita don da gaske yayi MAFARKI da ita Amma ya San Mai Naira ba zai yarda ya bashi contract din ta ba sai Kuma gashi yanzu Yana Kara kambama mishi ita inda har yake fad’ar ya jingine matar shi a gefe Saboda banbancin da ke tsakanin su.

“Kai Amma kuwa ka more mutumi na tunda fa naga ka gigice ai na San angulu ne Kai baka jewar Banza.

“Ai gemu na yarda da maganar ka Yasin yadda shawarmar ta take haka take itama. Kuma in dai test din hannu shine wancan test din to bakayi karya ba bari na dauko Maka Ina da sauran boga a mota kaji test din sa.

Ya Mike ya nufi motar shi ya dauko coils din da aka bade bogar a ciki ya kawo majalisar inda Mazan sukayi ta kawo harin dauka wata Kil suna son gasgata maganar gemu na test din girki shine test din mace.

Gemu ya Kai shawarma a Baki Yana tauna inda yan majalisar suke ta mayar da bayani kowa da Abinda yake fada Wanda zai nuna maka su din Yan Duniya ne Kuma duk akan wasila suke maganganun.

Gemu da ya gama mutuwa a son wannan Mata Amma Kuma ya Rasa ta yadda zai yaudari Mai Naira ya hada shi da ita don ya San yadda harkar take Babu Mai yarda ya bude maka yadda abin yake . Don haka sai ya Rasa ta yadda zai iya samun contact din matar Nan.

Wata Hikima tazo mishi wadda ya Gane sai ta wayar Mai Naira kawai zai iya samun contact din Nan Amma ta Yaya zai iya samo wayar tazo Hannun shi ? Sai ya shiga Saka ta yadda za ayi ya samo wayar har ya Nemo lambar ba tare da ya Gane Abinda yake nufi ba?

Ana ta fira a majalisar wacce mafi yawan ta akan Mata Ake yin ta kowa da inda ya Saka gaba.

Mai Naira ya Mike zai kama Ruwan inda wata dabara tazowa gemu yace,

“Kai na Gani da film din nan na anaconda a wayar ka ko ?

“Anya ban Goge shi ba Kuwa?

Bari na duba na Gani.

“Bani na Gani In ma ka Goge ai ba zan Rasa Wani ba na kwana biyu banyi kallon Nan ba.

Ya fada yana Mika hannu ya dauko wayar Mai Naira wacce take ajiye inda yake shi Kuma ya Miko mishi ya dauki buta ya karbi key a hannun garba Abubakar ya nufi toilet

Mai gemu yayi murmushi Yana ganin sa ar tashi ma Mai yawa ce.

Ya shiga received inda yaga lambar da ta kasance itace last call wacce Baya bukatar a fada mishi itace ta Mai shawarma duk da ba sunan da za a Gane ba ne Amma dai tunda itace last call din baya shakka itace don haka a kwanyar kanshi ma ya hardace ta inda ya SHIGA tura film din har Mai Naira ya fito ya karbi wayar shi inda wasila ke Kiran shi ya fige wayar daga hannun gemu Yana dauka Yana fadin,

“Yaya na taho ne gimbiya? To Gani Nan Zuwa yanzu kuwa yanzu kuwa don Kiran ki ya zarce na shugaban k’asa Yasin.

Ya fada Yana kashe wayar ya Mike da sauri ya figi makullin motar Yana fadin

“Ku tashi lafiya ni Kam zanje naji dadin Rayuwa ta kar shegen da ya kira ni don waya ta ma ko Nan da jibi bana zaton zan Bude ta zan Sarara na huta.

Ya shige motar suna mishi sharri da lalata Amma Bai tsaya jiran Basu amsa ba ya figi motar shi ya wuce.

Wasila Kam da ta Hadidiyi magungunan ta ta Kuma matsa na matsawa da budada jiki da turare ta fito cikin hijabin ta inda yusra ke fadin,

“Mama Ina zakije ? Kullum fa yanzu sai kin fita ko kina zuwa makaranta ne?

Ta Dubi yusrar Amma Bata iya tanka Mata ba ta fice tana Fadin

“Kauye zanje idan Uban ku ya dawo ki fada mishi na tafi sai na dawo wata Kil Gobe ko jibi na dawo.

Ta fice ta bar yusra da Binta da kallo inda xee ta bita tana kwala mata Kira.

Ta juyo tana kallon yarinyar wacce ta iso tana fadin,

“To mama wa zai Mana tuwo tunda yusra Bata iya ba kince Kuma sai kin kwana?

Ta Ji tamkar ta make zee din Amma tace

“Sai Uban ku ya San yadda zaiyi daku ni Kam ai na Soma gajiya da tsuguno bakin kurfoti da sunan girki ..

Ta wuce ta bar zee da Yi Mata Rakiya da ido tana kallon ta har ta bacewa ganin ta ta juyo gida

Tana Isa bakin Sauki ta hangi motar Mai Naira ta Isa ya bude Mata kofar ta shiga inda ya karbi wayar ta ya kashe Yana Fadin

“In kika bar wayar ki a Bude ai zata bamu matsala Nima Dole na kashe tawa sai jibi ko zan kunna ta

Suka Sauka a hotel din da yake da D’aki don sauke Matan da Ake son shakatawa.

inda a kullum ya Zubawa surar wasila ido Kara birkita shi take take da Kara nuna mishi Bai San ta ba har gobe da sabon Salon da zai Gani a tare da ita. Don haka Babu Bata lokaci suka shiga Masha ar su inda take Kara birkita Mai Naira Wanda yake nufin morewa Rayuwar sa da wasila wacce take Kara kanainaye shi da son mallake shi ya Bata hatimin nasara

A kwana Biyun Nan Kam ya Mori kudin shi ita Kuma ta San ta gogu Amma ba ta da matsala in dai an sauke Mata kayan

*****

Tunda Farida ta dawo gidan Sameer ko musu Mai tsanani Bai sake faruwa ba . A kullum Yana Gida Rungume da Farida ko majalisar ma ya Rufe zuwa sai dai Aiki Wanda yake fito da shi daga gida da Kuma ya dawo shikenan.

Sati Biyar da komowar Farida ya samu sauyin wurin Aiki daga barikin SOJA na katsina zuwa barikin SOJA na pertercout Al Amarin da Baiyi mishi Dadi ba don shi da gida idan ya koma pertercout sai sati . Amma da yake Aikin Basu ya gaji Hakan yau kana Nan Gobe kana can Amma dai ba don Rai na so ba tunda ko Babu komai ba za a hada da katsina ba inda Aikin yake da sauki Kuma ga iyalan sa da iyayen sa a gida . Amma dai Dole sauyin in ya samu Dole ka karba Kuma ka tafi ko baka so.

Farida kam Zullumin ta yafi nashi don ta San a da can da yake kusa da Gida ma Yana hasashen Wani Abu bare Kuma yanzu da sai yayi sati kafin yazo? Kuma ta tabbatar Dole Sameer yayi zargi akan ta ba Kuma zai Daina zargin ta ba mudddin Rayuwar shi Domin kuwa itace taja ya zarge ta. Kai ba ita ba duk macen da ta sake tayi Abinda tayi Dole ta zama abin zargi a wurin miji Domin kuwa har Abada Yana Nan Yana Nazari akan ki.

Tun da ya samu takardar wannan sauyin ta kula da Abinda yake ZUCIYAR sa duk da Bai fito fili ya furta ba Amma ta gama karantar sa

Ya SHIGA damuwa matuka Gaya Amma a haka ya cije yayi shiri Ranar Lahadi ya aje Mata komai na bukatar gida da Kuma kud’in da zai Zamo ba tsaron lalurar Amma fa cike da damuwa ya bar garin katsina zuwa pertercout inda Kuma Farida tsab ta Gane damuwar shi ta Rashin sanin Abinda zaije ya Dawo a kanta.

A kwanan shi Daya ne take a can ya Kira ta Yana tambayar me take Kuma a Ina take Kuma meye meye Wanda ya nuna Yana Nan akan Doron zuciyar shi wacce take kulla mishi zargin Faridar dama ita ta San Hakan.

Ta Yi bashi dukkan amsoshin shi Amma Bai iya saurara Mata ba a kullum da kalolin tambayar da zai sauke mata wacce ta nuna Yana son kama ta da wani Abu

Karshe sai ya Daina Kiran ta sai dai yace ta hau online zai Kira ta Vedio call don ya ga me take Kuma a Ina take Kuma me take Kuma ita da wa? Tun Al Amarin Bai fara zo Mata wuya ba har ta Soma gajiyawa don a ko yaushe zai Kira ta ne yace ta hau online zai Kira ta Vedio call kuma matukar tace ba haka ba yanzu ne zai hau masifa Kuma ya tabbatar da Bata gaskiya.

Ranar da ya Kira ta kuwa wayar Babu caji Bai same ta hauka ne kawai baiyi ba don Babu abinda zuciyar shi take Saka mishi sai tana can tana.

Yayi ta zarya har zuwa yamma da ya Kira ya samu yayi ta masifa Yana tambayar Abinda take har wayar ta sauke caji bayan shi ya Kira ta Vedio call ha cajin ya sauka Kuma Babu gen bare ta Saka caji. Tun daga wannan Rana ya kafa dokar kar ta sake ya Kuma Kiran wayar ta yaji in ma Babu Mai a gen zai turo Wanda zai zuba a tayar Mata ta Saka wayar caji.

Hawaye kawai take saki Domin kuwa masifar Sameer ta ishe ta Babu wata hanya da Bata nuna son kama ta da laifi yake ba. Ita Kam Bata ji Dadin wannan sauyin wurin Aiki ba Domin kuwa tashin hankali aka Gallo Mata ko da yaushe tana kwakume da waya don Kar ma ya Kira Bata dauka ba Nan Bata da mafita yanzu ne zai ce ga Abinda takeyi har Bata dauki wayar ba.

<< Tana Kasa Tana Dabo 10Tana Kasa Tana Dabo 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×