Skip to content
Part 12 of 59 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Zee Zee ta juyo gida tana kuka don allah yayi ta acici ce da Bata iya jurewa yunwa ko Alama bare Kuma ta dawo gida Bata ga an Dora girki ba yanzu ne zata fasa kuka shiyasa ta tambaye wasila ba zatayi tuwo ba Saboda taga ta fice a daidai Lokacin da ya kamata ace ta Dora girkin…

Yusra ta fito tana tambayar Zee Zee me Akayi Mata?

“Mama ce tace ba Zatayi tuwo ba Kuma tayi tafiyar ta ni Kuma yunwa nake ji.

Yusra ta Rasa me zata ce mata . Sai ta ke kallon ta tana kukan ta har ta Gaji tayi shiru kafin bacci ya dauke ta a Nan inda take.

Sagir ya shigo Gidan daga gareji inda ya kusa yin tuntube da Zee Zee Dake Kwance a k’asa bayan ta gama kuka.

“Kai yusra me yasa baki dauke ta anan ba ?

Ya fada Yana sumgumo Zee Zee inda yusra ke fada mishi kukan yinwar da tayi har tayi bacci.

Ya Dubi yusrar Yana fadin. “To Ina mama take ne?

“Mama ta tafi kauye tace ma sai tayi kwana Biyu.

Ya ajiye Zee Zee ya fito da kudi d’ari Biyu ya mikawa yusra Yana fadin.

“Bari ayi magaruba sai ki siyo muku taliya da manja kafin Zee Zee ta Farka.

Ya wuce Yana cire kayan jikin shi na Aiki Amma zuciyar shi tana Raya Mishi mamar su ba kauye ta tafi ba. Akwai wani Abu da take Yi Wanda Allah NE kadai ya San Dashi sai Kuma ita…

Ana gama sallar magaruba sai ga ishaq ya shigo Gidan inda ya iske yusra da Zainab suna cin taliyar da sagir ya Siya musu…

“Ah ! Yusra Ina mamar taku ne? Zee Zee ce tayi maza ta ce, “Tace kauye zata je har nace ba zatayi tuwo ba tace ba Zatayi ba…

“Bata tafi Daku ba kenan.

Ya wuce zuwa D’akin shi inda yake jin Bai yarda da matar ta shi ba zuciyar shi tana Raya Mishi Wani Abu. Wanda Dole ya Saka ido Domin kuwa me kiwo ne da za a tambaye shi Abinda aka bashi kiwon.

Yana zaune Yana tunanin Abinda ya kamata yayi sai ga sagir ya shigo ya zube a Gaban shi Yana hawaye ya kasa cewa uffan kanshi a k’asa Babu Abinda ke dukan zuciyar shi sai Bak’in cikin yadda mamar su Bata tausayin su yusra da Zainab.

ISHAQ ya kama shi Yana Fadin, “Me ya faru ne sagir? Wani Abu ya faru a garejin naku ne?

“Abba Babu Abinda ya faru a garejin mu sai dai bana Jin Dadin yadda mama Bata tausayin su yusra. Yanzu fa na dawo gidan Nan na samu Zainab tayi bacci a Dokin kofa kadan na taka ta wai kukan yinwa tayi har bacci ya dauke ta Amma mama wai ta tafi kauye ta bar su Bata san sunci ko Basu ci ba? Abba ba zakayi Mata magana ba kullum fa yanzu mama sai ta fita baka lura ba ? Ni Ina take zuwa ne da ba zata iya zama gida ba ko Ka san inda take Zuwa ne?

Tambayoyin sagir sai suka bawa ishaq tsoro don Dole kuwa ya zama abin tuhuma ga kowa tunda ai a karkashin ikon sa take Dole ya zama shugaba.

“Abba Ina tsoro Wallahi Kuma yanzu haka fa ba kauyen ta tafi ba? Na saki da mama tunda tace an kwantar da Anty murja Asibiti Kuma abin ya zama ba haka ba Ranar Nan fa har da kud’in amurka na Gani a hannun ta.

Zufa ta Soma karyowa ishaq yaji Wani tabbacci akan maganar yaron don shi kanshi Abinda yake Rayawa kenan wasila ba kauyen ta tafi ba.

Sagir ya Mike ya fice daga D’akin inda ya nufi D’akin wasila ya Soma bincike d’akin cikin sa a Kuma ya Gano Abinda ya tayar da hankalin shi Domin kuwa Dalar amurka ya ke Nema sai ga tarin kudade ya samo sama da Dubu d’ari Biyu Wanda Suke can karshen adaka.

Ya zube kudin a Gaban ishaq Wanda ya Zubawa kudin ido na tsayin Lokaci kafin ya ce,

“Kwashe kudin ta ka mayar Mata inda ka dauko su sagir kar ka sake ko Naira ka daukar Mata.

Sagir ya kwashe kudin ya mayar inda suke kafin ya fice daga gidan.

ISHAQ ya jima Yana kullawa da kwancewa kafin ya samo mafitar da zai tabbatar da maganar sagir ta Cewa ba Lallai wasila tana kauyen tace zata ba.

Sai yaji Dole ya nufi kauyen Nan gobe ko don ya Kara tabbatar da Cewa sagir Yana Ankare da komai Kuma yayi Nisan tunani..

Haka ya dauko Zee Zee da yusra da suke bacci ya kawo su d’akin shi Suka kwana da safe ya Kira sagir ya bashi makullin gidan Yana Fadin.

“Ka makullin Nan sagir idan ka dawo daga Aiki don zan Kai wa wasila su Zee Zee can kauyen kar ka Dawo ka samu Gidan a Rufe.

Ya karbi makullin Yana Fadin,”To Abba kana da kudin mota ne?

“Akwau sagir na samu Aiki ai yau din. “To Allah ya kiyaye hanya ya sa ku dawo lafiya.

Ya fice gareji ishaq Kuma ya kwashi su Zee Zee zuwa kauyen iyayen wasila Wanda yake cikin dutsin ma wato Gaggo

Tafe yake Amma tunani yake Wanda ya kasa yarda da jaye jayen da zuciya take jawo mishi Amma Bai yarda ya dauki Daya ba ya BARWA lokaci alkali.

Suka iso gidan wanda ya zamo na hadaka ne kasancewar kauye da Kara Yan Uwa Ake haduwa a wuri daya saboda zumunci don haka ya San ko Ina Kai tsaye ya wuce sashin kakannin wasila da iyayen ta yayun iyayen ta da kannen su inda kakar tasu ta tarbe su tana musu sannu da Zuwa ya zube Yana gaishe ta ta Amsa tana tambayar shi iyalin da su hurera wato Goggon su wasila duk ya amsa da suna lafiya ya kawo Abinda ya Rik’e musu ya Bata tayi ta Godiya tana Saka Albarka tana Rik’e da Zee Zee da yusra tana karbo musu gauda da kulele Amma basu San shi ba.

Yayi ta zuba idon inda zai ga wasila Amma ko da wai tsohuwar Bata Yi mishi maganar ta ba sai ya Rasa ta yadda zaiyi tambayar Amma sai yayi ta cikin Hikima Yana Fadin.

“Ai kuwa iya kun jima Baku zo katsina ba.

“Kai ai na jima gaskiya kasan ance in kaji Shiru lafiya Amma su iyayen naku sukan shuga kuma itama hurera ai tana Zuwa su dai yaran nata ne in ba sabga ba sai ajima murja da wasila bamu Saka su ido ba.

Ya tare ta da fad’in, “Ai kuwa satin da ya wuce tace zata zo na zaci ma tazo.

“A a Rabo na da wasila ai anyi fin shekara gara ma murja itace Bata Rufa shekara ba Amma wasila tafi shekara ga shekara biyu ma Dan kad’an za a cire.

Yaji Wani Duka da ya sauka a ZUCIYAR shi Amma ya maze ya Mike yanayiwa iya sallama ya wuce inda iya tace ya bar Mata yaran suyi kwana Biyu tunda anyi hutun makaranta.

Ya yarda ya bar Mata su yusra ya taho Yana Jin kanshi Yana Sarawa saboda tashin hankali. In kuwa haka ne akwai Abinda wasila take kullawa Wanda Babu gaskiya a cikin shi Wanda Kuma yayi sake Bai Gano ba har sagir yafi shi dogon lissafi ya fahimci Uwar shi ta sauya sauyin da ya ke bukatar Saka ido.

Ya dawo gida Kai tsaye ya wuce gidan su wasila wurin Goggo ta tarbe shi Suka Gaisa tana Fadin
“Ai Bana tambaye ka wadan nan marasa jin maganar ba tunda an kwaza kauye,

“Ai ba da su ta tafi ba Goggo.

“Yau ga iyashege a wurin wa to ta barsu?

“Nima sai jiya da na dawo na samu ta tafi shine yau na kwashe su muka tafi dutsin ma Amma Goggo bamu same ta ba don iya ma ce Mana tayi a Shekara biyu kadan ne Babu Rabon ta da wasila shine nace ko dai ba dutsin ma ta tafi ba?

“Bata je ba kace ? Ikon Allah ni Kuma can tace min zataje to Ina Kuma tayi?

“Nima shine nace bari Nazo naji ko ba can ta tafi ba?

Goggo ta kame baki cike da Mamaki kafin tace,

“Tashi kaje ISHAQ bari yanzun Nan zan kure Ramin karyar yarinyar Nan dama nayi Mamaki don Bata tab’a yin wannan abun Arzikin ba murja ce Mai wannan kokarin sai fa maimuna Amma Banda wasila.

Ya Mike Yana fadin, “Ai na baro su yusra a can iya tace na bar Mata su suyi kwana Biyu…

“Kayi daidai ta haka ne ma zaka kure Mai karya ai Nima Dole na San abinyi tunda da ni ta fake tayi karyar ta tunda tace nayi maka magana Raina ya bani to ita Kuma Aikin me take da ba zata iya tambayar ka ba? Amma kayi hak’uri ishaq na San kana kan Yi.

“Babu komai Goggo Allah ya kara lafiya, Ya Mike Yana aje Mata Yan kudin yayu Mata sallama ya fice
Goggo ta Mike tana Fadin.

“Ai Dole ma na nufi Gago yanzu In ba haka ba kuwa ai zanji kunya ne tunda da ni tayi karyar ta in Banda yaron ma Yana da mutunci ai sai yayi zaton mun hada Baki ne Alhalin ban San tsiyar da ta shirya ba.

Ta Mike tana wanke jikin ta ta murtsuka Mai Tai shirya inda ta bar mairo a gidan ta nufi dutsin ma

Iya ta ganta da Rana tsaka tana Fadin, “Ince dai lafiya yau Muna ta ganin mutanen katsina.

Goggo ta zauna tana Gaishe da iya wacce itace mahaifiyar ta Suka gaisa inda su yusra suke cikin yara suna ta wasa Goggo ta Soma baza idanu kafin tace da iya

“Wai iya wasila Bata zo ba kuwa ?

“Haram ni Rabo na da ita fin shekara Nan tace zata zo ne? Mijin ta dai ya zo sai Kuma Ya’yan ta gasu.

“Yarinyar Nan akwai tsiyar da ta shirya iya kinji kinji yadda mukayi da ita don Allah ba sai taja mijin ta da yake ganin girma na yace mun hada Baki ne? Wannan yarinya bata Kaunar ta wanye lafiya Dani Amma bari ki Gani iya ko can dangin Uban ta ta sauka kafin tazo muku Nan har can din zan je ai Kuma zama Bai ganni ba.

Goggo ta Mike sukayi sallama da iya ta wuce bindawa Amma can din ma Babu labarin wasila don sunce Bata je ba.

Dole Goggo ta koma gida tana tunanin me take nufi da wannan karyar?

Washe gari kuwa Wanda yayi daidai da kwana Biyun wasila sai gata ta dawo gida Amma ta samu gidan a kulle saboda sai ta juya ta nufi gidan Goggo wacce ta ganta da tulin Kaya.

“Kai sannu da hanya mutanen gago ya kuka baro su? Wasila ta maze tana fadin, “Wallahi lafiya Lau suna ta Gaishe ku.

Ta fito da sabulu da man shafawa tana bawa Goggo tana fadin

“Ga irin tsarabar kauye Goggo…

“Kai madalla Allah ya amfana yo Ina kika baro yaran ne ?

“Ai ban tafi da su ba suna gida.

“A a ai ishaq ya Kai su yace in zaki dawo sai ki taho da su tunda Nima ai da su nace ki tafi ko?

Razanar da ta bayyana a fuskar wasila itace ta nunawa Goggo akwai wani Abu.

“Bai Kai su ba Goggo ya dai fada ne kawai.

“Ya Zaki ce Bai Kai su ba tunda Nima naje Kuma na baro su a can? To Ina suke yanzu in Basu can?

Zufa ta Soma yankowa wasila Goggo ta zura Mata ido.

“Kinga kar ki ja min magana da Nisa Domin kuwa kullin ki ya warware mijin ki ya Gane ba inda kika ce zakije kika je ba. Nima Kuma naje gago iya ta fada min bakije ba. Dama kin shirya Bata min suna ne? Kika sa na Kira mijin ki na Rok’e shi Alfarma Ashe akwai Abinda kika kulla a Ranki?

Tukun da fari ma Ina kika je da kika shirya wannan munafuncin? Goggo ta Zubawa wasila ido inda taga gagarumin sauyin da wasilar ta samu na danyacewar fata Kuma ga Wani sheki tanayi tamkar wata matar gwamna.

Kallon da Goggo take mata ne ya ishe ta ta kasa cewa komai inda zufa take karyo Mata inda taji Goggo ta dauki Wani salati da sallallami tamkar wacce taga balaki inda taga Goggo na nuna kayan jikin ta tana fadin,

“Sai yanzu na dago Abinda kika fara kenan ? Dubi kayan jikin ki kice kin fara bak’ar kasuwar Nan ta Matan Zamani? Shine Dalilin da kika wulakanta ni kika sani nayi Abinda za aganni a mutuniyar banza ? To tashi ki Isa gidan mijin ki duk abinda ya biyo baya kuwa zan barki da Allah duk abinda kikayi Zaki ganshi a kwaryar kanki tashi kije dama ai murja ta fad’a min wata karyar da kikayi to ga ta Biyu ma ta bayyana Ina me tabbatar Miki da karya ta uku sai Allah ya tona Asirin ki bana bukatar Jin Komai daga bakin ki Amma Abinda kikayi mini na barki da Allah.

Goggo ta fada tana watso mata sabulun da Man shafawar da ta Bata tana fadin

“Kwashe tsiyar ki bana bukatar Allah ya Baki sa a in dai Duniya ce gaki ga ta Nan Wanda Bai zo ba ma tana Jiran shi.

Jiki a sanyaye wasila ta Mike tana daukar kayan ta ta fice tana Jin wata muzanta na sauko mata Amma Bata da zabi ita kadai ta San matsalar da Rashi ya haifar Mata don Haka sai a ga laifin ta don ta nemi gujewa talauci?

Ta koma gida inda ta iske sagir ya dawo daga gareji don haka a Bude ta iske Gida inda taji wata fargaba duk da tana da kokarin shanye damuwa.

Ta shiga gidan tana Neman inda zata ga ishaq Wanda aka ce yaje Gago Bata je ba.

Kallon da sagir yake Mata ya kara tsorata Amma ta wuce Bata bi ta kanshi ba .

Tana shiga D’akin sagir Yana shigowa inda ta mayar da Hankalin ta akan shi.

Ya durkushe a gaban ta da Duka kafafun shi Yana fitar da HAWAYE Abinda ya tsorata ta Amma bata tanka ba tana kallon shi cike da fargaba don ta San Shima ya samu Labarin karyar da ta kuma a karo na Biyu..

“Mama kiyi Hak’uri da Abinda da zan fada Miki Amma gaskiya kina yin abubuwa da yawa Wanda kuskure ne . Yanzu ace ba Zaki iya zama gida ba ko don su yusra da Zainab. ? Mama ke kike so a cikin Duniya da kike Neman zama wata ta daban ? Nayi Miki alkawarin duk abinda kike so in Sha Allah zan sama Miki shi ta hanyar halal in Sha Allah ba zan tab’a Nemo haram na kawo Miki ba. Dukkan Abinda kika sani a cikin Duniya in bawa zaiyi hak’uri zai same su Amma mama dubi yadda kika mayar dashi ba a bakin komai ba . Mama Yaya kike so na kalle ki kina wulakanta shi a gaba na? Jiya Abba yaje Gago Ake fada mishi kinfi shekara bakije ba mama Ina kika je? Ya kamata ki Daina karya don ga Alama Bata karbe ki ba tunda duk in kikayi ta sai Asirin ki ya tonu . To zan Rok’e ki da girman Ubangiji da na ANNABI MUHD S A W ki Hak’ura da Duk Wani Abu da zuciyar ki take Raya Miki Domin kuwa ba bu Alheri a ciki ni Kuma in kika yarda da shawara ta nayi Miki alkawarin kome kike so ki fada min ALLAH zai Dubi nufi na ya kama min na kawo Miki Amma don Allah ki tsaya ko don su yusra da Zainab.

Yayi shiru ko zata tanka Amma jikin ta ya mutu murus ta kasa tankawa sai ma tausayin sagir da yusra da Zainab da ya kamata Domin kuwa hakikatan ta zalunce su!

Tayi Kasa da kanta tana Nazari Amma Kuma ZUCIYAR da tayi Nisa ta tuna Mata irin kud’in da Mai Naira ya juye Mata sai taji duk abinda Ake nema Duniya don kudi Ake yin shi Kuma tana son ta inganta Rayuwar ta Dole kuwa ta nemi kudi..

Haka sagir ya fito daga D’akin Bata iya Cewa uhum ba .

ISHAQ ya dawo ya dawo gida ya samu wasila ta dawo gidan Amma Kuma jikin ta a Sanyaye..

Yayi murmushi yana fad’in, “Kai Yan tafiya an dawo ? Sannu da hanya Ina su yusrar?

Ta Dube shi cike da Jin haushin bin diddigin da yake Mata tana Fadin

“Suna inda ka kaisu Mana? Sai kuma me? Yayi murmushi Yana Fadin,

“Sai na barki da ALLAH wasila Domin kuwa shine ya fini sanin manufar ki aka karyar nan Guda Biyu wadda Dukkan wacce kikayi sai da ya tona Asirin ki don Haka ki sani matukar dai kina dauka ta a banza wofi kina Rufe min Halin da kika ciki to very soon zai bayyana min ke da Abinda kike lullube mini don na ga komai don Haka Babu komai a Raina Amma na barki da ALLAH kuma Zai Bude min Abinda kika lullube.!

Ya wuce ta ya barta da wani irin matsiyacin firgici da Zullumi musamman da yake ya barta da ALLAH Kuma Zai Bude mishi Abinda ta lullube ya hayyu ya qayyum.

<< Tana Kasa Tana Dabo 11Tana Kasa Tana Dabo 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×