Skip to content
Part 14 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Gidan shakatawar Mai gemu can ya Sauki bakuwar shi wasila wacce tun a mota yake Zuba Mata idanu Yana Jin tamkar ya Soma lasar ta.

Ya sallami Direban Wanda ya aika ya siyo mishi kayan fruit da madarar fan ice.

Ya Mika Hannu ya kamo hannun wasila Wanda yake dauke da Jan lallen Yana Rungumo ta ya fito da ita daga mota suka nufi cikin Gidan shakatawar Wanda aka tsara da wata irin daular don kawai a kawo Matan da za a shakata da su.

Yana Rungume da wasila wacce ta tabbatar da son mutumin Nan yayi Mata ba zata don yadda take Jin bugun zuciyar ta tamkar wacce Bata taba hada jiki da wani Namiji ba. Sai Mai gemu Wanda yake nuna Mata tashi barikin ta zarce wacce ta Sani

Direban Mai gemu ya dawo da Aiken da akayi mishi ya fice.

Mai gemu da kanshi ne yake shiryawa wasila kayan tarbar da aka shirya Mata duk da Bata ci Wani Abun kirki ba Mai gemu ya Rufe kofar da ita inda itama ta bayar da Kai bori ya hau akan Mai gemu Wanda ya Kara dasa Mata wata matsiyaciyar soyayya a ZUCIYA Taji Lallai duk Mazan baya ma cutar suke sai wannan shine ya tabbatar Mata da ba mata ne kawai suka Tara suna ba Suma Mazan suna suka Tara.

Sagir ya dawo gidan inda yusra taji Abban nasu Yana kakarin Amai. da Gudu ta fito daga D’akin su ta nufi D’akin shi ta same shi sai kakarin Amai yake Amma Babu komai a Cikin sai kumallo tsanwa sharrr.

Ta K’araso gareshi tana mishi Sannu Amma Bata da Hikimar Bashi bare ta Wani Abu baya ga Sannun.

Ta fita waje ta dauko parker da k’asa ta Zubawa Aman ta kwashe tas ta fita ta Zubar ta dawo tana fadin

“Abba ko kawo maka Abinci?

Ya Dube ta da so Samu ne fura yake so kafin ya tafi Allura don ciwon kan yafi matsa mishi.

“Ga kudin da mama ta bamu Nan akwai canji ko na siyo Maka wake da shinkafa?

Yayi saurin girgiza Mata Kanshi. Don baya bukatar wani Abu da ya fito daga hannun wasila bare Kuma kud’in ta da ya gama zana yadda take samun su.

Ya koma ya kwanta Yana dafe Kai Yana Kara jin matukar Bak’in ciki don Babu abinda ke zagaya idanun shi sai wasila a motar da ya Ganta. Tambayoyin da suke jibge a zuciyar shi shi kanshi yasan sun Fi karfin shi bare Kuma ita da yake son Sanin waye me motar ? Meye Dalilin ta na fita Bai sani ba? Meye Kuma alakar ta da Mai motar? Kuma me ye na fita da inda za a Kuma ?

Sagir ya dawo daga gareji yusra ta tare shi da fad’a mishi Abba baya da lafiya har yayi amai tsanwa sharrr…

Da sauri sagir ko kayan shi Bai cire ba ya nufi D’akin ishaq Yana Fadin

“Abba baka da lafiya ne? Ya dago Yana Duban shi…

“Zazzabi ne sagir ka Dawo? “To Abba ko za ayi maka Allura ne?

“Zanje ne sai Gobe in Sha Allah…

“A a Abba bari na Kira ilyas Mai kyamis sai yazo yayi maka…

Ya fice da sauri sai ga shi tare da Mai kyamis din Wanda ya duba shi Yana tambayar ishaq Abinda yake ji . Ya fada mishi zazzabi ne da ciwon Kai…

“A bashi Wani ya ci sai ayi Mishi Allura.

Cewar Ilyas Mai kyamis

Sagir ya fita ya samo mishi Madarar yuoght Mai sanyi ya kawo mishi yasha akayi mishi Allura tare da magani.

Sagir ne ya biya ilyas Mai kyamis kudin sa ya fice.

Hawaye ya kawo fuskar ishaq Wanda shi kadai yasan Dalilin su.

Sagir ya Soma share mishi Yana Fadin.

“Ka yi hak’uri Abba ban San Abinda yasa ka Hawayen Nan ba Amma kayi hak’uri komai daga Allah yake kuma Yana sani akan Komai.

Ya Rik’e Hannun sagir Yana Fadin, “Sagir Allah ta ala yayi maka daukaka Mai Albarka ko Bana Raye sanoda Kai yaro ne Mai Albarka. Ina kuka ne don Jin Dadin da Ubangiji ya bani Kai gashi Kuma haihuwa tayi Ranar ta . Ban samu ko Naira ba a yau Kai komai ma banci ba sagir sai gashi kayi min suturar da na Rasa Ubangiji yayiwa Rayuwar ka Albarka tare da dukkan Ya’yan musulmi.

“Ameen Ameen Abba Allah ta ala ya amsa yasa Kuma kana Raye ne Zanyi wannan Albarkar don ka Kara tabbatar da haihuwa tayi Albarka…

“Kayya dai sagir bana tunanin Hakan Amma dai bawa Bai Tara sani da Allah ba Ina fatan hakan in Kuma Bai nufi na Gani ba Allah ya tsare ka ya Kuma kare ka ya baka dukkan Alherin da yake cikin DUNIYA da LAHIRA yayiwa ZURIAr ka Albarka fiye da zaton ka yasa su ji kanka fiye da Wanda kayi mini.

“Ameen Ameen Abba Amma in Sha Allah zaka Gani.

Ya juya Yana tuna Bak’in cikin da wasila ke shayar da shi ba zai barshi yayi tsayin kwanan da zaiga fatan shi akan sagir ba. Amma Yana tuna komai Yana Rubuce a kaddarar bawa babu Kuma Wanda ya Tara sani da Allah sai yayi istigifari.

Kafin magaruba jikin ishaq yayi sauki har ya fita sallar magaruba. Sagir ne ya siyo musu taliya da manja har da shi ishaq din don haka ita suka ci sagir ya fice makarantar dare da yake daukar littatafan shi ya tafi daukar karatu.

Koda aka gama sallar Isha I da ishaq Kai tsaye ya wuce bakin sauki venture tamkar Wanda aka ja haka ya Isa Yana Jan tunga da son yaga shin motar da ta aje wasila itace zata maido ta ko kuwa?

Yana zaune Yana sakawa da kwancewa har Tara da Rabi kafin hasken ya shigo Bakin sauki ya Kuma Kalli motar ya ga tana fakawa gefe sai kawai yaga wasila tana fitowa ta kuma wuce abunta don batayi zaton samun shi a wurin ba.

Ya jima a wurin kafin ya Mike ya nufi Gida inda zee zee ta iske shi D’akin shi da kirjin zaka tana ta cizga tana Fadin.

“Abba kaji Abinda mama tace? Ya Dubi yarinyar Yana Fadin, “Ina kika samu Nama haka ?

“Mama tazo dashi Mai yawa shine tace kar mu sake mu fito da shi mu Zauna a d’aki mu cinye ni Kuma na kawo maka wannan.

Ta fada tana Kai Naman a bakin shi yayi Maza ya kauce yace, “Ba tace kar ku fito ba Zainab kika fito? Maza ki koma kar na kara jin tace kar kiyi Abu kinyi.

Ta wuce da sauri ta fice yabi bayan ta da kallo Yana jin zuciyar shi na fada mishi hanyar da wasila ke bi Amma ya kasa yarda ya karbi wannan zargin.

Haka ya zuba wa wasila ido Bai taba nuna Mata ya Ganta a motar ba Kuma Bai nufi yin maganar ba Abinda dai ya sani kawai Allah ne zai Bude mishi kofar da take kulle ya Kuma yaye hijabai.

Wasila kuwa da take Jin a yanzu Kam taci ta gyargyare Domin kuwa ta Gano kaddara na tare da ita Amma Bata San yadda zata siyar ba sai a wannan lokacin? Hakika Mai gemu ya nuna Mata ba kowane Namiji bane ya iya soyayya Kuma ya nuna Mata zahirin soyayya. Ga kuma kudin da ya sauke Mata har kwarya Biyu. Milyon Biyu Abu kamar wasa take ganin wai milyon Biyu a account din ta.

Ba kudin ne Abinda yafi burge ta ba irin Mai gemu da soyayyar shi Mai tsayawa a Rai wacce ta cancanci kowace irin sadaukarwa a gare ta don shi Kam ta Soma tunanin mallakar shi ko da Kuwa zata Rabu da wancan karfen kafar wato ishaq.

Abinda wasila ta manta shine Bata hau Wani matakin kariya ba saboda Gudun tsautsayi na daukar ciki . Don haka a wannan takin ta ki yarda Mai Naira ya Ganta Domin kuwa baya burge ta a komai Mai gemu ne Sabon yayi a zuciyar ta a yanzu Wanda yafi kowa iyawa a cikin kowan kuwa har da Mijin ta na Aure da kuma Wanda ya Soma Bude mata ido a harkar wato Mai Naira.

Shi Kam Mai gemu yadda ya samu wasilar sai yaga Mai naira ya rage Mata qeality da yawa akan yadda ya Samu. Duk maitar shi ga mata Bai taba samun wacce tayi mishi kamar yadda wasila tayi mishi ba . Don haka Bai iya Rufe kwanaki Biyu Bai nemi wasila ba ita kuma da ya kira ta duk uzurin ta zata ajiye shi gefe guda ta bi shi.

A yau Kam wata matsiyaciyar mota wasila ta Gani sabuwa dal Mai gemu ya danka mata key din motar Yana fadin.

“Ga mota Haj kamar ke ace Baki mallaki mota ba? Ai kuwa ni nafi kowa Jin kunya ace Baki da mota in ma wannan batayi Miki ba zan sauya Miki da wata.

Wasila da murna ta kashe ta bata san lokacin da ta Rungume Mai gemu tana bashi Hot kiss a gefen fuska ba.

Ya kuwa Rik’e fuskar ta Yana mayar da martani.

Sati takwas daidai da killewar su da Mai gemu ta tashi da wani Al Amari Wanda bata bukatar a fada Mata ciki ne da ita Amma sai da ta dire a gaban likita Wanda ya tabbatar Mata da Hakan.

Al Amarin da yayi matukar tayar Mata da Hankali ya Kuma firgita ta matuka Gaya.

“Bana bukatar shi a tare Dani Dr Ina son yadda za ayi a fidda min shi.

“Eh to gaskiya sai dai Bama irin wannan Aikin a Nan duba marasa lafiya muke da bayar da taimakon ga mara lafiya Amma Bama kisan Kai.

Wasila ta Mike ta fice inda ta nufi okmos wata Asibiti da suka kware da Zubar da ciki inda aka auna ta aka Gane satikan cikin Wanda magani kawai za a Bata don haka aka Bata kwayoyin magani Wanda zata Sha guda Biyu kafin cikar awa biyu zata zubar da shi.

Ta dawo gida tana afa kwaya biyar a maimakon biyu da aka ce . Ta hau da Ruwa ta kora.

Ai kuwa Bata Rufe minti Biyar da Sha ba ta Soma ciwon ciki mai kama da mutuwa.

Tana d’aki su yusra Kuma suna makaranta ishaq kuma Yana shago don haka ita kadai ce a Gidan Babu mataimaki sai Allah don haka ta dandana kudar ta matuka Gaya ciwo kamar na mutuwa tana ta murkususu a gado har zuwa yamma kafin ta samu relief Amma maimakon taga jini ko fitar tayi Amma ko jini dis Bata Gani ba.

Sai ta saurara Amma har aka kwana Bata Kuma Ganin wata Alama da ta nuna Mata cikin ya fita ba.

Bata kuma Shan Maganin ba Gudun kar ta Sha ta ZARCE barzahu Amma Kuma cike take da fargaba don ta tabbatar da fitar wannan cikin shine tonon Asiri gareta.

Don haka ta kashe wayar ta don sawun giwa ne ya take na rakumi Babu Abinda take so a yanzu irin fitar cikin don haka ta koma okmos aka duba ta aka ga ciki na Nan daram Bai fita ta Kuma Fadi adadin maganin da tasha guda Biyar Amma Bai fita ba.

Mamaki ya kama likitan Wanda ya San ko Guda aka Sha sai ciki ya fita Amma ga wata ta Sha Biyar Bai fita ba.

“To sai dai kiyi Hak’uri ya kara sati uku zuwa sati shida sai a fidda Miki shi.

“A a ba zai yuwu ba Dr ba zan iya barin cikin Nan a jiki na ba har Wani Lokacin don matukar Yana tare da ni to tashin hankali ne kwance a gareni koma nace tonon Asiri.

<< Tana Kasa Tana Dabo 13Tana Kasa Tana Dabo 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×