Skip to content
Part 15 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

“A Yanzu dai gaskiya ba Zai yuwu a kafa Miki injin ba in akayi Hakan Zaki iya samun matsala da mahaifar ki Amma in cikin ya Kara kwari sai a fidda Miki shi Amma bari na sauya Miki Wani maganin ki jarraba shi mu Gani Amma na Sha Mamaki ace kin Sha har kwaya biyar Amma ko jini Baki gani ba Lallai jinin ki Yana da karfi gaskiya.

Wasila ta Zubawa bakin likitan Da yake Mata bayani ido Amma Sam Bata ji ta gamsu da wannan Bayanin ba ta Yaya Rabon ta da Zuwa turakar Miki fin shekara sai Dare Daya a Ganta tana Laulayi? Ai Asirin ta ya To ni ya gama. “Yanzu Dr Babu wani Abu da za ayi Dole sai an Kai wannan lokacin?

“Hakan dai zaifi Miki sauki ne ana iya finciko shi daga mahaifar sai dai ana yawan samun matsala ne idan baiyi kwari ba. Idan yayi kwari yafi saukin fiddawa don mu Nan Asibitin har cikin wata Tara Muna iya fiddawa Amma Wanda kwanakin sa Basu da yawa Yana da matukar hatsarin gaske don sau da yawa akan Rasa Rai ne wurin fidda irin shi don haka ne ma yasa ba a Yi sai ya Kai sati goma Sha shida ko Ashirin…

“Kar ki damu in Sha Allah da ya Kai wannan satikan lafiya Lau za a fidda shi ko da Kuwa ya Kai wata Tara.

Dole wasila ta Hak’ura ta sake karbo wasu kwayoyin tazo gida ta ambama Suma dai sai Ciwon da ta samu Amma ko dis na jini Bata Gani ba bare ta yarda ciki ya fita.

Wayar ta a kashe yayin da manyan Mazan da suka sabgartu da shashanci da ita Sukayi matukar takura saboda Rashin samun wayar ta ita Kuma tana Ganin a yanzu Bata da sukunin kula su tunda ta jawowa kanta Aikin da ya dame ta.

Gashi Kuma Bata yarda sun San gidan ta ba sai dai tayi mahada da su a sauki venture don haka duk nacin Mai Naira da me gemu suka kasa samo ta musamman Mai gemu Wanda yafi Mai Naira maita akan ta kullum sai ya Kira wayar ta Amma a kashe.

Kafin cikar kwanakin da take Jira Takoma Asibiti laulayi Mai tsanani ya Rufe ta Wanda ko Ruwa ta Sha sai ya dawo . Kan kace me? Ta kwanta jinya Sosai Abinda ya nunawa ishaq cewa lallai Dole ya yarda da Abinda zuciyar shi take Raya Mishi matar tashi Maza take bi tunda ya San ta da Laulayi yayin ciki baya Mata da kyau . Ciki Hudu tayi a gidan shi Amma Babu Wanda tayi shi da Sauki. Sai gashi yanzu da shi kanshi ba zai iya Cewa ga tsayin Lokacin da ya dauka Rabon shi da ita ba Kuma wai tana Laulayi…

Ya Kadu matuka Gaya da ganin irin Aman da wasila take shakawa Wanda ko Ruwa ta Sha sai ya dawo in ba yuoght ba Babu Abinda ke iya zama a cikin ta.

Ya tsura Mata ido har ta Kadu da Kallon shi ta juyar da kanta gefe

“Tashi muje Asibiti..

Ta juyo a guje tana kallon shi Jin yace wai suje Asibiti…

“Babu inda zanje Ina gida ma sai Allah ya kawo min sauki Asibiti suna bayar da lafiya ne?

“Wallahi sai kin tashi mun tafi wasila ba zan barki da ciwo a gida ba.

Ta Mike zaune tana kallon shi da Jin karfin Halinsa.

“Sai dai ko ka tsinke igiyar Auren ka malam Amma Wallahi Babu inda zanje yaushe kayi bajintar iya ciyar da gidan ka sau UKU a Rana da har kake dukan kirjin dawainiyar Asibiti da takalifi?

“To ni da ke zan ga Wanda zaiyi kaffara Amma Wallahi sai munje Asibitin Nan

Ya fita waje tabi shi da kallo inda Wani tashin hankalin ya ke sakadar ta me mutumin Nan yake nufi da sai sunje Asibiti?

Ya Gano Abinda kike lullube mishi be shiyasa yake son kama ki ta hanyar zuwa Asibiti don a fada mishi ciki ne da ke yaji dadin watsa ki?

Ta shiga Neman mafita akan wannan mutumin da yake Neman nuna Mata iko.

Minti Sha Biyar da fitar ishaq ya dawo gidan tare da Goggo wacce suka shigo Gidan a tare tana fadin
“Ai Kai dai ka barni da yarinyar Nan Wallahi tallahi na kusa cewa kurunkus kan Dan Bera akan ta don ba ita kadai na Haifa ba bare ta Wahalar Dani ko ita kadai ce Dani zan Hak’ura tunda ba Ruhin mu daya ba.

Wasila ta fito tana yiwa Goggo barka da Zuwa.

“Kar fa kice Zaki min lab lab irin na munafunci Amma Baki iya yiwa mijin ki ladabi ? To me kike nufi da yace a tafi Asibiti kika ce ba Zaki je ba? To ni nace kiyi musu da shi ne? To Maza ki dauko mayafin ki mu tafi Wallahi in Kuma ba haka yanzu kiga Abinda zai faru.

“Nifa lafiya ta kalau Goggo zafi ne ya taso min in dai ba sharri yake nema na dashi ba.

“In ya neme ki da Sharrin Bai Isa bane? To in dai Babu munafunci a cikin Lamarin ki fito Muje.

Dole ta dauko mayafin ta Suka wuce Asibiti inda bisa Dole ta yarda da dukkan Abinda likitan ya nema don auna ta inda awo ya fito ciki ya bayyana a tare da ita.

ISHAQ ya zuba Mata ido kafin ya dauko Goggo ya mayar da ita Gida ya baro wasila wacce take cikin matukar tashin hankali don ta San Yana can Yana fadawa Goggo duk abinda ke Nan . Tana zaune a Asibiti dama Abinda yake son kamata kenan ? Ya kuwa kamata don haka ko da ya sauke Goggo Bai koma Asibitin ba ya wuce gida Yana Jin zazzabi yana Rufe shi.

Ta dawo gidan jiki a Sanyaye tana Jin gara kawai ta Rabu da ishaq ta Rabu da Auren shi matukar tana son kwanciyar hankali Amma in ba haka ba kuwa zai jawo Mata JANHURUN masifa ne kawai.

Zaman d’aki ya kamata don Bata son ko hada ido da ishaq Wanda yake kwance Riris zazzabi ya Rufe shi Amma ba zazzabin ne damuwar shi ba irin ZUCIYAR shi da yake Jin tamkar Zata tsinke daga matsirar ta.

Sai da sagir ya dawo ya samu ishaq cikin Halin ciwo Dole ya Kira Mai kyamis Amma yace gaskiya su tafi Asibiti zai Fi.

Dole kuwa ya Nemo Napep suka nufi Asibiti ishaq bai san Wanda yake kanshi ba.

A emergency aka sauke ishaq Wanda ciwon zuciya ya kama Dole ya karbi taimakon gaggawa.

Sagir Wanda aka nemi kudin magani Amma kud’in da suke tare dashi ba su wuce Dubu biyu da d’ari biyar ba Dole ya koma garejin su wurin ogan su ya ranto kudi ya dawo aka siyi magani.

Kwanan ishaq uku a Asibiti aka sallame shi Suka dawo gida Amma wasila ko ya ka Kara ji bare sannu ta fatar Baki

Al Amarin ya Zame mishi gaba kura baya siyaki. Ya gaji da ganin wasila a gidan shi gara ya sallame ta ta matsa daga inda yake taje ta Wala yadda take so ta huta boye boye Shima ya huta da ganin Bak’in ciki bare zuciyar shi ta nemi bugawa.

Amma Kuma da wace fuskar zai Kalli Goggo da sagir idan ya saki wasila? Akwai Nauyi Mai yawa da yake ji na Goggo haka ma sagir Yana kunyar yaron ya San ba zaiji Dadi ba.

Ya jima a gida baya fita sai dai sagir ne ke ta daukar takalifi gidan yaron akwai himma da zuciya shiyasa yake tausayin shi yaro ne Amma Mai tunanin irin na manya.

Sai da yayi sati Biyu kafin ya warware ya Soma fita Aiki duk da har yanzun shi da wasila sai dai ido wai bebiya ta Auri makadi.

Lokacin da likitan ya Diba Mata yayi ta fice Asibiti don a burke Mata cikin Nan ko don ta fita Daga tarkon da ishaq ya Dana Mata.

Ta Isa Asibitin ta biya kudin kayan Aikin da aka nema Daga gareta aka kuwa zurkuda Mata Allura kafin aka k’ak’aba Mata injin din a jiki da nufin fatattake Abinda yake cikin aka Kuma Yi nasarar Hakan Amma fa ta Ji jiki don da kyar ta iya Gane gida jiwa na dibar ta.

Sai dai me? Dare nayi jini ya balle Mata kafin safe ta Bata zani biyar da jini Abinda yayi matukar tayar Mata da Hankali . Kafin safe ma ta sume inda yusra ce ta ga Halin da Uwar tasu take ciki ta sheko Aguje ta fada mishi.

Ya Isa d’akin yaga yadda jini yake bin kafafun wasila dole ya je ya dauko Goggo suka nufi Asibiti.

Abinda yayi matukar basu mamaki shine Bayanin likitan Wanda ya samu shawo kan matsalar Zubar Jinin yadda likitan yace musu zubar da ciki tayi shine aka Samu matsala aka tab’a mahaifar ta wacce itace Silar Zubar Jinin.

Goggo tana kame da Baki ta kasa cewa uffan sai kallon wasila da ke kwance tana baccin Wahala take
Shi kuwa ishaq Bai iya tankawa ba sai ma cewa Goggo yayi zaije shago ya dawo.

Ta samu da kyar tace sai ya Dawo . Don ta Ji wata irin kunyar ishaq din don ma Allah yayi mishi kawaici Amma ace mace ta Zubar Maka da ciki wannan ai ya Kai karshen kiyayya.

Sai la asar wasila ta farko taga Goggo da ta zuba Uban tagumi ta Kuma ga inda take wato Asibiti don ita dai a D’akin ta tasan ta kwana abinda kawai ta Rik’e shine jini ya balle Mata Amma gata a Asibiti wata Kil ma ta bayyana kowa yaji.

Goggo Bata lura da farkawar wasila ba saboda har ga Allah hankalin ta ya tafi akan meye Dalilin zubar da cikin da tayi? Me yasa? Ko kuwa don tana ganin yanzu ishaq bashi da Abunda take ganin zata Tara ZURIA dashi?

Sagir ya turo kofar D’akin ya shigo don ya dawo gareji yusra ke fada mishi mama Bata da lafiya har Goggo tazo sun tafi Asibiti.

A rude sagir ya cire kayan Aikin shi ya nufi Asibitin.

Goggo ta dago kanta taga shigowar sagir ta amsa sallamar shi tana fadin, “Har an taso daga wurin Bak’in man ne Halan? Kai kam matar ka zatayi juriyar wankin Bakin Mai . mutum kullum cikin Bakin Mai yake.

“Kece wacce Zaki fara wankin Bakin man Nan Goggo, Ya fada Yana nufar gadon wasila da ta ke sauraren su.

“Sannu mama Ashe jiki baiyi Dadi ba? Yanzu nazo yusra take fada min Kuna Asibiti.

Goggo ta juyo tana fadin,”Au kin farka ne Dama Yar banza Mai Bak’in Halin tsiya? To dama Jira nake ki farka likita yace ciki ne kika zubar Wanda aka Samu matsala shin dama Abinda kike shiryawa kenan?

Saboda kina Ganin ishaq bashi da komai kika kashe mishi Dan shi saboda Halin tsiya? To bari na fada Miki wasila wallahi na gaji da Halin ki zan cewa ishaq ya sallame ki kawai ya huta don na tabbata idan Yana tare Dake Bak’in cikin ki Yana iya kashe shi to In dai zan bashi shawara ya karba Wallahi ya Rabu Dake don ke kam ba macen Arziki bace….

“Wallahi Goggo ni dama zaiyi hakan da ya fiye min don tuni dama nake son ya sauwake min Auren shi Amma ya kasa Ganewa Aure ace miji baya iya ciyar da gidan shi komai sai na kama.

Sagir ya zuba Mata ido Yana Jin Abinda ke faruwa.

Musamman Amsar da ta bawa Goggon na gara ishaq ya sauwake mata Auren shi da Kuma Zubar da cikin da ya tsinta a yanzu tini ya hada biyar da uku suka bashi takwas.

Gaban shi yaci gaba da Sarawa inda Goggo Kuma take kuka tana Fadin.

“Haka kika ce? Amma kuwa ke butulu ce to tunda ma haka kika ce in Sha Allah in dai ke ba autar mata bace ishaq ya barki bari Kuma na har Abada. Ni Kuma da na zama abokiyar mayar da martani a gareki na barki da Allah kiyi duk yadda kike so.

Wasila ta kasa cewa uffan inda sagir yake kallon ta Yana Fadin, “Wai mama kece kika zubar da cikin? Goggo ce fa a gaban ki kike fadawa magana? Sai ya fashe da kuka Yana Rik’e kanshi.

“Kyale ta sagir kar wannan ya Dame ka ai babu komai ba ta Haifa ba itama ?ai Kuma shikenan tunda ta Haifa.

“Ki yi Hak’uri don Allah Goggo kar kiyi Mata Baki . Ya’yan da ta Haifa Yan Uwa na ne idan aka jarrabe ta dasu ni aka jarraba don Allah don ANNABI ki yafe Mata.

“Na yafe sagir ko don Kai din da Yan Uwan ka hakika Kai aka jarraba Kam idan aka sauke Mata Abinda tayi akan Ya’yan ta Allah ya tsare ku ya nuna Mata iyakar ta akaran kanta…

Ya Mike Yana Fadin.

“Mama ki Roki Goggo gafara ta yafe Miki Wallahi ba Zaki taba Ganin daidai ba matukar tace Miki Allah wadai. Duk Mai kaunar ki Kuma Dole zai fada Miki gaskiya. Yaya Zakiji idan yusra ko Zainab Taki Yi Miki biyayya? Gaskiya mama kina kuskure da yawa.

“Rabu da ita sagir bana ko shakka wasila ta dauko wata hanya ne tunda har ta iya mayar min da magana…

Wasila ta tashi Zaune tana fadin, “Ki yi hak’uri Goggo nifa dama na Gaji da Auren Nan Wallahi sai Kuma naji kince ya sauwake mini shine nace Miki Nima nafi son Hakan.

“Gaskiya mama in Wani yake zuga ki kina yin kuskure Goggo ce fa?

Sagir ya fada Yana tashi ya bar Asibitin Yana dauke kwallar idon shi .

A Bakin kofa sukayi kicibus da ishaq ya dawo Wanda yace da sagir ya dawo saboda ganin kwallar sa…

Ya zauna Yana gaishe da goggo Yana tambayar Mai jiki?

“Ai Mai jiki gata Nan ishaq ta farka don haka zan tambaye ka ta nemi izinin wannan wulakancin da tayi Maka na Zubar Maka da ciki ? To in har Amsar itace a a sai nace duk Hukuncin da Zakiyi ISHAQ ba zanga laifin ka ba Kuma ko da na Rabuwa da ita ne…

“A a Goggo Bata Nemi izini na ba Kuma wasila ta zama ni na zama ita ba zan iya cin mutuncin ta ba ko don sagir da yusra da Zainab Amma Dukkan Abinda take ji ko takeyi Goggo yazo idona da kunnuwa na Kuma Ina sane da komai Amma ba barta da ALLAH akwai lokaci Kuma Ina Jin nauyin ki Goggo ba zan iya Rubuta saki ga Ahalin ki ba ko Babu komai za a ci Alfarmar ki don haka kisan kai ne tayi Kuma ita da Ubangiji Wanda zata bawa bayanin manufar ta Amma ni Daga gareni Goggo komai ya Wuce.

Goggo ta Mike tana Fadin, “Allah ta ala ya kawo maka mafita ta Alheri ISHAQ ya Dubi zaluncin da matar ka tayi Maka yayi maka kyakkyawan zabi Wanda zai shafe maka Bak’in cikin da aka shayar da Kai. Ni Kam Ina jin kunyar ka bani Kuma da Bakin baka Hak’uri Amma in Sha Allah Ina da zafin yawun Yi maka Addua.

“Nagode Sosai Goggo Allah ta ala ya amsa Adduar ki Sosai Nagode.

Goggo ta kama hanyar fita tana fadin, “Ni Kam Nayi gida tunda marar lafiya ta iya kera Rashin mutunci a gadon Asibiti zaman me Kuma Zanyi?

ISHAQ ya bi bayan ta Yana mata Rakiya har ya tsayar Mata da Napep ta wuce.

Wasila tana Zaune akan Gadon masifa na cinta ishaq ya dawo, Ta sauko daga Kan gadon ta kuwa cacumo Rigar shi tana Fadin.

“Idan dai ka haihu a cikin Uwar ka da Uban ka ka sauwake min Auren ka don ba gaji da zama da Kai Wallahi.

Sagir ya Mike Yana Fadin, “Mama akan idona? Mama me yake faruwa da ke ?

“Kai in ka Kuma Yi min magana Wallahi zanci Uban Uban ka kaji? Kun gama hada ni da mahaifiya ta Kuna min Wani lab lab lab? To a gaban ka sai meye? Ka bashi Baki Mana ya sauwake min Auren shi don na gaji da zama da shi.

ISHAQ yayi murmushi Yana Fadin, “Ban iya yadda Ake sakin Aure ba sai dai ki bari har na koyo shi don ni Kam Ina kiyaye halal na Kuma kiyaye Haram don Haka ki sani Baki ba zai iya furucin wannan kalmar ba sai dai kina da zabi ke da kanki Amma ni ai na zuba Miki ido sai yadda kike so.

Ya finciki hannun ta Daga Rigar shi ya wuce sagir ya biyo bayan shi Suka bar wasila cike da Bak’in ciki Domin kuwa borin kunya take Kuma ta Gane a tsiraice ISHAQ yake kallon ta tun daga maganar cikin har zubarwar da tayi.

Babu Wanda ya kuma leko ta Asibitin har washe gari aka sallame ta ta Soma canki canker akan inda zata nufa tsakanin gidan ISHAQ da Kuma gidan Goggo. Gidan ishaq shi ya Fi Mata sauki don haka ta nufi Can zuciyar ta na Raya Mata yanzu ne zata ci ganye Wanda take lullube wa ko don ISHAQ ya gaji ya furta Mata kalmar sakin da zata tafi ta wataya yadda take so Kuma ta samu kudaden ta.

<< Tana Kasa Tana Dabo 14Tana Kasa Tana Dabo 16 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.