Skip to content
Part 17 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

“Na sake ki… Na sake ki Farida Wallahi na sake ki tunda kinfi son kiga gawa ta a Duniya. Ashe da gaske ZUCIYA ta take da ta kasa yarda da Aminta Da ke sai gashi.

Farida da take juya Kai tana son Rufe mishi Baki Akan JANHURUN masifar da yake shirin janyo musu sai dai tuni ta makara.

“SAMEER ! Ta fada da k’arfi tana kame kanta Shima sai a sannan ya kula da Abinda yayi sai Kuma yayi sak!..

Haj da ta bi bayan Farida da kallo Jin ta ambaci kalmar Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un Kuma ta ga ta wuce da sauri sai abin ya daure Mata Kai har Isa Direba yaja motar Haj tace mishi

“Isa koma baya naje Naga lafiya Farida take wannan ta awizin? Naga kidima da Rudani s tare da ita in na barta ban San abin da takewa tsoro da shakka ba.

Isa ya juya kan motar suka juyo Haj ta balle murfin motar ta fito ta nufi cikin Gidan inda ta Soma jiyo k’arar Farida inda tsoro Mai tsanani ya kamata to waye haka? Ta San dai Sameer baya gari Kuma ba week End bane bare tayi zaton ko ya zo din.

Tana shiga ta hango Sameer Wanda ya shake Farida Yana fadin “Na sake ki Farida Wallahi na sake ki…

Wani irin matsiyacin Mari Haj ta kifa mishi ta sake kifa mishi Wani kafin ya saki Farida Yana Duban Haj da idanu a juye tamkar Wanda ya kora kayan maye.

“Shikenan ka kawo karshen komai da kanka. Ina Hankalin ka Yake ne? Me yasa ka kasa fin k’arfin zuciyar ka har shaidan ya Rinjaye ka? To ka Ida sa tsinke igiyar Auren ka sai ka hutawa zuciyar ka da zargi dama karshen alewa kenan k’asa Kuma duk Mai yawaita zargi irin naka karshen sa nadama gata Kuma Kayi baka ma Soma ba tukuna.

Ya zube Yana son fidda HAWAYE Amma ya kasa Amma sai da ya kwaso kayan Nan da ya Gani singileti da shotniker Yana Fadin.

“Haj Dubi Kayan Wani Kato a gida na fa? Kuma na Kira wayar ta a kashe na Kuma dawo gida ban sanar mata ba saboda Ina da hujjojin da suka sa nake zargin ta Amma sai na Samu Bata gida Kuma tun Rana na dawo Amma sai yanzu ta dawo Haj? Bata fada min zata fita ba ni Kuma don na kama ta akan yawan Abinda zuciya ta take Raya min akan ta sai gashi naga hakan Anya Haj yarinyar Nan ba fitar take in Bana gari ba? Haj kin yarda ba zargin ta nake ba? Akwai Abinda na Gani in ma nayi zargin?

“Ya Isa haka Sameer! Haj ta katsee shi.

“Ka yi bincike ne kaji dalilin fitar ta ne da ka yanke Mata wannan danyen Hukuncin? Me yasa muguwar zuciyar ka take Raya Maka Abinda baka baje shi a faifai ka dauki Mai kyau ka watsar da na banzar ba a matsayin ka na mutum ba Dabba ba? Ina amfanin hankalin ka in har kana da shi? Daga zato kawai sai tabbaccin zaton ka? Me yasa bakayi Mata uzurin Jin ta Bakin ta ba?

“Haj kayan wani kato fa nake fada Miki a gida na Kuma ta fita Bata sanar Dani ba sai yanzu ta dawo Kuma zo ki ga Gadon ta yadda aka yamutse shi Alamar an Tatss!

Haj ta wanke shi da Mari kafin ta Rufe shi da duka tana kuka tana Fadin, “Kai kam Allah ya wadaran Halin ka Sameer. Na Rasa inda ka Samo wannan matsiyaciyar zuciyar ka take wacce ta ke Jin Dadi zargin matar Auren ka . Anya kana iya yiwa na kasan ka Adalci kuwa? Mutumin da Bai yiwa Kansa Adalci ba yaushe zaiyiwa na kasa da shi ? To kayiwa kanka ni Kam na tausaya Maka don na San ba zaka Kuma Samun kwatankwacin Farida ba Kai da ita Kuma haihata haihata tunda ka tsinke igiyar da tayi muku Saura.

Haj ta fada tana zama tana kuka kukan takaici da Bak’in ciki ta dafe kanta da wannan bak’in cikin na Sameer.

Farida ta Mike cike da wani matsiyacin Bak’in ciki da tana kuka ba kukan dukan da Sameer yayi Mata sai kukan sauran igiyar Auren su da ya tsinke wacce ta tabbatar da wani garari ne zai same su don ita da Sameer Kam an jarrabe su jarrabar da suka tabbatar da ita zasu tafi LAHIRA kafin kuma su tafi LAHIRAR zasu Sha wuya a Duniya.

Ta Isa inda kayan suke Wanda Sameer ya watsar a tsakar falon ta Kai Hannu ta dauka inda ta tuna Dalilin shigowar kayan da Abinda ya kawo su sai ta kuma fashewa da kuka tana Fadin.

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un bashariyya Ashe kaddara ce ta Saka ki.

Haj ta dago tana fadin, “Tashi mu tafi Farida ai Kuma zaman ku ya Haram ta tunda yayi ta yanke ta gundule in ya so ya Rubuta ya kawo ko Kuma ya Rik’e tunda ya zama shaidani Mai yarda da hudubar zuciya.

Jin wannan maganar ta Haj yasa Sameer ya Mike a Rikice Yana Fadin. “Kuje Ina Haj ? Don Allah Kar ki fadawa kowa wannan maganar na janye magana ta Wallahi na janye.

“Yadda kake kowa ma haka yake? Ai kuwa Kai kaga shaidani da idon ka tunda gashi ya zuga ka kayi Abinda ya Soma damun ka don Haka na Godewa Allah da yasa akayi Hakan akan ido na da bangani ba haka zaka ajiye ta Kuma zaman Zina? Kai kam kaji haushi Wallahi Kuma a yau Farida ta gama kwana a gidan ka tunda Babu Kira me zaici gawayi?

Matar tayi sallama ta shigo inda Farida ta Dube ta Amma haushin ta ya cika Farida har ta kasa cewa komai.

Ta Gaishe da su haj da Sameer Wanda yake kallon ta kafin ta dubi Farida tana Fadin

“Maman Saddam nayi ta zuwa daukar kayan nan Amma na samu Gidan a Rufe sai yanzu aka gyara Mana wutar shine nazo dauka na gode.

Ta fada tana karbar kayan mijin nata daga hannun Farida wacce tayi kaico da Bak’in cikin shigowar kayan a gidan ta Wanda sune maassasin kashe Mata Aure da jefa ta a garari da ta Sani da Bata yarda da Gaisawar da suka fara da bashariyya wacce take ganin makotaka ce ta shardanta girmama makota ka.

Farida da idonta ke tsiyayar hawaye ta mikawa bashariyya kayan mijin ta ta fice inda hankalin bashariyya yayi matukar tashi don ganin hawaye a fuskar wannan Mata Mai fara a da faram faram baccin da taga Mai gidan da wata Mata da sai ta tambayi damuwar maman Saddam din.

Fitar bashariyya ya bawa Farida Damar rera kukan ta Wanda take jin gara mutuwa da wannan Al Amarin wanda ta tabbatar da dab take da mutuwar.

Haj ta Dube ta tana fadin, “Kayan waye wannan Farida?

Ta dago kanta tana share HAWAYE tana Fadin, “Haj makociya ta ce dazu da safe ta shigo ta ce zata Goge kayan Mijin ta su an yanke musu wuta . Tana cikin gudar ne aka dauke wuta shine ta bar sauran Wanda Bata Goge ba akan sai an dawo da wuta zata zo ta goge . Wallahi na manta da kayan Nan da na San zai gansu da ban yarda ta ajiye min su ba Amma.

Sameer ya Mike Yana Jin wani Abu Yana Shirin fincike mishi zuciya daga matsirar ta.

“Shiyasa bincike yake da kyau da ya tambaye ki da yaji Sabanin zaton shi In ma Bai tambaya ba akan idon shi zata zo karbar kayan mijin ta.

“Na jima Haj Ina fada mishi Hakan kafin ya yanke mini Hukunci ya Fara bincike tukuna Amma baya yin Hakan . Kuma inda naje da yake son cewa na bar gida Kuma na kashe waya ko da muka je gidan makokin nan Haj naga yadda su Hajara suke kuka ya sa na kashe wayar Amma kinji ya kawowa Ranshi na shirya Rashin gaskiya na kashe waya Kuma ga kayan namiji ya gani to Haj a fada mishi inda naje don ya tabbatar da shine ya Kalli Abinda yake kallo a munafunci ni Kam Nayi kuskuren da ba zan maimaita kamar shi ba Ina ma Ina da Amon sautin da zan fadawa Yan Mata suji ? Allah ya sani banyi Abinda nayi don son kaina ba sai don na faranta ran Sameer Ashe ban sani ba shine kuskure mafi Muni a Rayuwa ta . Allah Kar ka bari wata Diya mace ta kuma irin kuskuren da nayi.

“Haj ta Dube shi tana fadin “To kaji Abinda kayiwa kallon ha inci? Kuma inda kake maganar ta tafi sai dare ta dawo Muna tare da ita can gidan makokin baba iro da Allah yayiwa Rasuwa ni na Kira wayar ka amma ban same ka ba Kuma nice nace da Farida ta tafi tayi ta azziya nice na Bata izinin fita batayi gaban kanta ba.

Ya Zubawa Bakin Haj ido da take mishi bayanin Abinda ya kalla s Baibai yayin da wata irin nadama Mai tsanani ta baibaye shi.

Ya zube a Gaban Farida Yana Rik’e Hannun ta Yana Fadin, “Don Allah kiyi min Afuwa Farida Wallahi ban San Hakan ba da ban furta kalmar Nan ba. Don Allah na janye kalmar Nan Allah ma ya San a fusace nayi furucin…

Ya juyo ga haj Yana fadin, “Allah ya sani Haj da fushi nayi furucin Nan to ki Rufa mini Asiri na janye sakin Nan Haj igiya Daya ce tayi saura idan na Rasa Farida Duniya ta shiga matsala…

“Sai dai kuwa ka Rungumi Duniyar ka matsalar ta Domin kuwa nafi tsoron Allah da kowa . Me kake nufi da na Rufa maka Asiri? In barku kuyi zaman Zina kenan ? Ka taba Jin inda aka bayar da fatawar sakin da akayi cikin fishi da Wanda akayi cikin dadin Rai? Dama shi sakin har da wani na fushi ne ? To fada min Wanda akeyi cikin FARIN CIKI? Kai ka shiga hankalin ka Dani bana son harkar jahilci yau ga maganar baba iro ta bayyana a Kuma Ranar da ya bar Duniya. Yasha fada Maka matukar bakayiwa zuciyar ka linzami ba to zata kayar da Kai ne a inda Babu Mai tayar da Kai gashi Kuma a yau ta kayar da Kai inda Babu Mai tayar da Kai don Haka ko Bana Raye ba zaka sake zama da Farida ba tunda ka yarda shaidan ya Raba ka da ita kishi Kuma baka fara shi ba don in kishi kake to ka shirya mutuwa Ranar da ka tabbatar da wani ne ya Auri Farida zaka ce na fada maka da can ba kishi kake ba sai Ranar da ka Gane Wani ya mallaki Abinda kakewa kishin . Ka Kuma San ko da Farida zata dawo gareka sai taje Hannun Wani Mijin ko zata halasta a gareka sai ka shirya mutuwa ta Silar kishin ka Amma kamar yadda ANNABI ya haramta ga wuta haka Farida ta haramta a gareka….

Wani irin tsini da yaji ya soki zuciyar shi har Yana Jin tamkar an yiwa zuciyar tashi illa ya dafe gurbin zuciyar Yana fidda kwalla Amma ya kasa cewa komai inda Farida ta Mike ta ja mayafin ta tana shirin ficewa Saddam da Hanan suka bi ta a baya Haj ma ta Mike tabi ta a baya suka fice inda Haj tace Farida ba zata je gidan su ba gidan ta zataje don tana kunyar Hajiyar Farida ace an saki Faridar…

Ba haka Farida taso ba taso kawai a Barta ta wuce gidan su don in tana Gidan su Sameer to zai Rik’a zuwa ne Yana Ganin ta Amma in a gidan su take ba zai Samu wannan zarafin ba Amma Kuma ba zata iya yiwa Haj gardama ba Dole suka fice tare suka bar Sameer Wanda ya Kwana cikin ciwon zuciya Domin kuwa ya gama shiga tashin hankali har Ciwon zuciya na far mishi da safe Kuma ya lallaba zuwa Asibiti aka bashi magunguna ya dawo gida Yana jinya Yana Kuma tsinewa shaidan da zuciyar shi da suka assasa mishi wannan bak’in cikin.

Washe gari Haj zata koma Gidan makokin Amma Dole ta bar Farida a gida wacce ta kwana kuka da Tashin hankali, Ta daura alwala tana gabatar da sallar walha.

Ta sallame sallar kuka na keto Mata zuciya inda ta ja waya ta Kira hajiyar su wacce ta dauka taji farida na kuka…

“Me yake faruwa ne Kuma? Hajiya ta tambaye ta…

“Haj Sameer ya sake ni…

“Inna lillahi wa Inna ilaihir Raju un da akayi me Kuma Farida?.”

Ta Soma Rattaba wa Haj Abinda ya faru tun daga Rasuwar baba iro zuwan su Gidan makokin da ya dawo Bai same ta ba har zuwa dare da Kuma shigowar makociyar ta bashariyya wacce tazo Goge kayan Mijin ta aka dauke wuta ta barsu a gidan ya dawo ya gansu ya Kuma hada shaidan da zuciyar shi Wanda Suka bashi ifiritun da ya sabbaba mishi mutuwar Aure don ya dauka Wani Namiji ne yazo gidan nashi ya Kuma dauki matar tashi Zuwa zanen da ZUCIYAR shi tayi mishi har ya tsinke igiyar Daya cikin fushi da fita hayyaci…

“Ikon Allah Sameer baya yiwa kanshi Adalci yanzu irin wannan ke da Dadi? Sai ki taho gida tunda zama ya kare in dai ba Haram zaku yi ba?…

“Hajiyar shi ce tace Nazo gidan ta ni Kuma bana son gidan ne Haj Kuma Ina Jin nauyin ta

“Ai Kuma Al Amarin ya gama lalacewa Farida ta ko Ina dai maganar Guda ce ! Babu wani gyara ko kwaskwarima don haka da nan da can din duk Daya ne in dai ba wani gyaran Ake kokarin kawo Muku ba Amma dai gama ta gama Farida ni na San sai Sameer yazo Nan wurin matukar baiyiwa zuciyar shi linzami ba

“Ni Kam Haj zan taho gida ne don bana son ma yazo gidan ya same ni.

“To Farida ni Kam ai sai dai nayi Muku ADDU A Allah yasa hakan shine Alherin ku damu gabadaya.

Ta aje wayar tana mamakin Al Amarin Sameer. Farida kam ba zata iya zaman gidan su Sameer ba …

Saddam ya shigo D’akin yaga Farida tana kuka ya Rungume ta Yana Fadin.

“Daddy’ ne ya Kuma Dukan ki Mami ? Bana son shi fa tunda yace ba zai Kuma Dukan ki ba Kuma ya Kuma Wallahi bana son shi.

Ta Mike tana daukar Jakarta ta fito daga D’akin Haj ta samu Mai Aikin Haj tace Mata idan haj ta dawo tace Mata ta tafi Gida.

Sai da yamma Haj ta dawo Daga gidan makokin ta samu Farida ta bar Sakon ta tafi gidan su Abinda ya tayar Mata da Hankali don da kunya ace wa iyayen Farida Yar igiyar da ta Ragewa Farida Sameer ya tsunka ta Amma ya ta iya? Dole da safe ta nufi gidan su Farida inda tayi ta bawa Hajiyar Farida hakuri har da kukan ta Amma haj tace Babu komai fa kaddara ce Rabuwar Aure Kuma kowane bawa Yana tafe ne bisa Doron kaddarar sa ba zai tab’a zamewa ba har sai ya biye kaddarar sa da Bakin sa ko da zuciyar shi da gabban jikin shi . Wannan kalaman sune suka kwantar da hankalin Haj ta dawo Gida cike da Bak’in cikin mutuwar Auren Farida.

Kwanan Farida biyu da Dawowa gida ta Soma Ramewa daga tsaye don Bata iya cin Abinci Bata iya doguwar magana kullum tana d’aki ko tana kuka ko tana salla . Kallon Al Amarin su take KAMAR A MAFARKI wai sun Rabu ita da Sameer akan Wani Abu da Bai Isa ya zama Dalili ba Kai Lallai Mai zargi ba zai tab’a Zaman lafiya da Al Ummar da yake tare da su ba . Kuma Zaiyi ta kallon abubuwa da yawa wanda ba haka abin yake ba Sabanin zaton sa ne kamar dai yadda ta faru da su . Kan kace me ? Farida ta Kare daga tsaye inda ciwo ma ya sark’e ta ta kwanta jinya jinyar zuciya da Abinda ZUCIYAR take so wato SAMEER.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Kai lallai wannan Sameer ya jawo muku JANHURUN masifa gashi Nan zai kai ku LAHIRA baku Shirya ba Amma dai har yanzu TANA K’ASA TANA DABO ko akwai wata mafita ne Nan gaba da zai samo musu? Oho sai dai mu nade kafafun wando mu bi su ga su sai can dab da kiyama wa zai mutu wa Zai tashi?💄🍀✨☘️🫸🏻🌍🫷🏻

<< Tana Kasa Tana Dabo 16Tana Kasa Tana Dabo 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×