Skip to content
Part 5 of 75 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Saddam kuka yake Yana yarfe Hannuwa inda mama Umar take ta Rarrashin su shi da Hanan . Amma Saddam Kam yaki yin shiru sai yarfe hannu yake inda Hanan Kam tana bayan maman Umar ta Goya ta duk da ba bacci take ba sai yatsun hannun ta biyu da yake cikin Bakin ta tana tsotso.

Amal Yar maman Umar da kukan Saddam ya tayar daga bacci ta dubi Hanan a bayan maman ta sai ta tayar da Rigima irin ta yaro Mai kishin yaga Uwar sa ta dauki Wani yaron. Tuni maman Umar ta Gane kukan Amal na Goyon da tayiwa Hanan ne . Sai ma da taga Amal din tana kamo kafar Hanan wai ta sauko daga bayan Uwar ta .

Maman Umar tayi murmushi tana sauke Hanan Amal Kuma ta jawo zanin ta mikawa Uwar ta t Kuma Dare bayan Uwar ta aka Samu lafiya.

Hanan Mai hakuri ce matuka Gaya Akasin Saddam Wanda yake nuni da jinin Uban sa Yana yawo a jikin sa.

Maman Umar ta kama Hannun Saddam tana ganin yadda yake yawan yarfe hannun inda taga har yayi kumbure ya Haye suntum.

“Ya subuhanallahi me ya samu hannun ka Saddam?

Tayi tambayar tana Duba Hannun.

Cikin rishin kuka Saddam yace, “Ba daddy bane ya taka ni da takamin shi Bai zafi?

“Ai kuwa hannun Nan babu lafiya Saddam Dole a duba shi ko dai akwai gocewa ko karaya.

Haka ta yanke shawarar Kai Saddam Asibiti wurin Hajiyar Farida don Akwai damuwa a hannun yaron .

Haj tana zaune ta zubawa Farida ido wacce akayiwa Allurai da Karin Ruwa Kuma har yanzu Bata farko ba don a sume ta kawota Asibiti sai dai sauka da hawan numfashin ta da yake motion.

Ta zuba tagumi tana mamakin Abinda ya samu Farida haka tamkar wacce tayi hatsarin mota .
Idan kuwa ya zamo duka ne wannan lallai rayuka suna dab da Baci.

Ta zuba tagumi tana Lissafin Dokin Rano sai ga shigowar maman Umar wacce take tafe da Saddam da Hanan da Kuma Amal. Saddam Kam har yanzu Bai Daina kukan da yake ba.

Suna shigowa ya fado jikin Haj Yana nuna Mata hannun shi Wanda yake ta hayewa.

“Maman Umar a can aka baro Miki yaran Nan? Sannu da kokari kinji Allah ya bar zumunci.

“Wallahi yanzu ma hannun Saddam ne naga Yana ta hayewa Alamar akwai ciwo shine yace Daddyn sa ne ya taka shi da takalmin sa Ina zaton ko ya samu gocewa ne. Yaya Farida Bata farka bane?
Ta Kare da tambayar Haj .

“To gamu dai Bata farka ba. Ta Soma Duba Hannun Saddam inda tace ya samu matsala Kam
A Nan Haj ta Mike ta nufi waje da Saddam.

Mintuna Sha Biyar Haj ta dawo da Saddam Wanda aka nadewa hannu da bandeji inda maman Umar ta Mike zata koma Amma Haj tace ta bar Mata yaran don za a Dora Mata Wahala ne .

Maman Umar ta so haj ta bar Mata yaran Amma tace in aka barta da Wahalar su ba ayi Mata Adalci ba. Dole ta wuce bayan tayiwa Farida fatan samun lafiya .

*****

A guje yake tafe Yana tunanin Lallai akwai kuskure matuka Gaya a cikin Abinda yayi. Gashi tun baije ko Ina ba Yana Shirin girbe Yabanyar shukar shi.

Ya Isa gida Yana fargaba da Zullumin bayyanar muguntar sa akan bello ta fada .

Mai Aikin Haj ce take fada mishi Haj tana can Asibiti ta tafi check up din da da Ake Kai ta duk karshen wata Kuma bellon ne ya karbo mota ya tafi kaita saboda ta gidan ta lalace Kuma.

Ya juya da sauri inda ya nufi Asibitin ya samu Haj kace kace cikin kuka tana share Hawaye.

“Yauwa Sameer ungo wayar akwai lambar da aka kirani Kira su Muji wane Asibiti aka Kai shi ?

Ya karbi wayar da sanyin jiki Yana Fadin.

“To shi Bellon Haj Ina ya tafi ne da ya kawo ki bai iya tsayawa ki gama?

“Matar ka muka Gani tazo ganin likita Kuma ta gama ganin likitan shine tace kace ta Jira ni Kuma nace da bellon ya Mika tan gida kafin na gama sai ya zo . Shine ya dauke ta Suka tafi Ashe azal ce da tsautsayi ke Kiran shi don ance Wani marar Imani da tsoron Allah NE ya hankada shi a kwatami.

Wata matsiyaciyar sarawa ta dirar mishi aka yaji hajijiya na Neman kwada shi da k’asa ya daure ya Kira wayar da yaga an Kira wayar haj ya Soma tambayar Mai wayar da Kuma inda marar lafiyar yake.

An fada mishi Yana federal medical center

Ya juyo Yana fadawa Haj suna federal medical center.

Da sauri Haj ta Mike tana shiga mota suka fito daga Asibitin suka dauko hanyar zuwa medical center inda wata mota take biye a bayan su har zuwa medical center inda suka cimma motar Sameer suka Kuma kama shi suna fadin shine Mai motar da ya tura Wanda yayi hadarin Nan a kwatami.

Haj ta sake Baki ganin suna Shirin wucewa da Sameer Amma ta dakatar dasu tace ba shi bane don Dan Uwan sa ne ba zai aikata wannan Aikin ga bello ba.

Rikici yaso sarkewa Amma da yake Shima Sameer din zaune yake da kuturin sa Yana nuna katin sa suka ga ko waye sai lamarin ya zama tamkar Zubawa wuta Ruwan Sanyi. Duk dai wasu sunce koma waye shi Dole ya fuskanci Hukunci tunda in ana haka yaushe Duniya zata zauna lafiya masu kaki suna haka Ina Kuma ga sauran gama gari?

Bello Yana kwance akan Gadon Asibiti yayin da jikin shi duk ya koje sai Kuma kafadar sa da take daure da wani Uban bandeji Mai yawa sai kan shi Shima da ya Sha dauri. In Banda wannan Babu inda wani ciwo Mai girma yake a jikin bello sai fa buguwa ta cikin jiki.

Haj Kam Kuma take yayin da Sameer yake kallon Bello Shima bellon shi yake kallo da wani Abu Mai kama da Jin zafi ko tsana.

“Yaya Sameer me Nayi maka kayi min haka? Kaga yadda ka so kashe ni baccin Allah ya takaita min Wahala da yanzu ai na mutu.

“Wai tsaya bello me Sameer din yayi ne?

Sameer ya sulale zuwa tsuguno Yana kama Hannun Bello Yana Fadin.

“Ka gafarce ni bello ban San Kai bane.

“Ko ba ni bane in Wani ne kayi mishi haka shikenan haka Ahalin sa zasu wanzu cikin tashin hankali irin wanda kuke ciki yanzu?.

“Wai da gasken dai shine ya hankada ka a kwatamin? To akan me? Ko kuwa muguwar zuciyar sa marar sassauci da shegen kishin sa na halaka don ka dauko mishi matar tashi? Su duka sukayi shiru inda Haj Kuma ta Soma fada tana Fadin

“Bana ko shakka haukan shi ne ya tashi mahaukacin wofi don ya Kai Maka ita Gida Halan shine ka Nemi kashe mini shi ? To Shima akace Maka mahaukacin ne irin ka da kake zaton son Faridar yake halan?

“Kiyi Hak’uri don Allah Haj Wallahi ban zaci shine ba ta Yaya zan kashe Bello ni kuwa?

Bai Rufe Baki ba haj ta kwasa mishi Mari tana Fadin.

“Kai Rufa min Baki kaji tun baka fusata ni ba Wallahi. In ba haka bane Yaya ne to?

Ya Kuma kirnewa Yana fidda numfashi ba wai Marin Haj ne damuwar shi ba irin yadda ta dauki Al Amarin na kishin sa da Bello.

“Nace Yaya ne in ba Hakan ba ? Ni Kam dama Raina ya bani matukar ka Saka kakin Nan tsiya ta auku yadda kake da wannan bak’ar zuciyar meye ba zai faru ba? To ka sani matukar a haka zaka Rayu kana tare da tarin nadama a Rayuwar ka. Kai kenan zargi ya dabaibaiye zuciyar ka in baka sani ba ai zargi Raba Aure yake gashi har kana Neman kashe Dan Uwan ka saboda muguntar ka.

Ta Dubi bello tana fadin. “Ya akayi ne bello da har ya nemi kashe mini Kai?

Bello ya ja numfashi Yana Fadin.

“Ba haka yaso ba Haj Amma Yana kuskure gaskiya musamman zargin matar sa da yake ya bari ya kamata da laifin da zai hukunta ta ba laifi bane . Dama na kula da Farida Bata son Abunda zai jawo Mata Wani Abu da zai nuna ta don na jima da Gane ya na son kama ta da laifi.

Ya zayyane wa haj yadda abin ya faru tun a mota ta ke fada mishi idan ta koma bai zo ba wani abu ne na daban Amma dai Bai dauka da gaske bane sai da ya kaita gidan y taho Kuma yaga motar Yaya Sameer din tana biye dashi duk da Kiran wayar shi da yake don ya fada mishi shine Amma Bai daga ba daga karshe ma yaso ya ratse mishi Amma Ina sai ji yayi motar shi tana hankada shi kwatami.

Haj ta Kuma kwasa mishi Mari tana Fadin.

Kai kam anyi mahaukacin wofi Wallahi Kuma nasan Dole yayiwa yarinyar Nan haukan shi tunda ba hankali ne dashi ba.

“Kiyi Hak’uri Haj ki kyale shi don Allah! Cewar bello Wanda yaga yadda Sameer din yake huttai Allurar mazan ta motsa Amma Kuma Nan Gani Nan bari tunda yayi kadan ya Kai Hannu a jikin Haj.

Akayi Basu takardar likita wadda mutanen da suka kawo mishi dauki suka biya komai Haj Kuma tace zata tsaya jinyar bello inda Sameer ya Bata hak’uri yace ta koma gida shi zai tsaya tare dashi.

“In tafi in barka da shi ka k’arasa kashe shi ko? To jeka Nagode bana bukatar ka a Nan don in Ina ganin ka Ina tuna Kaine kayi mishi haka to kaima zaka Rasa Wani Abu don komai na yayo zan Maka Maka ne jeka ka bani wuri. Yadda tayi Maganar dole ya Mike ya fice.

Sai da ya Isa gida ne Kuma nadama Mai yawa ta sauko mishi Yana tunanin inda Farida take . Sai a nan Kuma yaji Kunya da muzanta sun kama shi da wane idon zai Dubi Haj? Da wane ido zai Dubi Yaya dauda Wanda ya kere shi a Rashin mutunci?

Ya Dubi inda yake kayan da ya watsar a wurin ne sukayi watsa watsa ga jakar Farida da hijabin ta har da nikabin ta a yashe.

Ya Soma dauko Jakarta da nikabin Yana damkewa Yana tunanin Bai taba nadama irin ta yau ba.

Ya zaro wayar shi ya Soma Kiran wayar Farida Amma sai yaji wayar a cikin Jakarta Dole ya mike ya nufi gidan su Farida gaban shi na faduwa don hakikatan Yana shakkar idon Haj da Kuma Yaya dauda don ta Haj Mai sauki ne Amma Yaya dauda kam ya fishi fitina.

Kusan a lokaci Daya suka faka motocin su shi da Yaya dauda Wanda zuwan sa kenan daga Kaduna.

Fuska a hade yake dama bai cika fara a ba don Haka sai ya Dube Sameer din Shima Kuma da sauri ya sara mishi saboda sanin ko a gidan giya akwai jagora.

Dauda ya daga mishi Hannu kawai ya wuce zuwa cikin Gidan inda ya samu Haj Bata Nan sai muktar Wanda yake gaishe da Yaya dauda irin gaisuwar nan ta sarawa saboda dauda akwai son girma duk da kasancewar sa soja dama can haka yake kamar gyambo wurin son girma bare Kuma kaki da ya hau Kansa sai ya Kuma turewa.

“Muntari Ina Haj ne? Ya tambaye muktar din Wanda yake fada mishi tana Asibiti wurin Anty Farida da Bata da lafiya..

“Subuhanallahi tun yaushe ? Dazu ne aka bugo waya to tana can dai Bata Dawo. “Wace Asibitin suke ne?
“Na Kira ta tace Dr K Dara suke.

“Ok ta bari na Isa na ga jikin nata. Ya Mike ya fice inda ya Kuma shige motar shi Bai ko waiwayi Sameer ba yaja motar shi Kai tsaye ya fige ta a guje ya wuce duk da kasancewar su a gari Daya Kuma masu kaki iri Daya sai dai girman da dauda yayiwa Sameer yasa Dole akwai respect Babu wasa tare da dauda haka Shima Sameer din Yana bayar da girma matuka Gaya ga Kuma shakka da Sameer din yakewa dauda.

Jiki a Sanyaye Sameer ya sarawa motar dauda da take wucewa girman kenan ko a me babban ka yake Dole ka girmama shi ka Sara mishi har da kamewa da bushewa ko da Kuwa ya zabga Maka Mari ne ko ya zagi Uwar ka.

Ya juyo Yana nufar cikin Gidan muktar ya amsa mishi Yana mishi Sannu da Zuwa. Ya bawa muktar din hannu Yana Fadin.

“Muktar Kai kadai ne a gidan halan?

“Eh Wallahi Yaya Sameer Haj suna Asibiti ne bata dawo ba.

“Asibiti Kuma? Wurin wa? Ya tambaya don zuciyar sa ta Soma fada mishi dukan da yayiwa Farida dukan Shan gishiri ne Wanda Dole sai likita ya Saka Hannu..

“Wurin Anty Farida ne don gado aka Bata. Gabansa ya Sara Yana Duban muktar Amma ya kasa cewa komai Dole ya mike yana bade tabarmar kunyar sa.

“Bari na leka su muktar ban San suna Asibiti ba wane Asibitin ne suke?

Ya tambaya Yana Duban muktar din Wanda ya ke bashi amsa da Cewa Asibitin Dr K Dara ne ..
“Ok to bari na k’arasa Nagode.

“Kaga kuma rashin sani yanzu Yaya dauda ya tafi da kun tafi tare.

Gaban shi yayi wata matsiyaciyar sarawa don Jin cewa Yaya Dauda ma can ya tafi Lallai kuwa zuwan shi Akwai matsala su hade da dauda ace yayiwa Farida wannan dukan na shan gishiri anya kuwa ?

Amma kuma wata zuciyar tana fada mishi kuma idan baije ba ya kai kunyar Haj a ina? Amma kuma hakikatan zuwan akwai matsala da damuwa. Hakika Bai taba yin nadama irin ta yau ba musamman da ya Bata Ruwa biyu na mahaifiyar sa da ya kassara Mata danta Bello da Kuma na mahaifiyar Farida wacce in ta barshi da dauda yasan ya shiga uku ko a wurin Aiki kuwa yasan punishment din da zai bashi sai ya kusa kashe shi. Amma Kuma bashi da zabi Dole ya Isa Asibitin ya ga Abinda zai iya Yi don Farida dai matar sa ce Kuma baiji kamar Yana iya Rabuwa da ita ba don an jarrabe shi da ita Kuma Abinda yakeyi ma son ne yaja shi ga kishi har yayi Hakan. Don haka sai kawai ya tashi motar ya harba titi ya nufi Asibitin Dr K Dara duk da zuciyar sa Bata yarda ta tsaya wuri Daya ba Amma dai Dole yaje Kuma Dole a bashi matar sa tunda har gobe a karkashin ikon sa take in an nuna mishi iko a Wani wurin Shima zai nuna nashi ikon a wani wurin.

<< Tana Kasa Tana Dabo 5Tana Kasa Tana Dabo 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×