Skip to content
Part 24 of 58 in the Series Tana Kasa Tana Dabo by Hadiza Gidan Iko

Farida na kwance abin Duniya ya ishe ta Babu Abinda take bege a yanzu irin Sameer Wanda Haj ta ce ko wayar Nan da Ake yi kullum a Daina ta . Don haka sai wayar Farida ta zama a kashe kwanaki da yawa In har ta Buda ta to uzurin gaggawa ne da ta gama Kuma zata kashe don ta Gane Akwai kuskure Mai yawa da Sukeyi ko akan firar wayar da Sukeyi ita da Sameer Wanda a yanzu cikin idda take Bata bukatar irin wadan Nan abubuwan. 

Saddam ya Dubi Farida Yana fadin “Wai Mami Ina Daddy ne ya Daina Zuwa kawo Mana sweet?

Ta Dubi Saddam din Bata iya tanka mishi ba don Bata son Yi mishi karya don Kar ya iya ta.

Ta dauko Jakarta wacce Bata Rabo da sweet din ta bashi ya karba Yana murna. A zaton ta sweet din Kawai yake so shiyasa ta bashi Ashe yaro Uban sa yake son Gani jini ne yake Aiki .

Kwana biyu Saddam ya Kuma tambayar ta daddy tace mishi Yana partacout Yana Aiki.

“To ni dai a kaini wurin shi can.

Ta Dubi Bakin yaron Yana Fadin a Kai shi wurin shi can.

Bata tanka mishi ba sai ma sweet da ta Tara mishi a gaban shi har ta shashantar dashi.

Washe gari kuwa kuka Saddam yake shi wurin Daddy zashi…

Kuka Saddam yake bil hakki da gaskiya wurin Uban shi zaije Abinda ya tabawa Farida zuciya.

Ta Zubawa yaron ido tana kallon yake tuma a k’asa Yana kuka duk Rarrashin Duniya yaki sauraren ta

Idon ta ya ciko da kwalla dama Abu ga me son Zuwa birni bare Kuma sarki yayi Kira.

Jin kukan Saddam yasa Haj lekowa taga yadda yake tuma Yana kuka take tambayar Farida.

“Me Akayi mishi shi Kuma wannan? Ta fada tana kama shi Yana gunjin kukan shi.

“Haj wai wurin Uban shi za a kaishi.

Ta fada idanun ta fal kwalla.

Wani Abu ya tab’a zuciyar haj na tausayin Saddam da Uwar shi har da Uban shi

“Dauki wayar ki ki Kira mishi Mana in yaji muryar shi a waya ai zai Daina Kukan.

Farida ta Mike dauko waya inda Haj ta Soma Rarrashin Saddam tana fadin.

“Haba Mai gidan wa ya fada Maka Namiji Yana kuka irin haka? In baka bari ba zan fasa Auren Nan gaskiya miji baya Jin Wahalar kuka me kenan?

“Bari ga Nan zata Kira Maka Daddyn ka a waya kaji ko? Ya Soma share fuska Yana yin Shiru sai dai abin haushin wayar Sameer a kashe . Duk nacin Kiran Farida Dole ta Hak’ura tana Fadin

“Saddam wayar shi a kashe sai dai kayi Hak’uri.

Saddam ya Kuma kecewaa da kuka Yana kwacewa daga hannun Haj

Duk Rarrashin Duniya yaki sauraren su sai Fadi yake shi wurin Daddy zashi.

Duk ya Ruda musu gidan da kukan Kuma yaki karbar rarrrashi.

Ana cikin Hakan Yaya dauda ya iso katsina daga kaduna ya samu rigimar Saddam wanda yaki jin rarrashi.

“Kai mutumi na me ya same ka ?…

Ya fada Yana kamo Saddam ya taho ya kwanta a jikin shi, “Haba Saddam Babba da Kai kake kuka me kake so ne? Ya fada yana shafa kanshi.

“Wurin Daddy na zani kwana haka ban ganshi ba.

Ya fada Yana wara Yan yatsun shi.

Yaya dauda ya Dubi Haj wacce take tsaye tana kallon su. Farida ta fito tana mishi Sannu da Zuwa ya amsa Yana kallon ta . Ta zube tana Gaishe shi ya Amsa Yana kallon zuwan nata ba na bakunta bane.

“Ya akayi ne Haj Saddam ya jima Bai ga Uban sa ba har yake Zamani haka?

“Kaddara Mana ! Cewar Haj, Yaya dauda ya zuba mata ido Yana Neman Karin Bayani.

“Auren iyayen shi ne ya kare dan sauran igiyar daya ya Ida guntule ta.

“Akan Abinda muguwar zuciyar sa take Raya Mishi na zargin ko Haj? Yaya dauda ya tambaya…

“Ai ni na Rasa Abinda yaron Nan ya Gani a tare da Farida har yake zargin ta ya Hanawa Kansa zaman lafiya ya Hana Mata. Daga fa makociyar ta tazo gugar kayan mijin ta aka dauke wuta ta bar su in an Dawo da wuta tazo ta Goge shikenan ya kawowa zuciyar sa Wani Namiji ne ta kawo . Sai Kuma akayi Wani Arashi kanin mahaifin su ya Rasu a Ranar suna gidan makokin ya Kuma Dawo Bai same ta gidan ba sai ya hada UKU da Biyar suka bashi takwas shine fa ya tafka Mata Saki Amma Kuma da tsiya wai shi cikin fushi yayi sakin don haka Bai saki ba . Kai yadda ka San Wanda ya zautu yaron Nan har tausayi dai ya bani na Kuma fada masa gaskiya Babu wani saki na cikin fushi da wanda ba na fushi saki duka saki ne in dai ba gyaran wahayi Ake son ci ba.

Yaya dauda yayi shiru Yana Rungume da Saddam Wanda yake Fadin, “Daddy’zaka Kaini wurin Daddy na?

“Zan Kai ka Saddam kar ka Damu in zan tafi sai mu tafi na aika mishi da Kai tunda kana son Zuwa ai ?.

Yayi Maza ya Amsa da yeah.

“To Allah ya kyauta Haj yasa kuma hakan shine Alherin Amma gaskiya ni da kaina na San ko ba yau ba sai Auren Farida ya k’are ko da Kuwa an wuce wannan lokacin Kuma zuciya Mai zargi irin na Sameer Babu Ranar da zasu huta su da Matan su matukar dai akwai wannan zargin sai dai ADDU A kawai.

Farida ta fito daga D’akin ta zube a Gaban Yaya dauda tana Fadin

“Yaya dauda don Allah don ANNABI kayi min Afuwa akan abubuwan da nayi maka. Sai a yanzu na Gane Abinda kake nufi da Kuma na yarda da Abinda kake nufi da banzo wannan galan din ba don Allah ka yafe mini ka nema min gafara wurin Anty lubna itama na kasa fahimtar ta sai a yanzu nake Gane Abinda kuke son Yi min gata da shi. Gani Sameer yayi min saki UKU Kuma an jarrabi zuciya ta da son shi fiye da son da nayi mishi a baya na Kuma san har da Alhakin ka Yaya dauda.

“Babu komai Farida na yafe miki na san kuruciya ce kawai take damun ki kuma da irin haka Ake hankali ai Kiyi ta ADDU A kar Kuma ki yarda son ZUCIYAR ki ko shaidan suja ki ga Sameer da kika tabbatar da ya gama zama haramiyar ki ki karyata son da kike mishi sai ki Zauna lafiya Amma in kika gasgata son shi to Zaki Wahala ne don shi son da kike Gani Farida karya tafi yawa a cikin shi da so dukkan shi gaskiya ne da Sameer Bai Dora ayar zargi a kanki ba na Baki assignment kije ki baje shi a faifai Zaki Gane Abinda nake nufi.

Ya Mike Yana Rik’e da Hannun Saddam Wanda Bai yarda ya saki ba don ma kar ya Gudu suka fita Yaya dauda Yana cewa Haj zaije cikin gari ya dawo kafin ya wuce dama yazo Wani daurin Aure ne.

Suka dawo shi da Saddam Wanda ya cewa Farida ta Bada kayan shi su wuce.

“Wai da gaske kake ne dauda?

“Eh Haj Akwai Wanda zan bawa shi ya kaishi har wurin Sameer din akwai Wanda yazo daga partacout din jiya na ma Kira shi Bai wuce nace akwai yaro da zan bashi Dan Sameer ne ya wuce mishi da shi yace Babu matsala da yake da iyalin sa ya zo Babu wata matsala.

Farida ta hadawa Saddam kayan shi a Jaka ta Rungume shi tana kuka tana shafa kanshi don Gani take tamkar sun Rabu ba zai Kuma dawowa ba.

Yaya dauda yaga yadda Saddam yake ta murna Yana dagawa Haj hannu Yana fadin ya tafi wurin Daddyn shi.

Da haka Yaya dauda yayiwa haj sallama suka wuce shi da Saddam.

A Ranar da suka iso Kaduna a Ranar Kuma Yaya dauda ya bawa Abokin shi captain Abubakar Saddam yace dan Sameer ne da yazo ya samu yaron Yana kuka shi wurin Daddyn Sa zashi shine ya dauko shi don Allah ya Bawa Sameer din shi tunda barrack Daya suke

Da haka su Saddam suka dauki hanya zuwa partacout inda Saddam ya samu Yara sa annin Sa suna ta wasa

SAMEER

Hankalin Sameer ya Kasa kwanciya. Babu Abinda yake bege sai Farida wacce yake jin tamkar Bai taba sanin ta ba Bai taba sanin son ta . Al Amarin da ya so zarar da shi don shi kadai ma magana yake .

Shine Dalilin da ya sa ya kwashe sama da sati Biyar Bai je katsina ba sai dai yayiwa Farida waya wacce kullum fa zata amsa wayar shi sama da sau Biyar.

Wannan saukin da ya samu abubuwan Sukayi mishi sassauci tunda Yana Jin muryar Farida.

Sai dai Kuma a cikin kwanakin ya Daina samun wayar Abinda ya kuma tayar mishi da Hankali duk nacin Kiran ya kasa samun ta .

Abinda kawai yafuye mishi shine ya samu Wanda zai iya Yi mishi Alfarmar da Farida zata dawo gareshi. Shine Abinda kawai yafiye mishi don haka sai ya SHIGA lalubo Wanda zai samu da batun Kuma Wanda ba zai duba mishi Farida ba bare Kuma ya nemi tab’a mishi ita.

Yayi matukar Nazari kafin zuciyar shi ta tsayar mishi da wani kurtun SOJA a Nan barracks din su Mai suna Nazir Wanda yake kasa da shi a matsayi Kuma Mai bashi girma Sosai Kuma Wanda ya tabbatar da in dai ya Saka shi wannan Aikin zai yarda Kuma bare in ya fada mishi da zai biya shi kudi.

Ya ji saukin damuwar shi saboda Ganin kamar ya gama samun mafita.

Ya Mike ya fito cikin barracks din Neman Nazir ya Kuma aika a Nemo mishi shi..

Yana zaune Nazir din ya taho da sauri Yana Sara mishi ya girgima shi kafin yace

“Oga an ce kana nema na wani Abu z a a samo maka ne?

Ya kamo hannun Nazir ya zaunar da shi kusa Dashi Yana Fadin

“Nazir wani Aiki zan Saka ka Wanda Kuma zan biya ka da kudi masu Nauyi Ina fatan Kan kace ba zaka iya ba.

“Kar ka Damu Oga in Sha Allah zanyi Maka shi tunda ka Zabe ni ai ba zan baka kunya ba.

“Nagode Nazir ka Gane?

“Matata ce na yiwa saki biyu Amma aka ce wai Auren mu ya haramta duk nayi mata Wani Saki cikin fushi Amma Saboda Rashin Adalci aka ce Shima saki ne sai suka hada da wancan saki Biyun suke ce uku kenan Aure ya kare .

“To ni Kuma sai a yanzu aka jarrabe ni da son matata Nazir Amma na Gane ba za a bari na mayar da ita ba shine na yanke shawarar samun Wanda zan hada su Auren KISAN WUTA na biya shi ya Aure ta ya Sako min ita in mayar da Kaya na Amma Kuma gaskiya ba zan boye Maka ba Nazir Bana son a tab’a min matata don bil hakki zan iya mutuwa akan kishin Hakan shiyasa zan sanar da Kai Babu wannan harkar har zuwa Ranar da wa adin Auren naku zai Kare. Ka Gane?

Ya fada Yana kure Nazir da ido Yana ganin yanayin da Nazir din ya shiga Wanda zufa ta Soma karyowa…

“Ya akayi ne Naga kana hada Zufa Nazir?

“Kayi min Afuwa Oga Wallahi an kusa Biki na October ne end Kuma ga Al Amarin da ka zo da shi ..

“Kar ka Damu Nazir Babu Abinda zai SHIGA tsakanin ka Auren ka da Wannan. Ka Gane Mana nazir. Auren kawai nake so ka karba Amma Babu nauyin komai a kan ka . Kai ko da an daura ne da kwana Biyu ka sake ta Babu wata matsala. Kuma ni zan biya komai na hidimar Babu ko Nairar ka Kuma zan baka Dubu d’ari UKU ladar Aikin ka kaga zaka k’ara a hidimar Auren ka ko Kuwa?

Nazir da yaji Dubu d’ari UKU sai yayi murmushi Yana Fadin

“Ka kuwa taimaka mini Oga Wallahi Zanyi Amma ta Yaya Zanga ita matar ?

“Zamu je ne da Kai Amma sai ta k’arasa iddar ta yau saura kwana Sha shida ta gama in yaso zanje na Sanar Mata na samo Mata mijin da zai Aure ta ba zata ki ba duk yadda nake so haka zatayi kaga da kaje kuka gana sai ka fad’a Mata da gaske kake zaka tura maganar Aure ni Kuma sai na shirya Maka komai ayi a gama in yaso ko Sat Biyu ne sai ka sauwake mata kaga ma har a gama wannan contract din ba a fara Hidimar bikin naka ba.

“To shikenan Oga komai kace haka za ayi duk yadda akayi yayi mini.

“Yauwa Nazir bari Naga lokacin da zanje gidan naga yadda zamuyi da ita sai na fad’a maka Nagode Sosai da Goyon bayan da ka bani.

Nazir ya Mike Yana Sarawa Sameer ya kame kafin ya wuce Yana Gudu.

Sameer yayi murmushi Yana shafa fuskar shi saboda Jin Dadin yadda ya Samu hadin kan Nazir ya San Babu wata matsala Kuma kamar anyi an gama ne.

Yana Shirin tashi ne yaga motar captain Abubakar Abokin Yaya dauda ne shiyasa ya tsaya har motar ta K’araso inda yake inda ya tsinto muryar Saddam Yana Fadin

“Daddy! Ya Soma Sarawa captain kafin ya leka motar inda ya ga Saddam Wanda yake kokarin Bude motar ya fito..

Ya damke yaron ya Rungume yana shafa kanshi Yana fadin

“My son ? Captain ya fito Yana Bashi hannu suka gaisa Yana fada mishi dauda ne ya bashi Saddam yace ya kawo mishi shi ya iske Yana kukan Daddyn shi zashi.

“Nagode Sir da yake na jima ban je gida ba shiyasa yake son Zuwa Nagode Sosai.

Sukayi sallama captain ya wuce shi Kuma Yana Rungume da Saddam Yana ta jera mishi tambayoyi.

“Kukayi nayiwa Mami nace wurin Daddy zani sai uncle ya taho da ni Daddy ka Daina kawo Mana sweet Mami tana kuka fa.. tace ka Daina Zuwa.

Ya Zubawa yaron ido Yana kallon shi ya kuma San Dalilin kukan na Farida ba zai Wuce begen shi ba kamar yadda yake begen ta har baya iya BACCI.

Ya hada Ruwan zafi yayiwa Saddam wanka ya dauke shi zuwa restaurant yayi mishi oder abinci da kayan lashe lashe Suka Dawo gida Yana Rungume da yaron Yana ta jera mishi tambayoyi Yana bashi amsa wasu na daidai wasu Kuma na shirme . A haka har bacci ya dauke Saddam Wanda gajiya ce ta ishe shi don ma Yana yaro.

Sameer ya shimfide shi a gado Yana kallon shi Yana tausayin kansu da kewar da take damun su Amma dai in Sha Allah Komai ya kusa Zuwa karshe tunda Nazir ya share mishi HAWAYEN shi…

Washe gari yayiwa Saddam wanka ya dauke shi a motar shi zuwa wurin Aiki inda akayi ta daukar Saddam ana mishi Alheri. Kan kace me ? Yaro Saddam yayi farin jini cikin barracks din su kowa Saddam yaro Mai SHIGA Rai kowa yaja shi kowa yaja shi Kuma tafiya yake har Ogan su Sameer daukar Saddam yake har gidan shi yake kwana.

<< Tana Kasa Tana Dabo 23Tana Kasa Tana Dabo 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×